Bukatan mutum game da aiko annabawa
Lallai mutum ba tare da addini ba da shari'a zai wayi gari Kaman dabba ne wanda bashi da wani hadafi face maslahar kansa da kuma abunda zai samu na dukiya cikin wannan duniya babu ruwan shi da cewa ta wani hanya ya samu, ita kamar birki ne wanda yake tsara harkokin mutum da kuma toshe sharrin dake cikin zuciyar sa, idan babu addini dokan daji ne zai jagoranci mutum wanda me karfi yake cin mara karfi kuma a cire rahama a cikin zuciya, addini da shari'a rahama ne ga mutane baki daya wanda ya wajaba ayi kira zuwa ga aiwatar da ita saboda ta lamuntar maka hakkokin ka da kuma rayuwan ka me daraja ta halin arzikin ka da talaucin ka da duma halin lafiyar ka da rashin lafiyar ka da halin karfin ka dana raunin ka domin sanin haka saura kaji bangare cikin bangarorin shari'a wanda aka saukar ma Muhammad manzon Allah s.a.w wacce kuma ya karade dukkanin lamuni ga hakkokin mutum wanda zai zo mas aba tare da ya nema ba ko kuma wahala domin samun ta ba a duk lokacin daya aiwatar da ita, yana cewa: " dukkanin ku makiwata ne kuma dukkanin ku za'a tambaye ku akan abun kiwon ku, shugaba me kiwo ne kuma za'a tambaye shi akan abun kiwon sa, namiji me kiwo ne akan iyalan gidan sa kuma za'a tambaye shi akan kiwon sa, mace me kiwo ce akan gidan mijin ta kuma za'a tambaye ta akan kiwon ta, me aiki me kiwo ne akan dukiyar me gidan sa kuma za'a tambaye shi akan kiwon sa,- sai yace kamar ina tsammanin yace: mutum me kiwo ne akan dukiyar mahaifin sa kuma za'a tambaye shi akan kiwon sa- dukkakinin ku makiwata ne kuma za'a tambayeku akan kiwon ku" buhari da muslim ne suka rawaito shi.
saboda haka ne Allah yake daukan aiko manzanni a matsayin ni'ima cikin ni'imomin da Allah yayi ma mutum da kuma rahama cikin rahamar sa wanda ya daukaka dashi da ita yadda be barsu hakan ba kara zube suta amfani da zaton su dason zuciyar su ko kuma hankulan su wanda yake da iyaka da rauni wacce ta gagara warin shiryar dasu ba tare da shari'a ba da kuma addini, daga cikin abunda Allah yaba mutum na hanyoyin sani da ilimi daji da gani da hankali basu da iko akan shiryar dashi da masu jagora zuwa ga hanya wacce taka kaiwa zuwa ga manufa wacce saboda itace aka halicce mutum kuma bazata ita sanya masu shari'a ba da dokoki wacce zata tsara rayuwan su ta kuma tabbatar da adalci a tsakanin su da daidaito kuma ta lura da darajar su ta mutane a cikinta ba'a banbanta wani akan wani acikinta sai da tsoron Allah da aiki na kwarai, shari'a ce wacce bata bin son rai kuma bata tasirantuwa da abunda ke kewaye da ita wanda yake da tasiri na waje wacce take da tasiri wurin gyaruwanta da karade wanta da kuma kasance warta na duniya baki daya wacce tayi daidai da ko wani wuri da zamani, Allah madaukaki yace: " yaku yan adam idan manzannin mu suka zo maku suna karanto maku ayoyin mu duk wanda yaji tsoron Allah ya kuma gyara to babu tsoro a garesu kuma baza suyi bakin ciki ba (35) wanda kuma suka karyata ayoyin mu sukayi girman kai daga garesu wannan sune yan wuta suna masu dawwama a cikin ta (36)" suratul a'araf.
Dabi'ar mutum da kuma yanayin sa wanda Allah ya halicce sa akai bazata iya yin wannan aiki ba me girma kuma wannan ba aibi bane hasali ma al'amari ne na dabi'a wanda yake nuna buqatarr sa zuwa ga mahaliccin sa wanda zai tafiyar dashi akan tafarki da shari'a wacce zata gyara halin sa, hankula sunada rauni bazasu iya tsara halin me ita ba to tayaya zata zata iya tsara halin mutune baki daya saboda gazawarta da kuma karancin dabararta da kuma sabanin su da kuma banbancin su wurin iyaka abunda yake daidai a wurin wasu zai iya zama akasin haka a wurin sauran haka kuma saboda kasancewar sa be san komai ba sabanin abunda yake gani ko kuma tabawa da kuma rashin saninta da abunda zai faru nan gaba, abunda aka amshe shi ayau gobe za'a iya kin amsan shi, Allah madaukaki yace: " Allah yana son ya sawwaka maku kuma ya halicci mutum da rauni (28)" suratun nisa'i.
Kuma haka dabi'ar hankali wanda Allah ya halicce ta akai na gaggawan isa zuwa ga abu da kuma kokwanto da rashin tabbatan ta a hali daya kanaso kuma tana ki, tana bayarwa kuma ta hana, tana karfafawa da kuma yin inkari… zuwa dai karshe dukkan haka bazai bata cancanta ba na zama me yin doka da tsarin rayuwan mutum ba, Allah madaukaki yace: " kuma mutum yana yima kansa addu'a na sharri kamar yadda yakeyin addu'ar akheri akan sa, mutum ya kasance me gaggawa (11)" suratul isra'i
Kokwanton wannan hankula da kuma kai komanta da rashin tsayawan ta akan hali daya sai aka yita akan amsan kyauta dayawa da kuma son kai dayawa sama da kowa ya samu da kuma rikewa sama da bayarwa, Allah madaukaki yace: " kace da ace kune kuke rike da taskar rahamar ubangiji na to da kun rike saboda tsoron bayar wa, mutum ya kasance me tsaban rowa (100)" suratul isra'i.
Kari kuma akan yadda aka halicce sa akai na dabi'a wannan hankulan na mantuwa da kuma rashin sanin sinadarin da suke kewaye da su abunda ya kasance ayau daidai zai iya kasancewa a gobe kuskure, kuma abunda ya kasance gaskiya a yau abunda zai faru gobe zai iya karyata shi haka dai ka kiyasta akan haka akwai wasu daga cikin bincike na hukuncin mutum wanda suke daidai a jiya amma hankali ya karyata su ayau, kamar yadda bata zama wacce bata sabo ba tana bayar da hukunci ne sakamakon halin yanzu da kuma bukatan mutane wanda take rayuwa a cikinta, ka dub aka gani zagaka dayawa daga cikin wannan dokoki da tsari na kasashe wanda zababbun mutanen su suka rubuta ya fara cancanzawa saboda wani abu da ya fura shi kadai a wannan kasa wanda hakan ya tilasta mata canza wannan tsari nasu da dokoki da abunda zai dace da yanayin su wanda suke ciki abunda wannan hankali take sanya shi ya zama doka da kuma shar'anta shi bashi da tabbas sannan kuma bai zama me dacewa ba da dukkanin zamani da wurare sabanin shari'ar ubangiji, Allah madaukaki yace: " lallai an halicci mutum me butulci (19) idan sharri ya same shi baya hakuri (20) kuma idan alheri ya same shi baya godiya (21)" suratul ma'arij.
Muduba mugani misali abunda hankula suka gabatar akan wasu mutane cikin al'umma na kayan yaki masu kisa da lallatawa cikin ababen da suka kirkiro na mulkan mutane wanda suke lallata kasashe da mutane da sunan mulkin mallaka kuma suna alfari da ikon su na kirkiro ilimi- sunce- shin wannan baya cikin sakamako na rashin shari'a cikin rayyuwan su da kuma rashin imanin su da gaibu na cewa akwai fa tashi bayan mutuwa da kuma hisabi akan ayyuka idan alheri mutum ya aikata to zai ga alheri idan kuma sharri ya aikata to zai ga sharri, da ace sun kaance sunyi imani da gaibu da basu aikata komai ba sai abunda yake alheri ne ga kawunan su da mutane kuma sun nisanci dukkanin abunda yake da sharri acikinsa gare su da mutane baki daya, Allah madaukaki yace: " duk wanda ya aikata kwatankwacin kwayan zarra na alheri zai ganshii (7) wanda kuma ya aikata kwatankwacin kwayan zarra na sharri shima zai ganin shi (8)" suratul zilzilat.
Haka kuma lokacin da wannan hankula suka gabata a karkashin rashin imani da gaibu na abun bauta sai abun bautan da suke gina masu gidajen su kamar su duwatsu da bishiya ko kuma abun bautan da suke dafa abinci da bun sha a kan su kamar wuta ko kuma abun bautan da mutum yake cin su kamar shanu ko kuma abun bautan da suke kashewa Kaman bera ko kuma abun bautan da suke tabbatarwa cewa sune mafarin sharri kamar shedanu… da dai sauran su.
Saboda haka ne aiko da manzanni yana cikin abun da suke bukata na halittan su domin su bayyana masu shari'a wacce zata kare su baki daya daga kura kurai ya kuma masu bayanin hukunce hukunce na daidai, kamar kuma yadda muka ce ne lallai mutum da abunda aka bashi na hankali da ilimi suna tsayawa ne akan riskan abubuwan da suke iya gani ko kuma tabawa cikin wannan duniya amma duk abunda yake na gaibu ne bazasu iya sanin sa ba ko kuma riskan sa sai ta hanyar manzanni, misali tsohon tarihi na mutanen da suka gabata gabanin mu bazamu iya sanin sub a face ta hanyar abunda masani tarihi suka rubuta mana badan rubutun su ba da ace hankulan duniya baki dayan su zasuyi aiki domin sanin wannan tarihi bazasu taba iya sani ba, haka manzanni wanda hakan yana cikin karramawan Allah a garesu na aiko masu da manzanni lokaci bayan lokaci duk lokacin da mutane sukayi nisa akan hanyar gaskiya sai Allah ya aiko masu da manzo wanda zai mayar dasu zuwa kan hanyar gaskiya da kuma yi masu bayanin shari'a wanda zasu tsara harkokin su nasu dana mutane baki daya da kuma manhajin da zasuyi tafiya akai domin isa zuwa gareshi, kuma domin ya zama hujja akan su cikin aiko su kamar yadda Allah madaukaki ya bayyana haka cikin fadin sa: " manzanni masu bishara da gargadi saboda kada mutane su zama sunada hanzari akan Allah bayan aiko da manzanni, Allah ya kasance mabuwayi kuma me hikima (165)" suratun nisa'i.
Sai wahayi wanda aka saukar akan manzanni ya zama rayuwa ga mutane da kuma haske wanda zasu rika ganin gaban su dashi da kuma haskaka duhun jahilci dashi, da kuma hanya ta tsira a garsu na abunda suke ciki na bata, da kuma nasara ko kuma rashin rasara wanda ya ratayu akan rikon su dashi ko kuma saba masa babu hanya wanda yake kai halittu zuwa ga mahaliccin su sai ta shi duk kuma wata hanya wanda bashi ba to me halakarwa ce da batarwa kamar yadda Allah ya bada labari cikin fadin sa: " kace yanzu zamu rika kiran wani abu koma bayan Allah wanda bazai amfanar damu ba ko kuma cutar damu kuma mu koma zuwa ga kafurcin mu bayan Allah ya shiryar damu kamar wanda shedanu suka batar dashi yana cikin dimuwa yanda mutane wanda suke kiransa zuwa ga shiriya sun ace masa zo muje ga hanyar gaskiya nan, kace shiriyar Allah ita ce shiriya kuma an umurce mu da mika wuya ga ubangijin talikai (71)" suratul an 'am.
Sa'annan bayan haka sai zabi ya rage ga mutum wurin amsan abunda Allah ya saukar akan manzon sa ko kuma yaki amsa domin ya tsira ta sanadiyyar sa ko kuma halaka idan yaki amsa kamar yadda Allah madaukaki ya fadi: " da ubangijin ka yaso da mutanen duniya sunyi imani baki dayan su, yanzu shin zaka rika tilastama mutane ne har sai sun zama muminai (99)" suratu yunus.
Mahalicci yayi gaskiya me tsarki da daukaka cikin bayyanawar sa cewa lallai wahayin da ya saukar akan manzanni kamar misalin ruhi ne ga jiki, kamar yadda rayuwan gangan jiki bazata kasance ba sai da ruhi haka rayuwan zuciyar mutum da tabbatawanta da kuma natsuwan sa baya kasance wa sai ta hanyar sa, Allah madaukaki yace: " haka kuma mukayi wahayin ruhi cikin al'amarin mu zuwa gareka baka kasance kasan menene littafi ba ko kuma imani ba gabanin sa sai dai mun sanya shi haske muna shiryarwa dashi ga wanda muke so cikin bayin mu, kuma lallai kai kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya (52)" suratu shura.
Dostları ilə paylaş: |