Annabawa baki dayan su suna kira ne zuwa ga bautan Allah shi kadai:
kira ga tauhidi da kuma tsarkkae Allah da bauta da tsawatarwa daga shirka shi ne kiran annabawa da manzanni baki dayan su ga mutanen su, Allah madaukaki yace: " bamu aiki wani manzo ba gabanin ka face munyi masa wahayi cewa babu abun bautawa da gaskiya sai ni saboda haka ku bautamani (25)" suratul anbiya'i.
basu kasance suna kiran mutane zuwa ga su bauta masu ba ko kuma bautan wanin su ba sun kasance suna tsawatarwa akan haka matuka hakamar yadda Allah madaukaki ya bayyana haka cikin fadin sa cewa: " be kasane ga wani mutum ba Allah ya bashi littafi da hikima da annabta ba sa'annan yace ma mutane ku zama bayina ba koma bayan Allah sai dai ku kasance bayin Allah da abunda kuke karantawa cikin littafi da kuma abunda ake karantar daku (79) kuma be umurtan ku da ku riki mala'iku da annabawa a matsayin abun bauta shin zasu umurce ku ne da kafurce bayan kun kasance musulmai (80)" suratu al'imran.
Nuhu amincin Allah ya tabbata a gareshi farkon manzanni ya zauna cikin mutanen sa tsawon shekaru dubu daya babu hamsin yana kiramn su zuwa ga bautan Allah da barin abunda suke kai na shirka, Allah madaukaki yace: " hakika mun aiki Nuhu zuwa ga mutanen sa sai yace yaku mutane na ku bautawa Allah baku da wani Allah sai shi lallai ina tsoron muku azaba wani rana me girma (59)" suratul a'araf.
Haka shima annabi Ibrahim baban annbawa amincin Allah ya tabbata a gareshi ya nemi mutanen sa da su bautawa Allah shi kadai babu abokin tarayya, Allah madaukaki yace: " da Ibrahim a lokacin daya cema mutanen sa ku bautawa Allah kum akuji tsoran sa hakan shi yafi zama maku alheri idan da kun kasance kun sani (16) lallai abunda kuke bautamawa koma bayan Allah gumaka ne kawai wanda kuke kirkira da hannun ku, lallai abunda kuke kira koma bayan Allah baya mllaka maku arziki saboda haka ku nemi arziki agun Allah kuma ku bauta mashi da gode masa gareshi zaku koma (17)" suratul ankabut.
Da annabi Hudu amincin Allah ya tabbata a agreshi kiransa ya kasance ga mutanen sa akan kadaita Allah da kuma barin shirka a gareshi, Allah madaukaki yace: " mun aika zuwa ga adawa dan uwan su Hudu yace masu yaku mutane na ku bautawa Allah baku da abun bauta sai shi ku baku kasance ba sai masu kirkire kirkiren karya (50)" suratu hudu.
Haka annabi Salihu shima amincin Allah su tabbata agareshi kiransa ya kasance ga mutanen sa akan kadaita Allah shi kadai da kuma barin masa shirka da komai, Allah madaukaki yace: " mun aika zuwa ga samudawa dan uwansu Salihu yace masu yaku mutane na ku bautawa Allah baku da wani abun bauta bayan shi" suratu hudu ayata 61.
Haka shima annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gareshi bayan Allah ya tsiratar dashi da mutanen sa daga fir'auna da sarakuna sa sun nemi daya sanya masu abun bauta wanda zasu rika bautamawa sai ya bayyana masu mummunan sakamako game da aikata haka, Allah amdaukaki yace: " kuma muka ketarar da bani isra'ila rafi sai suka zo wurin wasu mutane wanda suke bautan gumaka sai sukace ya Musa muma kasanya mana abun bauta kamar yadda wannan muatnen suke da abaun bauta sai yace masu lallai ku mutane ne masu jahilci (138) wa'innan da kuke gani halakakku ne akan abunda suke kai kuma barna ne abunda suke aikatawa (139) sai yace yanzu zaku nemi abun bauta koma bayan Allah bayan ya daukaka ku akan mutane baki daya (140)" suratul a'araf.
Haka shima annabi Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi a lokacin da aka aikeshi zuwa ga kafiran bani isra'ila domin ya kirasu zuwa ga gaskiya da kadaita Allah sai ubangijin say a tambaye sa bayan yana sane da abunda ke zuciyar sa, Allah madaukaki yace: " a lokacin da Allah yace ya Isa shin kai kace ma mutanen ka su rike ka da mahaifiyar ka a matsayin abun bauta koma bayan Allah sia yace tsarki ya tabbata a gareka baya halatta a gareni na fadi abunda bani da hakki akan sa idan ni nafada masu haka to ai kasani kasan abunda ke cikin zucya na amma bansan abunda cikin zuciyar ka ba lallai kai ne masanin gaibu (116) bance masu fa sai abunda ka umurce ni dashi cewa su bautawa Allah ubangiji na da ubangijin ku kuma na kasance me sheda akan tsawan lokacin danayi acikin su amma bayan ka kashe ni kai ne me ganin su da bibiyan su kuma ka kasance me sheda akan komai (117)" suratul ma'ida.
Shima annabi Muhammad amincin Allah ya tabbata a gareshi cikamakon annbawa kiran sa ya kasance akan kadaita Allah da barin duk wani abu koma bayan sa na gumaka da sassake, Allah madaukaki yace: " yaku mutane ku bautawa ubangijin ku wanda ya halicce ku da wanda suka gabace ku tabbas zaku samu tsoron Allah (21)" suratul bakara.
Dostları ilə paylaş: |