Mawallafi Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة



Yüklə 299,48 Kb.
səhifə23/33
tarix05.01.2022
ölçüsü299,48 Kb.
#63788
1   ...   19   20   21   22   23   24   25   26   ...   33
Littafin Attaura: addinin da yahudawa sukeyi ayau sun cancanza shi da kuma bautan wanin Allah ta bangaren akida da cewa Uzaiu dan Allah ne, kuma abun bauta a wurin su yakanyi zunubi da kuma farin ciki kuma yana fadawa cikin nadama, kuma yana umurni da sata kuma mugu ne me tsananin riko, kuma shine abun bautan bani isra'ila kawai banda sauran mutane, kamar yadda suke kudurtawa cewa sune yaran Allah zababbu sauran mutane kuma basu kai su dajraja ba kuma duk wanda mahaifiyar sa ba bayahudiya bace bazai taba zama bayahude ba, suna daukan sa addini ne nasu su kadai kawai banda sauran mutane wanda hakan baya dacewa ya zama addini na duniya wanda ko wani mutane zasuyi shi, kamar yanda suke ganin cewa rayukan yahudawa wani bangare ne na Allah -Allah ya tsarkaki da daukaka daga abunda suke fadi daukaka me girma- idan mutumin da ba bayahude bay a duki bayahude to kamar ya duki buwayan abun bauta ne, addini ne wanda aka gina shi akan kiyayya da rook akan wasu mutane wanda ya hakatta cikin addinin su amfani dasu da kuma mamaye su da satan masu dukiya da masu ha'inci da karya da kuma basu bashi da riba me yawa da shedar karya akan wand aba bayahude ba saboda duk wanda ba bayahude ba a cikin akidar su kamar dabba yake, kuma hakika alkur'ani tuni ya gabatar da hujja me karfi da yake karyata wannan akida na yahudawa yadda Allah madaukaki yace: " yahudawa da kiristoci sunce mune yaran Allah da kuma masoyan sa, kace to dan me yasa yake azabtar daku da zunuban ku baku kasance ba face halittu cikin halittun sa yana gafartawa wanda yaso ya kuma azabtar da wanda yaso, mulkin sammai da kasa da abunda ke tsakanin su ga Allah suke kuma gareshi makoma take (18)" suratul ma'ida.

kuma mu sani cewa mafiya yawan yahudawan wannan zamani basu da asali zuwa ga Ibraniyyin na bani isra'ila tsofaffi wanda suka samo asali daga Ibrahim amincin Allah ya tabbata agareshi daga yaraon sa Isra'ila wanda shine Yakubu amincin Allah ya tabbata a gareshi, kasancewar sun cudanya da mutanen duniya wanda suka shiga addinin yahudanci domin mulkin mallaka na addini, amma yahudawa na asali sune wanda suke da asali daga tsatson Isra'ila (Yakubu amincin Allah ya tabbata agareshi) amma sauran yahudawan da basu ba suna daukan su a matsayin makaskantu a daraja.
1   ...   19   20   21   22   23   24   25   26   ...   33




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2025
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin