Mawallafi Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة



Yüklə 299,48 Kb.
səhifə24/33
tarix05.01.2022
ölçüsü299,48 Kb.
#63788
1   ...   20   21   22   23   24   25   26   27   ...   33
Littafin injila (bible): wanda kiristoci suke addini dashi ayau ya bi ta matakai da yawa da cancanzawa na zamani cikin tarihi maban banta wanda yasha banban da sakon da aka saukar masu daga wurin Allah sun cancanza shi da shigar da bautan wasun Allah wanda yan siyasan su da bokaye suke da hannu dayawa cikin wannan aiki na canza shi yadda akidar su itace imani da dayan uku watan Uba da Da da Ruhi me tsarki, suna kiransa da suna abun bautan dayan uku da kuma kasancewar abun bauta dayan ukun ne kamar yadda suke fadi, kuma sun samu sabani akan sa dayawa saboda ba'a iya fahimtar sa kuma ko wace bangare a cikin su tana kafurta dayan bangaren saboda haka, kuma Allah madaukaki yayi hukunce da kafurtan su baki dayan su indai basu daina fadin abunda suke fadi ban a shirka, Allah madaukaki yace: " hakika wanda sukace Allah dayan uku ne sun kafurta, babu wani abun bauta sai Allah shi kadai kuma idan basu hanu ba daga abunda suke fadi ba to lallai azaba me radadi zata shafi wanda suka kafurta daga cikin su (73)" suratul ma'ida.

Kuma kamar yadda take shari'a wacce aka aiko Isa da ita amincin Allah ya tabbata a gareshi ga wanda ya bace cikin bani isra'ila daga bayan musuamincin Allah ya tabbata a gareshi bawai na dukkanin mutane bane kamar yadda masihi ya bayyana cikin bible na matta, lamba na (10:5,6) da fadin sa: " zuwa ga hanyar mutane kada kubi, da garurrukan samurawa kada ku shiga, kawai ku tafi da yanci zuwa ga batattu cikin bani isra'ila".

Daga cikin haka zai bayyana cewa halinta na yanzu shari'a ce ta bautan wanin Allah saboda abunda ke cikinta na shirka da Allah yadda suka sanya Isa da mahaifiyar sa suka zama abun bauta wanda suke bautamawa koma bayan Allah tare da sanin cewa Isa amincin Allah ya tabbata agareshi kiransa ya kasance akan kadaita Allah ne da barin yi masa shirka kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari akan haka da cewa: " a lokacin da Allah yace ma Isa dan Maryma kai ne kace ma mutane su rike ka da mahaifiyar ka a matsayin abun bauta koma bayan Allah, sai yace tsarki ya tabbata a gareka baya halatta a gareni na fadi abunda bani da hakki akan sa idan ni nafadi haka hakika kasani kasan abunda ke cikin raina amma ni bansan abunda ke cikin rank aba lallai kaine masanin gaibu (116) bance masu komai ba sai abunda ka umurce ni dashi cewa ko bautawa Allah ubangijina da ubangijin ku, kuma na kasance ne sheda a garesu tsawon zaman danayi acikin su, amma a lokacin da ka kashe ni kai ne me ganin su kuma kai me sheda ne akan komai (117)" suratul ma'ida.



Kuma hakika kiristoci sun dauko dayawa daga cikin manyan addinai da akidoji na wanda suka gabace su, sai suka tasirantu da addinai na kariya wanda ya kasance a kasar farisa gabanin haihuwar annabi Isa da karni shida wacce ta kunshi kissa iri daya da kissar raba fikira da jin ubanjiki, haka kuma sun dauko cewa alla dayan uku ne daga addinin hindu yadda abun bauta a wurin su guda uku ne masu suna " fashanu" watan me kiyayewa da " sifa" watan me halakarwa da kuma " burahma" watan me samarwa, kamar yadda suka dauko akidar rataya domin kankare zunubi, da tsantseni da sufanci da kuma tsarkaka daga kudi domin shiga cikin mulkin sammai, kamar yadda wasu akidu da tunani na buzanci wanda ya gaaci kiristan ci da karni biyar ya dawo cikin ta, yadda ilimin kwatanta addinai ya nuna Kaman ceceniya me girma tsakanin mutumin buzanci da mutumin almasihi amincin Allah tabbata a gareshi sannan kuma kasancewar yanayi na haihuwar masihi da rayuwan sa da kuma yanayin da buzanci yabi yana cikin abunda yake tabbatar da wannan tasirin na kiristanci dashi cikin dayawa na akidun su, kamar yadda ya cudanya da addinin babalawa na da can kasancewar hukuncin " ba'al" allan rana yayi kama da hukuncin masihi amincin Allah ya tabbata agareshi, daga haka canzawan injila da kuma shigan abunda baya cikin san a akidun bautan wanin Allah yana daga cikin abunda yasa ya rasa yanayin san a asali wanda isa amincin Allah ya tabbata a gareshi yazo dashi daga wurin ubangijin talikai.
1   ...   20   21   22   23   24   25   26   27   ...   33




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin