Addinin buzanci: falsafa ce wanda aka kirkiro wacce take kama da addini wanda ake dauka a matsayin tsari na dabi'u da mazahaba na hankali wanda aka ginata akan maganganu na falsafa, da kuma karantarwa wanda bana wahayi ba kawai ra'ayoyi ne da aikdu cikin wasu addinai, ta kuma bayyana ne a kasar indiya bayan addinin hindu cikin karni na biyar gabanin haihuwan annabi Isa. Bayan mutuwar wanda ya kirkire ta me suna Sadahartaa Jutama wanda ya canza daga addinin buzanci shekara 480-560 na karni gabanin haihuwan annabi Isa. Ta canza zuwa ga akida batacciya wacce ta kunshi bautan wanin Allah, yadda suke kudurcewa cewa Buza shine Allah, kuma shine me tsarkake mutane wanda yake daukan dukkanin zunuban su, daga cikin abunda yake nuni akan kasancewar ta addini ce ta bautan wanin Allah fadin su cewa: a lokacin da Buza ya shiga cikin tsari nasu sai gumaka suka masa bauta, saboda haka ne buzawa suke salla ga buza yadda yasu sawwara masa gumaka suka sanya su cikin wuraren bautan su da wuraren su na game gari suna masu dukurcewa cewa zai shigar dasu aljanna.
Cikin wasu kantarwan buzanci akwai dabi'u masu kyau kamar kiran su da sukeyi na son juna da yafiya da mu'amalantar mutane da abubuwa masu kyau da kumayin sadaka ga talakawa, kuma sunada ruhbananci da kuma nisantar wakoki da caca da daurama kai abunda bazata iya ba da tsoro da tsawatarwa daga mata da dukiya da kuma kwadaitarwa game da aure da kuma fatali da dukkanin abunda ya sabawa dabi'a mutum wanda aka halicce sa akai na son dukkanin abunda ya dace su karanta, kuma suna dauka cewa littattafan su sunada matsayi kuma magana ne wanda ya jingunu zuwa ga buza ko kuma labari ne game da ayyukan sa wanda wasu daga cikin mabiyan sa suka suruta.
kenan zai bayyana mana cewa ita akida ce ta shirka wanda bana ubangiji bane magana ce akan falsafa da kuma ra'ayoyi na wanda ya kirkireta da kuma mabiyan su wanda suka zo a bayansa wanda suke kira nanata su tsawon zamani har yazu zuwa abunda suke ciki a yanzu.