Kafin kurewar lokaci:
Muyi nazari da hankulan mu masu lafiya da fidiyar mu me ingancicikin abunda muke akan sa, domin lallai rayuwa bata da tsayin da mutum zai batata ga abunda ba zai amfanar dashi ba, Allah madaukaki yace: " ku sani cewa fa lallai rayuwar duniya was ace ta yara da manya da kuma kawa da alfahari a tsakanin ku da kuma gasan tara yara da kudiya Kaman misalin ruwan sama ne wanda ya shayar da gonaki sai kayan wannan gona ya burge masu shi bayan wani lokaci sai kaganshi ya koma yallo sa'annan kuma ya bushe, kuma a lahira akwai azaba me girma da gafara daga Allah da yarda, rayuwan duniya kuma ba komai bace face jin dadi na rudu (20)" suratul hadid.
Hakan bayana nufin mutum ya guji duniya bane baki dayan ta da yanke dukkanin alaka da ita hakika musulunci ya hana hakan, Allah madaukaki yace: " ka nemi gidan lahira cikin abunda Allah ya baka kuma kada ka manta da rabonka na duniya, kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka, kada kayi barna a doron kasa lallai Allah bayason masu barna (77)" suratul kasas.
Allah madaukaki ya mana ni'imar hankali domin muyi amfani dashi cikin abunda zai jawo mana alheri duniyar mu da lahiran mu sai dai abun takaici dayawa daga cikin mutune suna amfani dashi ne cikin abunda zai jawo masu amfani ne kawai anan duniya koda kuwa a aljihun wasu ne kuma zai cutar dasu irin wannan nau'i na mutane kuwa Allah madaukaki yayi bayanin su cikin fadin sa cewa: " sun san zahirin komai na rayuwan duniyar su amma gafalallu ne game da lahira (7)" suratul rum.
Me wayau da dabara da hankali shine wanda yayi amfani da hankalin shi domin maslahar sa ta duniya da lahira ya cimma aiwatar da abunda zai sashi farin ciki dashi duniya wurin cin gajiyan dukkanin abunda Allah ya halitta a wannan duniya na maslahar sa da kuma gyara rayuwan sa da kuma sanin abunda zai kusanci ubangijin sa dashi domin ya kasance cikin shirin abunda yake jiran sa bayan mutuwar sa.
Mutum yana bukatar tsaya da nazari cikin ransa cikin abunda yake nashi da kuma abunda yake kansa na addini kasancewar al'amarin tafiyar baya dacewa agun mutum me hankali ya kai kansa zuwa ga bin addini ko kuma akida na karya wanda aka canza kuma bata dace da hankali ba me lafiya, da abunda Allah ya bashi na hankali zai iya banbancewa tsakanin gaskiya da karya da kuma daidai da kuskure, Allah yayi maka ni'ima na hankali domin kayi tunani bawai ka rika bi hakan b aba tare da tambaya ko kuma tunani gabanin haka, abun takaici shine hakan shine ke faruwa a wurin mutane dayawa ya samu iyayen sa da kakannin sa akan akida da addini shikenan kawai sai ya bisu da gado, kamar addinin indiya misali akwai dayawa daga cikin akidun cikinsa wanda yake aka kirkiro sabo wanda yake kashe shaukin gabanin fidira na bautan wasu halittu kamar bera da farji da shanu da dutse da sauran su har takai ga wani daya daga cikin malamai yace " a indiya ana bautan komai sai Allah kadai!" yana nufin addinai wand aba musulunci ba a kasar indiya, kuma hakan ya faru ne saboda bi da takalidanci (shine bin abu ko kuma mutum akan wani aiki daya keyi ba tare da tambayar sa ba menene dalilin sa akan haka) ba tare da lura ba da kuma taka tsantsan, wannan jinsin na mutum sune wanda Allah madaukaki ya zarge su ya kuma bayyana rashin amfanuwar su da fadin sa cewa: " idan kace masu kuzo zuwa ga abunda Allah ya saukar sai suce a'a mudai abunda muka samu iyayen mu akai ya wadatar damu, koda kuwa iyayen nasu basu san komai ba kuma ba shiryayyu bane (104)" suratul ma'ida.
Kada amun tsammani cewa ina zagin akidun wasu ko kuma isgilanci dasu, ba ha ka bane domin kuwa hakika alkur'ani ya hana mu hakan, Allah madaukaki yace: " kada ku zagi abunda suke bautamawa koma bayan Allah sais u zagi Allah saboda kiyayya da rashin ilimi kamar haka ne muka kawatawa ko wani al'umma ayyukan su sa'annan kuma zuwa ga ubangijin su zasu dawo sai ya basu labari game da abunda suka aikata (108)" suratul an'am.
Sai dai kawai kwadayi ne nakeyi na cewa asan wannan addini na gaskiya kuma abunda nakeso shine alheri ya samu kowa da aminci, tausayina irin ta mutum da tsorona akan su a karshen al'amari me ciwo shine mutum yam utu yana bautan wanin Allah da wani shari'a wanda ba shari'ar da aka saukar ma Muhammad s.a.w ba da ita wanda aka yardan masu da ita shine abunda yasani yin haka.
Domin ka kai zuwa ga gaskiya kayi amfani da hankalinka da tunanin ka cikin abunda kake ciki ka natsu sannan ka fara tunani cikin mallakin sararin samaniya da kasa da abunda Allah ya halitta a cikin su kuma kazama daga cikin wanda Allah ya fadi akan su cewa: " wanda suke ambaton Allah a tsaye da zaune da kuma kwance suna tunani cikin halittun sammai da kasa, ya ubangijin mu baka halicci wannan bah aka kawai domin barna tsarki ya tabbata a gareka ka tsire mu daga azabar wuta (191)" suratu al'imran.
Domin ka gane asalin hakika, Allah madaukaki yayi maka bayani da kasancewar be halicci wannan duniya ba domin wasu da yara da many aba cikin fadin sa cewa: " kuma bamu halicci sammai da kasa ba da abunda ke tsakanin su a matsayin was aba (38) bamu halicce sub a sai dagaskiya sai dai dayawa daga cikin mutane basu sani ba (39)" suratul dukkan.
Gaskiya itace ba'a halicci mutum ba domin wasa ba'ayi masa umurnin aikiata komai ba sannan ba'a hanashi aikita wasu abubuwan ba, kuma baza'a bashi lad aba ko kuma masa ukuba, Allah madaukaki yace: " shin kuna tsammani ne cewa mun halicce ku ne domin wasa kuma bazaku dawo ba zuwa gare mu (115) daukaka ya tabbata ga Allah me mulki na gaskiya babu abun bautawa da gaskiya sais hi ubangijin al'arshi me girma (116)" suratul muminun.
A dabi'ance ko wani mutum cikin al'amuran duniyan shi yana neman abunda yafi falala da kuma kamala da kuma abunda zai tabbatar da murnan sa shin cikin abinci ne ko kuma abunsha ko tufafi da sauran ababen more rayuwa, to haka ya dace daga gareshi ya rika aiwatar da haka akan akidar sa da addinin say a rika neman addinin da yafi falala da kamala wanda babu cin karo a cikin sa kuma be sabama fidirar mutum ba ingantacce, kuma hankali me lafiya wanda ake samun murnan zuciya da ita da natsuwa da kwanciyar rai. Ina mika kira na cikin wannan littafi ga makaranci me daraja da ya karanci musulunci addinin karshe zai same shi addini ne na kadaita Allah (tauhidi) wanda beci karo ba da fidirar mutum ko kuma hankali, addinin da Allah ya yardan ma halittun sa dashi hakan bazai zo maka sai ka tsarkake zuciyar ka daga son rai da sha'awar duniya da tsaban bangaranci na addini bayan gan da katar din Allah saboda haka ka tashi tsaye domin karantar sa daga asalin sa ingantattu kum ka amsheshi daga wurin amalaman addini bayin Allah wanda basa neman komai na burin duniya wurin karantar dashi kawai fatan su da babban burin su shine samun yardan Allah da kuma ceton yan uwan sa mutane daga wuta, ka nesanci duk wanda ya mayar da addini da shai'a a matsayin hanyar neman dukiya, Allah madaukaki yace: " lallai wanda suke boye abunda Allah ya saukar cikin littafi kuma suna neman wani lada dan kadan dashi to wannan ba komai suke cima cukunan sub a face wuta kuma Allah bazayyi magana dasu ba ranan alkiyama kuma bazai tsarkake sub a kuma sunada azaba me radadi (174)" suratul bakara.
Ka yaki kanka wurin neman Allah da gaskiyar da ta bace maka da sannu Allah zai kasance tare dakai zai shiryar dakai ya kuma maka jagora, saboda fadin Allah madaukaki cewa: " duk wanda yayi kokari cikin al'amarin mu to da sannu zamu shiryar dashi hanyoyin mu kuma lallai Allah yana tare da masu kyautatawa (69)" suratul ankabut.
Dostları ilə paylaş: |