Lallai Allah madaukaki yana sama, akan al'arshin sa akan sammmai ta bakwai sai dai wasu maguzawa zasu iya tambaya cewa a ina Allah yake suna nufin asalin wurin da yake cikin wannan duniya, sai muce masu lallai Allah madaukaki shine wanda ya halicci zamani da wuri, wuri da zamani halittu ne cikin halittan sa saboda haka bazasu iya karade shi ba kuma zamani baya mas hukunci, hakika ya kasance kuma babu abunda ya kasance gabanin sa ko kuma bayan sa ko saman sa da zatin sa ya daidaita akan al'arshin sa kuma ilimin mutum bai kai kusa gareshi ba, Allah madaukaki yace: " shine na farko da karshe da zahiri da badini kuma shi masani ne ga dukkan komai (3)" suratul hadid.
Siffofin Allah baza'a iya karade su ba cikin wannan littafi dan karami sai dai zamu ambaci wasu daga cikin siffofin Allah wanda ya halicci wannan duniya ya kuma samar dashi kamar haka:
Shine Allah daya bashi da abokin tarayya kuma bashi da kishiya ko makamanci cikin Allantakar sa da renon sa da siffofin sa, Allah madaukaki yace: " kace shine Allah shi kadai (1) Allah wanda ake nufi da bukata (2) be Haifa ba kuma ba'a haife shi ba (3) kuma babu wani tamkar a gareshi (4)" suratul ikhlas.
Shine Allah rayayye rayuwa ta har abada wanda baya mutuwa, Allah madaukaki yace: " shine rayayye babu wani abun bautawa da gaskiya bisa cancanta sais hi saboda haka ku bauta masa shi kadai gareshi addini yake, godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai (65)" suratul gafir.
Sauran mahalukai kuma da ba shi ba dukanin su zasu kare kuma zasu gushe, Allah madaukaki yace: " dukkanin abunda ke kanta me karewa ne (26) fuskan ubangijinka ne kadai zai wanzu ya cancanci a girmama da karamci (27)" suratul rahman.
Ya tsayu da zatin sa ya wadatu daga bayin sa baya bukatar wanda zai karfafa shi ta ko wane fuska sannan kuma shine wanda ya tsayama wanin sa, babu wanda ya iya ya tsayu babu shi, Allah madaukaki yace: " Allah wanda babu wani abun bauta da gaskiya bisa cancanta sai shi, rayayye tsayayye, gyangyadi baya daukan sa ko kuma bacci, dukkanin abunda suke cikin sammai da kassai nashi ne" suratul bakara.
Shi me hikima ne cikin ayyukan sa da maganganun sa da ikon sa, yana sanya komai a wurin sa cikin hikimar sa da adalcin sa, me hikima ne cikin halittun sa da kuma tafiyar dasu, kuma masani ne da maslahar su, Allah madaukaki yace: " shine mabuwayi akan bayin sa kuma shi me hikima ne kuma masani (18)" suratul an'am.
Shi ne me iko babu abunda ya gagare shi cikin sammai da kassai, Allah madaukaki yace: " duk inda kuke sai Allah yazo daku baki dayan ku, lallai Allah me iko ne akan dukkan komai (148)" suratul bakara.
Kuma shi masani ga komai ya kuma karade komai da karadewan sa cikakke, jahilci be taba riga ilimin sa kuma mantuwa bai taba samun sa ba, yasan abunda yake boye, yasan abunda ya kasance da abunda zai kasance da dukkanin wani mahaluki da abunda be kasance ba da zai kasance kuma ya zai kasance din, Allah madaukaki yace: " babu wani abu da yake boyewa ga ubangijin ka na kwayan zarra cikin sama ko kasa ko kuma wanda yafi hakan kankanta ko kuma wanda ya fishi girma face yana cikin littafi bayyananne (61)" suratu Yunus.
Shine mahaliccin komai da samar dashi daga rashin sa, Allah madaukaki yace: " shine Allah mahalicci me aiwatar da abunda yayi niyya na halitta me sawwara halitta yadda yakeson su, gareshi sunaye masu kyawu suke, abubuwan da suke sammai da kasa suna masa tasbihi kuma shi mabuwayi ne me hikima (24)" suratul hashri.
Shine me azurta dukkanin bayin sa, yana basu abaunda suke bukata na rayuwan su, Allah madaukaki yace: " babu wata dabba a doron kasa face ga Allah arzikin ta yake kuma yasan iyakan zamanta anan duniya da makomarta bayan mutuwar ta komai yana cikin littafi a bayyane (6)" suratu hud.
Lallai shie me iko ne akan rayawa da kashewa da kuma tayar da mutane bayan mutuwar su da hisabi, Allah madaukaki yace: " kace Allah shine yake rayaku sa'annan ya kashe ku sa'annan ya taraku zuwa ranan alkiyama wanda babu kokwanto akan sa sai dai dayawa daga cikin mutane basu sani ba (26)" suratul jasiya.