Shin Allah yanada bukata daga halittun sa?
Sanannen abu ne ga hankali cewa duk wanda ya mallaki wani abu to yana da iyanci na yin amfani da abunda ya mallaka ganin daman sa – Allah shine me misali na kololuwa – Allah madaukaki shine wanda ya halicci duniya da abunda ke cikinta shine mamallakin ta kuma ya juyata yadda yake so a duk lokacin daya so yadda kuma yaso, mutum halittace cikin halittun sa, Allah madaukaki yace: " lallai ubangijin ku shine Allah wanda ya halicci sammai da kasa cikin kwanaki shida sa'annan ya daidaita akan al'arshi, dare yana lullube rana yana neman sa da gaggawa da rana da wata da taurari horarru ne da umurnin sa, ku saurara halitta da umurni nashi ne, tsarki ya tabbata ga Allah ubangijn talikai (54)" suratul a'araf.
Shine me raba arziki da kuma jujjuya al'amura na ruwa da fari da girgizan kasa da talauci da arziki da rayuwa da mutuwa da lafiya da rashin lafiya da tsira da tabewa duka hakan cikin hukimar da Allah yake son su ne kuma yayi umurni yana kaddara su kuma babu wani mahaluki da ya isa ya hana hakan ko kuma ya kalubalance shi akan aikin sa ko kuma ya fita karkashin mulkin sa da da yadda yake so" ba'a tambayan sa akan abunda ya aikata amma su ana tambayan su (23)" suratul anbiya'i, Allah madaukaki kuma yace: “ Ubangijin ka yana halittan abunda yaso kuma yana zaban wanda ya so, basu suke da zabi ba, tsarki ya tabbatan masa kuma ya daukaka daga abunda suke masa tayarra dashi (68)" suratul kasas.
Hikimar sa a bayyane take ana sanin ta ba karam ba tana a boye bane yadda baza'a santa ba, abunda ya kaddara wanda zahirin sa yake zama sharri badinin sa zai iya zama alheri amma mu bamu sani ba ko kuma akasin haka, Allah madaukaki yace: " kuma kila ku ki abu amma alheri ne a gareku kuma kila ku so abu amma sharri ne a gare ku, Allah shine masani amma ku baku sani ba (216)" suratul bakara.
Wanda ya samar da wannan duniya yanada ikon samar da wanin ta cikin abunda ya sani wanda mu bamu sansa ba, bashi da bukata zuwa ga halittun sa hasali ma sune mabukata zuwa gareshi cikin dukkanin ayyukan su, Allah madaukaki yace: " yaku mutane kune mabukata zuwa ga Allah shi kuma Allah me wadata ne kuma me godiya (15) idan yaga dama zai tafiyar daku sai yazo da wasu halittu na daban (16) kuma hakan ba gagararre bane agun Allah (17)" suratul fadir.
Kamar yadda jikin su yake da bukata zuwa ga ababen rayuwa na dole domin rayuwa kamar su abinci da abinsha haka zukatan su ke da bukata zuwa ga mahaliccin wanda zasu rika bauta mawa suna kum akai masa bukatun su suna kuma kankantar dakai a gare sa suna jin natsuwa da aminci na kusancin sa, kamar yadda jariri yakejin aminci a tsakanin cinyar mahaifin sa haka mutum yake da bukata zuwa ga mahalicci wanda zai baje a tsakanin sa ya kuma rika mika masa koken sa zuwa gareshi, karkashin kaskantar dakai da jayuwa da bauta ga wannan mahalicci zuciya take samun abinci da natsuwa da tsira, kuma bazata iya samun wannan abinci ba sai ta hanyar manzanni wanda suke zuwa masu da wahayi daga wurin mahalicci wanda ya halicci zuciyar ka ya kuma sanya masa abinci ta hanyar abunda suke zuwa dashi na sharia, Allah madaukaki yace: " shin wanda yayi halitta be sani ba kuma shi me rangwame ne kuma me bada labari (14)" suratul mulk.
Abunda ke karfafa rayuwan mutum da jujjaya dukkanin al'amuran su dukkanin haka yana komawa ne zuwa ga ganin daman sa da kuma iradan sa, be halicce su domin samun karfi daga gare su kuma be halicce su ba domin wasa kuma be halicce su domin su amfanar dashi ko cutar dashi ba, shi mawadaci ne daga garesu su kuma bukata zuwa gareshi kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari cikin hadisin kudusi: " yaku bayina lallai bazaku iya kaiwa ga cutar dani ba bare ku cutar dani kuma bazaku iya kaiwa ga amfanar dani ba bare ku amfanar dani, yaku bayi na da ace farkon ku da karshen ku mutanen ku da lajannun ku zasu kasance akan zuciyar mutum daya daga cikin ku wanda yafi ku tsoron Allah hakan zabai karamun komai ba cikin mulki na, yaku bayina da ace farkon da karshen ku mutanen ku da aljannun ku zasu kasance akan zuciyar wani mutum wanda yafiku fajirci hakan bazai ragemun komai ba cikin mulki na, yaku bayi na da ace farkon ku da karshen ku mutanen ku da aljannun ku zasu kasance a wuri daya sais u tambayeni sai naba kowa abunda ya tambaye ni hakan bazai ragemjun komai ba cikin abunda nake dashi sai kamar abunda allura zai rage idan an tsoma shi cikin kogi an fito dashi, yaku bayi na wannan ayyukan ku ne nake kididdigewa sa'annan ya sakanya maku dasu duk wanda ya tarar da alheri to ya godema Allah wanda kuma ya tarar da akasin haka to kada ya zargi kowa sai kansa" sahihu muslim.
Ayyukan bayi zai dawo masu koda alheri ko kuma da sharri, za'a masu hisabi akan su idan alheri mutum ya aikata zaiga alheri idan kuma sharri ya aikata zaiga sharri, daga cikin rahamar Allah da adalcin sa ya sanya hisabi da sakamako da lada da ukuba saboda kada me datti yayi daidai da me kyau, Allah madaukaki yace: " idan kun kyautata to kanku kuka kyautata mawa idan kuma kun munana shi ma haka" [suratul isra'I ayata 7].
Dostları ilə paylaş: |