Sinadarin (gangan jiki):
Abunda yake karfafashi da lafiyar sa shine tsabtace shi da tsarkake shi da kuma kosar dashi sha'awar sa na dabi'a na abinci da ruwa da aure, Allah madaukaki yace: " yak u yayan Adam ku dinga rike kawar ku lokacin zuwa ko wani masallaci da salla kuma kuci ku sha kada kuyi almubazaranci, lallai Allah baya son almubazzari (31) kace wanene ya haramta maku adon Allah wanda ya fitar dashi domin bayin sa da dadaden abubuwa na arziki kace anyi su ne domin wanda sukayi imani a rayuwan duniya kuma a lahira nasu ne su kadai kawai banda wanin su, kamar haka ne muke bayyana ayoyin mu ga utane masu sani (32)" suratul a'araf.
An umurce sa da yin magani ga jikin idan bashi da lafiya ta hanyar ko wani irin magani wanda yake halal, manzon Allah s.a.w yace: " lallai Allah ya saukar da cuta da kuma magani, ya sanya magani ga ko wace cuta saboda haka kuyi magani, amma kada kuyi magani da haramun" (hadisi ne ingantacce) dabarani ne ya yarawaito shi daga Ummi darda'i Allah ya kara mata yarda, kuma albani ya ingantashi cikin sahihul jami'u lamba ta 1762.
Kosar da sha'awa ta halittan dan Adam yanada dokoki da ka'ida wanda Allah ya shar'anta masa domin ya daukaka shi daga nau'in dabbobi kada ya zama irin su, Allah madaukaki yace: " kuma daga cikin ayoyin say a halitta maku mata domin ku samu na tsuwa zuwa garesu kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakanin ku lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (21)" suratul rum.
|