Allah madukaki yayi gaskiya da yake cewa: " lallai idan kabi dayawa daga cikin mutanen duniya zasu batar dakai daga hanyar Allah ba komai suke bi ba face zato kuma ba komai suke kai ba face kaddarawa (116)" suratul an'am.
Bari mu dauki wasu daga cikin addini da mazhabobi a gurguje wanda suka fi yaduwa da mabiya cikin duniya domin mu gani yadda mafiya yawan su basa dacewa da hankali lafiyayye da kwakwalwa shiryayya saboda abunda ke cikin su na shirka da sanya halittu su zama abun bauta da girmama su, bazamuyi masu karya ba lallai cikin wasun su akwai kira zuwa ga dabi'u kyawawa da kuma hani ga munanan dabi'u, ko wnai makaranci zai iya gano haka karkashin baiwan da Allah yayi masa na hankali wanda yake rarrabewa tsakanin daidai da kuskure, da abunda yake na hankali da wanda bana hankali ba da wanda ya kamata da wanda be kamata ba: