Mawallafi Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة



Yüklə 299,48 Kb.
səhifə27/33
tarix05.01.2022
ölçüsü299,48 Kb.
#63788
1   ...   23   24   25   26   27   28   29   30   ...   33
Sekanci (gamayyan addinu): bawai addni bace ko kuma mazahabanci a'a ana daukan ta ne a matsayin tafiya na gyaran addini wanda suka tasirantu da musulunci kuma sunyi kokari wurin hadawa tsakanin akidu da addinai wanda suka yadu da kuma hada kansu su zama akida guda daya, yadda wasu mutanen addini suka kirkirota daga cikin hindu wanda suka bayyana a karshen karni na goma sha biyar cikin farkon karni na goma sha shida bayan haihuwar isa suna masu kira zuwa ga saban addini wanda ya hada tsakanin musulunci da hindu karkashin tuka me suna " ba hindu bane kuma ba musulunci bane". Sai dai basu samu nasara ba akan haka yadda jahilcin su da musulunci da kuma akidar su da ilimin su ya kaisu zuwa ga bata daga hanyar ta daidai da ace sun san musulunci da suncan cewa lallai addini fa baya kasancewa sai idan wahayi ne daga Allah babu halin yin kokarin mutum a cikin sa kokarin sun a hada addinai kuma da mazahaboi mabanbanta domin kusanci a tsakanin su da fitar da akida daya wanda kowa zai taru akai, sa'annan suka wayi gari bayan haka makami a hannun turawa suna amfani dasu wurin ayyuka wanda yake kira zuwa ga fitowar su daga hindu, mulkin mallakan turawa ya kasance yanada tasiri babba wurin taimakawa wannan tafiya tasu da kuma samun nasarar su yadda wannan kira na wayi gari cikin turawa yanada wasu siffofi wanda yake banbance shi dayawa daga sauran mutane cikin jihohi wanda suke kai yawan kasha ashirin 20% na rundunonin hindu na garin burtaniya.

Daga wannan zai bayyana cewa wannan tafiya wanda suka nufi gyara da ita sai dai basu samu nasara ba yadda ta samu mataimaka da rayata gabanin fara mulkin mallaka cikin kasashe da kuma amfani dashi na samun bayi da kuma rusa musulunci na kwarai kasancewar gaskiya fa bazata taba haduwa ba da karya kuma kadaita Allah bazai taba haduwa ba da shirka.
1   ...   23   24   25   26   27   28   29   30   ...   33




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin