DALILIN SABANIN YA'YAN ADAM:
Annabi s.a.w ya baiyana dalilin sabanin launukan yan-adam, da chudanyarsu da halayensu, sai yace: “Lallai Allah ya halicci Adam daga damqa da yayi daga kowace qasa *daga kowane yankinta*, sai Yan-Adam sukazo gwargwadon qasa, cikinsu akwai ja, baqi, fari, fatsi-fatsi dakuma tsakankanin hakan, da mai sauqi *mai taushi*, da mai baqin ciki *mai kaushin dabi'a*, da lalatacce *mai lalatacciyar dabi'a*, dakuma mai kyakykyawa.
HALITTAR HAU'WA'U UWAR MUTANE:
Bayanda Allah ya halicci Adam a.s, sai aka halicci matarsa Hauwa’u daga gareshi, an halicceta daga qashin haqarqarinsa na hagu, don ha samu natsuwa gareta kuma don mutane su yadu daga gareta, Allah yace: “Yaku mutane kuji tsoron Ubangijinku da ya halicceku daga rai guda, sannan ya sanya matarsa daga gareshi, kuma ya watsa maza dayawa daga garesu da mataye, kuji tsoron Allah da kuke roqo dashi da kuma zumunci, Lallai Allah ya kasance mai bibiya gareku”
Kuma Annabi s.a.w na cewa: “Duk eanda yayi Imani da Allah da ranar qarshe, kada ya cutar da maqocinsa, kuma kuyi wasiyar Alkhairi ga mata, domin su an haliccesune daga haqarqari, kuma lallai mafi karkacewa a qashin haqarqari shine samansa, in katashi miqeshe ka karyashi, in ka barshi kuma bazai gushe a karkacensa ba, don haka kuyi wasiyat Alkhairi da mata”
Dostları ilə paylaş: |