Mutum a farkonsa bai kasance wani abu ba da ake ambatonsa ba, allah ma'daukakin sarki yana cewa " lallai ne wata mudda ta zamani tazo akan mutum, bai kasance komai ba wanda ake ambata. (46)"
sannan sai akazo farkon halittarsa daga wani ruwa wulaqantacce (wanda mutune suke qyamatarsa) allah ma'daukakin sarki yana cewa: ashe bamu halittaku daga wani ruwa wulaqantacce ba. * sannan muka sanya shi acikin acikin wani wurin nutsuwa amintacce. * zuwa ga wani gorgodon qaddara sananna.* sannan muka nuna iyawar mu? madalla damu, masu nuna iyawa(47).
alghazaly yana cewa: mutum ya kalli ni'imomin da allah ya masa yadda ya daga matsayinsa daga qasqanci da wulaqanci da tozartawa zuwa wannan girma da 'daukaka sai ya wayi gari akwai shi ya zama samamme ya zama rayayye bayan da matacce ne, ya zama mai iko bayan da gajiyayye ne, ya zama mai magana bayan da kurma ne, ya zama yana gani bayan da makaho ne, ya zama mai ilimi bayan da jahili ne bai san komai ba, ya zama shiryayye bayan da 'batacce ne, ya zama mai iko ne bayan da gajiyayye ne bashi da ikon komai, ya zama mawadaci bayan da matalauci ne sannan ya zama wani abu saboda allah, duk ya kamata ya duba wannan ni'imomi ko yasan irin falalar da allah ya masa, yasan cewa shi ba komai bane, inda allah yaga dama da baiyi shi haka ba, don haka sai ya qara 'daura 'damarar godewa ta hanyar godewa (allah) ta hanyar bauta masa da yi masa biyayya a abunda yayi umurni ayi ko a bari."