Mawallafi Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة



Yüklə 277,39 Kb.
səhifə32/44
tarix07.01.2022
ölçüsü277,39 Kb.
#80427
1   ...   28   29   30   31   32   33   34   35   ...   44
DAGA CIKIN SHARUDDAN ZAKKAH:

  1. mallakar nisabi, ya kasance yana da dukiyar ta kai iyakar da musulunci ya tabbatar na zakka kuma ya zarta akan amintar buqatuwansa na larura na abinci da tufafi da abin sha da muhalli.

  2. cikar shekara, dukiyar ta shekara daya cif, idan bata cika shekara ba to ba za'a fitar da zakkar ba. shari'a ta iyakance wadanda suka chanchanta su ci zakka, acikin fadin allah: "abun sani kawai, dukiyoyin sadaka na talakawa ne da miskinai da masu aiki akansu, da wa'danda ake lallashin zukatansu, kuma acikin fansar wuyoyi da mabarta da acikin hanyar allah da 'dan hanya (matafiyi) farilla daga allah kuma allah ne masani mai hikima. suratul tauba aya ta 60.

Kuma ita wani abin gwaji ne da kamantashi da biyu cikin dari,manufar musulunci ta wajabta zakka shi ne yanke talauci daga alumma da kuma magance hadarinsa wadanda suke faruwa saboda shi kamar sata, da kisan kai, da kuma cin mutunci, da kuma raya daukar nauyi na alumma a tsakanin musulmai, ta hanyar toshe buqatun masu buqata kuma suke tambaya da masu baqata marasa tambaya, kamar yadda take tsarkake zuciyar mai arziki daga rowa da qauro da kuma cire kwadayi da son duniya da kuma kutsawa cikin sha'awowinta wanda hakan yake mantar da su yan uwansu talakawa da mabuqata.

kuma tana tsarkake zuciyar talakawa da masakai daga qiyayya da qulli da tsana ga mawadata yayin da suka gansu suna fitar da abinda allah ya wajabta musu akan dukiyoyinsu kuma suna musu alqawarin ciyarwa da kuma kyautatawa da kuma kulawa.

AZUMIN RAMADAN: wata daya ne a cikin kowace shekara wanda musulmai suke azumtarsa ta hanyar kamewa ga barin wasu dabi'u da allah ya hallici mutum da buqatuwa garesu na daga ci da sha da kuma jima'i daga bullowar alfijir izuwa faduwar rana, ba kuma al'amari ne da a musulunci aka fara farlanta shi ba bari dai an farlantawa alummomin da suka gabata, saboda fadin allah: ya ku wad'anda kuka yi imani an wajabta azumi agare ku kamar yadda aka wajabta shi ga wa'danda suke gabanninku, ko zaku ji tsoron allah." suratul baqara aya ta 183.

ba iyakar abinda ake nufi da azumi ba kamewa daga dabi'u na jiki kamar ci da sha kawai ba, bari dai dole ne kamewa ga dabi'u da buqatu na boye na barin qarya, da gulma (ambaton ka ga dan uwanka da abinda baya so), da annamimanci (yada gulma) da algus da yaudara da yasasshen zance da abinda yayi kama da hakan na ayyuka ababen qi, sannan barin wandannan abubuwa marassa kyau wajibi ne ga musulmi a wajen ramadan ana qarfafa wajabcin barinsu sosai a ramadan saboda fadin annabi: )wanda bai bar fadin qarya ba da aiki da ita da wauta (alokacin azuminsa) to babu wata buqata ga allah acikin (wannan mutum) ya bar abincinsa da abun shansa." bukhari ya ruwaito 1804.

azumi yaqi ne tsakanin zuciya da sha'awarta da kwadayinta yana da fa'ida a alumma manzon allah (saw) ya bayyana ta acikin fadin sa: duk aikin da dan adam zaiyi yana gareshi ne saidai azumi kawai domin shi nawa ne kuma nine mai sakawa akanshi, lallai azumi kariya ne idan ya kasance ranar da dayanku yake azumi kada yayi abinda zai kusanci mace, kada yayi musu da daga murya, idan wani ya zageshi sai yace lallai ni mai azumi ne, na rantse da wanda raina ke hannunshi warin bakin mai azumi yafi tiraren almiski kanshi a wajan Allah, mai azumi yana da farin ciki guda 2, yayi farin ciki lokacin da zaiyi bude baki, da kuma farin ciki lokacin da zai koma ga ubangijinshi, sahihul bukhari 1805.

ta hanyar azumi ne musulmi yake sanin buqatun yan uwansa wadanda basa roqo idan suna buqata daga talakawa da masu buqata wadanda basa sa samun abincin da zai ishe su, da kuma abinda za suyi sutura, da kuma matsuguni, sai ya riqi lura bada haqqoqinsu, da kuma tambayar halayensu da kuma bibiya da bincikar buqatunsu.

HAJJI: shine tafiya zuwa 'dakin allah mai alfarma domin yin wasu ayyuka ke'bantattu a wasu wurare ke'bantattu a wasu lokuta ke'bantattu, wannan wani rukuni ne da ya wajaba akan kowane musulmi mai hankali, baligi, namiji ne ko mace yinsa sau daya a rayuwa da sharadin iko na jiki da na dukiya, duk wanda ya kasance maras lafiya kuma rashin lafiyar tasa ba'a sa ran warkewarsa kuma rashin lafiyar tasa ta hana sa yin aikin hajji kuma alhalin yana da dukiya to sai ya wakilta wani yaje yayi masa, haka nan duk wanda yake talaka bai mallaki dukiyar da ta fi qarfin buqatunshi na yau da gobe ba da kuma buqatun wanda suke kansa ba to hajji ya fadi akansa, saboda fadin allah: "kuma akwai hajji 'daki domin allah akan mutane ga wanda ya samu ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta, to lallai allah mawadaci ne daga barin talikai." suratul ali-imran aya ta 97.

ana fassara hajji a matsayin babban taron da yake tara musulmai a bigire daya, suna ambatan allah daya, suna maimata kira daya, "amsawarka ya allah amsawa gareka, amsawarka babu abokin tarayya gareka amsawarka, lallai godiya da ni'ima gareka suke da kuma mulki babu abokin tarayya gareka" ana nufin: ya allah mun zo wannan muhalli ne domin amsa kiranka da kwadayi cikin samun yardarka da kuma tabbata daga garemu da kadaituwarka kuma kai ka chanchanta da bauta ba tare da tambaya ba.

babu banbanci tsakaninin mai arziki da talaka da mai girma da maqasqanci da fari da baqi da balarabe da wanda ba balarabe ba dukkansu daya ne agun allah babu wanda ya fi sai wanda ya fi da tsoron allah, ba komai bane haka ba sai dai qarfafa yan uwantaka tsakanin musulmi da kuma hadinkai.


Yüklə 277,39 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   28   29   30   31   32   33   34   35   ...   44




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2025
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin