HALITTAR SAMMAI DA QASSAI DA ABINDA KE TSAKANINSU:
Allah Madaukaki yace: “Kuma (Allah) shine ya halicci sammai da qasa bisa gaskiya, dakuma ranar da zai ce ‘kasance' sai ya kasance, maganarsace gaskiya, kuma mulki gareshi yake a ranar da za'ai busa cikin qaho, shine masanin boye da baiyane, kuma shine mai hikima mai bada labari (73)
WANI YANKI NA ABABEN HALITTAR ALLAH CIKINSU AKWAI:
*Allah yace: “Kuma muka sanya sama tazamo rufi abin kiyayewa, amma su gameda ayoyinta suna masu juya baya (32) Kuma (Allah) shine ya halicci dare da yini da rana da wata, kowannensu yana jujjuyawa a cikin falaki (33).
*Allah madaukaki yace: “Shin kune kukafi wahalar halitta kokuwa sama da muka ginata (27) ya daga gininta sannan ya daidaitata (28) kuma ya lullube darenta kuma ya fidda hantsinta (29) sannan bayan haka ya shimfida qasa (30) ya fidda ruwanta da makiyayanta daga gareta (31) sannan ya kakkafa duwatsu (32) (don) suzamo guziri gareku da dabbobinku (33)
*Allah madaukaki yace: “Sai muka aiko da iska ----****--- sai muka saukar da ruwa daga sama, sai muka shayar daku shi kuma bakune ke taskanceshi ba (22)
Ita (Iska) kala kala ce kamar Yanda Allah madaukaki yayi bayani, daga ciki akwai wacce take Rahmah ce, Allah na cewa: “Kuma shine wanda yake aiko da iska tana mai bushara gaba ga rahmarsa, har ta janyo girgije mai nauyi, sai mu jashi ga mayaccen gari sai mu saukar da ruwa dashi, sai mu fitar da dukkan nau'in yayan itatuwa, da haka ne muke rayar da matattu (munyi hakan ne don) kozakuyi tunani (57)
Daga ciki kuma akwai wanda Azabane da uquba, Allah madaukaki yace: “Kokuwa kun amince ya maidaku cikinta wani lokaci na daban sai ya aiko muku da iska mai qarfi sai ya dilmiyar daku da bisa abinda abinda kuka kafirce masa, sannan bazaku samu wni mai taimako akanmu ba (69)
Kuma Madaukaki yace: “Sai iska mai qarfi ta afka mata cikinta (iskar) akwai wuta sai (gonar) ta qone…”
Kuma s.w.a yace: “Sai muka aike musu da iska mai qarfi cikin kwanaki *****”
Kuma ya hukunta Halittarsu ta zama Sammai Bakwai da Qassai Bakwai, Allah s.w.a yace: “Allah ne ya halicci sammai bakwai da kuma qasa kwatankwacinsu, yana saukar da Umarni a tsakaninsu, don kusan cewa lallai Allah mai ikone bisa komai kuma ya tattara sani ga dukkan komai (12)
Haqiqa sammai da qassai a farko sun kasance a manne suke sashe ahade da sashe, Allah yace: “Ashe wadanda suka kafirta basuga cewar sama da qasa sun kasance a hade bane sai muka rabasu, kuma muka sanya duk wani abu mai rai ya zamo daga ruwa, ashe bazasuyi Imani ba(30)
Kuma Allah ya baiyana tsawon kwanakin halittar sammai da qasa da abindake cikinsu, sai s.w.a yace: “Kace dasu, yanzu ku zaku kafirta da wanda ya halicci qasa cikin kwanaki biyu, kuma ku sanya masa kiahiyoyi, lallai wannan (da yayi halittar nan) shine Ubangijin talikai (9) kuma ya sanya duwatsu a samanta kuma yayi albarka cikinta kuma ya qaddara lokutanta cikin kwana hudu daidai ga masu tambaya (10) sannan ya daidaitu zuwa ga sama asannan tana hayaqi sai yace da ita da qasa kuzo kuna masu biyayya ko bisa dole, sai suka ce munzo muna masu biyayya (11) sai ya hukuntasu sammai bakwai cikin kwanaki biyu kuma yayiwa kowace sama wahayin umarninta, kuma muka qawata saman duniya da fitilu da tsaro, wannan shine hukuncin mabuwayi masani (12)