Daga cikin halittun Allah boyayyu da ya haliccesu don bautarsa akwai Aljanu, Allah yace: “Ban halicci Aljanu da mutane ba face don su bautamin (56) bana buqatar arziqi daga garesu kuma bana buqatar su ciyar dani (57) Lallai Allah shine mai azurtawa kuma ma'abocin qarfi mai tsanani'
Dukkan hukancindake hawa kan Yan-Adam yana hawa kansu, Allah yace: (Ka tuna sanda muka juyo maka da wani yanki na Aljanu, suna sauraron Qur'ani, a yayinda sukazo wajen sai sukace -ga yan'uwansu- kuyi shiru, bayanda aka gama sai suka juya ga jama'arsu suna masu gargadi garesu (29) sukace ya jama'armu lallai mun saurari wani littafi da aka saukar bayan Musa, yana shiryarwa zuwaga gaskiya kuma ga hanya madaidaiciya (30)
Allah ya haliccesu daga wuta, Allah yace: “Ya halicci mutum daga busashiyar qasa (14) Kuma Aljanu ya haliccesu daga yunbun wuta (15)
Kuma Allah madaukaki yace: “kuma haqiqa mun halicci mutum daga baqar qasa mai wari (26) Kuma Aljanj mun haliccesu gabanin haka daga wuta mai ruruwa (27)