Uban Halittu kuma tushensu, Allah yace: “Ka tuna asanda Ubangijinka yace ga Mala'iku: “Lallai ni zan sanya wakili a bayan qasa”, sai sukace: “Yanzu zaka sanya wanda zai barna cikinta kuma ya zubda jini cikinta, Alhali mu muna tsarkake sunanka kuma muna Girmamaka”, Sai Yace: “lallai ni nasan abinda baku saniba (30).
Daga gareshine Mutane suka tsatso, kuma gareshi auke komawa kamar Yanda Allah madaukaki ya bada labarin hakan a fadinsa: “Yaku mutane kuji tsoron Ubangijinku da ya halicceku daga rai guda…”
Kuma mai tsira da Amincin Allah yanacewa yana mai baiyana wannan haqiqa: “Ya ku muytane lallai Ubangijinku daya ne, kuma Ubanku dayane, Dukanku daga Adam kuke, Kuma Adam daga Qasa yake, lallai mafi karamcinku wajen Allah shine mafi jin tsoron Allah cikinku, balarabe baida wata falala akan wanda ba balarabe ba, ko wanda ba balarabe ba akan balarabe, ko ja akan fari, ko fari akan ja, face da tsoron Allah”