Bayan Adam a.s da qarnuka goma, sai sabani ya afku (tsakanin yan-adam), sai Allah ya aiko da Manzanni, an karbo daga Ibn Abbas r.a yace: “Yakasance tsakanin Nuhu da Adam akwai Qarnuka goma, dukansu sun kasance bisa shari'ah da gaskiya, sai Allah ya aiko da Manzanni suna masu bushara da gargadi”
Don haka farkon Manzanni bayan sabani shine Nuhu a.s, Allah madaukaki yace: “Lallai mu munyi wahayi gareka kamar yanda mukai wahayi ga Nuhu da Annabawa a bayansa” kuma Haqiqa Allah ya ambaci wadansu daga cikinsu a littafinsa, Allah madaukaki yace: “Kuma wannan itace Hujjarmu da muka bayarda ita ga Ibrahim akan mutanensa, muna daga darajar wanda mukaso, kuma lallai akwai mafi sani akan kowane masani (83) Kuma mun bashi Is-haqa da Yaquba, dukkansu mun shiryar dasu, da Kuma Nuhu wanda muka shiryar dashi gabanin su, kuma daga cikin zuriyarsa akwai Dawuda da Sulaimana da Ayyuba da Yusufa da Musa da Haruna, kuma da haka ne muke sakankawa masu kyautatawa (84) Da Zakariya da Yahya da Isa da Il-yaasu, dukkansu suna daga cikin salihai (85) Da Isma'ila da Al-yasa'u da Yunusa da Lutu, kuma dukkansu mun daukakasu akan talikai (86) Kuma daga cikin Ubanninsu da matayensu da zuriyarsu, haqiqa mun zabesu kuma mun shiryar dasu zuwaga hanya madaidaiciya (87)
Allah madaukaki yace: “Kuce munyi Imani da Allah da abinda aka saukar mana, da abinda aka saukar ga Ibrahima da Isma'ila da Is-haqa da Yaquba da jikokinsu, da abinda aka bawa Musa da Isa da Abinda aka bawa Annabawa daga Ubangijinsu, bamu rarrabewa tsakanin kowane daga cikinsu, kuma mu masu miqa miqa wuyane gareshi”
Allah yace: “Da Isma'ila da Idrisa da Zhal Kifl, dukkansu suna daga cikin masu haquri (85)
Dukda sanin cewa Akwai wasu da Qur'ani bai bada labarinsu ba, Allah madaukaki yace: “Da Manzannjn da muka baka labarinsu gabanin haka da Manzannin da bamu baka labarinsu ba, kuma Allah yayi Magana da Musa Magana”
Sai ya kasance Allah mai girma da daukaka yana aiko da Annabawa da Manzanni daga lokaci zuwa lokaci, suna masu mayar da mutane zuwa ga kadaita Ubangijinsu da bautarsa, Dukkansu Amincin Allah yatabbata garesu, daga na farkonsu zuwa na qarshensu, da'awarsu ta hadu bisa Tauhidi, wanda shine kadaita Allah madaukaki da bauta, a qudurce da baki da aikace, da kaficewa dukkan abinda ake bautawa koma bayan Allah, Allah madaukaki yace: “Kuma haqiqa mun aika Manzo cikin kowace Al-Umma, akan ku bautawa Allah kuma ku gujewa dagutu, daga cikinsu akwai wanda Allah ya shiryar, daga cikinsu akeai wanda bata ta tabbata akansa, kuyi tafiya aban qasa kuga yanda qarshen masu qaryatawa ya kasance (36)
Amma Shari'o'I da farillai da ake bauta dasu sun sassaba, domin akan farlantawa waninsu (Annabawa) abinda ba’a farlantawa wani ba (ga Al-ummaraa), wannan wani gwaji ne daga Allah, Allah yace: “Kowanne daga cikinku munsanya masa tsari da shari'a, da Allah yaso da sai yasanyaku Al-ummah da, saidai (ya rarrabaku ne) don ya gwadaku cikin abinda ya baku, don haka sai kuyi rgegeniya wajen Alkhairi” Har aka rufe Manzanci da Muhammad s.a.w, wanda aka aikoshi ga Mutane baki daya, Allah yace: “Muhammadu bai zama Uban daya daga mazajenku ba sai dai Manzon Allah ne kuma cika makin Annabawa”