Yakasance daga cikin abinda Manzannin Allah suke kira gareshi shine Imani da samuwar abin bauta guda daya, wanda shine mahalicci, mai jujjuya lamura, wanda za'a dinga bautarsa shi kadai, kuma adinga komawa gareshi, wannan na daga cikin abinda ke gaadar da rabauta ta ruhi da natsuwar rai da hutawar hankali, wannan shine abinda Ubangijinmu ya baiyana ga Manzonsa, da fadinsa: “Bamu aikoka ba face rahama ga talikai”
Dalili kuwa gameda samun dacewa ga masu Imani da Allah da abinda yazo daga gareshi shine abinda muke gani a yankunan da suke qaryata samuwar Mahalicci mai girma da daukaka, kuma take maqarqashiya ga shari'o'insa, da abinda take rayuwa ciki na daburcewa da damuwar rai, da raurawar ruhi mara tsari, wanda aqarshe take qarewa ga shan qwayoyi da kayan maye, don qoqarin cike gibin ruhi da take rayuwa dashi, kai har wasu ma abin kan kaisu ga Qunar baqin wake -muna neman Tsarin Allah-, abinda kuwa na sani, lallai wadannan duka ba abubuwanda ake neman dacewa dasu bane, domin dacewar da za'a samu cikin wadannan in ma an samu ta lokacice taqaitatta kuma tauyayya, kai misalinta tamkar wanda yasha ruwa mai gishiri ne (ruwan teku) baya qosar da qishi kuma zai qara masa qishine akan qishinsa, sai dai Imani da samuwar Allah, da qanqan da kai da miqa wuya gareshi, da qanqan da kai gabansa da bin karantarwarsa shine ke gaadar da tsallakewa wannan dukkansa, da samun dacewa ta haqiqa da hutawar rai.