Lallai imani da Allah da gasgata cewa lallai akwai Allah da kua tsarkakeshi da bautas shi kadai shine asalin shari’ar musulunci, domin kasancewarshi imani zai bibiyeshi da sauran rukuna imani wanda manza Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi ya fada acikin hadisin da malaika jibril yake tambayanshi: ka bani labara game da imani, sai annabi yace: imani shine kayi imani da Allah da malaikunshi da littafanshi da manzanninshi da ranar sakamako, da kuma imani da qaddara alkhairinta da sharrinta. Imam muslim ne ya ruwaitoshi (15.)