allah ya bayyana cewa halittar bata ta'ba kasancewa ba sai ruwan namiji da mace sun ha'du (ma'ana ruwan namiji ya shiga qwan mace a mahaifarta) allah ma'daukakin sarki yana cewa
"to mutum ya duba, daga me aka halitta shi? * an halittashi daga wani ruwa mai tuku'dar juna. * yana fita daga tsakanin bayan mutum da kuma qirji(48). kuma allah ma'daukakin sarki ya bayyana cewa wannan ruwan ta hanyarsa ne ake samun hayayyafa tsakanin bil adam, allah ma'daukakin sarki yake cewa: kuma shine ya halitta mutum daga ruwa, sai ya sanya shi nasaba da surukuntaka, kuma ubangijinka ya kasance mai ikon yi(49). - kuma allah ya bayyana cewa wannan sabuwar halittar tana kasancewa ne a ke'bantaccen wuri, kuma nesa daga duk wani abunda zai mata tasiri daga waje kamar iska ko qura ko wani abu makamancin haka har izuwa lokacin da allah zai yi izinin fitowarta, allah madaukakin sarki yana cewa: " ashe bamu halittaku daga wani ruwa wulaqantacce ba. * sannan muka sanya shi acikin acikin wani wurin nutsuwa amintacce. * zuwa ga wani gorgodon qaddara sananna.* sannan muka nuna iyawar mu? madalla damu, masu nuna iyawa." suratul mursalat aya ta20,21,22-23.
- kuma allah madaukaki ya bayyana cewa wannan halittar tana faruwa ne acikin duffai guda 3 acikin yanayi daban daban har zuwa yanayin qarshe da allah yaga dama sannan ya fitar dashi duniya, allah madaukakin sarki yana cewa: " yana halittaku acikin cikukkunan uwayenku, halitta a bayan wata halitta acikin duffai uku(50).