Allah mabuwayi mai daukaka ya bayyana mana haqiqannin duniya kuma ya bamu labari lallai ita duhu ce: allah madaukaki yana cewa: " ku sani cewa rayuwa duniya wasa ce da shagala da qawa da alfahari a tsakanin ku da gasar wadata ta dukiya da 'diya, kamar misalin shuka wadda yabanyarta ya bayar da sha'awa ga manoma, sannan ta qeqashe, har ka ganta ta zama rawaya, sannan ta koma rauno, kuma a lahira akwai azaba mai tsanani da gafara daga allah da yarda, kuma rayuwar duniya bata zama ba face 'dan jin da'din ru'di kawai." (72)، allah madaukaki yace: "saboda haka abunda aka baku ko menene to jindadin rayuwar duniya ne, kuma abunda ke wurin allah shine mafifici kuma shine mafi wanzuwa ga wadanda suka yi imani kuma suna dogaro da ubangijinsu (ka'dai)." suratul sura aya ta 36.
Allah madaukaki yana cewa: " ka buga musu misalin rayuwar duniya, kamar ruwa ne wanda muka sauqar dashi daga sama sannan tsirin qasa ya garwaya dashi sannan ya wayi gari dudduga, iska tana shiqarsa kuma allah ya kasance mai yawan ikon yine akan dukkan komai. * dukiya da 'diya sune qawar rayuwar duniya, kuma ayyuka masu wanzuwa na qwarai sun fi zama alkhairi awurin ubangijinka ga lada kuma sunfi alkhairi ga buri(73) .
Kasancewar duniya wulakantacciya ce shiyasa allah yah ore ma mumini da kafiri ita.allah mai tsarki da daukaka yana cewa: "kuma alokacin da ibrahim yace, ya ubangijina! ka sanya wannan gari amintacce ka azurta mutanensa daga 'ya'yan itacen, wanda yayi imani daga gare su da allah da ranar lahira, allah yace, wanda ya kafirta ma ina jiyar dashi da'di ka'dan, sannan kuma ina tilasta shi zuwa ga azabar wuta kuma makomar ta munana(74).kuma allah yana cewa: " dukkansu muna taimakon wa'dannan da wa'dancan daga kyautar ubangijinka, kuma kyautar ubangijinka bata kasance hananniya ba.* ka duba yadda muka fifitar da sashensu akan sashe! kuma lallai lahira ce mafi girman darajoji kuma mafi girman darajoji kuma mafi girman fifitawa(75)
kuma an kar'bo daga sahal (ra) yace: manzon allah (saw) ya wuce ta gaban wata mushen tunkiya sai yace: shin kuna ganin wannan tunkiyar wulaqantacciya ce ga ma'abotanta? sai sahabbai suka ce " ai saboda wulaqantacciya ce suka jefar da ita, sai manzon allah (saw) yace: na rantse da wanda numfashi na yake wajensa, duniya ita ce mafi wulaqantuwa a wurin allah akan wannan tunkiyar gs ma'abotanta, kai da ace duniya matsayinta ya kai kwatankwacin sauro da bai shayar da kafiri kur'bin ruwa 'daya ba(76).
kuma allah madaukakin sarki yana kwadaitar da mu dan gane da ranar lahira da ni'imomin ta, yana cewa: ba haka ba! kuna za'bin rayuwa ta kusa (wato) duniya * alhali lahira ita ce mafi alkhairi kuma mafi wanzuwa(77).kuma manzon allah (saw) yana cewa: " wallahi ita duniya ba komai bace akan lahira face kamar 'dayanku ya saka yatsarsa 'dinnan a kogi, sai ya duba da mai ta dawo?." muslim ne ya ruwaito.
lahira bata kasancewa (wato samun dacewa) sai dai wasu mafifita daga halitta wadanda allah ya yarda da su, allah madaukakin sarki ya fada: " to amma wanda yayi kyauta, kuma yayi taqawa * kuma ya gaskata kalma mai kyau * to zamu sauqaqe masa har ya kai ga sauqi * kuma amma wanda yayi rowa kuma ya wadatu da kansa * kuma ya qaryatar da kalma mai kyau * kuma zamu saqaqe masa har ya kai ga tsanani(78).
wannan baya nufi "arrahbaniyyatu" (shine barin jin dadin duniya da gujewa mutanenta) da barin dadda'da da dadda'dan abubuwan da allah ya halatta mana na daga abubuwan ci da sha da tufafi da kuma aure, allah madaukakin sarki yana cewa: " kace, wanene ya haramta qawar allah, wanda ya fitar saboda bayinsa, da masu da'di daga (abunda) ya azurtasu(79). kuma manzon allah (saw) yace: "mumini mai qarfi yafi alkhairi da kuma soyuwa zuwaga allah akan mumini mairauni amma acikin kowanne akwai alkhairi،kayi kwa'dayin abinda ke amfaninka kuma kanemi taimakon allah kada ka gajiya, kuma idan wani abu yasame ka kada kace inda na aikata abu kaza-kaza da zai kasance kaza, sai dai kace allah ne ya qaddara haka, kuma abunda yaga dama ya aikata, saboda lallai ita tana bu'de aikin she'dan(80).
abinda shari'a take nema shine tsaka-tsakiya a rayuwa, allah madaukakin sarki na cewa: kuma ka sanya hannunka ququntacce zuwa ga wuyanka, kuma kada ka shimfi'da shi dukkan shimfi'dawa, har ka zama abun zargi wanda ake yankewa(81)