musulunci ya zo da dukkanin ibadu na fadi da baki da kuma na aiki da kuma na qudircewa, ibadar fadi da baki da ta aiki ita ake cewa rukunan musulunci da su ne ake hukunta musulunci akan mutum daga barinsa, musulunci ba ya nufin kallafawa mabiyansa da wadannan rukunai iyaka alamura na fili kawai kadai dai ana nufin tsarkake zuciyoyinsu da kuma dai-daituwarsu da tsarkaketa ta hanyar yin wadannan ibadu, musulunci yana son yin wa'danan rukunai ya zama wata hanya don gyara alumma da dai-daita su, allah ta'ala yana cewa dangane da sallah: " lallai sallah tana hana alfasha da munana."
allah yana cewa dangane da zakka: " ka riqi sadaka (zakka) daga dukiyoyinsu, da zaka tsarkake su, ka tsarkake su daidai da ita." suratul tauba.
allah yana cewa dangane da azumi: "ya ku wad'anda kuka yi imani an wajabta azumi agare ku kamar yadda aka wajabta shi ga wa'danda suke gabanninku, ko zaku ji tsoron allah." suratul baqara aya ta 183.
allah yana cewa dangane da hajji: " hajji watanni ne sanannu, toh wanda yayi niyyar hajji to babu jima'i kuma babu fasqanci kuma babu jayayya acikin hajji." suratul baqara aya ta 197.
ibadu a musulunci ta na taka rawa a wajen assasa halaye na gari da kuma habbaka su, kuma yana mai kariya akan hadin kan alummar musulmi da kuma lura da shi.