shine muhammad 'dan abdullahi (s.a.w) na qarshen manzanni kuma cikamakinsu, allah yana cewa: " "muhammadu bai kasance uban kowa ba daga mazajenku sai dai shi ya kasance manzon ku kuma cikon annabawa." suratul ahzab aya ta 40.
allah ya aiko sa ga mutane duka ba iya larabawa ba kadai, allah yana cewa: " kuma bamu aiko ka ba face zuwa ga mutane gaba 'daya kana mai bushara da garga'di." suratul saba' aya ta 28.
allah ya aiko sa domin dacewa ga 'dan adam kuma don ya bayyana musu hanyar gaskiya da alkhairi kuma yayi musu gargadi da hanyar banza da sharri, allah yana cewa: bamu aiko ka ba face ka zama rahama ga halittu."
rayuwar sa (s.a.w) dukaninta gaskiya ce da amana, ba'ayi alqawari agareshi yayi yaudara ba balle qarya, ko ha'inci ko yaudara, an sanshi a tsakanin mutanensa da amintacce, sun kasance suna basa amanarsu, kuma suna basa ajiyar kayansu idan za suyi tafiya, an sanshi kuma acikin su da gaskiya, saboda abunda aka sani na gaskiya cikin abunda yake fa'da kuma yake labarta shi, yayin da aka sau'kar masa da wahayi na farko sai ya sanar da matarsa khadija allah ya yarda da ita, ya ce ma ta: yana jin tsoro kada ransa ya tafi, sai tace masa: a'a wallahi allah bazai ta'ba cutar da kai ba saboda kana taimakon gajiyayye, kana girmama baqo, kana taimakon gaskiya." bukhari ya ruwaito 3.
shine mafi cikar hali da kuma kyau, allah yana cewa: " kuma lallai haqiqa kana akan halayen kirki manya." suratul qalam aya ta 4