Mawallafi Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha د. عبد الرحمن بن عبد الكريم الشيحة



Yüklə 277,39 Kb.
səhifə4/44
tarix07.01.2022
ölçüsü277,39 Kb.
#80427
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   44
DALILAI AKAN SAMUWAR ALLAH

Lallai duk abinda yake cikin wannan halittar ta duniya yana nuni mai karfi sosai akan samuwar Allah madaukakin sarki, ta yadda babu wani yanayi da mutum zai iya shakkah acikinsu cewa akwai samuwar Allah, maabota lafiyayyen hankali da tinani tsaftatacce suna isa zuwa ga wannan dukkan wani isa, amman masu musun samuwar Allah suna neman wani dalili wanda suke ga zasu gani ko ji da kansu, kuma suna yima kansu tifka da warwara wajen domin su suna neman abubuwan zahiri kafin suyi imani da Allah, domin su sun yarda ne da abubuwan da suke iya gani a zahiri, kuma sunyi imani da magan’disu duk da cewa basu taba ganinshi ba, amman sunga alamunshi ta yadda yake jawo karfe zuwa karfe amman kuma basa ganin abinda ke jawosu din, haka kuma sunyi imani da samuwar hankali da tinani amman kuma basu taba ganinsu ba, saidai sunga alamunshi domin su wadannan abubuwan suna bayarda natija mara kyau wani lokaci wadda muke sanin hakikaninta ta hanyar hankali, misali shine muna ganin sanda acikin ruwa tana bayyana ne Kaman karyayya acikin ruwa, idan mutum ya hangota daga nesa, amman tinanin mu kodayaushe yana tafiya ne a sama ko munkasance a bangaren kudu, ko arewa ko kuma a tsakiya, duka wadannan surorin suna nuna cewa lallai da badan hankali ba da mun samu sakamako wand aba daidai ba maimakon mu samu sakamako na daidai, kuma da badan hankali ba da babu da masaniya akan komai, shin masu wannan tinanin sunyi daidai wajen da suka sanya cewa komai sai abinda mutum yake iya gani ko yake ji ?? kuma shin sunyi gaskiya yayinda suka ki yin imani da Allah akan dalilin cewa baa ganinshi ?? duk da cewa suma akwai abubuwan da sukayi imani dasu kuma basu taba ganinsu ba ??lallai neman dalilin yin imani da Allah ya nisantar da mutane da yawa daga sanin Allah ta hanyar yin tinani acikin halittunshi, Allah yana cewa: fir’auna yace yakai hamana ka ginamin gadoji domin naje sama, saman sammai domin naga ubangijin annabi musa domin ni lallai ina zatonshi ne daga cikin makaryata, hakane kuma aka kawata ma firauna munanan ayyukanshi kuma aka kareshi daga bin hanyar Allah, kaidin firauna bai kasance cikin komai ba sai ‘bata(32.)

Kuma hakan bai takaitu kawai akan wani zamani banda wani ba, ah ah lallai hakan dai al’ada ce ta wadanda basu yarda da Allah ba tin farkon duniya saboda jahilcinsu, Allah yana cewa: lallai wadanda basu da ilimi suna cewa me zai hana Allah ya musu Magana ko kuma wata aya tazo musu, hakan din ne wanda suka gabacesu suka ce, zuciyoyinsu sunyi kama da juna, hakika muna bayyanar da ayoyi ga mutane masu yaqini(33), ko ta sanadiyyar girman kai, Allah yana cewa: wadanda basa son haduwa damu suna cewa inama asaukar musu da mala’iku ko kuma anuna musu ubangijinsu, hakika sunyi girman kai kuma sunyi bijirewa iya bijirewa, a ranar da zasuga mala’iku babu wata bishara a ranan ga masu laifi saidai suce musu lallai hanuwar rahamar Allah a gareku(34).

To ta sanadiyyar zalinci, wannan kuma shine abinda yahudawa sukayi tin a zamanin da, Allah yana cewa: a lokacin da kuka ce yakai annabi musa bazamu taba yin imani dakai ba har sai munga Allah a zahiri, sai tsawa ta kamasu alhali suna masu kallo.(35)


Yüklə 277,39 Kb.

Dostları ilə paylaş:
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   44




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2025
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin