Kada ka bar wani bangare da shakku wajen neman wani karfi daka samu ko kuma kake kula dashi wajen tafiyar dashi, zai zama dayan abubuwa uku ne:
Kodai ya zama wannan duniyar itace ta samar da kanta, wannan tinanin kuma abune wanda bazai taba yuwuwa ba kuma bata ne tin daga asalinshi domin lallai duk wani abu yanada abinda ya samar dashi.
Ya kasance wannan duniyar akwai wanda ya samar da ita, kuma wannan abun ko dai ya zama shima acikin duniyar yake, wannan maganar kuma ko a hankalce baa bin yuwuwa bace, domin abu kafin a sameshi ba yadda zaayi ya halicci kanshi.
Ko dai ya zama wannan duniyar da abinda ke cikinta akwai wanda ya samar da ita kuma ba acikinta yake ba, kuma ya sabama ita duniyar, wanda wannan shine Allah madaukakin sarki, kuma wannan shine abind muminai sukai imani dashi, amman wasunsu daga cikin wadanda basu da addini suna shakkun hakan, Allah yana cewa: shin an haliccesu ne daga wani abu ko kuma sune sukai halittar, ko kuma sune suka halicci sammai da qassai, saidai basa samun yaqini, suratu door aya ta 37.