Mawallafi Dr. Abd Ar-Rahman bin Abd Al-Kareem Ash-Sheha


Rayuwar sa a doron duniya



Yüklə 241,3 Kb.
səhifə9/29
tarix05.01.2022
ölçüsü241,3 Kb.
#66966
1   ...   5   6   7   8   9   10   11   12   ...   29
Rayuwar sa a doron duniya:

Wannan itace mataki ta daukan nauyi na aikata ayyukan wajibobi wanda aka daura masa da kuma masa jarabawa ta yadda Allah madaukaki ya halittama mutum wasu gabbai na ji da gani da hankali wanda zai iya fayyace gaskiya da karya ta hanyar su da kuma sanin abubuwa masu amfani da masu cutar wa, Allah madaukaki yace: " Allah ya fitar daku daga cikin mahaifiyar ku baku san komai ba sai ya sanya maku ci da gani da tunani koda zaku gode masha (78) suratun nahli.

Ya haliccesa cikin sura me kyau ya kuma sanya masa wasu gabbai ajikin sa wanda yake amfani dasu wurin cin amfanin alheran wannan duniya ya kuma halitta masa wasu abubuwa cikin jikin sa wanda zasu gina masa jiki, Allah madaukaki yace: " shin baku gani ba cewa lallai Allah ya hore maku dukkanin abubuwan da suke cikin sammai da kassai ya kuma cika maku ni'imomin sa akanku na bayyane da na boye, daga cikin mutuane akwai wanda suke jayayya da Allah ba tare da ilimi ba ko wata dalili ko littafi me haske (20)" suratu lukman.

Kuma kasancewar Allah be halicce sub a face don su bauta masa ya kasance daga cikin tausayin say a aiko masu da manzanni ya kuma saukar masu da littattafai domin su bayyana masu yadda zasu bauta masa su kuma masu jagoranci zuwa ga hanyar gaskiya domin su bi wannan hanyar da kuma nuna masu hanyar sharri domin su guje shi, Allah madakaki yace: " bamu aiko da manzanni ba face dan su zama masu bushara da gargadi, duk wanda yayi imani kuma ya gyara to babu tsoro akan su kuma bazasuyi bakin ciki ba (48) suratul an'am.

Ya kuma halittama mutum wannan duniya da abunda ke cikinta ya kuma sawwake masa amfani dasu domin ya raya ta da shuka da noma da sana'a da dukkaknin wani hanyar rayuwa domin ya more mata ya kuma zama ya taimaka masa wurin bautan Allah da kadaita shi, Allah madaukaki yace: " shine wanda yasanya maku abubuwan da suke cikin kasa sawwake a gare ku, kuyi tafiya a doronta kuma kuci daga cikin arzikinta, kuma a gare shi zaku koma (15) suratul mulku.

Sannnan kuma domin duniya da abunda ke cikinta su kasance wuri yalwatacce domin mutum ya rika tunanin da izina cikin ikon mahaliccin sa sai hakan ya kara masa imani da gasgatawa, Allah madaukaki yace: " lallai acikin halittan sammai da kassai da jujjuyawan dare da rana da jirgin ruwan da yake tafiya a kan teku da abun da zai amfanar da mutane da abunda Allah ya saukar daga sama na ruwa wanda ya raya kasa dashi bayan kekashewarta da abunda ya watsa akanta na dukkanin ababen dake tafiya akanta da tafiyar da iska da girgije wanda yake kai komo tsakanin sama da kasa akwai ayoyi ga mutane masu hankali (164) suratul bakara.

Dalilan hankali wanda suke nuni akan lallai za'a tayar da mutane bayan mutuwar su a cikin alkur'ani:

Duba da cewa maganar tayar da mutane bayan mutuwa wacce ta girgiza da shagaltar da kwakwalen mutane, sai wanda imani bai shiga zuciyar sa ba yayi inkarin haka, alkur'ani ya bayyana cewa lallai wannan batu ba sabon abu bane hakan ya dade tun fil azal,sai Allah madaukaki yace: " wanda suka kafirta sunyi zaton cewa lallai fa baza'a tayar dasu ba bayan mutuwar su, kace masu bah aka bane ina rantsuwa da ubangijina sai an tayar dasu sannan kuma za'a baku labarin abunda kuka aikata hakan abune mai sauki agun Allah (7) suratul tagabun.

Hakika hujjojin da wanda suka karyata tayar da mutane bayan mutuwar su suke nema agun annabawan su wanda zai tabbatar masu da hakan abune wanda yake nuna girman kan su da alfahari idan bah aka bas u kalli yanayin halittan kawunan su kawai ya ishesu, Allah madaukaki yace: " idan ana karanta masu ayoyin mu bayyanannu basu da wani hujja sai fadin su cewa ku zo mana da iyayeyn mu idan kun kasance masu gaskiya (25) suratul jasiya.

Kasancewar karyata tayar da mutane bayan mutawar su hanya ce ta wasiwasi wanda shedan ke bi wurin canza mutane daga imanin su ya kasance dayawa daga cikin ayoyin alkur'ani suna kara tabbatar da hakikanin kasancewar Allah da ikon sa akan tayar da mutane sai su karama mutum kaimi wurin tunani akan asalin sa, Allah madaukaki yace: " mutum yana cewa yanzu idan mun mutu za'a tayar damu kuma darayukan mu (66) shin mutum bazai tuna ba cewa lallai mun halicce sa gabanin rashin kasancewar sa a bakin komai ba (67).

A cikin tunanin mutum da hankalin sa ya sani cewa duk wanda ya iya kirkiran wani abu to lallai yana da ikon iya kirkiran wanin sa- Allah shine mafi kyawun wurin kololuwan buga misali- wanda ya samar da mutum bayan babu shi yana da ikon ya sake tayar dashi ya dawo dashi bayan ya kasance mutum, Allah madaukaki yace: " shine wanda ya fara kirkiran halitta sa'annan zai dawo da ita wanda dawowa da itan yafi masa sauki akan kirkiranta, shine wanda yake da kololuwa wurin buga misali a sammai da kassai kuma shine mabuwayi me hikima (27) suratul rum.

Ayoyin alkur'ani sun iya su gamsar ga duk mutumin daya bashi da tsaurin riko na addini da hukuncin hankalin sa da zurfi wurin bin fidirar sada kuma nisantar da ita daga abubuwa masu tasiri na waje daga cikin wannan ayoyi akwai:



  • Tunanin asalin mutum da samuwar sat un farko duk wanda ya samu ikon halitta tun farko yanada ikon dawowa da ita, Allah madaukaki yace: " yanzu mutum baya ganin cewa lallai mu muka halicce sa daga maniyyi sai gashi ya zama me jayayya bayyananne (77) yana buga mana misali bayan ya manta halittan sa, yana cewa wanene zai raya kasha bayan ya dagwargwaje (78) kace masa wanda ya kirkira halittansa a farkon al'amari shine wanda zai rayashi bawan dagwar gwajewar sa, kum ya kasance masani game da kowace halitta (79) suratu yasin.

  • Tunana akan matakai na halittan mutum, Allah madaukaki yace: " mutum yana tunani cewa za'a barsa ne kara zube (36) ashe be kasance ba guda bane daga maniyyi wanda aka kiyaye (37) sa'annan ya zama gudan jinni sai aka halicce sa aka kuma daidaita shi (38) sai ya sanya ya zama mace dana miji (39) shin wanda yayi haka bashi da ikon ya tayar da matattu (40) suratul kiyama.

  • Tunani akan raya kasa kesashishiya ta yadda Allah ya fitar da tsirai daga gareta bayan ta kasance babu komai akanta babu wani alamar rayuwa tattare da ita, Allah madaukaki yana cewa: " daga cikin ayoyin sa zakaga kasa kesashashiya idan muka saukar da ruwa akanta sai kaga ta kunbura ta ta fashe ta fitar da tsirrai, lallai wannan wanda ya rayata zai tayar da matattu, lallai ya kasance me iko akan komai (39) suratu fussilat.

  • Tunanin cikin halittan wannan duniya da abunda ya kunsa wanda yafi girma ga al'amarin halittan mutum duk wanda ya halicce sa lallai bazai gazaba wurin tashin wanda suka mutu wanda idan basu wuce girman kwayar zarraba daga gareshi, Allah madaukaki yace: " shin basu gani ba cewa lallai Allah wanda ya halicci sammai d kassai wanda bai gajiba wurin halittan su cewa bashi da iko wurin tayar da matattu tabbas shi me iko ne akan komai (33) suratul ahkaf.

  • Tunanin baccin mutum da tashin cewa hakan mutuwa ce karama wacce rayuwa ke zuwa bayanta, idan haka ne mutuwar mutum itace mutuwa babba wacce itama rayuwa zai biyo bayanta, Allah madaukaki yace: " Allah shine wanda yake kasha rayuka da kuma wanda bata mutu ba a lokacin baccin ta, sai ya rike ran da aka rubuta mata mutuwa sai ya sake sauran rayukan zuwa wani lokaci sananne, lallai acikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani (42)" suratul zumar.

Sa'annan Allah ya bayyana wa masu karyata tashi bayan mutuwa wani abu na daban wanda zasu rika fankama shi wanda shine cikakken ikon sa wacce babu wani abu da zai gagareta wurin tayar da mutane baki dayan su bayan mutuwar su tun daga kan annabi Adam har zuwa tashin alkiyama acikin keftawan ido da umurni guda daya, al'amarin say a kasance idan yana son abu ya kasance ce masa yake kawai kasance sai ya kasance, Allah shine yake da mafi kololuwan misali, acikin rayuwan mu tayau zakaga ewa kana da iko da dan kwayar abu ka haskaka bigari guda daya baki dayan sa, Allah madaukaki yace: " halittan ku da tayar daku bai kasance ba sai kamar tayar darai guda daya ce, lallai Allah me ji ne kuma me gani (28) suratul lukman.

Ayoyin alkur'ani dukkanin su abun tunani ne akan su da lura da izina dasu kuma Allah yayi gaskiya day ace: " hakika mun saukake alkur'ani domin ayi zikiro dashi shin akwai me wa'aztuwa da hakan (40)" suratul kamar.




  1. Yüklə 241,3 Kb.

    Dostları ilə paylaş:
1   ...   5   6   7   8   9   10   11   12   ...   29




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin