Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə45/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   41   42   43   44   45   46   47   48   ...   51

Martani:

Kamar kullun, muna son malam zurqe ya gaya mana isnadin wannan labari, tare da kuma bayyana mana wanda ya inganta shi, in har akwai.

Daga cikin abin da ke tabbatar da kasancewar wannan labari nasa qarya, har da cewar da ya yi, wai Quraishawan da suka zo wannan yaqi da mutanen Kinanata da Tihama sun kai mutane dubu goma, waxanda suka haxa da Quraishawa da Kinanawa da mutanen Tihamata. Wannan itace qarya ta farko a cikin labarin. Domin kuwa abin da tarihi ya tabbatar na adadin dukkan qabilu, da suka haxa da waxancan mutanen da ya ambata, da mutanen Najadu wato Tamimawa da Asadawa da Gaxafanawa, da kuma Jama'ar Yahudawa, dududu adadinsu bai kai dubu goma ba. Kuma su qabilun nan qungiya uku ne da suka haxa da: Quraishawa da 'yan korensu, wato mutanen garin Makka da maqwabtanta. Sai kuma mutanen Najadu wato Tamimawa da Asadawa da Gaxafanawa da waxanda suka bi su don su sha miya. Qungiya ta uku kuwa ita ce Yahudawan banu Quraizata.

Bayan wannan qarya kuma, sai cewar da marubucin ya yi wai Amru xan Abdi wuddin da Ikramata xan Abu Jahali, sun hau dawa kansu suka fita ta wata kafa suka faxa cikin kadarkon. Bayan kuma wai sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya yi layya da Amru sai sauran mushrikan da Yahudawan suka watse nan take.

Wannan magana qarya ce da ximinta. Musulmi sun ci gaba da tsare mushrikai da Yahudawa bayan wannan lokaci. Har zuwa lokacin da Nu’aimu xan Mas'udu ya shigar da wata yaudara tsakaninsu, kuma Allah Subhanahu WaTa’ala Ya aika masu da iska mai tsananin gaske da Mala'iku daga sama, kamar yadda Allah Ta’ala ya ba mu labari in ya ce:

ﭽ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﭼ الأحزاب: ٩ - ١٢



Ya ku waxanda suka yi Imani! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da waxansu rundunoni suka zo muku, sai muka aika wata iska a kansu, da waxansu rundunoni waxanda ba ku gani ba kuma Allah Ya kasance mai gani ga abin da kuke aikatarwa.
A lokacin da suka zo muku daga samanku da kuma qasa gare ku, kuma a lokacin da gannai suka karkata, kuma zukata suka kai ga maqosai, kuma kuka yi wa Allah ‘yan zace – zace. A can ne aka jarrabi muminai, kuma aka girgiza su, girgiza mai tsanani.
Kuma a lokacin da Munafikai da waxanda akwai cuta a cikin zukatansu ke cewa "Allah da Manzonsa ba suyi mana alqawarin kome ba, sai ruxi (3379-12)

Har zuwa inda Allah Subhanahu WaTa’ala ke cewa:



Kuma Allah ya isar wa muminai daga yaqi (33:05).

Waxannan ayoyi na Alqur’ani da abin da ma'abuta ilimin hadisi da tafsiri suka tabbatar da kansacewarsa ta dubban hanyoyi lafiyayyu, a cikin littafan tarihi shi ne muminai ba su yi yaqi a wannan rana da kowa ba. Ba kuma ta hanyar yaqi ce Allah ya tunkuxe musulmi maqiya ba.

To, yaya da rana tsaka, wani zai zo ya gaya mana cewa, wai layyar da Ali Raliyallahu Anhu ya yi da Amru ce ta sa Mushrikai suka watse suna tavavvu.

Qarya ta gaba da wannan malam Zurqe ya yi a wannan hadisi ita ce: Cewar da ya yi wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Kashe Amru da Ali Raliyallahu Anhu ya yi, ya fi ibadar mutane da aljannu baki xaya. Wannan tatsuniya ce. Kuma Allah ya tsarkake littafan hadisi nagartattu daga hikaito irinta. Kai har a naxe qasa babu mahalukin da zai iya kawo maka isnadin wannan magana ko da mai rauni ne, balle ingantacce.

Saboda haka, ba ya halatta a jingini wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama irin wannan zulala.Ba kuma zai yiwu don mutum ya kashe kafiri xaya kowane iri ne, ya fi ibadar da mutane da aljannu ke yi wa Allah falala ba.
6.5.4 Gudunmawar Ali a Yaqin Banun-Nadhir

Xan Shi’ar ya ce: Sayyidina Ali ne Raliyallahu Anhu ya kashe wanda ya harbi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ga haqoransa na gaba, ya kuma kashe wasu mushrikai goma bayansa, sauran kuma suka ruga aguje, a ranar da aka yaqi Banun-Nadhir.


Martani

Muna nan akan bakarmu ta neman isnadi. Na farko kenan.

Na biyu: Wannan abu da ya faxa ba gaskiya ba ne. Malamai sun haxa a kan cewa, banun-Nadhir su ne waxanda Allah Subhanahu WaTa’ala ya saukar da Suratul Hashri a kansu. Banun-Nadhir kuwa qabila ce ta Yahudawa, waxanda labarinsu ya faru kafin yaqin Uhudu da na Taron Dangi. Babu kuma wani abu a cikin labarinsu da ke nuna cewa an kashe wani ko an jikkata. Babu kuma wanda ya riwaito koda hadisi xaya a lokacin cewa, an karya haqoran Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. in da aka karya masa haqora shi ne, lokacin yaqin Uhudu.

Iyakar abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da musulmi suka yi wa banun-Nadhir a wannan rana, tsare su da suka yi; tsarewa mai tsanani, suka kuma sassare itatuwan dabinnansu. Amma ba wanda aka kashe, ko cikin musulmi ko cikin Yahudawa.


6.5.5 Malam Zurqe ya Sake Fesa ta

Xan Shi’ar ya ce: A wani yaqi da aka yi mai suna Gazwatus-Silsilati wani balaraben qauye ya zo wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya masa cewa: Wata jama'a daga cikin Larabawa na can suna shirin su iske ka Madina don su gama da kai. Wai sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Wa zai xauki tuta ya jagoranci wannan yaqi? Sai Abubakar ya ce: Ni, ya Manzon Allah. Sai Manzon Allah ya ba shi tutar, ya kuma haxa shi da dakarunsa mutum xari bakwai. Yayin da suka isa wurin Larabawan sai suka ce wa Abubakar: Koma wurin mutuminka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ka gaya masa yawanmu ya fi qarfinku xin nan. Abubakar ya koma. Kashegari sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake cewa: Wa zai xauki tutata ya jagoranci wannan yaqi? Wai sai Umar ya ce: Ni, ya Manzon Allah. Manzon Allah ya danqa masa tutar. Abin da ya faru ga Abubakar shi ma ya faru ga reshi.

Sai a rana ta uku, Manzon Allah ya ce: Ina Aliyu? Ali ya karva masa: Ga ni, ya Manzon Allah. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya danqa masa tutar. Shi kuwa ya tasar ma Larabawan. Haxuwarsu ke da wuya bayan sallar asuba Ali Raliyallahu Anhu ya aika shida ko bakwai daga cikinsu lahira, saura kuma suka watse suna sambatu. Kuma, inji xan Shi’ar haka ce ta sa Allah Ta’ala ya rantse da wannan aiki na Sarkin Musulmi Ali inda yake cewa:

ﭽ ﮕ ﮖ ﮗ ﭼ العاديات: ١



Ina rantsuwa da dawa kai masu gudu suna fitar da kukan ciki (99:1).
Martani:

Idan wannan malami ya haxu da almaijrai, farkon abin da za su neme shi shi ne isnadi, don tabbatar da gaskiyar maganar in har akwai shi.

Idan kuwa ya faxa hannun malami, to zai tabbatar masa da cewa, gaba xayan abin da ya kawo na waxannan yaqe-yaqe, na daga cikin dangogin qarairayin da ‘yan xariqu ke watsawa irin na tarihin Antaru da Baxxalu da ire-irensu. Duk da kasancewar tarihin waxannan mazaje taqaitacce ne, kuma cikin cokali, musamman dai shi Baxxalu. Abubuwan da suka faru gare shi a zamanin daular bani Umayyata, da yaqin da aka fafata da Rumawa duk bai fi a rubuta shi cikin xan qanqanin littafi ba.

Amma sai ga shi albarkacin ire-iren wannan marubucin, tarihin ya cika kundaye da dama. Haka abin yake a cikin qagaggun labaran Shaddadu da Dunafi da Zaibaqul Misri da makamantansu. Kamar yadda suka qaga wasu tatsuniyoyi masu ban mamaki suka jingina su ga sarki Haruna Rashid da Abu Ja'afar Al-Mansur da sauran sarakuna.

Waxannan hikayoyi, na wannan yaqi da sauran tatsuniyoyi irin su idan aka xora su a ma’aunin hankali da ilimi ba in da za su je. Babu wani littafi na tarihin yaqe-yaqe ko tarihin rayuwar magabata sananne da ya ambaci wannan yaqi. Kamar yadda babu wani zaqaqurin malami a wannan fage da ya ambace shi, irin su Musa xan uqbata da Urwatu xan Zubairu da Imamuz Zuhuri da xan Ishaqa da makamantansu. Haka waqidi da Ibnu Sa’ad, da Yahayal Umawi da Walidu xan Muslim da Muhammadu xan A’izu da sauransu. Babu xaya daga cikin waxannan da ya ambaci wannan yaqi. Haka kuma babu wani hadisi da aka ambace shi a ciki. Ko wata aya da aka ce ta sauka a kansa.

A taqaice dai yaqe-yaqen da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi musamman waxanda aka yi taho mu gama da Mushrikai a cikinsu har aka rasa rayuka, sanannu ne, kuma shahararru a kunnuwan mutanen duniya. Malaman da suka san rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama fiye da yadda suka san ta uwayensu, sun tattara waxannan yaqe-yaqe sun adana. Kuma sun yi haka ne a kan kari. Ka ga kenan ba zai yiwu a ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yayi irin wannan yaqi na a zo a gani ba tare da waxannan malamai sun ambace shi ba. Kamar yadda ba za ta yiwu a ce an farlanta wasu salloli bayan biyar da aka sani ba, ko an farlanta wani azumi bayan na ramalana, ko ace ai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tava yaqar mutanen Farisa, daga can ya wuce Yaman, amma kuma duk malamai basu riwaito haka ba. To, wannan shi ne misalin wannan yaqi. Da hankali da shari'a duk baza su yarda da akwai wani abu da aka yi biris da shi a cikin tarihi irin wannan ba.


6.5.6 Gudunmawar Ali a Yaqin Banul-Musxalaq

Xan Shi’ar ya ce: kuma Aliyu Raliyallahu Anhu ya kashe Malik da xansa daga cikin banil-Musxalaq, ya kuma kama da yawa daga cikinsu, waxanda suka haxa har da Juwairiyyatu ‘yar Harisu wadda Annabi ya zava wa kansa. Ana haka sai ga mahaifinta ya zo a wannan rana ya ce: Ya Manzon Allah! xiyata mai girman daraja ta fi qarfin bautarwa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce shi da ya ba ta zavi: Sai ya ce: Kai, amma dai Manzon Allah ka kyauta. Daga nan sai ya juya kan 'yar tasa ya ce, ya ke 'yata kada ki kunyata danginki. Ita kuwa ta karva masa da cewa: Ni dai na zavi Allah da Manzonsa.


Martani:

Kamar kullum, ba za mu daina ba, muna neman isnadi. Don wannan ita ce hanyar kunyata duk wani maqaryaci.

Na biyu: Da zarar masana tarihi sun kalli wannan magana za su tofa mata yawu, su wurga ta kwandon shara, saboda warin qarya da take yi. Wannan labari na xaya daga cikin irin labaran da ‘yan Shi’ah ke qagawa. Babu wani malamin Sunnah da ya riwaito cewa Ali Raliyallahu Anhu ya aikata wannan abu a yaqin banil-Musxalaq. Ali a rannan bai kashe kowa ba. Ba kuma shi ne ya ribato Juwairiyya ba. Kuma asalatan mahaifinta bai tako qafa ba, balle har a ba ta wani zavi.

Amma in don yaqi da Banul-Musxalaq an yi shi, an kuma kama Juwairiyyatu cikin fursunonin yaqi, amma nan take ta nemi a yanka mata abin da zata biya don ta fanshi kanta. Aka yanka mata, sai kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya biya mata. Daga nan ta zama cikakkiyar ‘ya. Ganin haka kuma sai gaba xayan mutane kowa ya 'yanta bawan da ke hannunsa albarkacinta. Suna masu cewa: Ba za ta yiwu mu bautar da surukan Manzon Allah ba.


6.5.7 Ali a Ranar Haibara

Xan Shi’ar ya ce: Albarkacin Sayyidina Ali ne aka ci birnin Haibara. Da farko, Abubakar aka fara ba tutar jagorancin yaqin, sai ya kasa tavuka komai. Sannan aka ba Umar, shi ma ya kasa tavuka komai. Daga qarshe aka danqa ta ga Sarkin Musulmi Ali, ya fita ya yi yaqi mai tsanani, ya kashe na kashewa. Sauran suka nakkasa, sai kuka. Ya kuma yi wannan abin al'ajabi ne jim kaxan bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa addu’a a idonsa mai ciwo ya warke.

Bayan wannan nasara da Ali Raliyallahu Anhu ya yi wai, sai mutanen Haibara suka rufe masa qofar birni. Nan take Sarkin Musulmi ya valle qofar shi kaxai ransa. Ya kuma shimfixa ta a matsayin gada akan kadarkon can. Alhali kuwa qato ashirin ne ke rufe qofar da buxe ta. Ta haka, sai musulmi suka sami dannowa suka shiga birnin, suka kwashe ganimarsa. Wai kuma bayan haka ne Ali Raliyallahu Anhu yake cewa: “Wallahi ba don qarfin Allah ba, mutum xari biyar ba za su iya valle kofar ba”.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: “Haka kuma ta hanyar sayyidina Ali ne aka sami nasarar cin garin Makka.


Martani:

Allah ya la'anci maqaryata. Wa ya kawo labarin daga cikin malaman tarihi ko hadisi? Ina kuma isnadinsa da ingancinsa? Ko shakka babu wannan qarya ce zalla. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa ba rana xaya musulmi suka ci birnin Haibara da yaqi ba. Garin tunga-tunga ne. Haka aka rinqa cin su da yaqi guda-guda. Wasu kuma suka miqa wuya salun-alun. A qarshe kuma suka karya alqawarin da suka yi sulhu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kai.

Kuma Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma ba su yi qasa a guiwa ba a waxannan yaqe-yaqe. Sai dai cewa Aliyu Raliyallahu Anhu ya valle qofar birni, yana iya zama gaskiya, don an riwaito hakan. Amma ba a riwaito cewa, ya shimfixa ta a kan kadarko a matsayin gada ba.

Amma ko shakka babu cewar da xan Shi’ar ya yi wai albarkacin qwazon Ali Raliyallahu Anhu aka ci garin Makka da yaqi, qarya ce. Rawar da Ali Raliyallahu Anhu ya taka a cikin wannan yaqi, ba ta fi wadda sauran Sahabbai suka taka armashi ba. Shahararrun hadisan da suka yi magana a kan wannan yaqi na cin garin Makka sun tabbatar da haka. Kamar yadda suka tabbatar da cewa, sayyidina Ali ya yi qudurin kashe wasu surukai biyu na yayarsa Ummu Hani’i waxanda ta ba mafaka. Amma hakan ta faskara, saboda ta yi gaggawar kai qararsa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya sa hannu a kan mafakar da ta ba su. Kuma sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya yi niyyar auren ‘yar Abu Jahali Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fusata har ya yi magana a kan wannan, sai Ali ya janye wannan zancen.


6.5.8 Ali a Yaqin Hunainu

Xan Shi’ar ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita a ranar yaqin Hunainu tare da musulmi dubu goma. Wai sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi masu mugun baki, ya ce: Ba za a iya yin nasara a kan mu ba yau saboda yawanmu. Sai ga shi an yi nasara a kansu. Babu wanda ya rage tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai mutane tara daga cikin banu Hashim. Sai kuwa xan Umar Aiman. Shi kuma Sarkin Musulmi yana gabansa yana fama da takobinsa har ya kashe mutum arba’in. Ya kuma karya lagonsu.

Martaninmu a nan, bayan buqatar da muke da ita ta marubucin ya bayyana mana inda ya ji wai Abubakar ya yi wa musulmi mugun baki. Don ko ba wanda ya faxi wannan mugun lafazi na qiren qarya daga cikin littafan tarihin yaqe-yaqe ko na rayuwar musulmi, ko na hadisi ko tafsiri da makamantansu. Labarin da ya inganta game da wannan magana shi ne: Babu mai iya galaba a kanmu yau don ba rashim yawa. Kuma wasu ne daga cikin musulmi suka faxe shi ba Abubakar ba.

Haka kuma cewar da ya yi: Babu wanda ya rage tare da Manzon Allah daga cikin banu Hashim sai mutum tara, ita ma qarya ce. Kamar yadda kan malamai ma’abuta ilimin hadisi da tarihin yaqe-yaqe ya haxu a kan kasancewar Ali Raliyallahu Anhu ya kasance gaban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana fama da takobinsa har ya aika mutum arba’in lahira, qarya ce.


6.6 Kuma Wai, Ali ya San Gaibi

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta biyar ita ce hasashe-hasashen da Ali Raliyallahu Anhu ya yi a kan waxansu abubuwa kafin su faru. Kamar hasashen da ya yi na cewa, Xalhatu da Zubairu ba suna nufin tafiya aikin umarah ne ba, a lokacin da suka nemi yin haka daga gare shi. A inda ya ce masu: Wallahi ni, ina hasashen ba kuna nufin tafiya umara ba ne, kuna dai so ku yi amfani da wannan dama ne, ku tafi varna. Haka kuma ta kasance.

Watarana kuma yana zaune a wani wuri da ake kira Zi-Qarnin yana karvar mubaya’a, sai ya gaya wa jama’ar da ke nan cewa, wasu mutane dubu xaya ba daxi ba ragi za su zo maku, daga garin Kufa don yin mubaya’a gare ni a kan mutuwa. Haka kuwa ta faru. Kuma qarshen wanda ya zo daga cikinsu shi ne Uwaisul-Qarni. Haka kuma ya bayar da labarin za a kashe Zus-Sudayyah, kuma ta faru.

Kuma wai, wani ya bayar da labarin cewa, wasu mutane za su qetaro, a cikin labarin yaqin Naharawan. Ali ya ce: Ba za su qetaro ba. Wani kuma ya sake bayar da irin wannan labari. Ya sake cewa: ba za su qetaro ba. Kuma wallahi idan suka qetaro kwanansu ya qare. Haka kuwa aka yi. Kamar kuma yadda ya bayar da labarin shi kansa za a kashe shi, kuma hakan ta faru.

Haka kuma Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu wai ya gaya wa wani mutum da ake kira Shaharbanu cewa, wani la’ananne zai yanke qafafunsa da hannayensa ya kuma rataye shi. Sai ga shi kuma Mu’awiyah ya yi masa wannan aika-aika. Ya kuma labarta wa Misamu at-Tammaru cewa shi ne mutum na goma da za a rataye a lokaci xaya, a qofar gidan Amru xan Huraisu, ya kuma nuna masa wani guntun kututture na shi, da itaciyar dabino da za a rataye shi a kanta. Haka kuwa aka yi. Ya kuma gaya wa Rushaidu al-Hajri cewa, za a datse hannayensa da qafafuwansa da harshensa, a kuma rataye shi. Ta faru. Ya kuma labarta wa Kumailu xan Ziyad cewa Hajjaju ne zai kashe shi, ya kuma yanka Qambar. Sai kuma ga shi hakan ta kasance. Haka kuma ya faxa wa Bara’u xan Azibu cewa, za a kashe Hasan, xansa shi Ali, ba kuma za ka taimake shi ba. Ya kuma gaya masa inda kisan zai afku. Haka kuma ta faru; ba daxi ba qari.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, kuma wai Ali Raliyallahu Anhu ya bayar da labarin mulkin Banul Abbas, da kuma cewa Turkawa za su karve mulkin daga hannunsu. Ya qara da cewa: Mulkin Abbasiyyawa mulki ne mai sauqi da babu tsanani a cikinsa, ta yadda da Turkawa da Dilamawa da Indiyawa da Barbar da Xailasana sun taru ba za su iya karve shi ba. Amma haka za ta faru ne a lokacin da aka wayi gari sugabanni da barori daga cikinsu sun saki hanya, suka kama gabansu. Da zarar haka ta faru sai Allah Ya ba wani sarki na turkawa galaba a kansu. Wanda zai faro daga inda mulkinsu ya fara, yana tafe yana cin qasashensu xaya bayan xaya. Babu wata tuta da za a xaga sama don a yaqe shi face ya kave ta. Duk kuwa wanda ya sha gabansa kashinsa ya bushe. Haka zai ci gaba da tafiya har ya yi galaba a kansu har qarshe ya danqa kambun nasararsa a hannun wani mutum daga cikin zuri’ata, wanda ke faxin gaskiya yana kuma aiki da ita.

Xan Shi’ar ya kammala da cewa: haka kuwa aka yi. Don ana nan sai ga Hulaku ya bayyana daga wajen Khurasana daidai inda mulkin Abbasiyawa ya fara, har Abu Muslim al-Khurasani ya yi masu mubaya’a.
Martani:

Ko shakka babu, babu wanda ya fi Ali Raliyallahu Anhu cancanta da yin hasashe a kan wani abu da bai faru ba. Kai girman darajarsa ma ya wuce nan. Kai an samu ma daga cikin mabiyan Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma wanda ke iya hasashen fiye da haka ninkin ba-ninkin, balle Ali. Amma kuma hakan ba ta sa suka kasance daga cikin waxanda suka fi kowa cancantar sarauta ba. Kuma irin wannan baiwar ma gata nan ko a wannan zamani namu balle nasu.

A wancan zamani an samu cewa Huzaifatul-Yamani da Abu Hurairata da wasu daga cikin Sahabbai kanyi wa mutane ninkin waxannan hasashe-hasashe. Kuma har ma Abu Hurairata kan tuqe isnadinsu zuwa ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama irin abin da Huzaifata ya yi, da ya kawo isnadinsa.

Akwai littafan karamomin waliyyai da labaransu da dama da aka wallafa, kamar littafin Zuhudu na Imamu Ahmad, da Hilyatul Auliya’i na Asfahani, da Sifatus-Safwati na Ibnul Jauzi, da Karamatul Auliya’i na Khallal, da irinsa na Ibnu Abid Dunya, da na Lalaka’i. Duk a cikinsu akwai karamomin manyan waliyyai, cikinsu har da mabiyan Abubakar da Umar, kamar Ala’u xan Hadrami, gwamnan Abubakar da wasu da dama waxanda in ana maganar sayyidina Ali su sha’aninsu bai ma taka karya ya karya ba. To, ina wata hikima ga kafa hujja da irin waxannan karamomi akan cancantar shugabanci?

Kuma labaran nan da ya kawo babu wanda yake da isnadi bale mu yanke masa hukunci. Amma kuma daga cikinsu akwai waxanda muke da yaqinin ingancinsu, akwai kuma waxanda ba mu iya tabbatar da kasancewarsu gaskiya ko qarya.

Amma dai ita cewar da ya yi Ali ya yi hasashen za su danqa kanbun nasararsu ga wani mutum daga cikin zuri’arsa, qarya ce kawai ya yi wa Ali Raliyallahu Anhu wadda ya xauko ta daga na baya-baya cikin malamansu.

Haka kuma jin da waxansu Gulatu ke yi na cewa Ali Raliyallahu Anhu ya san duk abin da zai faru gobe da jibi, ba tare da wata iyakancewa ba, shi ma qarya ne. ko wani sashe na gaibi bai sani ba balle dukansa. Sanin gaibu sai Allah!
6.7 Ana Karva Addu’ar Ali

Xan Shi’ar ya ce hujja ta shida ita ce: Aliyu ya kasance abin qarva wa du’ai. Ya roqi Allah ya karve hankalin Busra xan Arxa’ata. Aka kuwa sa masa tavin hankali. Haka kuma ya roqi makanta ta sami Aizaru, ta kuma same shi xin. Ya kuma roqi kuturta ta kama Anas a lokacin da ya voye imaninsa, ta kuma same shi xin. Kamar yadda ya roqar wa Zaidu xan arqamu kuturta shi ma, ta kuma same shi.


Martani:

Marubucin ya sani akwai daga cikin Sahabbai wanda ya yi wa Ali Raliyallahu Anhu fintinqau a wannan fage. Haka kuma an samu daga cikin tabi’una masu irin wannan karamar. Za’a kuma ci gaba da samun irinsu matuqar akwai mumini a bisa doron qasa. Sa’adu xan Abi waqas bai tava roqon Allah ba face Allah ya karva. Ya zo a cikin Buhari cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya roqa masa Allah da cewa: “Ya Allah ka datar da duk harbin da zai yi, ka kuma karvi duk du’ain da zai yi”. Haka kuma ya zo a cikin Sahihu Muslim cewa Umar ya aika wani mutum zuwa Kufa don ya tambayo masa labarin Sa’ad, a lokacin yana gwamna. Sai ya taras cewa mutane na faxin magana mai kyau game da shi. Amma wannan mutum bai qare rangadi ba sai da ya kai ga wani mutum daga cikin Bani Absu. Da ya tambaye shi labarin Sa’ad, sai ya qarva masa da cewa: Ai ba ya fita yaqi, ba ya kuma kula da talakawa, ba ya rabo dai dai. Da Sa’ad ya ji haka sai ya roqi Allah da cewa: “Ya Allah, idan ka san abin da wannan ya faxi a kaina qarya ce, amma ya yi don mutane su gani su yabe shi. To, ya Allah ka tsawaita rayuwarsa, ka kuma tsananta talaucinsa ka kuma sa fitina ta yi masa zoba.

Sai ga shi wannan mutum tsufa ya ci shi har ga qashi, har idanunsa sun yi kwarmi. Yana biyar kuyangi yana bobowa a kan hanya, yana cewa: Allah ne ya jarabce ni da haka sanadiyar mugunyar addu’ar da Sa’ad ya yi a kaina.

Duk da rashin isnadin da waxannan qissoshi da xan Shi’ar ya jingina ga Ali, akwai abubuwan da babu kokwanto akan kasancewarsu qarya! Kamar mugunyar addu’ar da ya ce ya yi wa Anas da kuturta, da makanta da ya ce ya roqa ma Zaidu xan Arqam.


6.8 Wata Hujjar Banza

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: hujja ta bakwai ita ce: a lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya fuskanci siffin, sai qishirwa ta riski jama’arsa a kan hanya. Sai ya ce su xan ratse kaxan. Ratsewarsu ke da wuya sai suka hangi wani xan gidan bauta. Sai suka qwala ma wanda ke cikinsa kira, suka tambaye shi ko Allah ya sa yana da xan ruwa? Sai ya ce masu ina! Ai tsakanina da ruwa ya kai tafiyar kwana biyu ga mai tafiya qasa. Ba don da ya kasance ana kawo mani xan wanda zan tsotsa ba kowane wata, da qyar in ga qarshensa, ai da qishi ya kashe ni. Sai kawai Sarkin Musulmi ya nuna wani xan wuri kusa da cocin, ya ce a tona shi. Ana tonawa sai ga wani fandun getso, aka yi aka yi a xauke shi aka kasa. Nan take Ali Raliyallahu Anhu ya sa hannu shi kaxai ransa ya ije shi, sai ga ruwa. Suka sha suka yi tanqal.

Qarewarsu ke da wuya, inji xan Shi’ar, sai wannan malamin kiristan ya faxo, ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu: Lallai na tabbata ko dai kai Annabi ne, ko kuma wani babban mala’iki a faxar Allah. Sai wai Ali Raliyallahu Anhu ya ce masa: A’a, babu ko xaya. Illa dai ni ne wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar wa wasiccin halifancinsa in ya wuce. Nan take wai sai malamin ya musulunta a hannun Ali. Sai kuma ya ce, haqiqa wannan coci daman an gina ta ne a kan sunan wanda zai valla wannan fardun getso, wanda kuma zai fitar da ruwan da ke qarqashinta. Kuma an yi malamai da dama a gabanina, amma ba su riske ka ba. Kuma a qarshe dai wannan malami ya yi shahada tare da shi Sayyidina Ali.

Sannan xan Shi’ar ya ce, Sayyid Al-Himyari ya waqe wannan labari na Ali.


Martani:

Wannan qissa ko shakka babu tana xaya daga cikin qarairayin da jahilai ke tsammanin su wani abu da ke bayyana darajar Ali Raliyallahu Anhu. Alhali kuwa ba haka abin yake ba. Hasali ma duk wanda ya qirqiri wannan qarya ya jahilci matsayin Ali Raliyallahu Anhu da darajojinsa, balle ya san irin abin da ya dace a jingina gare shi na yabo da gwarzantawa. Da ya sani da bai danganta xaukakar Ali Raliyallahu Anhu ga nuna fandun getso ba, da fitar da ruwa a qarqashinsa ba.

Irin wannan ba wani abin godogo ba ne, don ya sha samuwa ga wasu halittu da yawa, waxanda darajarsu ba ta kama ko qafar ta Ali Raliyallahu Anhu ba. Kamar yadda ta sha faruwa har ga wasu daga cikin masoya Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum. Fiye ma da irin wannan. To, babban abin mamaki ma da la'akari shi ne, da a ce faruwar irin waxannan gamdakatar ya taqaita ne ga sauran mutane, sai a ce wata ni'ima ta karama ce daga wurin Allah. To amma, sai ka taras hakan ta faru har a cikin waxanda ba salihai ba.

Shi kuwa sauran abin da ke cikin wannan qissa, kamar cewar da ya yi wai malamin ya ce: An gina wannan coci a kan sunan wanda zai tona fandun getso ya kuma fitar da ruwa a qarqashinsa. Wannan ba al'adar musulunci ce ba, balle Ali ya xaukaka da ita. Coci-coci ne da wuraren bautar Yahudawa da na masu bautar addinin kakanni ake ginawa a kan sunayen waxanda suka qaga su. Amma su musulmi ba su gina wuraren ibadarsu wato masallatai, waxanda Allah ya yi kira a xaukaka a kuma inganta don ambaton sunansa kawai a ciki, sai a kan sunan Allah. Ba dai a kan sunan wani abin halitta ba.

A qarshe kuma ita ma cewar da ya yi wai Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Shi ne wanda Manzon Allah ya bari ya gaje halifarsa bayan ya wuce, qarya ce yake yi wa Ali. Domin kuwa ta tabbata Ali Raliyallahu Anhu bai tava furta wannan magana ba da xai; ko a zamanin halifofi uku kafinsa, ko a kwanukan yaqin siffin.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   41   42   43   44   45   46   47   48   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin