Tafarkin sunnah


Wai Ali ya yi Yaqi da Aljannu!



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə46/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51

6.9 Wai Ali ya yi Yaqi da Aljannu!

Xan Shi’ar ya ce hujja ta takwas ita ce: Abin da malaman Sunnah suka riwaito cewa, a lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita zuwa yaqin Banil-Musxalaqu, dare ya yi masu a kan hanya, a kusa da wani kwazazzabo mai zurfi. Kwaram, sai ga Jibrilu Alaihis Salam ya sauko ya gaya wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, akwai wasu Aljanu da suke zaune a wannan kwazazzabo, kuma suna shirin cutar da shi da Sahabbansa. Nan take sai Manzon Allah ya kira Aliyu ya yi masa addu'a ya kuma umurce shi da kutsawa cikin kwazazzabon, ya kuwa kutsa ciki, ya kashe Aljannun.


Martani:

Martaninmu a nan shi ne: Abu na farko dai, matsayin da Ali ke da ya fi qarfin wannan abu ya zama wani abin alfahari gare shi, ko da hakan ta tabbata. Domin kuwa an samu cewa wasu da ba su kai darajarsa ba ma sun yi irin wannan aiki. Amma kuma tattare da haka, wannan hadisi na xaya daga cikin hadisan qarya waxanda aka jingina ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali kamar yadda malamai masana hadisi suka tabbatar. Babu kuma wani abu mai kama da haka da ya faru a yaqin Banul-Musxalaq.

Kuma cewar marubucin wai malaman Sunnah ne suka riwaito wannan hadisi. Idan yana nufin cewa, an riwaito hadisin ne ta wani isnadi tabbatacce, ko a cikin wani littafi da ake iya dogara da kasancewar kawai ya riwaito abu, ko wani wanda aka yarda da shedunsa a kan hadisi ya inganta shi. To ba haka ba ne. Haka ma in yana nufin mafi rinjayen malamai sun riwaito shi. Duk wannan qarya ne. Amma idan yana nufin wani daga cikin waxanda hujja ba ta kafuwa da abin da suka riwaito, ya riwaito shi; to, babu wata fa’ida da hakan ke iya tabbatarwa.
6.10 Rana ta Sake Hudowa Saboda Ali!

Xan Shi’ar ya ce hujja ta tara ita ce: Sake hudowar da rana ta yi har sau biyu saboda buqatar Ali Raliyallahu Anhu ga hakan. Na farko a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Na biyu kuma bayan rasuwarsa.

Xan Shi’ar ya ce: Na farko, ya faru ne kamar yadda Jabir da Abu Sa’id al-Khudri suka riwaito cewa, watarana Malaika Jibrilu ya sauka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama don ya gana da shi a kan wani muhimmin batu daga wurin Allah. A lokacin da gahin wahayi ya buge Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai san lokacin da ya jefa kansa a kan qafafun Aliyu Raliyallahu Anhu ba. Bai kuma farfaxo ba, sai bayan da rana ta faxi. Ala tilas Ali Raliyallahu Anhu ya sallaci La’asar daga zaune yana mai nuni don ba ya iya sauke Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga jikinsa. A lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya farka, sai ya umurce shi da cewa: Ka roqi Allah ya sake dawo maka da rana don ka sallaci La’asar xinka a tsaye. Nan take kuwa ya roqi Allah, sai ranar ta sake hudowa ya yi sallar a tsaye, inji xan Shi’ah.

Na biyu, kuma inji shi, ya faru ne a lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya ke qoqarin qetare tekun Furata a Babila tare da jama’arsa. A daidai lokacin da wasu daga cikin jama’arsa ke can suna fafutukar qetarewa da dawa kai, sai Ali Raliyallahu Anhu ya yi sallar tare da wasu daga cikin jama’a. Mafi yawansu kuma ba su samu yin sallar ba. daga qarshe suka yi qorafi a kan haka. Ganin haka sai wai, Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya roqi Allah ya sake dawo masa da rana. Ya kuwa yi hakan. Kamar yadda al-Himyari ya waqe wannan labari.


Martani:

Martaninmu a nan shi ne: Muna fatar xan Shi’ar ya fahimci cewa martabar Ali Raliyallahu Anhu da xaukakarsa a wurin Allah Subhanahu WaTa’ala da kasancewarsa masoyi a wurinsa, abu ne sananne ta hanyoyi tabbatattu, waxanda qwaqqwaran ilimi ya tabbatar, ta yadda ba sai an qara masu gishiri da irin qarairayi marasa tushe ba.

Ba mu musun cewa, akwai wasu malamai da suka riwaito wannan hadisi na sake hudowar rana ga Ali Raliyallahu Anhu irin su Xahawi da Alqali Iyal da wasunsu, waxanda suka kuma lissafa al’amarin a jerin karamomin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Amma malamai masu darajar tankaxe qwaya daga tsakuwa a fannin ilimin hadisi, sun tabbatar da cewa, wannan hadisi matsayin tatsuniyar Gizo da Qoqi ya ke. Kamar yadda malam Ibnul Jauzi ya ambaci hadisin a cikin littafinsa Al-Maudhu’at (Gizo da Qoqin Hadisai). Ya kuma ce: Ko shakka babu wannan hadisi qarya ce. Kuma masu riwayarsa sun rikirkita a wajen riwayar tasa.

Ita kuwa qissa ta biyu da marubucin ya ce ta faru a Babila, ko shakka babu qarya ce. Waqen kuma da Himyari ya yi ba ya zama hujja. Ko banza ba a gaban idonsa aka yi ba. Ya taras da an kitsa qaryar ne tsawon shekaru, shi kuma ya waqe ta. Kuma dama irinsa shahararren xan ta’adda ne, mai wuce gona da iri.

Kuma duk wanda ya bari sallah ta kubce masa, bai yi ta a kan lokaci ba; ba dalilin zaune ba na tsaye, to, babu abin da ke karkare zunubinsa sai tuba. Idan ya tuba kuma babu buqatar ya ranka ta. Wannan wanda ya yi sakaci kenan. Amma idan ba sakaci ya yi har sallar ta wuce shi ba, kamar ya kasance bacci ne ya kwashe shi ko mantuwa ta xibge shi har lokacin sallar ya fita, to babu wani laifi a kansa don ya sallace ta bayan faxuwar rana. Ba ya buqatar a dawo masa da ita.

Irin waxannan mas’aloli masu girma, waxanda ba a al’adanci faruwarsu ba, da sun faru kuwa, to, kusan kowa na qoqarin a ji su ga bakinsa saboda kasancewarsu a kan kari. Idan aka taras cewa mutum xaya ne ko biyu kacal suka riwaito su, kuma ga su ba amintattu ba, to, ba sai an tafi da nisa ba, an san shegiyar ce; ‘yar gida Musailamu.


6.11 Wata Kuma Mu’ujizar Sayyidina Ali!

Xan Shi’ar ya ce hujja ta goma ita ce abin da ma’abuta tarihi suka riwaito na cewa, watarana ruwa ya yi ambaliya a garin Kufa, hankalin mutane ya tashi. Suka yi gudun ruwan ya ci su. Sai suka sheqa wurin Sarkin Musulmi Ali. Nan take Ali ya hau jakar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita tare da jama’a. da suka isa gavar tekun Furata, sai ya sauka ya yi sallah, ya yi addu’a, ya kuma daki ruwan da wata sanda da ke hannunsa. Nan take sai ruwan ya faxa. Sai kuma wani nau’i na kifayen da ke ciki suka kai gaisuwa gare shi. Sauran nau’o’an kuma ba su ce masa ko qala ba. Jama’ar da ke tare da shi suka tambaye shi dalilin haka. Wai sai ya karva masu da cewa: Kifayen da Allah ya nufa suka gaishe ni, su ne Allah ya tsarkake. Su kuma waxanda Allah ya hukunta da zamansu najasa, abin nisantawa sune suka yi biris da ni.


Martani:

Da farko dai, mun gaji da hattara sa, ina qaho? Marubucin ya kawo mana isnadin wannan qissa, wanda zai nuna tabbatuwa da ingancinta. Idan kuwa ba zai iya ba, to, ya sani fa duk wata hikaya; “Qwai ba zakara” abu ce da kowa ma ke iya samarwa. Amma hakan ba zai iya fa’idantar da komai ba.

Abu na biyu kuma shi ne: Jakar Annabi ba ta tava kasancewa hannun Ali Raliyallahu Anhu ba. Idan baka sani ba, to ka sani.

Abu na Uku kuma shi ne: Babu wani marubuci abin dogaro da ya riwaito wannan hikaya. Da kuwa qissa ce ingantatta, da an sami mazaje da dama sun riwaito ta a kan kari. Amma kuma sai ga shi marubucin bai ambaci isnadin qissar ba. To, ta yaya kuwa za a saurari huntuwar riwaya, don kawai wani ya ambace ta a cikin rubutunsa.

Abu na huxu kuma: Babu wani nau’i na kifi wanda ba halas ba a ci shi a shari’a. Don ta tabbata cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ruwan gulbi mai tsalki ne, kuma mataccen namansa halas ne”. Kuma Allah Ta’ala ya ce: An halatta maku farautar ruwa da abincinsa, domin jin daxi a gare ku, kuma domin matafiya (5:96). Haka kuma magabata daga cikin Al’umma da manyan malamai sun haxu a kan cewa, naman gaba xayan nau’o’an kifi halas ne. Ali Raliyallahu Anhu kuma na tare da sauran Sahabban da suka yarda da hakan. Ka ga ba ta yiwuwa ya ce wani najasa ne, wai, don bai gaishe shi ba.

Amma ba mamaki, kasancewar ‘yan Shi’ah Jahilai shi ya sa suke haramta abin da Allah ya halatta, ta hanyar qirqira irin waxannan hikayoyi.


6.12 Ali Bai Buqatar Irin Wannan Al’amara

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha xaya ita ce, abin da masana tarihi da yawa, suka riwaito cewa: Watarana Ali Raliyallahu Anhu na huxuba a kan mimbari a Kufa, wai sai ga wani maciji jan-nasuru ya bayyana, ya kuma xaura anniyar hawan mimbarin da Ali ke a kai. Mutane suka firgita, sai suka yi ca! Su kashe shi. Sai wai Ali Raliyallahu Anhu ya hana su. A qarshe dai suka tattauna da macijin, sannan ya sauko ya tafi abinsa. Daga nan sai mutanen suka tambayi Ali Raliyallahu Anhu labarin macijin. Sai ya ce masu: Ai sarkin Aljannu ne, wata qissa ta rikice masa, shi ne na wayar masa da kansa a kai. Daga nan sai mutanen Kufa suka raxa wa qofar da macijin ya biyo suna “qofar maciji”. Wai, daga baya ne da Umawiyyawa suka so bice wannan falala ta Ali Raliyallahu Anhu sai suka jibge wasu gawawwaki a qofar har tsawon wani lokaci, har sunanta ya koma “qofar Gawa”.


Martani:

Ko shakka babu akwai mutane da dama waxanda ba su kai darajar Ali Raliyallahu Anhu ba, aljannu kan kai wasu buqatu irin na neman fatawa a wurin su. Wannan kuma ba tun jiya kawai ba, har ma yau. Idan ma har ta tabbata hakan ta faru, to, ai darajar Ali Raliyallahu Anhu ta wuce nan. Domin kuwa daraja ce da ake iya samu ga wanda ma bai kai xaukakarsa ba. Idan kuwa hakan ba ta faru ba, darajar Ali ba za ta rage da komai ba Raliyallahu Anhu.

Amma fa babu wanda ke buqatuwa zuwa ga tabbatar da xaukakar Ali Raliyallahu Anhu ta amfani da irin waxannan tatsuniyoyi sai wanda bai tava gani ko jin faruwar irin waxannan karamomi ga wani ko wasu ba. Wanda ya zauna da nagartattun mutane masu riqo da addini, waxanda fiye da irin wannan karama ta gudana gare su, ko kuma ta tava kasancewa ga shi kansa fiye da haka. Duk wanda ya shedi xaya daga cikin waxannan abubuwa ba zai ji wannan qissa ta xaga darajar Ali Raliyallahu Anhu da komai ba.

7.0 Zango na Bakwai

Dalilan Shugabancin Sauran Imamai

Cikon Sha Biyu
7.1 Samun Nassi a Kansa

Xan Shi’ar ya ce: Fasali na huxu a cikin shugabancin sauran imaman da suka rage daga cikin sha biyu. Mun sami wannan hujja ta hanyoyi da dama. Hanya ta farko ita ce “Nassi” wanda ya yaxu ya zama gama-gari a duniyar Shi’ah, suka gaji saninsa ta hanyar kunne ya girmi kaka cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Husaini: “Wannan Imami ne xan Imami, xan’uwan Imami kuma baban Imamai tara. Na taran nasu shi ne jigonsu. Sunansa kamar sunana ne. Kuma laqaninsa irin nawa. Zai cika duniya da adalci kamar yadda zai tarar an cika ta da zalunci da babakere”.


Martani:

Za mu mayar da martani a kan wannan magana ta fuskoki da dama kamar haka:



Fuska ta farko: Muna da tabbacin wannan qarya ce ya ke ma ‘yan Shi’a. Domin kuwa wani yanki ne kawai na ‘yan Shi’ar suka yarda da wannan magana ba dukansu ba. A yayin da sauran rassa na Shi’ah ke fito-na-fito da ita. Ka ga dai wannan magana ko ga qarya ba ta kai ba a idon ‘yan Shi’ah Zaidiyyah. Su ne kuwa mafiya hankali da ilimi a cikin rassan Shi’ah. Su ne kuma zavavvu a cikinsu. Haka abin yake a wurin Shi’ah Isma’iliyyah.

A taqaice, Shi’ah na da rassa da yawa qwarai. Manya kuma daga cikinsu sun fi ashirin. Kuma gaba xayansu, idan ka xebe Isna- ashariyya, wato, ‘yan-sha-biyu, babu reshen da bai qaryata wannan magana ba. To, ina zancen zama gama-gari a duniyar Shi’ah?



Fuska ta biyu: Wannan magana ta yi taho-mu-gama da wasu Nassosa da, rassan Shi’ah waxanda ba ‘yan-sha-biyu ba, ke riwaitowa, waxanda ke walwale ta. Kamar waxanda suka aminta da cewa, wanda ba daga cikin sha biyun ba, na iya shugabanci. Ko abin da ‘yan Rawandiyyah suka riwaito. A taqaice, duk abin da waxannan rassa suka tafi a kai, a kan wannan mas’ala, ya sava wa wancan da su ‘yan-sha-biyu ke qoqarin tabbatarwa.

Fuska ta uku: Muna tabbatar wa da wannan xan Shi’ar cewa, babu wani magabaci daga cikin magabatan Shi’ah da ya riwaito wannan magana cikin wani littafi nasa, ko ya kafa hujja da ita a cikin wata huxuba. Tarihin kuwa ba voye yake ba. Wannan magana da yake qoqarin wa duniyar musulmi a yau, daga baya ne suka qaga ta, bayan rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da fiye da shekara xari biyu da hamsin. Sun qirqira wannan qarya ne a daidai lokacin da wanda suka ce shi ne imamin na sha xaya, Hasan xan Aliyu al-Askari ya rasu. Sai suka ce wai, yana da xa Muhammad wanda ya yi dibilwa, kuma shi ne magajinsa. Na sha biyu kenan. To, a lokacin ne wannan tatsuniya ta fara bayyana.

Fuska ta huxu: Gaba xayan Ahlus-Sunnah da malamansu, waxanda adadinsu ya ninka na ‘yan Shi’ah ninkin-ba-ninki, na da masaniya tsattsagagga wadda kokwanto ba ya iya girgizawa, a kan cewa wannan magana qarya ce aka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Suna kuma qalubalantar ‘yan Shi’ah da kiran su zuwa ga mubahala a kan haka. Kamar yadda sauran rassan Shi’ah ke kiran ‘yan-sha-biyun zuwa ga haka. Da kuma malaman Shi’ah za su buga kai ga qasa su ce, lalle su, suna da masaniya a kan tawaturancin wannan magana, to, wannan masaniya tasu ba ta kama qafar wadda malaman Sunnah ke da ita ba a kan kasancewar wannan magana qarya.

Fuska ta Biyar: Ba a cewa magana ta zan mutawatira (gama-gari) sai ya kasance an sami waxanda ake iya karvar maganarsu a matsayin ilimi, a dama da hagu da kuma tsakiyarta. To, ita wannan magana ta rasa ko xaya. Don kafin rasuwar Hasan al-Askari babu wani da ke furta zancen Malam-na-Voye (Mahadi) a matsayin shugaba. Haka kuma babu wani ma da ke magana a kan shugabancin wasu Imamai goma sha biyu. A zamanin halifancin Ali Raliyallahu Anhu babu wannan magana. Haka ma zamanin Umawiyyawa. Waxanda ma ke zancen wannan shugabanci a lokacin suna raya cewa ne akwai nassi da ke tabbatar da shugabancin Ali Raliyallahu Anhu ne shi kaxai.

Amma iqirarin cewa akwai Nassi da ke tabbatar da shugabancin Imamai goma sha biyu da maganar “Malam-na-Voye”, ba a sami wani mutum xaya da ya faxe ta ba a kwanakin farko, balle haka ta zama riwaya mai tushe.



Fuska ta Shida: Masu ilimi na da yaqinin cewa farkon lokacin da Shi’ar ‘yan-sha-biyu ta bayyana, mutanen da ke jin cewa, akwai nassi a kan shugabancin waxancan mutane, shi ne qarshen kwanakin Halifofi shiryayyu. Wanda kuma ya qirqira wannan qarya shi ne Abdullahi xan Saba’i tare da qungiyarsa ta maqaryata. Amma kafin wannan lokaci ko vurvushinsu babu.

Fuska ta Bakwai: Hadisan da Sahabbai suka riwaito a kan darajoji da martabobin Abubakar, Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum sun fi wannan nassi, qarfin tabbata a idon jahilai ma kafin malamai. Idan kuwa har zai halatta wani ya dubi waxannan riwayoyi na Sahabbai, a kan darajojin waxannan mutane ya yi suka a ciki, to yin suka a cikin wannan riwaya ta farko ya fi halatta. Idan kuwa akwai wani uzuri da har za a iya yi wa wanda ya soki riwayar Sahabbai, to kuwa yin sa ga wanda ya soki riwayar wani shi ne mafifici.

Fuska ta takwas: Babu wani mutum xaya daga cikin Shi’ah ‘yan-sha-biyu da ya riwaito wannan magana ta hanyar isnadi mai sadadden asali, balle har ya zama mutawatiri. Kuma ko da an same su, to lalle ne ya kasance sun hardace wannan nassi. Kafin su iya yin haka kuwa dole ne sai sun ta maimata shi. To, muna son xan Shi’ar ya faxa mana waxanda suka hardace wannan lafazi na wannan nassi, kamar irin yadda ake hardato lafuzzan Alqur’ani, da na kalmar shahada da na kiran sallah, tsara bayan tsara har zuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Lalle ne kuma wanda zai kawo xin, idan har akwai su su kasance adadi mai yawa, don daxa tabbatar da ma’anar tawaturanci.

Domin mu, a duk lokacin da muka yi iqirarin wanzuwar tawaturanci a cikin wasu darajoji na Sahabbai, to a wasu lokuta, mukan bayyana irin yadda tawaturancin nasu ya tabbata ta fuskar ma’ana, kasancewarsu ba su da waxansu lafuzza da ke da buqata da a riwaito su ta wata kevantattar siga, balle har a buqaci daddaqe su har a hardace; kamar tawaturancin da ya tabbata a kan halifancin halifofi huxu, da yaqin barasar Raqumi da na Siffin, da Auren Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Nana A’isha da na Sayyidina Ali da Fatima. Da makamantan haka.

Akwai ma lokacin da mukan tabbatar da tawaturancin a cikin lafuzzan wasu riwayoyi, waxanda ake iya riqon maganar waxanda suka hardace su a matsayin limi.

Faska ta Tara: Dukkan riwayoyin da aka riwaito daga Ahlul- Baiti, masu tawaturi, sun qaryata wannan riwaya taku. Babu xaya daga cikinsu wadda ke nuna cewa, akwai wani nassi a kan waxancan Imamai. Hasali ma dai su da kuke ce ma Imaman, suna qaryata ku ne, ballantana su tabbatar maku da nassin shugabancin “Sha-biyu”.
1. Hadisin Mahadi

Xan Shi’ar ya soma da kawo wani hadisi da ke cewa: An samo daga xan Umar daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama: “Wani mutum zai bayyana a qarshen zamani daga cikin zuri’ta; sunansa xaya da nawa, kuma laqabinsa xaya da nawa. Zai cika duniya da adalci. Wannan shi ne Mahadi”.


Martani:

Hadisan da ake kafa hujja da su a kan bayyanar Mahadi ingantattu ne. Abu Dawuda da Tirmizi da Ahmad da wasunsu duk sun riwaito su, ta hanyar Ibnu Mas’ud da waninsa.

Kamar faxar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin hadisin da Ibnu Mas’ud ya riwaito cewa: “Ko da rana xaya za ta rage wa duniya, sai Allah ya tsawaita wannan rana har wani mutum ya bayyana daga Jinina, ko daga cikin mutanen gidana, sunansa zai dace da sunana. Na mahaifinsa kuma ya dace da na mahaifina. Zai cika duniya da adalci da raba daidai, kamar yadda a ka cika ta da zalunci da babakere. Akwai hadisin harwayau a cikin littafin Tirmidhi da Abu Dawuda ta hanyar Ummu Salamata Raliyallahu Anha.

Daga cikin waxannan hadisai kuma akwai wanda abu Dawuda ya riwaito ta hanyar Abu Sa’id wanda ke cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mahadi na daga cikin tsatsona, a layin ‘ya’yan Fatima”. A cikinsa kuma ake cewa: “Zai mallake duniya cikin shekaru bakwai”.

Abu Dawudan dai harwayau ya riwaito shi daga Ali Raliyallahu Anhu cewa, watarana ya kalli Hasan sai ya ce: “Wannan xan nawa zai zama shugaba, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce. Kuma wani mutum zai fito daga tsatsonsa, wanda za a kira da sunan Annabinku. Zai kuma yi kama da shi ga halaye, amma ba zai yi kama da shi ga halitta ba, zai kuma cika duniya da adalci”.

To, ka ji hadissan. Amma Allah ne kaxai ya san iyakar taunar karan shanun da aka yi wa waxannan hadisai. Wasu suka kore su gaba xaya. Suna hujja da wani hadisi da ke cewa wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Babu wani Mahdi in ba Isah xan Maryamu ba”. Wannan ko hadisi ne mai rauni da ke cikin Musnad na Shafi’i.

To, sannan su ‘yan-sha-biyu da ke iqirarin cewa, mahdinsu ne na voye waxannan ingantattun hadisai ke nufi, sun manta sunan Mahdinsu: Muhammadu xan Hasan. Shi kuwa wannan Mahadi da Annabi ya bayar da labarinsa tare da siffanta shi, suransa muhammadu xan Abdullahi.
7.2 Samuwar Ma’asumai a Kowane Zamani

Xan Shi’ar ya ce abu na biyu da ke tabbatar da shugabancin sauran Imaman shi ne; mun riga mun bayyana cewa wajibi ne a sami Imami ma’asumi a kowane zamani. An kuma yi ijma’i a kan babu wasu ma’asumai bayan waxancan Imamai.


Martani:

Mun riga mun rosa yankin maganarsa ta farko, cewa lalle ne a sami ma’asumi a matsayin Imami, kowane zamani. Ko ma ko a cikin ‘yan Shi’ah an samu waxanda suka tafi a kan cewa waxancan imamai nasu ba Ma’asumai ba ne.

To, sannan a yau shekarar wannan ma’asumi, da suke ta quzamin zai bayyana, fiye da xari huxu da hamsin da haihuwa, kamar yadda suke tabbatarwa kuma wai ya shige ne cikin wani kogo mai dausayi a qarqashin qasa a shekara ta 260H, a lokacin yana xan shekara biyar da haifuwa. Wasu daga cikinsu kuma suka ce bai kai haka ba. Amma duk da waxannan zunzurutun shekaru, har yau tsit kake ji kamar an shuka dusa; babu wani abu na amfani ga jama’a, irin wanda shugabanni da alqalai da malamai ke gudanarwa da ya tava bayyana daga gare shi, wanda ke iya tabbatar wa duniya ko ma dai mabiyansa kawai, cewa, lalle dai akwai shi. Balle har a wayi gari a ce ya taka wata rawa daga can voye irin wadda shugaba ma’asumi ya kamata a ce ya taka. To, a irin wannan hali, ko da ta tabbata cewa akwai shi xin, me ye amfanisa? To, balle daxa idan dama babu shi!
7.3 Darajojin Imamai Goma Sha biyu

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta uku ita ce, darajojin da kowane xaya daga cikinsu ke da, irin waxanda ke tabbatar da zamansa Imami.


Martani:

Qololuwar abin da waxancan darajoji ke iya tabbatarwa shi ne cancantarsu ga zama Imamai. Amma ba za su iya tabbatar da kasancewarsu imaman ba. Kamar yadda kasancewar mutum ya cancanci zama alqali, ba tana nufin ya zama alqali ba, har sai in naxa shi.

Kuma ta tabbata cewa, akwai wasu daga cikin Quraishawa waxanda suka cancanci zama imamai, kamar yadda cancantar waxancan ta tabbata. Ka ga su ma waxannan Quraishawa suna zama imamai kenan don wannan cancanta? Mafi yawan masu hankali sun gamsu da cewa shi Imamin nasu na sha biyu Amaryar Boqo ne. A haka kuwa, babu ta yadda za a yi ya zama imami sai fa in a kan mutanen voye!.

Wasu cikin Imaman nasu, musamman na sha xaya da na sha biyu, ba wanda ya san su da wani ilimi ko riqo da addini irin wanda aka san saura da shi kamar Aliyu xan Husaini da Abu Ja’afar al-Baqir da Ja’afarus Sadiq da makamantansu. To, ta ina suka cancanta?


8.0 Zango na Takwas

Ayubban Sauran Halifofi, Inji Shi

Xan Shi’ar ya ce: Fasali na biyar: Duk wanda ya yi halifanci kafin Ali Raliyallahu Anhu ba halifa ba ne ta fuskoki da dama.


Martani:

Idan xan Shi’ah na nufin musulmi ba su karvi waxancan halifofi uku a matsayin shuganni ba, ba su kuma yi masu mubaya’a ba, balle su sami wata dama ta zantar da hukunce-hukuncen shari’ah kamar haddi da sauransu, da tabbatar da cewa kowa ya sami haqqinsa. Kuma musulmi ba su yi yaqi a qarqashin jagorancinsu ba, ba su kuma yi sallolin jam’i da na idi a bayansu ba, ko waxansu abubuwa daban-daban, waxanda kalmar shugabanci ke tabbatarwa. Idan wannan ne abin da xan Shi’ar ke nufi, to, ya sha qarya. Kuma abin da ya yi xin nan girman kai ne. Tabbatuwar waxannan abubuwa da ya ke qoqarin korewa, abu ne sananne ta hanyoyin da suka fi yawan shurin masaki. ‘Yan Shi’ah da sauran qungiyoyin bidi’a ba wanda bai san haka ba. Kuma ai kasancewar shugabancin waxancan halifofi ga musulmi ya karva sunansa, shi ya sa ‘yan Shi’ah ke sukar su.

Kuma wani babban kuskure da suke yi shi ne, kodayaushe sai su yi ta yanke hukunci wane shugaba ne, wane ba shugaba ne ba, a dunqule; ba tare da sun yi bayani ba. Shin idan suka ce wane shugaba ne, suna nufin naxin da aka yi masa da ayyukan da ya gabatar, ko ko a’a, suna nufin ya cancanta ya zama shugaba ne kawai koda ba a naxa shi ba?

Wata irin wannan kuma sai ka taras suna amfani da kalmar “Imamu” ga wanda suka qudurce cancantarsa kawai. Amma kuma a kaikaice, sai su nuna wa duniya cewa, kalmar ta haxa cancanta da naxi da gudanarwa. Ka ji kai!

To, a taqaice idan ‘yan Shi’ah na nufin Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum sun zama halifofi ne kawai ba tare da sun dace ba. Aliyu Raliyallahu Anhu ne ya dace. Ko ko a’a, sun dace amma Aliyu ya fi su dacewa da ita. To wannan qarya ce. Kuma wannan fage ne na qwanciqwalinto.

Saboda haka, za mu iya basu amsa a kan wannan batu; a dunqule, kamar yadda suke yi, sannan kuma mu zo mu warware masu zare da abawa.

A dunqule, muna iya cewa: Ahlus-Sunnah na da masaniyar cewa, shugabancin da waxancan halifofi suka yi, sun yi shi ne a kan dacewa da cancanta. Wannan masaniya kuwa da muke da ita kamar yankan wuqa take. Ta yadda ba za ka taras da mutum biyu daga wasu qungiyoyin musulunci na gardama a kanta ba, sai fa idan akwai xan Shi’ah a cikinsu.

Qarewa da qarau ma, mafi yawan malaman wannan al’umma cewa suke yi Abubakar da halifofi biyu bayansa su ne mafi cancantar mutane da shugabanci a lokacin da suka yi shi. Sukan ma take kwano, su ce: Kai mu a saninmu babu wanda ya kai gare su a girman daraja cikin wannan al’umma baki xaya.

To, kuma ina son xan Shi’ar ya sani cewa, babu wani dalili qwaqqwara, kai ko ma mai rauni da za a zo mana da shi wanda zai tayar da mu daga wannan tantagaryar masaniya da muke da ita. Domin kuwa qwararan dalilai ba su kau da juna balle xaya ya farke wa xaya laya. Shi kuwa mai rauni ba ya iya komai da qwaqqwara irin wanda ke hannunmu.

Wani abin kuma shi ne, duk abin da xan Shi’ar ko wani mai suka, zai zo da shi a kan shugabancin waxannan halifofi uku, to, ba ya fita daga xayan abubuwa biyu: Ko dai ya zama riwaya ce wadda ba ingantatta ba. Ko kuma mu leqa shi mu kasa ganin abu xaya da ke iya tabbatar da rashin ingancin shugabancin nasu, a cikinsa. Da zarar kuwa hujjojin nasu suka kasa fita wannan qangi, to, ba za su iya ruguza taron haxin guiwar masaniya da ke hannunmu ba.

Da zarar kuwa irin wannan dalili yankakke ya tabbata, a kan dacewar halifofin da shugabancin, kamar yadda ya tabbata a wurinmu, to, babu buqatar sai mun ci dugadugan sauran qyaleqyalin da suka yi wa qaryar. Tsayawa bayar da amsa a kan waxannan wofintattun Shubuhohi, bayan an rosa ginshiqansu, vata lokaci ne.

Babu wani mutum da ke iya rosa masaniyar da aka sakankance da ita, alhali makamin da ke hannunsa sungumin ragga ne kawai. Kasancewarsa mai kai kora, ko wanda ake kawo wa ba za ta daxa shi da komai ba. Amma a matsayinsa na mai kariya, idan ya gama gane varnar da ke cikin shubuhohin, ya kuma sanar da wani, to, ya bunqasa iliminsa, ya kuma taimaki gaskiya ga duk mai nemanta ta hanyar fira ko tattaunawa. Idan kuwa har bai gano varnar da ke cikin shubuhar ba, wadda take matsayin gaskiya a wurin mai ita. To, shakkar da ke tare da shi ba za ta iya tunkuxe ta ba. Idan an biyo mu a hankali za mu faxi dalilai masu yawa a kan cancantar halifofin nan guda uku, da kasancewarsu sun sha gaban kowa a fagen cancantar, in Allah ya so.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin