Tafarkin sunnah


Abubakar da Manzon Allah a Ranar Badar



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə51/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51

9.12 Abubakar da Manzon Allah a Ranar Badar

Xan Shi’ar ya ce: Babu wata falala ga Abubakar a cikin kasancewarsa tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin dabi ranar yaqin Badar. Domin kuwa hakan ba ta daxa Manzon da komai ba, saboda ba ya da buqata da wani ya xebe masa kewa. Saboda wadda yake xebewa tare da Ubangijinsa ta ishe shi.

Ya kuma ci gaba da cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zaunar da Abubakar ne a wurinsa, don gudun ya tura shi fagen fama ya dagula al’amurra. Don yana da tarihin gudowa daga yaqoqa daban-daban, inji shi. To, ka auna ka gani, wane ne mafi girman daraja, tsakanin wanda ke rafke da hannuwa alhali ga mazaje can na rafkewa, da wanda ke can ana goga qashi da shi don xaukaka kalimar Allah?!
Martani:

Wannan maganar da shehin ya furta ba a kan hanya take ba. Cewar da ya yi, Abubakar Raliyallahu Anhu na da tarihin gudu daga fagen fama a yaqoqi daban-daban, ya tabbatar da cewa, bai san tarihin yaqe-yaqen da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ba.

Yaqin Badar shi ne yaqi na farko a tarihin musulunci. Kafin sa babu wani yaqi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko Abubakar suka yi da kafirai. To, a wane yaqi ya gudu kenan kafin Badar? To, ko a yaqin Badar ma da duk yaqoqan da aka yi a bayansa, ba inda Abubakar bai je ba, ba kuma inda aka bada rahoton ya yi raki, balle ya juya baya. Ko a ranar yaqin Uhudu, shi da Umar tsaye suke qyam kamar iccen giginya. Wanda dai ya shiga sahun waxanda suka firgita a ranar, jin cewa, Annabi ya mutu kamar yadda shexan ya yaxa, shi ne Usman. Kuma Allah ya gafarta masu. Amma Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma ba a sami wani malamin tarihi da ya tava cewa, suna cikin waxanda yaqi ya ci a ranar Hunainu ba. Hasali ma su suka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ganbun tsari dama da hagu a wannan rana.

Da ta tabbata cewa, Abubakar matsoraci ne, kamar yadda wannan xan Shi’ah ya bayar da rahoto, da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai zave shi don ya zauna tare da shi a cikin dabin ba. Domin kuwa ba ya halatta a tafi yaqi tare da wanda yake haka. Ga al’ada kuma duk wanda zaka gani kusa ga uban tafiyar yaqi, lalle za ka taras da shi namijin gaske, wanda bai san tsoro ba. To, balle wanda aka zava daga cikin dubu aka ce ya zauna tare da shi.

Duk wanda ya san tarihin musulunci ya san cewa zuciyar Abubakar Raliyallahu Anhu ta fi ta sauran Sahabbai faxi da qarfi. Tun lokacin da aka aiko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Abubakar yake tsaye tsayin goxiyar Adamu, a cikin cikar jaruntaka da saxaukantaka, yana gumurzu da wahalhalu, har Allah ya karvi ransa. Ba a tava jin lokacin da ya yi raki ko qasa a guiwa gaban maqiya ba. Hasali ma lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwanta dama, sai da zukatan wasu Sahabbai suka girgiza, hantarsu ta kaxa, cikannansu suka xuri ruwa, Abubakar ne ya yi musu ganxo da yardar Allah. Haka yake a duk sauran wurare da rakin wasu daga cikinsu ya bayyana. A cikin ire-iren wannan halin ne Anas Raliyallahu Anhu ya ce: “Abubakar ya yi mana huxuba a lokacin da muke kamar kuraye. Bai gushe ba yana qarfafa mu har muka koma kamar zakoka”.

An kuma riwaito cewa, watarana Umar Raliyallahu Anhu ya ce wa Abubakar: Ya halifan Manzon Allah! Ka yayyafa wa mutane ruwa. Sai Abubakar ya kama gemun Umar ya ce, me kake tsoro bayan ka musulunta, ina jaruntakar da kake da ita a zamanin jahiliyya?! Don me zan yayyafa masu ruwa; don qaryace-qaryacen da suka watsu a tsakaninsu, ko don waqe-waqen jahiliyyah?!

Ya ci gaba da cewa wai, ba a haxa wanda ke zaune rafke da hannuwa, alhali maza na can na rafkewa, da wanda ke can ana rafkewar da shi don xaukaka kalmar Allah.

Ba haka abin yake ba. Kasancewar Abubakar tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan yanayi, ya fi shiga cikin filin daga. Domin kuwa,Manzon ne qarshen wanda maqiya ke son su kai ga. Saboda haka ne kashi xaya daga cikin uku na musulmi suka tsaya gadinsa, xaya kashin suka fatattaki maqiya, a yayin da sauran suka tattara ganima. A qarshe kuma Allah ya raba ta a tsakaninsu baki xaya.

Sai kuma cewar da ya yi wai, kewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke xebewa da Ubangijinsa ta wadatar da shi daga buqatar wani abokin xebe kewa.

Abin da za mu ce a nan shi ne, ai wannan magana ba ta ko taso ba. Domin kuwa maganar ba ayar Qur’ani ba ce ko hadisi, balle xan Shi’ar ya yi qoqarin juya akalarta ko qaryata ta. Koda ko waxanda suka faxi wannan magana, ba suna nufin kasancewar Abubakar tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin dabin ta xebe kewar hira ce ba. A’a, suna nufin yana ba shi gudunmawa ne a cikin sha’anin yaqin da ke gudana kamar yadda sauran Sahabbai ke can kowa na bayar da tasa gudunmawa.

Idan ka fahimci abin haka, wannan matsayi da Abubakar ya kevanta da shi daraja ce da babu wanda ya samu irinta daga cikin Sahabbai. Domin babu kowa tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai shi. A yayin da ita ko waccan daraja da Aliyu Raliyallahu Anhu ya samu ta kasancewa cikin fagen fama, duk Sahabin da ke tare da shi a can ya same ta.

Ta kuma tabbata cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Abubakar Raliyallahu Anhu sun fito daga cikin dabin, har Annabi ya harbi abokan gaba, harbin da Allah Ta’ala ya kwarzanta da cewa: Kuma baka yi jifa ba a lokacin da kayi jifa; kuma amma Allah ne ya yi jifar 8:17. Haka shi ma Siddiqu ya fatattake su, har ma bayan qare yaqin xansa Abdurrahmanu ya ce masa: “Ai na gan ka ranar yaqin Badar amma sai na lave don kar ka gan ni”. Sai Abubakar ya ce masa: “Ka kuru! Da na gan ka sai wani ba kai ba”.



9.13 Abubakar ya yi Hidimar Manzo da Dukiyarsa

Xan Shi’ar ya ce: amma cewar da Ahlus-Sunnah suka yi, wai Abubakar ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama hidima da dukiyarsa, ta hanyar xaukar nauyinsa, qarya ne. domin kuwa Abubakar ba mai arziki ba ne. Hasali ma mahaifinsa talakka ne na qarshe, ta yadda kullum sai ya roqo mudu xaya daga Abdullahi xan Jud’ana kafin ya sami abin da zai sa ga baki. Da kuwa Abubakar na da dukiya, da ya xauki nauyin mahaifin nasa. Ko a lokacin jahiliyyah yara yake karantarwa. Da musulunci ya bayyana kuma sai ya kama sana’ar xunki. Bayan ya zama Sarkin Musulmi ne mutane suka hana shi wannan sana’a, suka yanka masa albashin dirhami uku kowace rana daga cikin baitul-mali don ya ci da iyalinsa.


Martani:

Haqiqa babu zalunci da qiren qarya kamar mutum ya musa abin da duniya ta gama sani, littafan hadisi da na tarihi da tafsiri da ire-irensu suka cika maqil da bayaninsa. A lokaci guda kuma ya yi qoqarin tabbatar da wasu riwayoyi waxanda daga bakinsa ne aka fara jin su, kuma babu wata madogara da ya ambata mai qwari balle a ji sanyi.

A irin yadda wannan magana take, ko mafi jahilci ya turke xan Shi’ar yana iya tabbatar masa da zamanta qarya, da kasancewar abin da muka faxa a matsayin masu tattaunawa da shi, gaskiya. Ina mamakin yadda mutum zai jajirce yana yayata labarin da ba ya da tushe. Idan kuma har xan Shi’ar na ganin abin da muke faxi sharholiya ce, to, ya faxa mana wani amintaccen malamin hadisi ko tarihi da ya riwaito wannan magana da shi ya faxa a kan Abubakar.

Zancen kuwa hidimar da Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta dukiya, abu ne ingantacce, da riwayoyi suka tabbatar ta hanyoyi da fuskoki da dama. Har Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasa barin abin a zuci ya ce: “Babu dukiyar wani da ta amfane ni kamar dukiyar Abubakar.” Ya kuma tava cewa watarana: “Mafificin wanda ya amfanar da mu da kansa da dukiyarsa shi ne Abubakar”. Haka kuma ta tabbata cewa, Abubakar ya fanshi wasu bayin da ba za su kasa mutum bakwai ba daga hannun kafirai, waxanda ake azabtarwa saboda imaninsu da Manzo, cikinsu har da Bilal da Amiru xan Fuhairata.

Ita ma maganar talaucin mahaifin halifa Abubakar da ya yi ba ta da asali. Koda kuma a qaddara ta inganta ba ta cutar da kome, domin gaba xayan al’amarin ya faru ne a zamanin jahiliyyah. Kuma Abdullahi xan Jud’ana ya rasu ne kafin bayyanar musulunci. Shi kuwa abu Quhafata mahaifin na Abubakar ba a tava sanin yana roqo ba. ga shi kuma mutum mai wadatar zuci, domin ko lokacin da xan nasa halifa Abubakar ya cika, kuma aka ba shi kashi xaya cikin shida na dukiyarsa a matsayin gado gaba xaya ya mayar da ita ga ‘ya’yan na Abubakar.

Cewa, Abubakar malamin ‘yan yara ne a lokacin jahiliyyah, abu ne da ke qara fitowa da xaukakarsa, tare da bayyana irin ilimin da yake da shi tun a wancan lokaci, idan har maganar ta kasance gaskiya. Duk da yake ‘yan Shi’ah kamar mushrikan zamanin jahiliyyar Larabawa su ke. Kullum alfahari da tinqahonsu bai wuce asali da girman iyaye, ba addini ba. saboda haka za ka taras kodayaushe, duk abin da za su yi wa wani gori da shi ba abu ne da zai nuna naqasar imani ko tsoron Allansa ba. wannan kuwa al’ada ce irin ta jahiliyyah.

Ita kuwa cewar da ya yi wai, Siddiqu ya kama sana’ar xinki bayan bayyanar musulunci har zuwa lokacin da ya zama halifa. A nan ma dai ya fesa ta. Duk da yake ko ta kasance gaskiya babu wani abin kunya ciki. Amma dai tarihi bai ambaci Abubakar ya tava sana’ar xinki ba. Abin da kawai aka sani shi xan kasuwa ne. Wani lokaci har ya kan bar gari ya tafi Sham don cin kasuwa. Wani lokaci kuma kasuwancin nasa kan daxe bai kai shi ga barin gari ba. Wannan kuwa abin alfahari ne, domin babu wata sana’a mai kadari a wajen Quraishawa da bayyana xaukakar mai yin ta kamar kasuwanci. Duk wani shahararre cikinsu a layin dukiya, zaka iske xan kasuwa ne, kuma da wannan sana’a ne suka shahara a duniya.

Gaskiya ne, bayan kasancewar Abubakar halifa ya so ya ci gaba da sana’a, amma ba ta xinki ba. Kasuwancin can dai ne nasa ya so ya xore da shi don nema wa iyalinsa abincin halas. Musulmi a lokacin suka ce atabau. Shugabanmu a kasuwa?! To, yaushe ya samu lokacin kula da ingancin rayuwarmu? Suka taru suka hana shi. Sannan suka haxu a kan yanka masa albashin da aka faxa.

Haka kuma xan Shi’ar ya ce, wai kafin hijirar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa Madina, ya wadata da dukiyar Khadijatu Raliyallahu Anha kuma babu yaqi a lokacin. Saboda haka ba ya da buqata da abin hannun wani balle a ce Abubakar ya agaza masa.
To, ai ciyarwar da ake cewa Abubakar ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ba ana nufin yana sai masa abinci ko sutura ne ba. Ta wannan vangare gaskiya, Allah ya riga ya wadatar da Manzonsa daga kowa. A’a, ana nufin ne Abubakar ya ciyar da dukiyarsa wajen hidimar bunqasa addinin musulunci don taimaka wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama isar da saqo. Saboda haka ya yi hidima ne don tabbatar da abin da Allah da Manzonsa ke so, ba don buqatun Annabi na qashin kansa ba. A wannan tafarki ne wannan tafarki ne ya fanshi Bialau da xan Fuhairata da Zinirratu da wasu da yawa, daga azabar da mushrikan Makkah ke yi musu.

Abu mafi ban ta kaici ma a cikin maganar xan Shi’ar duk bai fi cewar da ya yi wai, bayan hijira ma Abubakar fanko ya ci gaba da zama ba. Ta tabbata har zuwa wannan lokaci Abubakar na hidimar dukiya ga musulunci. Akwai watarana ma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwaxaitar da Sahabbai yin sadaqa, nan take Abubakar ya je ya kwaso gaban dukiyarsa da ke hannu ya kawo. Haka kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tava yekuwar agaza wa mutanen Suffa kamar yadda ya zo a cikin Buhari da Muslimu daga Abdurrahaman xan Abubakar. Nan take Abubakar ya tafi da uku daga cikinsu, shi kuma uban tafiyar Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwashi goma.

Wani abin ban mamaki ma da ta kaici duk bai fi cewar da xan Shi’ar ya yi wai, da Abubakar ya yi irirn waccan hidima ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da lalle surar Alqur’ani ta sabka akan ta. Kamar yadda aka saukar da Surar Hal Ata a kansayyidina Ali Raliyallahu Anhu.

To, ka ga wannan magana ba gaskiya ba ce a wurin malaman hadisi. Amma marubutan tafsiri masu kwasar karan mahaukaciya ba a mamaki don sun ambace ta. Kuma ai waccan sura da yake magana a Makka aka saukar da ita, dalilin da ke bayyana qissar da suka jingina ga surar kitsa ta aka yi.

Muna da tabbacin cewa, ba wata sura ko wata aya da ta tava sauka don Ali ya ciyar da wani miskini ko makamancinsa, domin kuwa ba ya da sararin yin haka, musamman a lokacin da ake Makka sa’adda yake cikin gandun iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Manzon ke kula da su. A Madina kuwa, sanannen abu ne cewa, ko a lokacin aurensa da sharifiya Fatima bai samu wani sukunin yin wata hidima ba, don ba ya da kome a lokacin sai sulke.

Amma Abubakar Siddiqu, babu wata aya da ta sauka tana yabon waxanda suka ciyar da dukiyarsu saboda Allah, face shi ne farkon wanda take nufi. Kamar inda Allah ke cewa:

ﭽ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﰄ ﰅﰆ ﭼ الحديد: ١٠

Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara, kuma ya yi yaqi daga cikinku, ba ya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). Waxancan ne mafifita girman daraja bisa ga waxanda suka ciyar daga baya kuma suka yi yaqi.. 57:10

Ta kuma tabbata Abubakar ne na farko kuma mafifici.

Haka nan ita faxar Allah Ta’ala da ya ce:

ﭽ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﭼ التوبة: ٢٠



Waxanda suka yi imani, kuma yi hijira, kuma suka yi jihadi a cikin hanyar Allah, da dukiyoyinsu da rayukansu sun fi girman daraja a wurin Allah, kuma waxancan su ne masu rabo. 9:20

Nan ma Abubakar shi ne liman.

Haka kuma malaman tafsiri irin su Xabari da Ibnu Abi Hatim da sauransu sun tabbatar ta hanyoyi da dama, daga Urwatu xan Zubairu da Abdullahi xan Zubairu da Sa’idu xan Musayyibu da sauransu cewa, ayoyin da Allah Ta’ala ke cewa: Kuma mafi taqawa zai nisance ta. Wanda yake bayar da dukiyarsa, alhali yana tsalkaka.. 92:17-18 duk an saukar da su ne a kan Abubakar.
9.14 Abubakar Xin ne Dai Liman

Xan Shi’ar ya ce: Cewar da Ahlus-Sunnah ke yi wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya shugabantar da Abubakar ya limanci Sahabbai kuskure ne. A’ishah ce dai ta umurci Bilalu bayan ya yi kiran sallah, da ya gabatar Abubakar ya yi limanci. Yayin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya farfaxo, ya ji kabarbari na tashi, sai ya ce, wane ne ke bayar da sallah? Waxanda ke tare da shi sai suka ce, Abubakar ne. Sai ya ce: Ku riqa ni in fita. Sai Abbas da Ali suka riqa shi ya fita. Ya je ya kama kafaxun Abubakar ya raba shi da Alqibla, shi kuma ya ci gaba da bada sallar.


Martani:

Abu na farko dai, gaba xayan malaman hadisi sun yi watsi da wannan. Idan kuma har xan Shi’ar na jin ba su yi masa adalci ba to, ga fili ga mai doki. Sai ya gaya mana wanda ya riwaito ta. Idan kuwa ba haka ba, to, jahilcin ya bayyana. Domin zaton yake yi wannan ne karon farko da Abubakar ya limanci Sahabbai. Alhali kuwa gaba xayan masu ilimi babu wanda bai san cewa, tsawon kwanakin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi yana jinya Abubakar ne ke bada sallah ba, har Allah ya karvi ran Manzo. Ya kuma yi haka ne tare da izinin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Hasali ma a rana ta farko, wani Manzo ne Annabi ya aika ma Abubakar da maganar ba A’ishah ba, kamar yadda ‘yan Shi’ah ke son cewa.

Cewar da suka yi A’ishah ce ta umurci Bilalu, bayan ya gama kiran sallah da ya gabatar da Abubakar, ba haka abin yake ba. A’ishah ba ta hore shi da haka ba, a matsayin umurnin qashin kanta ko na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Bilalu ne manzon da ya isar da saqon ga Abubakar bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kalli taronsu ya ce: “Ku ce wa Abubakar na ce, ya bayar da sallah”.

Nassosa da dama sun tabbatar da cewa, Sahabi Abubakar ya kwashe kwanaki da dama yana limanci, kafin wannan fitowa da Annabi ya yi, ya kuma kwashe wasu kwanukan yana yi bayan haka. Domin kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai sake samun damar limancin sallar ba, tun ranar da ya kwanta ciwo har zuwa wadda ya cika a cikinta. Babu kuma wanda ya tava limancin sallar bayansa. Hanyoyi kuma da dama sun tabbatar da cewa, kwanakin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi yana jinya suna da yawa.

To, muna neman wannan malamin da ya faxa mana wanda ya wakilci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a sauran kwanukan. Mu a iya saninmu, babu wani mutum kafin yau da ya ce Umar ko Ali ko waninsu ne ya wakilci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci. Da yake duk sallolin nan a cikin jama’a ake yin su, da wani ya tava limancin ba Abubakar ba da duniya ta ji. Ko da suvul-da-baka ko ba a samu wanda ya ce haka ba.

Kuma ko ba a gaya maka ba, ka san bata yiwuwa Abubakar Raliyallahu Anhu ko wani daga cikin Sahabbai ya yi limancin tsawon wannan lokaci ba tare da masaniyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Kai, haka ma ba zata tava faruwa ba, sai Sahabban sun nemi amincewarsa tun da ba shanu ba ne kafin su yi sallah bayan wani a madadinsa. Al’ada da shari’a duk ba za su yarda da haka ba.

9.15 Darajojin Abubakar a Cikin Hadissai1

Duk wanda ya bi diddigin littafan hadisi ingantattu zai taras da su cike da darajojin Abubakar. Kamar hadisan da ke nuna tsananin soyayyar da ke tsakaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, da kariyar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yake yi masa idan an tava shi, da haxa hancin ayyukan alheri da yake yi a rana xaya, da haqurinsa da kusancinsa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kariyarsa gare shi, da shugabantar da shi akan jama’a, a mafi girman ibadu; sallah da hajji da makamantansu.

Abin da ya dame mu a nan shi ne, mu tabbatar da kevantuwar da Abubakar ya yi da abokantakar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin zauren imani, irin abotar da babu wani mahaluki da ya yi tarayya da shi a ciki. Duk abin da ke cikin wannan abokantaka, na xaukaka da daraja da kykkyawan sakamako, wani bai same shi ba baya ga Abubakar. Hasali ma da za a qididdige kevancewa wuri xaya da Abubakar ya yi da Annabi, a kuma qididdige wadda Usman da Aliyu ko waninsu daga cikin Sahabbai ya yi da shi, tasa ta fi yawa nesa ba kusa ba. Kai babu ma wani daga cikin Sahabbai da ya tava kevewa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama face tare da Abubakar, ko ya isko su kafin su rabu.

Dangane kuma da abin da ya shafi cikar sanin haqiqar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kusanci ga reshi da tsabar sonsa da gasgata shi a komai, da taimako akan yaxa addini, Abubakar ya baxa wa kowa qura a wannan layin.

Kai, babu wani abu na falala daga cikin abubuwan da ke sa abokantaka da tare su karva sunansu, irin waxanda suka fifita Sahabban Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan waxanda ba su ba, face ka iske a cikinsu Abubakar ya yi wa kowa rata. Irin taren da ya yi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta girma da azziki da mutunci babu wanda ya yi ta daga cikinsu.

Abin da ya zo a cikin Buhari da Muslim daga Abu Sa’id al-Khudri na qara tabbatar da haka. Watarana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya zauna a kan mimbari, sai ya ce: “Haqiqa Allah ya bai wa wani bawa nasa zavi tsakanin duniya da abin da ke wurinsa, sai bawan ya zavi abin da ke wurin Allah”. Qare faxar haka ke da wuya, sai Abubakar ya fashe da kuka yana cewa: “Mun fanshe ka da uwayenmu maza da mata ya Manzon Allah!”. Abu Sa’idu ya ce: Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne bawan da Allah ya ba zavin. Amma daga cikinmu babu wanda ya gano haka sai Abubakar don ya fi kowa sanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga cikinmu.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ci gaba da cewa: “Babu wani daga cikin mutane da ya saxaukar da kansa da dukiyarsa gare ni kamar Abubakar. Da kuma ina da ikon zaven badaxayi daga cikin mutane da na zavi Abubakar. Amma sunan tarena da shi ‘yan’uwantakar musulunci. Kada ku bar kowace qofa daga cikin qofofin da kuka buxe a masallaci sai ta Abubakar”.

A wata hadisi na Buhari daga Ibnu Abbas ya ce: Watarana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita daidai lokacin da yake fama da rashin lafiyar ajali, yana xaure da wani qyalle a kansa, ya zauna a kan mimbari, ya gode wa Allah, ya kuma yi yabo gare shi. Sannan ya ce: “Haqiqa, babu wani mutum da ya saxaukar da kansa da dukiyarsa gare ni kamar Abubakr xan Quhafata. Da kuwa ina da ikon zaven wani badaxayi daga cikin mutane, da na zave shi. Amma ‘yan’uwantakar musulunci ta fi komai. Ku rufe duk wata qofa mai zuwa masallaci in banda ta Abubakar”. A wata riwaya ya ce: “Amma Abubakar xan’uwana ne, kuma abokina”.

Gaba xayan waxannan nassosa, na bayyana irin yadda Abubakar ya kevanta da falalar abokantakar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, da irin yadda ya tsare mutuncin taren fiye da kowa, har hakan ta wajabta kasancewarsa mafi cancantar zama badaxayinsa da haka na yiwuwa.

Abin da waxannan hadisai ke nunawa na kasancewar Abubakar Raliyallahu Anhu mafi kusanci da soyuwar mutane zuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne abin da Manzo xin ya bayyana qarara a cikin hadisin Amru xan Asi da aka tambaye shi: Wa ka fi so daga cikin mutane? Ya ce: “A’ishah”. Aka ce: Daga cikin maza fa? Ya ce: “Babanta”. Aka ce: Bayansa fa? Ya ce: “Umar”. Sannan ya lissafa wasu mutane. Buhari da Muslim suka riwaito shi. A riwayar Buhari Amru ya ce: Sai na kama bakina don kada ya kai ni na qarshe.



Allah ya daxa tsira da aminci ga bawansa kuma Manzonsa Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama da iyalansa da matansa. Allah ya daxa yarda da Abubakar da Umar da gaba xayan Sahabbai, cikakkiyar yarda da mafi tsarkin tsira. Allah ka tayar da mu a cikin tawagarsu. Amin.

1 Shafi na 80

2 Shafi na 145

1 Shafi na 371

2 Shafi na 358

3 Shafi na 51

1 Shafi na 508-509

2 Shafi na 383

3 Shafi na 350

4 Shafi na 510

1 Shafi na 475

2 Shafi na 506

3 Shafi na 374

1 Shafi na 527

2 Shafi na 51

3 Shafi na 528

1 Shafi na 500

2 Shafi na 521

1 Shafi na 365

1 Wannan tarihin mun rubuta shi a gurguje, kuma a taqaice ranar da za a kai littafin wurin xab’i. In Allah ya so za mu wallafa cikakken tarihin malamin a wani littafi mai zaman kansa in da za mu faxaxa magana akan aqidarsa da gudunmawarsa a wajen kyautatar da fahimtar musulmi ga Alqur’ani da hadisi. Shugaban Kwamitin Fassara.

1 Haryanzu dai ga shi za mu miqa wannan littafi zuwa maxaba’a amma da sauran wani vangare da ya rage wanda ba a gyara tuva-tuvan na’ura ba a cikinsa. Mai karatu zai samu gargada idan ya zo wurin. Muna ba da haquri, sai wani bugu na gaba idan Maisama ya nufa. Masu Fassara.

1 Suratul Anbiya’,18

2 Suratul Isra’i, 91

3 Suratu Saba a 49

1 Suratul Baqara: 213

2 Suratul Ali- Imarana 18

3 Suratul Taubati, 128

1 Suratul Mulk

1 Suratul Nisa’I 135

2 Buhari Kitabul Buyai (3/56) Muslim Kitabul Buyu, (3/1164)

1 Ibn Majh, (1/96-97)

2 Suratul Najm. 1-4

3 Suratul Ahzab 72

4 Suratull Najmi 23

1 Faxace faxacen da ke faruwa a yankunan gabas ta tsakkiya tsakanin musulmi da maqiyansu da abin da ke faruwa a yau a qasar Afganistan da Iraqi hujjoji ne masu qarfi cewa ‘yan Shi’ah na taimakon maqiya musulunci akan musumi. Masu fassara.

1 Suratul Hashari 15

2 Sunansa, Umar bn Ahmad bn usman Al bagadadi Ya rasu Shekara 385, Taskiratul huffaz 3/183

1 Anan sun yi biris da hadisin da ya tuzgo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa; “Al’ummata ba za su gushe ba akan fixira matuqar basu jingirin sallar magariba. Abu Dawuda ya ruwaito shi a cikinsunan 1/169 da ibn Majah 1/225, cikin musnadi 4/147-5/422.

1 Suratul Ma’ida: 64

1 Suna rabke sallar Azahur da La’asar, Magariba da isha, Sai kuma Sallar Asuba. Masu fassara.

1 Sahihu Muslim (4/1942)

2 Suratul Namli, 48

1 Suratul Baqar, 196

2 Suratul A’araf, 142

3 Suratul fajr 1-2

4 Buhari 3/47-48, Muslim 2/830-831

3- Buhari Kitab As saum, babi na 72 muslim 2/283



5 Bukuhari 2/20 Tirmizi 2/129

1 Buhari 6,48-49


1 Suratul faxir 13-14

2 Suratul Tauba 31

1 Muslim, 3/11356

2 Buhari, (2/82). Muslim, (1/100)

3 Muslim, (2/644). Buahri (2/80.) . a nan idan shi mamacin ne ya bada wasiccin fasa masa kunka kenan kamar yadda ake yi a zamanin jahiliya ko kuma yaqi karantar da iyalinsa. Masu fassara.

4


1 Allah Sarki! Yanzu dai an qara wasu shekaru xari huxu bayan maganar nan ta Ibnu Taimiyyah, da wasu xari huxu kuma a bayan su, amma dai labarin bai canza ba. ‘Yan Shi’ah na nan suna ta jiran gawon shanu don bayyanar wanda Allah bai ko halicce shi ba sai cikin qwaqwalensu. Daga Masu Fassara.

1 Iraqi a yau ta ishe mu misali. Daga Masu Fassara.

1 Don bai mallaki abin da zai fitar ma da zakka a lokacin ba. Masu Fassara.

1 Wannan fasalin ya faxi a cikin taqaitawar Sheikh Gunaiman. Saboda muhimmancinsa muka xauko shi daga asalin littafin Minhajus-Sunnati, bugun Darul Hadith, Alqahira, 1425H/2004M (4/39-40).

2 Ire-iren wannan bawan Allah da ‘yan Shi’ah ke xaukakawa, waxanda duniyar malamai ba ta ko san da su ba suna da yawa. Shi dai Askari ko a littafan Shi’ah duk da yawan qaryarsu yana da matuqar wuya ka ji sun ce sun samo wani ilimi daga wurinsa. Duba Biharul Anwar na Majlisi ga misali wanda, ya cika sifili xari da sha biyar, amma da qyar ka samu riwayar Asakari a ciki. Galibin riwayoyinsa daga Ja’afarus-Sadiq ne, wanda suka fi kowa sha’awar su zuqa ma qarya.

1 Yana nuni zuwa ga hadisin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, har abada akwai qungiyar shiryayyu wadda Allah ke taimako. ‘Yan Shi’ah kuwa sun fi kowa nisa da ita. Daga Masu Fassara.

1 Wannan babi mun cirato shi ne a can inda mawallafin yake mayar da martani akan cewar xan Shi’an wai, rakiyar da sayyidina Abubakar ya yi wa Manzo ba daraja ba ce. Cire waxannan hadissai daga wannan babin ya zo ne don zaren tunanin mai karatu ya tafi ba tangarxa. Masu Fassara.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin