Fuska ta farko: Ba mu aminta da cewa akwai wata buqata ga samar da shugaba ma'asumi ba. Dalili kuwa shi ne, kasancewar ita al’ummar tamu baki xaya ma'asumiya, a duk lokacin da ta zama tsintsiya maxaurinki xaya. Wannan ya ishe mu. Kuma hakan na daga cikin abin da malamai suka ambata a cikin hikimar kasancewar al’umma ma'asumiya.
Fuska ta biyu: Idan kuma ‘yan Shi’ar suka ce: A’a, ai muna nufin samun shugaba ma'asumi a cikin al’ummar, zai qara gwavin ma'asumancinta!
To, sai mu ce masu: Idan haka ne kuwa, ya kamata gaba xayan wakilan shugaban su ma a wajabta kasancewarsu ma’asumai domin ma'asumancinta ya qara kauri. Idan kuwa har duk lokacin da aka samu daxin ma'asumi xaya ko fiye, hakan ta fi dacewa ga al’umma, to da za a wadatu da kasancewarta ma'asumiya a matsayinta na al’umma, ha kan zai fi daxa tabbatar da bangon ma’asumancinta da moriyarsa kai tsaye.
Kar kuma ku manta da cewa, ba duk abin da mutane ke jin shi ne mafi kamala Allah ke aikatawa ba. Balle hakan ya zama wajibi a kansa.
Haka kuma daidaita wani da Annabi a cikin wannan sha’ani na daga cikin mafi girman shubuha, da qoqarin bice girman Annabi da turmuza fifikonsa. Domin kuwa idan yin imani da gaba xayan abin da wannan shugaba ma'asumi zai faxi wajibi ne, kamar yadda imani da gaba xayan abin da Annabi ya faxa yake wajibi, to annabta ba ta da wani matsayi kenan. Bayan kuma ga shi Allah Ya umurce mu da yin imani da gaba xayan abin da Annabawa suka zo mana da shi. Inda kuwa har akwai wani mai daraja irin tasu, da an wajabta mana imani da gaba xayan abin da zai faxa. Ka ga ba wani banbanci kenan ko?
Fuska ta uku: Shi wannan ma'asumi da kuke cewa akwai buqatar samuwarsa, yana da cikakken iko ne a kan tabbatar da kyautatuwar rayuwar jama’a da tunkuxe masu varna? Koko dai ba ya da shi? In dai har ba ya da shi to, ba zai daxa al’umma da komai ba. Domin kuwa cikakken iko shi ne sharaxi a kan haka. Amma kasancewarsa ma'asumi kawai ba tare da wancan cikakken iko ba, na kawai tabbatar da samuwar wani mutum ne na gari, wanda bai banbanta da sauran masu wa’azi ba.
Duk da wannan nauyi da muka rage maku na san kuna iya cewa: A’a muna nufin ma'asumin na da cikakken iko.
To kun kawo kanku mahalaka. Domin kuwa wannan cikakken iko da kuka ce waxannan imamai goma sha biyu na da shi, bai sa suka tabbatar da wani gyara ko suka tunkuxe wata varna ba. Kun ga ashe kenan kun mayar da su azzalumai ba ma’asumai ba. Domin sun qi yin gyara alhalin suna da iko a cewarku. Idan kuwa ba su da ikon ne, to, su kasasshi ne kenan. Dole ne ku naxa ganwo ku xau xayan waxannan qaddarori ko ma dukkansu. Wato, kasancewarsu kasasshi ko ba ma’asumai ba. Ciwon ido sai shafa!
Idan kuwa haka ta tabbata, to, mu lalura ta wajabta mana gane koruwar wancan dalili da kuke kafawa a kan samar da shi ma'asumin. Ko banza lalura ta fi qarfin bakin dalili.
3.5 Wai Ali ya fi Sauran Sahabbai – Inji shi!
Xan Shi’ar ya ce: Abu na biyar: Haqiqa wajibi ne shugaba ya kasance mafificin daraja a kan waxanda yake shugabanta. Aliyu kuwa shi ne mafificin daraja a kan mutanen zamaninsa, bisa dalilai. Kenan ba makawa a kan kasancewarsa shugaba. Saboda munin gabatar da wanda aka fi a kan wanda ya fi, bisa ma’aunin hankali da nassi. Allah Ta’ala Ya ce:
ﭽ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﭼ يونس: ٣٥
Shin fa, wanda yake shiryuwa zuwa ga gaskiya ne mafi cancantar a bi shi, ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai dai a shiryar da shi? To, mene ne a gare ku? Ya ya kuke yin hukunci? (10:35)
Za mu tattauna wannan magana tasa ta hanyoyi biyu:
Hanya ta farko: Bari mu soma daga inda ka tsaya, wato cewa Ali Raliyallahu Anhu shi ne mafificin daraja daga cikin mutanen zamaninsa. Abin da muka yi imani da shi, wanda kuma aka riwaito ta hanya tabbatatta daga shi Alin kansa da wasu ba shi ba, shi ne Abubakar ne mafi girman daraja a cikin wannan al’umma, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Umar kuma na rufa masa baya.
Hanya ta biyu: Eh, gaskiya ne. Mu ma mafi yawa daga cikin mutanenmu sun aminta da shugabantar da wanda yake mafifici, matuqar haka na yiwuwa. Amma kuma kamata ya yi xan Shi’ar ya shinfixa wata hujja a kan wannan iqirari nasa. Ko banza akwai malamai da dama da ke qalubalantar sa a kan haka. Wannan aya da ya kawo kuwa ba hujja ba ce a gare shi. Domin iyakacin abin da take cewa shi ne: Wanda ke shiryarwa zuwa ga tafarkin gaskiya ba daidai yake ba da wanda sai an shiryar da shi.
To, wanda ke shiryarwa ba lalle ne ya fi wanda ya shiryu ta hannunsa kome da kome ba. Kamar yadda mutum na iya samun shiriya ta hannun wanda ya fiya daraja da ilimi.
Kuma haqiqanin wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya, ba tare da wata togiya ba shi ne Allah. Shi kuwa wanda ba ya iya shiryar da kowa, hasali ma shi ake shiryarwa, sifa ce ta duk wani mahaluki da ba ya da ikon xora kowa a kan hanya sai shi kansa idan Allah Ta’ala Ya xora shi a kanta. Wannan shi ne abin da wannan aya ke nufi. Wato bauta wa Allah ta fi bautawa wani mahaluki.
Mu koma farkon ayar don mu qara fahimtar ta. Ga abin da take cewa:
ﭽ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﭼ يونس: ٣٥
“Ka ce: “Shin, daga abubuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?” “Ka ce: “Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi shi, ko kuwa wanda ba ya shiryarwa sai dai a shiryar da shi?” (10:35)
Idan muka daxa xauko karatun daga ayoyi huxu kafin wannan, ma’anar za ta qara fitowa fili. Duba yadda Allah yake cewa:
ﭽ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯﯰ ﯱ ﯲﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﭼ يونس: ٣١
Ka ce, “Wane ne Yake azurta ku daga sama da qasa? Shin, ko kuma wane ne Yake mallakar ji da gani, kuma wane ne Yake fitar da mai rai daga mamaci…? (10:31)
Har zuwa inda Yake cewa: “Ka ce “Shin daga abubuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?” (10:35)
Haka kuma akwai malamai da dama da ke da ra’ayin wajabcin shugabantar da mafifici, idan babu wata maslaha a cikin shugabantar da wanda aka fi xin, kuma ya kasance zukata sun fi karkata gare shi. Amma kuma wannan wajabcin na samun gindin zama ne, a lokacin da aka tabbatar da shugabantar da shi mafificin ba zai haifar da wata matsala ba. Amma kuma duk waxannan jaye-jaye da bincike-bincike, sun taqaita ne ga waxanda ke ganin cewa Ali shi ne mafifici a kan Abubakar da Umar. kamar Zaidiyyah da wasu daga cikin Mu’utazilawa. Ko kuma waxanda suka yi jemage, kamar wani vangare na Mu’utazilawan. Su ke irin wannan bincike.
Amma Ahlus-Sunnah, wannan magana ta wajabcin shugabantar da mafifici, abu ce karvavviya a wurinsu. Kuma Abubakar Siddiqu shi ne mafificin a wurinsu. Ka ga su ‘yan Shi’ah duk da yake abin da suka faxi a nan gaskiya ne, amma ba su iya kare shi da dalilai. Wannan kuwa ya faru ne saboda sun toshe wa kansu hanyoyin ilimi masu yawa, ta yadda ba za su iya gane gaskiya ba balle su kare ta, don ga shi sun kasa iya tabbatar wa Harijawa da kasancewar Ali Raliyallahu Anhu musulmi. Ko tabbatar wa Marwaniyawa da ingancin shugabancinsa. Ga shi ko sun jefa kansu cikin irin abin da waxanda suka yaqe shi, suka riqa dalili. Don tsananin jahilcin da suke da shi da abin da maganganunsu suka qunsa na varna da tubka da walwala, da biyar son zuciya bisa jahilci.
4.0 Zango Na Huxu:
Hujjojinsu Na Alqur’ani
4.1 Ayar ﭽ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﭼ المائدة: ٥٥
Xan Shi’ar ya ce: Hujjojin da ke tabbatar da shugabancin Ali daga cikin littafi mai girma sun fi a qirya. Sannan ya ce:
Dalili na farko: Faxar Allah Ta’ala da Ya ce:
Abin sani kawai, majivincinku Allah ne da Manzonsa, da waxanda suka yi imani, waxanda suke tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka, alhalin su masu ruku’i ne (5:55)
Kan malamai ya haxu, inji shi, a kan cewa wannan aya ta sauka ne a kan Ali Raliyallahu Anhu.
Ya ci gaba da cewa: Malam Sa’alabi ya riwaito daga Abu Zarri, wai ya ce: “Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da waxannan kunnuwa nawa. In qarya nake yi su kurumce. Na kuma gan shi da waxannan idanu nawa. In qarya nake yi su makance. Yana cewa: Aliyu shi ne limamin ‘yan ga mu mun fito, kuma ajalin kafirai. Duk wanda ya taimake shi, abun taimako ne. Kuma haqiqa Ni, na yi sallar azzahar watarana tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai wani mutum ya miqe ya yi bara cikin masallaci, ba a sami wanda ya ba shi komai ba. Sai ya xaga hannayensa sama, shi mai roqon. Ya ce: “Ya Ubangiji! ka sheda, na yi bara a cikin masallacin Manzonka babu wanda ya ba ni ko tarau”. A lokacin da yake wannan magana Ali Raliyallahu Anhu na kusa yana ruku’i. Sai ya miqo masa qaramin yatsansa na dama, da ke xauke da zobe. Mai roqon ya karva ya zare zoben. Ashe lokacin da wannan abu ke faruwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na gani. Qare sallarsa ke da wuya, shi Annabin, sai kawai ya xaga kansa sama wai. Ya ce: “Ya Ubangiji! haqiqa Musa ya roqe ka da cewa: “Ya Ubangiji! Ka buxa mini qirjina. Kuma ka sauqaqe mini al’amarina. Kuma ka warware mini wani qulli daga harshena. Su fahimci maganata. Kuma ka sanya mini wani mataimaki daga iyalaina. Haruna xan’uwana. Ka qarfafa halittata da shi. Kuma ka shigar da shi a cikin al’amarina. (25:32) Sai Ka karva masa ta hanyar saukar da ayar da ke cewa: Za mu qarfafa damtsenka da xan’uwanka, kuma mu sanya maku wani dalili, saboda haka (maqiyanku) ba za su iya kai gare ku ba”. (28:35) Wai, sai Annabi ya ci gaba da cewa: “To ya Ubangiji! Ni ne Muhammadu Annabinka kuma zavavvenka. Ya Ubangiji! Ni ma ka buxa mini qirjina. Kuma ka sauqaqa mini al’amarina. Kuma ka sanya mini mataimaki daga cikin iyalaina. Kuma ya kasance Aliyu, don ka qarfafa halittata da shi”.
Abu Zarri ya ce, inji xan Shi’ar: Kafin Manzon Allah ya rufe bakinsa sai ga Jibrilu Alaihis Salamu ya sauka daga wurin Allah. Ya ce: “Ya kai Muhammadu, karanta”. Ya ce: “Me zan karanta”? Jibrilu ya karva masa da cewa: “Karanta: Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da Manzonsa, da waxanda suka yi imani wanxanda suke suna tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka alhalin su masu ruku’i ne (5:55).
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Kuma malamin nan masanin Fiqihu wanda ake kira Ibnul Magazili, ya riwaito cewa, wannan aya ta sauka ne a kan Ali. Kuma kalmar can ta “Waliyyi” wadda ke nufin “Majivinci” tana nufin wanda ke da cikakken iko a kan abu. Kuma wannan aya ta tabbatar wa Alin da wannan wilaya kamar yadda Allah Ta’ala Ya tabbatar wa kansa da Manzonsa da ita.
Martani:
Muna tabbatar wa wannan xan Shi’ah da cewa: Wannan magana tasa ba ta ko kai matsayin a riqa ta zato ba, balle ya sami sassafci. Domin kuwa duk gaba xayan wannan rattahi da ya yi vata ne, kuma qarya ce tsagwaronta. Irin wadda wawaye kan kitsa. Ko da wannan magana ta xan tsalma wani abu a cikin kansa na ilimi, wanda ake iya ba matsayin zato a mata kanshari’a, to yarda da ambaton ta hujja abu ne da shari’a ke matuqar qyama. Domin kuwa ana amfani da kalamar “Hujja” ne a musulunci a kan abin da aka ambata qarara, wanda ya fa’idantar da ilimi tabbatacce. Kamar cewar da Allah Ta’ala Ya yi:
ﭽ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰﯱ ﯲ ﯳﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﭼ البقرة: ١١١
Kuma suka ce: “Babu mai shiga Aljanna face waxanda suka zama Yahudawa ko Nasara. Waxancan tatsuniyoyinsa ne. Ka ce: “Ku kawo dalilinku, idan kun kasance masu gaskiya (2:111).
Da kuma inda Ya ce:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚﭛ ﭜ ﭝ ﭞﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭼ النمل: ٦٤
Ko wane ne yake fara halitta sa’annan kuma ya mayar da ita? Kuma wane ne ya azurta ku daga sama da qasa? Ashe akwai wani abin bauta wa tare da Allah? Ka ce, ku kawo dalilinku, idan kun kasance masu gaskiya (27:64).
Duk wanda ke iqirarin cewa shi mai gaskiya ne, to dole ne ya kawo hujja a kan haka. Duk kuwa abin da za a iya karva da sunan gaskiya, to lalle ne ya kasance qarara.
Amma gaba xayan abin da ya ambata matsayin hujjoji tsattsage suke da qarya: Babu xaya daga cikinsu da gaskiya ta share wa fage. Balle a sami wanda ya yi mata he!. Don hasali, ba abu ne mai yiwuwa ba ‘yan sharar fagen gaskiya su yi wa qarya da vata zagi. In Allah Ya yarda nan gaba kaxan za mu tona asirin waxannan qaryace-qaryace xaya bayan xaya. Tare da samar wa kowane qwai da za mu yi zakara. Domin kuwa yarda da ambaton waxannan waqoqi nasa da sunan hujja na daga cikin mafi munin qarya.
Sannan kuma xan Shi’ar ya dogara a kan wasu zantuka da yakan riwaito daga wasu mutane a cikin tafsirin waxannan ayoyi kuma sau tari qarya ce yake yi masu. Ko da hakan ta tabbata gaskiya, to mafi yawan mutane ba su yarda da shi a kan haka ba. Idan kuwa har zancen wani mutum xaya, wanda ba a gama tantance gaskiyarsa a cikin zancen ba. Da kuma kasancewar mafi yawa daga cikin mutane sun yi ban hannun makafi da shi a kan zaman haka hujja. Idan irin wannan zance na iya zama hujja, to, yana kuwa iya kafa hujjoji da yawa. A qarshe sai tarayyar hujjojin nasa su ci karo da juna ta hanyar tubka da walwala. Alhali kuwa hujjoji ba su tubka da walwale junansu, matuqar sun karva sunan hujja.
Kai! In Allah Ta’ala Ya so za mu bayyana kasancewar waxannan hujjoji da ya kafa qarya, a kan waxancan abubuwa da yake iqirari. Za mu ko yi haka ne ta hanyar shimfixi qwararan hujjoji waxanda ba su cin karo da juna. Domin daxa fayyace kasancewar kalaman nasa soki burutsu, da zarar an kalle su kallo xaya. Kuma duk wanda Allah bai toshe wa basira ba yana iya tabbatarwa da gane haka. Haka kuma wannan gwagwarmaya da za mu shiga, za ta kafa hujjoji a kan kasancewar Alqur’ani da addinin musulunci da Annabcin Manzon Allah gaskiya; kuma suna ban hannun makafi da gaba xayan ruvavvin hujjojin da xan Shi’ar ya kafa.
Eh! Ruvavvi ne a haqiqa, ta yadda duk mai kaifin hankali da ya xan nazarce su, ya kuma kairdadi abubuwan da suke iya haifarwa, zai tabbata cewa wutarsu na iya canye koren gandun dajin imani.
Abu na gaba da za mu ce shi ne: Ko shakka babu mayar da martani a kan yadda ya rikita wannan aya wajibi ne. Za mu kuma yi shi ta fuskoki kamar haka:
Fuska ta farko:
Kafin komai, muna son xan Shi’ar ya tabbatar mana da ingancin wannan magana. Wato ya sake maimaita wancan hadisi, amma a cikin siga irin wadda ke sa hujja ta samu kafuwa. Domin kuwa jingina shi kawai da ya yi ga tafsirin Sa’alabi, ko iqirarin haxuwar kan malamai a kan sa, waxanda kuma ba masana ilimin riwaya ba ko waxanda ake iya gasgantawa idan sun riwaito wani abu. Sai fa idan ana iya tantance ingancin isnadinta.
Fuska ta biyu:
Cewar da ya yi: “Kan malamai ya haxu ga cewa ayar ta sauka ne a kan Ali”, magana ce ta banza kuma sosai, irin wadda aka saba yayatawa. Abin da ya tabbata dai, kamar yadda kan masana sirrin riwaya ya haxu, shi ne, waccan aya ba ta sauka kan Ali kawai ba. Kuma Alin bai yi sadaqa da zobe a cikin sallah ba. Haka kuma kan malaman hadisi ya haxu a kan cewa wannan qissa da xan Shi’ar ya riwaito qarya ce tsagwaronta.
Haka kuma kan malaman ya haxu a kan cewa, godogo da Sa’alabi da xan Shi’ar ya yi, a matsayin wanda ya riwaito wasu maganganu daga gare shi, ba wani kayan gabas ne ba. Domin Sa’alabi na riwaito hadissan Gizo da Qoqi a cikin tafsirinsa. Kamar hadissan da ya kan riwaito, ya saka su a farkon kowace sura don bayyana falalarta. Da wasu abubuwa masu kama da haka. A kan haka ne ma suke yi masa laqabai da: “Da’u fataken dare”.
Haka almajirinsa Al-Wahidi da wasu daga cikin malaman tafsiri makamantasu suke, suna riwayar qwaya da burtuntuna. Abin da kawai muke nufin tabbatarwa a nan shi ne, kasancewar wannan marubuci jahili kuma maqaryaci, don kowa ya gane.
Babban abin da ke tabbatar da haka shi ne cewar da ya yi: Haqiqa kan malamai ya haxu a kan cewa ayar ta sauka ne a kan Ali. Abin mamaki ni a wurina shi ne: Wane ne daga cikin ma’abuta ilimi ya naqalto wannan magana, a irin wannan al’amari, har shi ya same ta? Domin kuwa ba a yarda da ijma’i sai idan an ji haka daga bakin wani fitaccen malami a fannin riwaya.
Hakan ta sa ba a sauraren duk wani zaqaqurin magana, ko malamin tafsiri, ko na tarihi ko makamantansu, idan ya riwaito abu ba tare da tabbataccen isnadi ba. Sai kawai a saka maganar kwandon shara. To, ya kake zato idan ya yi iqirarin haxuwar kan malamai a kan wata magana ta qarya?!
Fuska ta uku:
Hala xan Shi’ar bai san cewa, malaman tafsirin da ya cirato wannan magana daga littafansu, da waxanda suka fi su ilimi, sun daxe da cirato wata magana da ke walwale wannan da yake iqirari ba? Shi malam Sa’alabi, ya riwaito a cikin wannan tafsiri nasa cewa, xan Abbas ya tafi a kan cewa, wannan aya ta sauka ne a kan Abubakar. Ya kuma riwaito Abdulmalik na cewa: “Na tambayi baban Ja’afar a kan wanda wannan aya ta sauka. Ya karva mani da cewa: “A kan gaba xayan muminai”. Na ce masa: “Wasu mutane na cewa: “Ta sauka ne a kan Ali”. Sai ya ce: “To ai Aliyu na daga cikin muminai”. An kuma samo irin haka daga malam Dhahhaku.
Fuska ta Huxu:
Mun yafe wa xan Shi’ar qaryar ijma’i da ya yi. Muna so ya tabbatar mana da maganar ta hanya xaya ingantancciya. Domin wanda Sa’alabi ya ambata mai rauni ne. A cikinsa akwai mazajen da ba a yarda da su ba. Balle daxa wanda xan magazili ya riwaito, wanda shi rauninsa ya vaci matuqa. Hadisan da ya tattara a cikin littafinsa, ko kurtu a makarantar ilimin hadisi ya san cewa qaryayyaki ne kawai aka kitsa. To isnadin nan guda xaya rak ingantacce da muke nema gare shi muna son ya qunshe wannan magana da waccan.
Fuska ta biyar:
Da wannan aya na magana ne a kan cewa Aliyu ya bayar da zakka a daidai lokacin da yake ruku’i, kamar yadda suke iqirari, da hakan ta zama wani sharaxi na wajabci a cikin cancantar shugabanci. Ta yadda musulmi ba za su jivanci kowa ba sai Ali shi kaxai. Ba zancen Hassan ko Husaini ko sauran Banu Hashim ake yi ba. Wannan kuwa ya sava wa abin da ku kanku ‘yan Shi’ah kuke cewa.
Fuska ta shida:
Ayar dai ta zo ne da lafazin jam’i ba na mutum xaya ba. Don haka, ba ta xanfaruwa a kan Ali shi kaxai.
Fuska ta bakwai:
Ta kuma tabbata cewa, Allah Ta’ala ba ya farin ciki, balle ya gode wa mutum a kan aikata komai, sai idan abin nan yardadde ne a wurinsa; ta hanyar kasancewarsa wajibi ko mustahabbi. Ita kuwa sadaqa da kyauta da ‘yanta bayi da ba da haya da aure da saki, da ire-iren su. Malaman musulunci sun yi ittifaqi a kan cewa aikata su a cikin sallah ba xa’a ba ne, balle su zama wajibi ko mustahabbi. Hasali ma da yawa daga cikin malaman na ganin aikata xayansu cikin sallah na vata ta, ko da ba a yi magana ba. Kai tana ma iya vaci dalilin wata ishara da aka fahimci maqasudinta, a wurin wasu daga cikin malamai. A yayin da wasu malaman suka qara da cewa, babu wani abu da ake iya mallaka ta wannan hanya, sakamakon rashin wani sanadari na shari’a a cikin harkar. Kuma da irin wannan aiki abin so ne to, da Annabi ya kasance farkon wanda ya aikata shi, ya kuma kwaxaitar da Sahabbansa a kan haka. Da kuma an sami cewa Aliyun ya tava aikata hakan a wasu lokuta.
Rasa xaya daga cikin waxannan abubuwa, na tabbatar da kasancewar sadaqa a cikin sallah ba wani aiki na madalla ba. Musamman ma da yake aikin tallafa wa mabuqacin ba ya wucewa. Ta yadda mai sadaqar zai iya haqura har ya qare sallah, sannan ya yi kyautar. Domin idan dai har sallah ta karva sunanta, to, ba za ta bayar da damar yin haka ba.
Fuska ta Takwas:
Mu qaddara cewa yin sadaqa a cikin sallah shari’a ne. Da ba a kevance lokacin ruku’i don aikata ta ba; aikata ta a lokacin da ake zaune ko tsaye ya fi dacewa. Amma sai a ce babu wanda zai zama shugaba gare ku sai xaya daga cikin waxanda ke bayar da sadaqa a lokacin da suke ruku’u? To, za a sami wani ya yi sadaqar a lokacin da yake tsaye ko zaune, bai cancanci wannan shugabacin ba ko?
Fuska ta Tara:
Cewar da ‘yan Shi’ah suka yi: faxar Allah Ta’ala a cikin ayar: Kuma suna bayar da zakkah alhali su masu ruku’i ne (5:55) wai hakan na nufin wanda zai bayar da zakkar ya kasance yana cikin ruku’i. Magana ce da ba ta sauraruwa. Domin Aliyu Raliyallahu Anhu ba ya cikin waxanda zakka ta wajaba kansu a wannan zamanin na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama saboda kasancewarsa talaka. Kuma ita zakkar azurfa na wajaba ne a kan wanda ya mallaki nisabi tsawon shekara. Aliyu kuwa ba ya cikin waxanda suka mallake shi.
Fuska ta Goma:
Wani abin kuma shi ne, da yawa daga cikin malaman fiqihu sun tafi a kan cewa fitar da zobe da bayar da shi a matsayin zakka ba ya isa, sai a lokacin da aka aminta da wajabcin zakka a cikin kayan ado. Aka kuma yarda da fitar da wani abu daga cikinsu a matsayinta. Sane muke da cewa, akwai malaman da suka yarda da a fitar da qimar abin da ya wajaba xin. To, amma ai yin wannan awo da gwaji don fitar da qimar, abu ne mawuyaci a cikin sallah. Kuma hasali ma ita qimantawar kanta ta sassava gwargwadon sassavawar yanayi.
Fuska ta Goma Sha xaya:
Wannan aya ba ta nufin a bayar da zakka lokacin da ake ruku’i. A’a matsayinta daidai yake da na ayar da ke cewa:
ﭽ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﭼ البقرة: ٤٣
Kuma ku tsayar da sallah, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi ruku’i tare da masu yin ruku’i (2:43).
Daidai kuma ta ke da ayar da ke cewa:
ﭽ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ آل عمران: ٤٣
Ya Maryamu! Ki yi qanqan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi Sujada, kuma ki yi ruku’i tare da masu ruku’i (3:43).
Gaba xayan waxannan ayoyi biyu suna umurni ne da ruku’i, kamar yadda ita ma waccan ayar ke yi.
Fuska ta Goma Sha biyu:
Mafi yawan amintattun malaman tafsiri na da da na yanzu, sun aminta da cewa wannan aya ta sauka ne, domin hani daga jivintar kafirai, da horo da jivintar muminai. Kasancewar wasu munafikai, irin su Abdullahi xan Ubayyu na jivintar Yahudawa, bisa dalilin cewa wai, suna taka-tsantsan ne, kada watarana reshe ya juye da mujiya. Shi kuwa wani daga cikin muminai wanda ake kira Ubadata xan Samitu ya ce wa Manzon Allah: “Ni kam ina Jivintar Allah da Manzonsa ne kawai. Kuma ba zan ko haxa hannu da waxancan kafirai ba balle jivintar su”.
Fuska ta Goma Sha uku:
Duk wanda ya yi nazarin Alqur’ani da kyau, zai fahimci cewa, takin qasar wannan aya (siyaqinta) na tabbatar da wannan abu da muka faxa. Domin kuwa a can kafin wannan aya kaxan cewa Allah Ta’ala Ya yi: Ya ku waxanda suka yi imani! Kada ku riqi Yahudawa da Nasara majivinta. Sashensu majivinci ne ga sashe. Kuma wanda ya jivince su daga cikinku, to lalle ne shi, yana daga cikinsu. Lalle Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai (5:51).
Ka ga wannan hani ne Allah ya yi daga jivintar Yahudawa da Nasara. Sannan sai kuma Ya ce: Sai ka ga waxanda a cikin zukatansu akwai cuta, suna tsoron gaugawa a cikinsu, suna cewa: ‘Muna tsoron kada wata masifa ta same mu. To, akwai tsammanin Allah Ya zo da buxi ko kuwa wani umurni daga wurinsa sai su wayi gari suna da-na-sani a kan abin da suka voye cikin zukatansu (5:52) har zuwa inda Ya ce: Saboda haka suka wayi gari suna masu hasara (5:53).
A nan kuma Allah Ya bayyana siffofin waxanda suke akwai cuta a cikin zukatansu ne. Wadda hakan ke sa su jivintar kafirai da munafukai.
Bayan haka kuma ya ce:
Ya ku waxanda suka yi imani! Wanda ya yi ridda daga cikinku daga addininsa, to Allah zai zo da wasu mutane, Yana son su, kuma suna son Sa, masu tawali’u a kan muminai, masu izza a kan kafirai. Suna yin jihadi a cikin hanyar Allah, kuma ba su tsoron zargin mai zargi. Waccan falalar Allah ce, Yana bayar da ita ga wanda Yake so. Kuma Allah Mayalwaci ne, mai ilimi.
A nan kuma Ya ambaci irin mugun aikin waxanda suka yi ridda, tare da tabbatar da hakan ba ta cutar da addinin Allah da komai. Ya kuma faxi siffofin waxanda zai maye gurbinsu da su.
Bayan haka ne Ya ce:
Haqiqa, Allah ne kawai majivincinku da Manzonsa, da waxanda suka yi imani, waxanda suke suna tsayar da sallah, kuma suna bayar da zakka alhalin su masu ruku’i ne. Kuma wanda ya jivinci Allah da Manzonsa da waxanda suka yi imani, to, rundunar Allah su ne masu rinjaye (5:56).
Waxannan ayoyi kuma sun qunshi bayani ne a kan yanayi da halayen waxanda suka shiga musulunci daga cikin munafikai, da kuma na waxanda suka yi ridda daga addini, da kuma na muminai waxanda duga-dugansu suke kafe a kan turbar musulunci fai da voye.
Da yake salon tafiyar waxannan ayoyi na cikin sigar “Jam’i” ne, tana magana ne a kan gaba xayan muminai waxanda suka siffanta da waxannan siffofi. Ba ta kevanta ga Abubakar ko Umar ko Aliyu ko waninsu ba. Sai dai su ne mafi cancantar al’umma da shiga cikin ma’anar ayoyin.
Dostları ilə paylaş: |