Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə33/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   29   30   31   32   33   34   35   36   ...   51

Fuska ta Goma Sha Huxu:

Lafuzzan da xan Shi’ar nan ya ambata a cikin waxancan hadisai na daga cikin abubuwan da aka tabbatar da kasancewarsu qarya, wadda aka yi wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa Aliyu ba shi ne Imamin ‘yan ga mu mun fiton rundunar musulmi ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne Imamin wannan al’umma ciki da waje. Haka kuma ba Aliyun kawai ne ajalin kafirai ba. Ya dai kashe wasu daga cikinsu, kamar yadda wasu Sahabbai takwarorinsa suka kashe wasu; babu wani daga cikin masu jihadin can, da aka yi artabu da kafirai tare da shi face akwai wani sashe na kafirai, da ya aika lahira.

Kuma ka ga cewar da xan Shi’ar ya yi wai Annabi ya ce: Allah zai taimaki duk wanda ya taimaki Ali, zai kuma tavar da duk wanda ya tavar da shi, hakan ba ta faru ba. Mun kuwa san Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya faxar abin da ba gaskiya ba. Kuma su kansu ‘yan Shi’ah sun tabbatar wa duniya da cewa gaba xayan al’ummar ta tavar da Alin, har zuwa lokacin da aka yi wa halifa Usmanu kisan gilla.

Alhali kuwa sanannen abu ne cewa babu lokacin da wannan al’umma ta sami gagarumin taimako daga wurin Allah, irin lokacin halifancin waxancan Sahabbai uku na kafin Ali Raliyallahu Anhu. Kuma ko lokacin da aka kashe halifa Usmanu Raliyallahu Anhu mutane kasuwa suka yi gida uku: Kashi na xaya ya goyi bayan Ali ya taya shi yaqi. Kashi na biyu kuma ya shaya daga da shi, kashi na uku kuma ya yi qoqarin shiga tsakani. To, ko a wannan lokaci Allah bai taimaki rundunar Ali Raliyallahu Anhu a kan waxancan rudunoni biyu ba. Rundunar Mu’awiyah ce Allah Ya ba nasara, har ya zama shugaba. Su ne kuma suka sami nasarar murqushe kafirai da cin garuruwa. Taimakon da Ali ya samu daga wajen Allah, a nan bai fi irin wanda takwarorinsa suka samu ba, wajen yaqar Harijawa da kafirai.

Haka kuma addu’ar da xan Shi’ar ya ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi bayan Alin ya yi sadaqa da zoben qarya ce lafiyayya. Domin kuwa sanannen abu ne cewa, akwai Sahabban da suka bayar da sadaqar wasu abubuwa saboda Allah, a waxansu lokuta da ake da buqata da su, waxanda kuma amfaninsu da darajarsu ta fi na wancan zoben da Aliyu ya bai wa wancan mutum.

Ya zo a cikin Buhari da Muslimu cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Babu wata dukiya da ta amfane ni, kamar dukiyar Abubakar. Mafi baiwa gare ni da abokantakarsa da dukiyarsa daga cikin mutane kuma shi ne Abubakar. Da na kasance mai riqon wani badaxayi daga cikin mutanen da ke bayan qasa, da na riqi Abubakar”.

Haka kuma Usmanu ya bayar da gudunmuwar raqumi dubu saboda Allah, a lokacin da za a je yaqin tsanani (Tabuka). Har Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk abin da Usmanu zai aikata, daga yau, ba zai cuce shi ba”.

Ka ji iyakar abin da Annabin ya ce, a kan waxannan Sahabbai.

Wani abin tambaya ma a nan shi ne: Ya za a yi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya roqi Allah da cewa: Ka sanya mini wani mataimaki daga cikin mutanena. Ya kuma kasance Aliyu. Don ka qarfafa al’amarina da shi? Bayan kuwa a lokacin har an yi hijira zuwa Madina, an kuma sami nasara kan kafirai. Ta hanyar taimakon da Allah ya yi wa Manzon da qarfinsa da ikonsa, da kuma na taron muminai. Kamar yadda Yake cewa:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭼ الأنفال: ٦٢



Shi ne wanda Ya qarfafa ka da taimakonsa, kuma da muminai (8:62)

Ya kuma ce:

ﭽ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜﯝ ﭼ التوبة: ٤٠

Idan ba ku taimake shi ba, to, haqiqa Allah Ya taimake shi, a lokacin da waxanda suka kafirta suka fitar da shi, suna su biyu, a lokacin da suke cikin kogon dutse, sanda yake cewa da sahibinsa; “Kada ka yi baqin ciki, haqiqa Allah Yana tare da mu” (9:40).

Wanda yake tare da shi xin, a lokacin da Allah ya yi masa wannan taimako, shi ne Abubakar, bayan da kafirai suka fitar da shi; sun kasance su biyu kacal, Allah ne na ukunsu. Haka kuma shi ne ya kasance tare da shi a cikin dabi a lokacin yaqin Badar ba tare da kowa daga cikin Sahabbai ba.

Babu wani Sahabbai ko bayan Abubakar, face akwai wata rawa ta a zo a gani da ya taka a cikin fagen taimaka wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ko shakka babu kuma Allah zai saka masu a kan wannan.

Duk wanda ke iqirarin cewa wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya roqi Allah Ya qarfafi al’amarinsa da wani mutum kevantacce, kamar yadda Annabi Musa ya roqa, ya shara wa Annabi qarya, ya kuma zalunce shi.

Kuma ko shakka babu Shirka da Ilhadi da Munafunci ne suka haxu suka haifi Shi’anci. Sai dai ba kodayaushe ne hakan ke bayyana a fuskarsu ba.

Fuska ta goma sha biyar:

Iyakar tawilin da ake iya yi wa wannan aya, ko ‘yan Shi’ah su sami sassauci, shi ne: Ayar na cewa lalle ne muminai su jivinci Allah da Manzonsa da mumunai ‘yan’uwansu. Ka ga hakan ta haxa har da Ali, tunda shi ma mumini ne, sai su jivince shi. Kenan babu wani kokwanto a kan cewa jivintar Ali wajibi ne a kan kowane mumini, kamar yadda yake wajibi a kansu su jivinci takwarorinsa muminai.

Allah Ta’ala na cewa:

ﭽ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡﮢ ﭼ التحريم: ٤



Kuma idan kun taimaki juna a kansa, to, haqiqa Allah shi ne mataimakinsa, da Jibrilu da salihan muminai (66:4).

A nan Allah Ya bayyana mana cewa, duk wani salihi daga cikin muminai mataimaki ne ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma Allah Subhanahu da mala’ika Jibrilu mataimakansa ne. Babu wani abu a cikin waxannan ayoyi da ke nuna maganar shugabanci ballantana a ce Ali ko wani take nufi.



Fuska ta goma sha shida:

Kuma da Allah Subhanahu WaTa’ala na nufin jivinta da ma’anar Shugabanci, da cewa zai yi: Abin sani shi ne shugabanku shi ne Allah da Manzonsa da waxanda suka yi Imani. Ba zai ce: Duk wanda ya jivinci Allah da Manzonsa ba. Domin kuwa a qa’idar harshen Larabci ba a cewa, an jivinci wanda aka naxa. Sai dai a ce: An naxa shi shugaba.



Fuska ta goma sha bakwai:

Rashin yiwuwar haka na daxa tabbata, idan aka yi la’akari da cewa Allah Subhanahu WaTa’ala Ya fi qarfin a ce masa shugaban wasu, ko sarkinsu. Allah ya fi qarfin haka; shi dai mahaliccinsu ne, mai azurta su, Ubangijinsu, mamallakinsu, wanda komai da kowa yake hannunsa. Ba a cewa: Allah shi ne Sarkin Musulmi, kamar yadda za a iya ce wa Ali ko wani shugaba haka. Kai ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi qarfin a ce masa sarki. Matsayinsa ya wuce haka nesa. Ai ko Abubakar Siddiqu Raliyallahu Anhu ka ga musulmi ba su ambace shi sarki ba, sai dai suka yi masa laqabi da halifan Manzon Allah. Umar ne farkon wanda aka ambata da laqabin Sarkin Musulmi daga cikin halifofi.



Fuska ta goma sha takwas:

Ba duk wanda Allah Ya ba shugabanci ne komai adalcinsa ba, mutanensa ke kasancewa rundunar Allah, kuma mai rinjaye. Domin kuwa da yawa Allah kan shugabantar da mutane adalai a kan munafukai da kafirai. Kamar yadda aka sami kafiran amana da munafukai a Madina qarqashin kuma jagorancin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.



4.2 Ayar ﭽ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁﮂ ﭼ المائدة: ٦٧

Xan Shi’ar ya ce: Faxar Allah Ta’ala da Ya ce:

ﭽ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﭼ المائدة: ٦٧

Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da manzancinsa ba kenan (5:67).

Xan Shi’ar ya ce, kan malamai ya haxu a kan cewa wannan aya ta sauka ne a kan Ali Raliyallahu Anhu. Kuma Abu Nu’aimi al-Hafizu daga cikin malaman sunnah, ya riwaito daga Adiyyu, da isnadinsa cewa: Wannan aya ta sauka ne ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan Aliyu xan Abu Xalib. An kuma samo daga cikin tafsirin Sa’alabi, wanda ya ce: Ma’anar wannan aya ita ce: Ka iyar da abin da aka saukar gare ka daga Ubangijinka a cikin falalar Ali. Ya ci gaba da cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kama hannun Ali, a lokacin da wannan aya ta sauka gare shi, ya ce: Duk wanda na kasance majivinci gare shi, to Aliyu majivincinsa ne.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, tunda kuwa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne majivinci Abubakar da Umar da sauran Sahabbai Raliyallahu Anhu bisa ijma’i, kenan Aliyu zai kasance majivincisu, ta hanyar zamowa Imami (Shugaba). Kuma harwayau dai ya zo a cikin tafsirin na Sa’alabi, inji shi, cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tara mutane a lokacin da yake a Ghadir Khum ya kama hannun Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Duk wanda na kasance majivinci gare shi, to, Aliyu majivincinsa ne. Nan take wannan magana ta tuma, ta watsu a cikin garuruwa. Har ta kai kunnen Harisu xan Nu’umanu al-fihiri. Sai ya hau taguwarsa ya iske Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wurin da ake kira Abxahu yana cikin taron Sahabbansa. Ya ce masa: Ya kai Muhummadu! ka gaya mana cewa, Allah Ya hore mu da shaidar da ba wanda ya cancanci bauta sai shi, kuma kai Manzon Allah ne, muka yarda maka. Ka kuma hore mu da yin salloli biyar, da fitar da zakka daga cikin dukiyarmu, da mu azumci watan Ramalana, duk muka karvar maka. Amma duk wannan ba ta ishe ka ba, sai ka xaukaka likkafar qaninka, ka fifita shi a kanmu? Don na ji kace: Duk wanda ka kasance majivinci gare shi, to Aliyu majivincinsa ne. To, wannan kuma daga wurin Allah ne ko daga wurinka? Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sha masa billahil-lazi cewa, umurni ne daga wurin Allah.

Sai kawai Harisu ya buga rigarsa ya tasar wa taguwar can tasa, yana cewa: Ya Ubangiji idan dai har gaskiya ne, wannan magana daga wurinka take, to ka yi mana ruwan duwatsun wuta daga sama. Ko ka zo mana da wata azaba mai raxaxi. Ai bai kai wurin taguwar ba sai Allah Ya jefe shi da wani dutse na wuta a maxiga, ya fito ta duburarsa, nan take ya faxi matacce. Allah Ta’ala kuma Ya saukar da cewa: Wani mai tambaya ya yi tambaya game da azaba, mai aukuwa. Ga kafirai, ba ta da mai tunkuxewa. Daga Allah mai mata kai (70:1-3).

Xan Shi’ar ya rufe maganarsa da cewa, wai, wani malami daga cikin Jumhuru (yana nufin Ahlus-Sunnah), da ake kira Naqqashu ya riwaito wannan magana a cikin tafsirinsa.

Don mayar da martani a kan wannan magana sai mu ce, bismillahi:



Fuska ta farko:

Tumun fari dai, wannan magana gaba xayanta qarya ce zaharani. Abu mafi zama qarya ma, a cikin maganar duk bai fi cewar da ya yi kan malamai ya haxu a kan saukar ayar a kan Ali ba. Babu wani malami xaya daga cikin malaman da suka san abin da suke yi, wanda ya faxi wannan magana ko waccan.

Ta kuma tabbata cewa kan malamai ma’abuta ilimin hadisi ya haxu a kan cewa, akwai qaryayyaki da yawa a cikin abin da Abu Nu’aimi ke riwaitowa a cikin littafansa: Al-Hilyatu ko: Fala’ilus-Sahabah. Haka ma cikin abin da Naqqashu da Sa’alabi da Wahidi ke riwaitowa a cikin tafsiri. Sun kuma haxu su malaman can a kan cewa wannan hadisi da Sa’alabi ya riwaito a cikin tafsirinsa, na qarya ne. Nan gaba kaxan za mu bayyana dalilan da muka gano kasancewarsu na qarya ta hanyarsu. Tare da tabbatar da rashin kasancewar Sa’alabi cikin jerin ma’abuta ilimin hadisi.

Amma kafin haka, bari mu ambaci wata qa’ida a nan, wadda ke cewa: Kasancewar ana samun qarya da gaskiya da yawa a cikin riwayoyi, ya sa dole a koma ga ma’abuta ilimin hadisi, a matsayinsu na rariya uwar tata a fagen, don a rarrabe tsakanin garin taba da na gero. Kamar yadda ake komawa ga malaman nahawu don banbancewa tsakanin Nahawun Larabawa da na Ajamawa. Da kuma yadda ake komawa ga malaman Lugga, don tantance abin da yake mallakar luggar da wanda ba mallakarta ba. Da kuma yadda ake tuntuvar malaman waqa da na Xibbu a kan abin da ya shafe su. Kowane “Allazi” daga cikin ilimi, da nashi “amanu” da aka san shi da shi. Wani ko “kafaru” ake samu gare shi. To, malaman Hadisi su ne mafiya girman daraja a kan sauran malamai. Su ne kuma mafiya gaskiya da xaukakar matsayi, da kishin addini.



Fuska ta biyu:

A cikin wannan hadisi da xan Shi’ar ya kawo, akwai abin da ke tabbatar da kasancewar sa qarya, ta fuskoki da dama. Xauki cewar da ya yi: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance a Ghadir.. zuwa qarshe, ka dube ta.

Muna tabbatar wa xan Shi’ar cewa, kan gaba xayan mutane ya haxu a kan cewa, duk abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa a Ghadir Khum, nada alaqa ta qud-da-qud da Hajjin bankwana. Har su ‘yan Shi’ah sun yarda da hakan. Saboda haka ne ma suka xauki ranar 18 ga watan zul-hajji a matsayin ranar Idi. Annabi kuwa bai sake komawa Makka ba bayan wannan hajji, Ya dai koma ne zuwa Madina bayan kammala aikin. Inda ya ci gaba da rayuwa tsawon sauran kwanakin Zul-hajji da Muharram da Safar. Allah Ya karvi rayuwarsa a farkon watan Rabai’ul Awwal. Ka ji wannan ko?

To, ka tuna xan Shi’ar cewa ya yi a cikin hadisin, bayan wai Annabi ya qare wancan jawabi ga jama’ar da ya tara a Ghadir Khum, har maganar ta watsu a cikin garuruwa. Ko kafin Harisu ya kawo masa waccan takakka, har wai ya isa wani wuri da ake kira Abxahu. Ita kuwa Abxahun nan idan ba ka sani ba, a Makka take. To auna wannan magana da ta samanta kaxan. Kai ne alqalin kanka.

Mu a wurinmu, wannan magana qarya ce irin wadda ba mai yin ta sai jahili wanda bai san wurin da ake kira Ghadir Khum ba.

Wani abin kuma shi ne: Ita wannan surah da ya ce ta sauka a Ghadir Khum kan malamai ya haxu a kan ta sauka ne a garin Makka kafin hijira; shekaru goma ko fiye kafin saukar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a Ghadir Khum. To, yaya kuma za a ce ta sauka ne bayan haka?

Ayar da kuwa xan Shi’ar ya ce Sahabi Harisu ya yi amfani da ita, ta sauka ne gab da qare yaqin Badar, kafin qissar Ghadir khum da shekaru da dama. Kuma ta sauka ne akan maganganun Abu Jahali da takwarorinsa. Sanannen abu ne dai a wurin malamai cewa, babu wani musulmi da irin haka ta tava kasancewa tare da shi, na yin fito-na-fito da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

Abin al’ajabi a nan, babu wani Sahabi da aka sani da irin wannan suna. Abin da ke qara tabbatar da wannan magana tatsuniya ce.



Fuska ta uku:

Abin da matuqar ban mamaki; Ga shi xan Shi’ar na raya cewa sun tabbatar da shugabancin Ali Raliyallahu Anhu ta hanyar amfani da waccan aya ta Alqur’ani. Alhali kuwa babu wani abu a cikin ayar da ke nuna haka ko kaxan. Ayar cewa ta yi: Ka isar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka (5:67). Wannan lafazi kuwa ya qunshi gaba xayan abin da aka saukar gare shi daga Ubangijinsa; bai taqaita a kan wani abu kevantacce ba.

Duk wanda ya yi iqirarin cewa, sha’anin shugabancin Ali Raliyallahu Anhu na daga cikin abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya isar na manzanci ko aka umurce shi da isarwa, to ya gigice, kuma babu wata aya ta Alqur’ani da zai iya tabbatar da hakan da ita.

Fuska ta huxu:

Ta tabbata cewa, idan aka haxa hancin wannan aya, da abin da ake da shi a hannu na tarihin Annabi. Savanin abin da ‘yan Shi’ar nan ke faxi, shi ne sakamakon da hakan za ta bayar; cewa dai, Allah bai saukar da ita ayar a kan sha’anin Ali ba. Bai kuma hori Annabi da hakan ba. Don lalle, da hakan na cikin saqonnin da Allah Ya hori Manzon da isarwa, da ya isar da shi; ba zai sava wa Allah ba.

Duk wanda ya zargi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da voye wani abu na wahayi, haqiqa ya yi qarya. Domin kuwa Allah Ta’ala cewa ya yi: Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka. Kuma idan ba ka aikata ba, to, ba ka iyar da Manzancinsa ba kenan (5:67). Inji Nana A’ishah.

Irin wannan sha’ani na daga cikin abubuwa masu matuqar muhimmanci a tarihin musulunci, wanda kuma mutune ke da qwarin guiwa, da karsashin ganin sun riwaito shi, in da ya faru. Ko shakka babu da ya tava faruwa da sun riwaito shi, kamar yadda suka riwaito abubuwa masu kama da shi, daga hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Musamman idan aka yi la’akari da irin yadda riwayoyin da ba su da asali, suka yawaita a kan darajojin Ali. Waxanda madubin ilimi ya tabbatar da kasancewar su qarya. Idan kuwa har mutane za su vata lokaci su riwaito irin waxannan qaryace-qaryace, to babu abin da zai hana su riwaito abin da yake na gaskiya da haqiqa kansa, matuqar ya kai kunnuwansu.

Musamman kuma da yake Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci al’ummarsa da isar da abin da duk suka ji daga gare shi. Don haka wannan magana dai baquwa ce. Ga qarin dalili a kan haka:

A lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu, wani daga cikin Ansaru ya bayar da shawarar a naxa sarakuna biyu; xaya daga cikinsu, xaya kuma daga cikin Muhajiruna. Aka sa qafa aka haure wannan shawara. Tare da tabbatar masa da cewa, babu yadda za a yi a ce madalla da shugabancin nan matuqar ba a hannun Quraishawa yake ba. Kuma Sahabbai sun riwaito hadisai a wurare da dama, daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama inda yake cewa: Shugabanci a hannun Quraishawa yake tabbata.

Har wannan majalisa ta xunkin duniyar musulunci ta ci ta watse, babu wanda ya riwaito wani abu da ke ko ishara zuwa ga shugabancin Ali. Kai ba a ma tava jin haka ba ko a wani zama mai kama da wannan. Qarshe dai musulmi suka yi wa Abubakar mubaya’a. Tattare kuwa da kasancewar a cikinsu akwai da yawa daga cikin banu Abdu-Manafi, Waxanda suka haxa da banu Umayyata da banu Hashimu da wasunsu. Waxanda sun fi son Ali xan Abu-Xalib da kusanta zuwa gare shi fiye da Abubakar. Amma babu xaya daga cikinsu da ya lalabo wannan “nassi”. Haka aka yi a zamanin halifancin Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum. Kai! Ko lokacin da shi Alin Raliyallahu Anhu ya hau gado, ba a ji daga bakinsa, ko na wani daga cikin danginsa, ko na wani daga cikin Sahabbai ba, cewa ya ji wani “nassi” a kan shugabancinsa. Bayan tutar Shi’ah ta fara reto ne aka fara jin xuriyar wannan “nassi”.

4.3 Ayar Cikar Addini

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Hujja ta uku daga cikin Alqur’ani ita ce: Faxar Allah Ta’ala da Ya ce:

ﭽ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﭼ المائدة: ٣

A yau Na kammala muku addininku, kuma Na cika Ni’imaTa a kanku, na kuma yarda musulunci ya zama addini a gare ku (5:3).

Wai saukar wannan ayar ke da wuya, inji xan Shi’ar sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Girma ya tabbata ga Allah a kan kammala addini da tunfaye ni’ima, da yardar da Ubangiji ya yi da manzancina da kuma shugabanci ga Ali bayan na wuce. Daga nan kuma wai sai ya ce: Duk wanda na kasance majivinci gare shi, to Aliyu majivincinsa ne. Ya Ubangiji ka jivinci duk wanda ya jivenci shi. Ka qi duk wanda ya qi shi. Ka taimaki duk wanda ya taimake shi. Ka yarvar da duk wanda yarvar da shi. Qarshen maganar xan Shi’ar kenan.



Martani:

Martaninmu a kan wannan magana zai kasance ta fuskoki kamar haka:



Fuska ta farko:

Bayyana ingancin wannan hadisi kawai ke iya zama dalili ga wannan xan Shi’ah inda yana yiwuwa. Amma jingina shi kawai ga Abu Nu’aimi a matsayin riwaya, ba ta sa ya zama ingantacce. Abu Nu’aimi dai tun farko bai cikin mariwaitan ingantattun hadissai. A littafinsa kowane iri akwai.



Fuska ta biyu:

In ban da a littafin Abu Nu’aimi, wanda ba madogara ne ba, ba inda ake iya samun wannan hadisi daga cikin littafan hadisi da ake dogara da su, ballantana a samar masa wani isnadi ingantacce. Don haka ne ma masana hadisi suka haxu a kan cewa qarya ne.



Fuska ta uku:

Abu ne tabbatacce a cikin littafan ilimi cewa, wannan aya ta sauka ne ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da yake tsayuwar Arafa. Kuma wani mutum daga cikin Yahudawa ya tava ce wa Umar xan Haxxabi: “Ya kai Sarkin Musulmi! Akwai wata aya a cikin littafinku, wadda kuke karantawa. Da mu Yahudawa aka saukar wa ita, da mun riqi ranar saukar ta, ranar idi”. Umar ya ce: “Wace aya ke nan?” Bayahuden ya ce: A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika ni’imata a kanku, kuma Na yarda musulunci ya zama addini a gare ku (5:3). Sai Umar ya ce masa: |Na kuwa san rana da wurin da wannan aya ta sauka. Ta sauka ne a ranar Arafa kuma a filin, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na tsaye”. Dubun dubautar hanyoyi sun tabbatar da wannan riwaya ta Umar.

Kuma ita wannan rana, tana gaban ranar Ghadir Khum da kwana tara. Ta kuma kasance ne ranar Juma’a 9 ga watan Zul-Hajji. To, ta yaya wani zai ce ta sauka ne ranar Ghadir?.

Fuska ta huxu:

Babu wani abu a cikin wannan aya, da ke iya zama dalili a kan shugabancin Ali, ta kowane hali. Iyakar abin da ta qunsa shi ne, labarin da Allah ya bayar na kammalawarsa ga addini da tunfaye ni’ima ga muminai, da yarda da musulunci ya zama addini. Kenan duk wanda ya yi iqirarin cewa, ta wannan hauji ayar ta zama dalili a kan shugabancin Ali, ya sheqa qarya lafiyayya.



Fuska ta biyar:

Addu’ar da xan Shi’ar ya kawo cewa Manzon Allah ya yi, “Ya Ubangiji ka jivinci wanda ya jivinci Ali, ka qi wanda ya qi shi. Ka taimaki wanda ya taimaki shi. Ka yarvar da wanda ya yarvar da shi”. Qarya ce, Annabi bai yi ta ba.

Amma cewa Manzon ya ce: “Duk wanda nake majivinci gare shi, to Aliyu majivincinsa ne”. Malamai nada maganganu biyu a kai. In Allah Ta’ala Ya so za mu ambato su idan lokaci ya yi.

Fuska ta shida:

Sanannen abu ne cewa Addu’ar Annabi ba ta faxuwa qasa; da ya yi da Allah Ya qarva. Amma bai karva wannan ba. Wanda hakan ke tabbatar da cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai yi ta ba. Abin da ke tabbatar da haka shi ne, kasancewar Sahabban Annabi da sauran musulmi sun kasu kashi uku a lokacin da Alin ya zama halifa. Wani kashi ya bi shi, ya zamo rundunarsa, wani kuma ya yaqe shi, wani kuma ya shiga tsakani. Mafi yawan nagartattun magabata na cikin wannan kashi na qarshe.

Wani abin mamaki ma shi ne, bai yi nasara a kan waxanda suka yaqe shi xin ba. Hasali ma su suka yi nasara a kansa. Da mulki ya koma hannunsu kuma, suka darzaza suna ta cin garuruwa, suna share kafirai.

Kuma ya zo cikin ingantaccen hadisi cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Wata jama’a ba za ta gushe daga cikin al’ummata ba, tana taimakon gaskiya ta yadda wanda ya sava masu ko ya yarvar da su, ba zai cuta masu da komai ba, har al’amarin Allah ya zo. Ma’azu xan Jabalu ya ce: Suna Sham.

Hakan ko ta tabbata. Domin ba a tava yin nasara a kan rundunar Mu’awiyah ba. A lokacin da suka yaqi Ali ko kafin haka ko bayan haka. Ka ga kenan Annabi bai yi waccan addu’a ba. Don ga shi rundunar Ali ba ta yi nasara kan ta Mu’awiyah ba. Hasali ma duk da ‘yan Shi’ah, waxanda ke jin Ali nasu ne su kaxai, sun kasance audugar kasuwa; ba a tava jin sun yi kaye ba. Duk wata nasara da ka ji sun yi, sun yi ta ne da taimakon wasunsu: Ko dai musulmi ko kafirai. Tattare kuma da iqirarin da suke yi na kasancewa mataimakan Aliyun. Ina taimakon na Allah da zai samu ga wanda ya taimaki Alin?

Wannan hujja kaxai da wasunta, sun isa tabbatar da kasancewar wannan hadisi qarya.



4.4 Ayar ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭼ النجم: ١ - ٢

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta huxu ita ce: faxar Allah Ta’ala: Ina rantsuwa da tauraron a lokacin da ya faku. Ma’abucinku bai vata ba, kuma bai qetare haddi ba (53:1-2). Xan Shi’ar ya ce: Malamin nan masanin fiqihu Aliyu xan magazili, Bashafi’e, ya riwaito daga xan Abbas, wanda ya ce: Na kasance watarana zaune a wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tare da wasu samari daga cikin banu Hashim. Sai wani tauraro ya faxi. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda wannan tauraron ya faxa gidansa shi ne “Wasiyyina”; wanda zai gade ni, idan na qaura. Sai kawai waxannan samari suka tashi, suka bi sawun tauraron. Sai kawai suka taras ya faxa gidan Ali Raliyallahu Anhu, suka dawo suka gaya wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: Haqiqa ka vace a cikin son Ali. Nan take kuma sai Allah Ta’ala Ya saukar da waxannan ayoyin.



Martani:

Martaninmu a kan wannan magana zai kasance ta fuskoki kamar haka:



Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   29   30   31   32   33   34   35   36   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin