Fuska ta farko:
Muna son xan Shi’ar ya tabbatar mana da ingancin wannan magana, kamar yadda muka saba. Domin kuwa nassi da ijma’i sun tabbatar cewa, magana a kan jahilci haramun ce.
Allah Ta’ala na cewa:
ﭽ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵﯶ ﭼ الإسراء: ٣٦
Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi (17:36).
Ya kuma ce:
ﭽ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﭼ الأعراف: ٣٣
Ka ce; Abin sani kawai, Ubangijina Ya hana abubuwan alfasha; abin da ya bayyana daga gare su da abin da ya voyu da zanubi da cin zalun jama’a ba da wani haqqi ba, kuma da ku yi shirka da Allah, ga abin da bai saukar da wani dalili ba gare shi, kuma da ku faxi abin da ba ku sani ba, ga Allah (7:33)
Duk abin da manzanni suka zo da shi daga wurin Allah dalili ne. Amma dalilin ba ya zama hujja sai an san shi ta hanya ingantatta. Saboda haka duk wanda zai kafa hujja da wani abu da aka ce an samo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama to wajibi ne a kansa ya tantance ingancinsa, kafin ya qudurta shi, ko ya yi aiki da shi, balle ya kafa hujja akan mutane. Kuma ko ya inganta, lalle ne a duk lokacin da ya kafa wa wani hujja da abin, to ya yi masa bayanin yadda aka yi ya inganta. Idan kuwa ya kasa yin haka, to ya zama, malam ba ka da hujja.
Ka ga a haka ba ta yiwuwa ko alama, a kafa hujja a kan wani abu da ya shafi tushen addini da hadisin da ba a san ingancinsa ba. Musamman idan ya kasance, yarda da shi na haifar da zubewar mutuncin zavavvun mutane.
Shi dai wannan xan Shi’ah da za a turke shi, a kan ya faxi lokacin da wannan abu ya faru, ba zai iya ba. Ko ya ce zai iya kuwa qarya yake yi don bai sani ba. Kamar yadda, da za a karva masa cewa: Eh, tafi mun ji, ba ka san lokacin ba. To, faxa mana yadda ka gane cewa riwaya ce ingantatta? Wannan ma ba zai iya ba. Don iya gane haka abu ne da ke da buqatar cikakkiyar masaniya da tarihin mariwaita. Shi kuwa jahili ne a wannan fage. Da kuwa yana da masaniya da halayensu, da ya riga kowa gane cewa wannan hadisi qarya ne.
Idan kuwa har aka yi sa’a tashin fari, ya ce: Ban san komai ba game da hadisin. To, tambayar da za a kashe shi mari da ita ita ce: To don me za ka kafa hujja da abin da baka san ingancinsa ba?
Abu na biyu kuma shi ne, magazili kansa, ba masanin hadisi ne ba. Haka yake kamar Abu Nu’aimi da takwarorinsa. Kuma ba ya cikin masu kawo hadissan qwarai. Hanyarsu xaya da Sa’alabi. Magazili asalatan hadisi ba safararsa ba ne. Ya dai kawai far ma abubuwan da wasu mutane suka tattara ne a cikin littafai, na darajoji da falalolin Ali, ya harhaxa ya rubuta. Kamar yadda Akhdabu Khuwarizm ya yi. Babu xaya daga cikinsu da ya san hadisi. Abubuwan da kowanensu ya riwaito cike yake da Gizo da Qoqin Hadisai. Irin waxanda ko xan sharar makarantar hadisi, na iya gane su.
Fuska ta uku:
Wani kuma abin da ke tabbatar da kasancewar wannan hadisi qarya, shi ne cewa xan Abbas ya shedi saukar Suratun-Najmi, bayan da tauraron ya faxa gidan Ali Raliyallahu Anhu. Alhali kuwa wannan sura na daga cikinsurorin farko da suka sauka a Makka. Shi kuwa xan Abbas ko da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya cika bai balaga ba, yana matashi. Wannan shi ya tabbata a cikin Buhari da Muslimu, daga bakinsa.
Ka ga kenan, lokacin da wannan aya ta sauka, ko dai ya kasance ba a haifi xan Abbas xin ba sam-sam-sam, ko kuma yana yaro, irin wanda ba ya iya gane komai. Domin kuwa ko lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hijira, shekarun xan Abbas ba su wuce biyar ba. A kan haka abu mafi zama kusa da gaskiya shi ne, ko da wannan aya ta sauka, ba a haifi xan Abbas ba. Tunda tana daga cikinsurorin farko da suka sauka na Alqur’ani.
Fuska ta huxu:
Babu inda tarihi ya nuna tauraro ya tava faxowa qasa a Makka ko Madina, ko wasu garuruwa kusa da su. Eh, gaskiya ne, lokacin da aka aiko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ana yawaita jifa da taurari. Amma duk da haka ba a samu cewa, tauraro ya tava saukowa qasa ba. Da hakan ta zama wani abu na keta hankali, kuma sananne a duniya. Hasali ma kai! Wani abu ne da bai tava faruwa a faxin duniya ba, balle ya zama abin kakabi. Kuma babu ma wanda irin wannan labari zai riqa fitowa bakinsa sai mafi wauta daga cikin mutane, wanda kuma ya ce wa musailamu cas; saboda cikar rashin kunya da wasa da addini. Kamar kuma yadda babu wanda zai saurare shi, balle har ya yarda da shi, sai mafi jahilci da wauta daga cikin mutane, wanda ke da wayewa da ilimin da ba su cika cikin cokali ba.
Fuska ta biyar:
A lokacin saukar wannan sura ta Najmu Aliyun kansa yaro ne qarami da bai ko balaga ba, balle a yi zancen aurensa da Nana Fatima. Kuma a lokacin ba a ko farlanta sallah ba, a cikin sigarta ta raka’o’i huxu da uku da biyu. Haka kuma ba a farlanta zakka ko hajji, ko azumi, da sauran muqarraban qa’idojin musulunci ba.
Shi kuwa zancen zaven wani a matsayin Yarima mai jiran gadon Annabci, in har hakan abu ne karvavve, kamata ya yi ya kasance bayan komai ya kammala. Kamar dai yadda suka kitsa tatsuniyar Ghadir Khum. Ka ga ko a kan haka, ba gaskiya ba ne a ce abin ya faru a wancan lokaci.
Fuska ta shida:
Abin da malaman tafsiri suka haxu a kai, dangane da sha’anin wannan aya, ya sava ma wannan tatsuniyar ta ‘yan Shi’ah. Domin su cewa suka yi, wannan tauraro da Allah Subhanahu WaTa’ala Ya yi rantsuwa da shi a farkon surar, ko dai yana nufin tauraro daga cikin taurarin sama ko na Alqur’ani. Babu wanda ya ce wani tauraro ne da ya sauka a gidan wani a Makka.
Fuska ta bakwai:
Ko shakka babu duk wanda ya ce wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya vace, kafiri ne. To, kafirai Annabi yake horo da riqon Ali a matsayin halifansa, ko su yake bar wa wasicci da shi?
Fuska ta takwas:
Idan kuma har wancan tauraro da xan Shi’ar ya ce ya sauka a gidan Ali, aradu ce ta faxa gidansa. To, saukar aradu a gidan mutum ai ba karama ba ce. Idan kuwa ya ce tauraron sama ne, to, ai taurarin sama ba su faxowa. Idan kuwa yula ce, to, shexanu a kan jefa da ita.
To, ko da za mu qaddara cewa, shexanin da aka jefa ne ya sheqa gidan Ali xauke da wutar, to, ai wannan ba wani abu ne da ke nuna xaukakarsa ba. Balle ma dai hakan ba ta tava faruwa ba.
4.5 Ayar Tsarkake Ahlul-Baiti
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta biyar ita ce: Faxar Allah Ta’ala da ya ce:
ﭽ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﭼ الأحزاب: ٣٣
Allah Na nufin Ya tafiyar da qazanta ne kawai daga gare ku, ya mutanen Babban Gida! Kuma ya tsarkake ku, tsarkakewa. (33:33).
Ahmad xan Hambali, inji shi, ya riwaito a cikin Musnadinsa daga Wasilatu xan Asqa’u, wanda ya ce: Na tafi neman Aliyu a gidansa. Sai Fatima Raliyallahu Anha ta ce: Ya tafi wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai ga su sun dawo tare. Suka shigo, ita kuma ta shigo tare da su. Sai Ya zaunar da Aliyu dama gare shi. Fatima kuma a hagu. Hassan da Husaini kuma a gabansa. Sannan ya kundume su cikin mayafinsa, ya karanta wannan aya. A qarshe ya rufe da cewa: “Ya Allah! Ka sheda, haqiqa waxannan su ne mutanen gidana”.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: An samo daga Ummu Salamata, wadda ta ce: “Watarana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cikin gidansa sai ga Nana Fatima Raliyallahu Anha ta shigo xauke da wata tukunyar qarfe, a cikinta da tuwon vula, ta isa da ita wurinsa. Sai ya ce mata: Koma ki kira mani maigidanki da ‘ya’yanki biyu. Nan take sai ga Aliyun da Hasan da Husaini sun iso, suka kuma shigo suka zauna suna cin wannan tuwo. Da shi da su, a lokacin duk suna kan wani mashinfixi nasa. Wanda a qarqashinsa akwai wani bargo Bahaibare”.
Ta ci gaba da cewa: Ni dai ina cikin xaki sai na ji Allah Ta’ala ya saukar da waccan aya. Qare saukar ta ke da wuya, sai kawai ya ja sashen bargon ya lulluve su da shi. Sannan ya xaga hannuwansa ya ce: Waxannan su ne mutanen gidana. Allah ka tafiyar da qazanta daga gare su, ka tsarkake su, tsarkakewa. Yana yi yana maimaitawa. Ta ce, sai na kutsa kaina cikinsu na ce: Ni ma ina daga cikinsu ya Manzon Allah. Sai ya ce: Ina dai yi miki fatar alheri.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Akwai dalili a cikin wannan aya na ma'asumancin Ali. Musamman da aka qarfafa maganar da lafazin “kawai” da saka harafin “Lam” a cikin bayanin Jumlar. Da kuma kevancewa a cikin zancen, ta hanyar amfani da “Ahlul-baiti” (Mutane Babban gida). Da kuma nanata maqasudin maganar, cewa: Ya kuma tsarkake ku. A qarshe kuma aka qara qarfafa ta da “tsarkakewa”. Wannan na nuna ba wani ma'asumi bayansu, inji shi. Saboda haka sai Ali ya zama shugaba. Musamman ma da yake ya sha iqirarin haka, a wurare da dama. Kamar inda ya ce: “Wallahi xan Abu Quhafata (Abubakar) ya karvi halifanci ne kawai. Amma ya san matsayina gare ta matsayin rai ne a cikin gangar jiki”. Kuma tunda har tsarki ya tabbata gare shi, ba zai faxi qarya ba. Ka ga kenan shi ne wanda ya cancanci shugabancin.
To, bari mu duba wannan magana tasa. Shi dai wannan hadisi haka yake. Kuma babu shakka wannan labari ya faru. Nana A’ishah Raliyallahu Anha na da riwaya ga wannan labari. Ga abin da ta ce kamar yadda ya zo a cikin Sahihu Muslim: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita watarana da hantsi, yana yafe da wani gwado mai kauri, wanda aka saqa shi da baqin gashi. Sai ga Hasan xan Aliyu ya zo, sai ya shigar da shi cikinsa. Sannan kuma Husaini ya zo, shi ma ya shigar da shi. Sai kuma ga Nana Fatima ta zo, ita ma ya shigar da ita. Can kuma sai ga Ali ya zo, shi ma ya shigar da shi. Sa’annan ya ce: Allah na nufin ne ya tafiyar da qazanta daga gare ku ya ku mutanen Babban Gida, kuma Ya tsarkake ku, tsarkakewa (33:33).
Wannan hadisi sananne ne, musamman ta hanyar Ummu Salamata wadda ta zo cikin littafin Ahmad da na Tirmizi. Amma dai duk da haka, babu wani dalili a cikin hadisin da ke nuna kasancewar waxancan mutane ma’asumai, ko shugabanni. Ballantana abin da zai keve Ali shi kaxai ba tare da Fatimar ba.
Da farko dai, waccan aya daidai take da xaya ayar wacce Allah ya ce a cikinta:
ﭽ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﭼ المائدة: ٦
Allah ba Ya nufin domin Ya sanya wani qunci a kanku (5:6)
Daidai kuma take da cewar da Allah ya yi:
ﭽ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﭼ البقرة: ١٨٥
Allah Yana nufin sauqi a gare ku, kuma ba ya nufin tsanani a gare ku (2:185).
Haka kuma daidai take da cewar da ya yi :
ﭽ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭼ النساء: ٢٦ - ٢٧
Allah Yana nufin ya bayyana muku, kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suke gabaninku kuma Ya karvi tubar ku. Kuma Allah masani ne mai hikima. Kuma Allah Yana nufin Ya karvi tubarku. Kuma waxanda suke bin sha’awowi suna nufin ku karkata, karkata mai girma (4:26:27)
Wannan kalma ta “Nufi” da aka yi ta nanatawa a cikin waxannan ayoyi, aka kuma danganta ta ga Allah Ta’ala, abin da take nufi shi ne: Allah na son abin nan da ya yi nufi, kuma ya yarda da shi. Ya kuma shar’anta shi ga muminai, tare da umurnin su da aikata shi. Kalmar ba ta nuna Allah Ya riga ya tabbatar da kasancewar abin da ya biyo bayanta, koko ba makawa sai hakan ta faru.
Babban dalili a kan haka shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai wadatu da saukar ayar kawai ba, sai da ya roqi Allah da cewa: “Ya Ubangiji waxannan su ne mutanen gidana, ka tafiyar da qazanta daga gare su, ka kuma tsarkake su, tsarkakewa”. Ka ga wannan roqon tabbatuwar waxancan abubuwa ne yake yi a wurin Allah. Da ayar na nufin abubuwan sun riga sun tabbata, to, ba sai ya yi roqo da fadanci ba. Don babu buqatar haka. Saboda bakin alqalami ya riga ya bushe.
Da kuma ‘yan Shi’ah za su ce mana: Eh, to mun ji waccan aya ta Alqur’ani ba ta nufin tababatuwar wancan nufin da Allah ya yi na tsarkakewa da tafiyar da qazanta. To, amma ai addu’ar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masu na nuni ga haka. Domin kuwa addu’arsa ai ba ta faxuwa qasa ko? Sai muce: Iyakar abin da muke son tabbatarwa a nan shi ne: Shi dai Alqur’ani ba ya xauke da wani abin da ke nuna tababatuwar abin can da xan Shi’ar ke iqirari na tsarkakewa da tafiyar da qazanta. Balle ya tabbatar da ma'asumancin Ali ko shugabancinsa. Shi kuwa riqon hadisi a matsayin dalili, wani abu ne daban.
Mataki na biyu:
Mu xauka cewa Alqur’ani ya tabbatar da tsarkinsu da tsirarsu daga qazanta. Kuma waccan addu’a da Annabi ya yi karvavva ce; dole ne abin da ta kunsa na tsarki da tsira daga qazanta xin can ya tabbata. Babu wani abu a cikin haka da ke nuna kuvuta daga aikata kuskure. Dalili kuwa shi ne: Umurnin da Allah ya yi wa matan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya nufin sun kuvuta daga aikata kuskure. Hasali ma kuskure abin gafartawa ne ga kowa; har su. Abin da salon tafiyar ayar ke nunawa shi ne: Allah na nufin ya tafiyar da qazantar varna da alfasha daga gare su, ya kuma wanke su tsabal daga kowane irin zunubi.
A taqaice dai “tsarkakewa” da Allah ke nufi, kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya roqa ba ta nufin ma'asumanci ittifaqan. A wurin Ahlus-Sunnah babu wani ma'asumi sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. A ya yin da su kuma ‘yan shai’a suke cewa: Ba wani ma'asumi baya ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Imami. Ka ga kenan an samu haxuwar kai a kan cewa wancan ma'asumancin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Imamai suke kevanta da shi, ya koru daga mata da ‘ya’ya mata na Annabin, da ma wasu matan ba su ba.
Idan kuwa haka ne, kenan wancan tsarki da xan Shi’ar ke iqirari, wanda mutanen can huxu suka samu, bai qunshi kasancewarsu ma’asumai ba, irin wancan ma'asumanci da ‘yan Shi’ar suka tabbatar kawai ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Imamu. Kuma waccan addu’a da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi babu wannan ma'asumanci a cikinta; bai roqa wa Ali ko waninsa ita ba. Ya dai kawai roqi Allah ne ya tsarkake su su huxu gangame; bai kevance kowa daga cikinsu da addu’ar ba.
Game kuma da cewar da ya yi wai: Aliyu ya yi iqirarin kasancewarsa mafi cancanta da halifanci. Kuma tun da har tsarkakakke ne daga qazanta, duk abin da ya faxi gaskiya ne, to, ga amsa:
Tun farko mu, ba mu yarda da Aliyu ya yi wannan magana ba. Domin kuwa muna da cikakkar masaniya da cewa, har zuwa lokacin da aka yi wa halifa Usmanu kisan gilla Aliyu Raliyallahu Anhu bai yi wannan furuci ba. Ko da kuwa yana da sha’awa a cikin zuciyarsa na son ganin ya zama halifa. Amma bai tava yin wata kalma mai nuna yana da wani wasicci daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na zama halifa ba da xai.
Mun riga mun sakankance da cewa, duk wanda ya ce Aliyu Raliyallahu Anhu ya tava faxar wata magana mai kama da waccan, to ya xauki alhakinsa. Sanin da muke da shi, na kasancewar Ali Raliyallahu Anhu mai tsaron Allah, ba za ta bari ya furta abin da ba gaskiya ba. Kuma abin da gaba xayan shababai suka san qarya ne.
Kuma cewa matsayin Ali Raliyallahu Anhu ga halifanci kamar matsayin rai ne ga gangar jiki. Kuma wai, Abubakar ya san da haka, ba magana ba ce. Domin kuwa ina aka samo ta? Da za a yi shekarun Abarshi ana bincike ba za a samar wa wannan magana gindin zama ba. Ba inda aka same ta sai cikin Nahjul-Balaga da ire-irensa. Littafin da malamai sun san mafi yawan abin da ke cikinsa ba komai ba ne face zuqi tamallau.
Ya za a kafa hujja da wannan hikaya, wadda sai bayan shekaru xari huxu da rasuwarsayyidina Ali aka fara jin xuriyarta? Lokacin da masu qarin gishiri a cikin tarihi suka yawaita. Saboda gari nasu; sun kafa daula ta kansu, wadda ke karvar duk abin da suka faxa; ko gaskiya ne ko qarya. Babu wanda ke turke su a wannan lokaci ya ce sai sun tabbatar da ingancin abin da suka faxa.
Muna nanata cewa, ba mu yarda Ali ya faxi waccan magana ta wasicci ba. Amma idan kun nace ya faxa bayan ta tabbata qarya, to, sai ku faxa mana in qarya ba ta cikin ababen qazanta da aka tafiyar masa.
Wannan bisa ga taku fassara ta tabbatar da tafiyar da qazantar, ba nufi kawai ba. Babu kuwa wani abu a cikin Alqur’ani da ke tabbatar da tafiyar da qazantar, ko kasancewar qarya da kuskure cikin ayarinta, koko tabbas Ali ya faxi waccan magana. Duk abin da za a faxa don qoqarin tabbatar da kasancewar waxannan riya ce-riya ce gaskiya, kame-kame ne kawai, babu su cikin Alqur’ani. Balle har a ce ga wata hujja cikinsa da ke tabbatar da shugabancin Ali.
4.7 Ayar:
ﭽ ﰂ ﰃ ﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﰋ ﰌ ﰍ ﰎ ﰏ ﰐ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭼ النور: ٣٦ - ٣٧
Hujja ta shida, inji xan Shi’ar ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
Akwai wasu mazaje a cikin gidajen da Allah ya yi umurnin a xaukaka, kuma a ambaci sunansa a cikinsu, suna yin tasbihi a gare shi, safe da maraice. Kasuwanci ko ciniki ba su xauke musu hankali daga ambaton Allah da tsayar da sallah da bayar da zakka. Suna tsoron wunin nan da zukata da gannai ke firgita a cikinsa (24:36-37).
Xan Shi’ar ya ce: Sa’alabi ya ce, ta wani isnadi daga Anas da Buraidata, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karanta wannan aya, sai wani mutum ya miqe tsaye ya ce: “Waxanne gidaje ne waxannan ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Gidajen Annabawa”. Wai sai Abubakar ya miqe tsaye ya ce: “Ya Manzon Allah! Ko gidan Ali na daga cikinsu?” Sai ya karva masa da cewa: “Eh. Shi ne ma mafi girmansu, saboda an siffanta wasu maza da ke cikinsa, da wani abu da ke nuna fifikonsu”. Saboda haka sai Aliyu ya kasance shi ne shugaba. Idan ko ba haka aka yi ba, to hakan za ta wajabtar da gabatar da maqasqanci a kan mafifici.
Martani:
Kafin komai, muna neman wannan marubuci ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya. Domin kuwa kan Ahlus-Sunnah da na Shi’ah ya haxu a kan cewa, jingina magana kawai ga Sa’alabi ba ya zama hujja. Domin Sa’alabi na cikin malaman da ke amsa sunan sunnah kawai bai isa hujja a kan karva duk maganarsa ko da kuwa tana maganar darajar halifa Abubakar ne, sai fa in an tabbatar da ingancinta. Kamar dai xan Shi’ar yana son ne ya ce, ga wani malami nan daga cikinku na kafa muku hujja da shi, don ya faxi abin da ya zo daidai da ra’ayina. To, ai Ahlus-Sunnah gaskiya suke bi ba malamai ba. To. Ta ya ya riwayar fataken dare mai maqoshin kolo a riwaya, wanda ke yaki halas yaki haram; da sahihi da la’ifi duk hajarsa ce take zama hujja akanmu?
Kuma kasancewar wannan hadisi qarya, a idon masana, shi ya sa malaman hadisi ba su ambace shi a cikin littafansu waxanda ake dogara da su ba. Tattare kuwa da cewa, waxansunsu kan xan yi sassafci wani lokaci a kan riwayar masu rauni. Kai wasu ma ana da tabbacin har na qage akwai a cikinsu; sai dai su ne mafi qanqanta a adadi. Amma duk da haka, da za ka ba su warqa-warqa, ba za ka tsinci wannan hadisi da makamantansa a ciki ba. Saboda qaryarsu ta vaci. Ta yadda ba su ambatuwa a cikin irin waxancan kundaye.
Malamai sun haxu a kan cewa wannan aya na magana ne a kan masallaci. Babu kuma wani gida; na Aliyu ko na wani da ya siffanta da waxannan siffofi. Duk musulmi sun aminta cewa, gidan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi na Aliyu daraja, amma ba su ce, wannan aya shi take nufi ba. Kuma babu ma wasu maza a cikin gidan nasa; sai shi xaya, da matan da ke ciki. Shi ya sa lokacin da Allah ya yi magana a kan abin da ya shafi gidan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa ya yi: Kada ku shiga xakunan Annabi (33:53). A wani wurin kuma ya ce wa matan Manzo: Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin xakunanku (33:34).
A cewar xan Shi’ar, kenan duk sauran muminai ba su da wani rabo a cikin ayar. Alhali kuwa wanda ya dubi ayar da kyau zai ga cewa, duk wanda ya siffanta da abubuwan da ta faxa to, yana cikin ta.
Bayan haka kalmar “gidaje” da Allah Ya ambata a cikin ayar, Ya ce kuma Ya yi umurni da a xaukaka su, a kuma ambaci sunansa a ciki, idan yana nufin wata ibada ne ta daban da masallatai ba su kevanta da ita ba; Wato yin zikiri da wasu nafiloli a gida ba masallaci ba, to, duk gidajen muminai na karva wannan sunan, ba ma sai gidajen Annabawa kawai ba, ballantana na Aliyu.
Idan kuwa tana nufin ibadar da masallatai suka kevanta da ita. Kamar sallolin farilla da ba a yi sai a cikin masallatan, to, ai gidan Aliyu ba masallaci ba ne. kuma a haka duk da darajar gidajen Annabawa da kasancewar su Annabawan na zaune a cikinsu ba za su shiga a cikin ayar ba kenan.
To, bisa ga wancan hadisi da ya kawo cewa, ayar tana nufin “Gidajen Annabawa” babu wani gida na wani Annabi a Madina, bayan gidan da matansa Sallallahu Alaihi Wasallama ke zaune. Kenan ba maganar gidan Aliyu Raliyallahu Anhu. Idan kuma suka ce, ai ana nufin gidan da wani Annabi ya taka qafarsa, to, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shiga gidajen da yawa daga cikin Sahabbai, ba na Aliyu kawai ba.
Duk yadda aka kaxa aka raya, ba yadda za a yi a tabbatar da cewa hadisin na nufin gidan Ali a kevance, a matsayinsa na xaya daga cikin gidajen Annabawa ba tare da na takwarorinsa da magabatansa daga cikin Sahabbai ba.
4.7 Ayar Mawaddah
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta bakwai ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣﭤ ﭼ الشورى: ٢٣
Ka ce: Ba ni tambayar ku wata sakayya a kansa, face dai soyayya a cikin zumunta (42:23).
Ahmad xan Hambali ya riwaito, inji xan Shi’ar, a cikin Musnadinsa daga xan Abbas, wanda ya ce: Lokacin da ayar ta sauka Sahabbai sun tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da cewa: Su wane ne makusantanka waxanda soyayyarsu ke wajaba a kanmu? Ya ce: Aliyu da Fatima da ‘ya’yansu biyu. Haka zancen ya zo a cikin tafsirin Sa’alabi, in ji shi. Akwai kuma kwatankwacinsa a cikin Buhari da Muslimu. Babu kuwa wani daga cikin Sahabbai bayan Aliyu da iyalan nasa, da son su ke wajabta. Kenan Ali shi ne mafifici a girman daraja, sai ya kasance shugaba. Sava masa na nuna rashin son sa, kamar yadda xa’a ga umurninsa ke tabbatar da ana son sa. Kenan wajibi ne a yi masa xa’a. wannan kuwa shi ne zama shugaba.
Martani:
Da farko muna son wannan xan Shi’ar ya tabbatar mana da gaskiyar wannan hadisi. Sannan kuma muna tabbatar masa da cewa, Ahmad bai riwaito wannan hadisi a cikin Musnadinsa ba. To, ballantana Buhari da Muslimu. Kai abin da ma ke cikin waxannan littafan na takin saqa ne da hadisin da ya kawo xin. Amma ba mamaki, domin mun san bai san waxannan littafai ba, yana dai amsa kuwwar wasu da ya ji sun faxa ne kawai.
A wurin malamai wannan hadisi qarya ne. Ahlus-Sunnah kuma sun yi ittifaqi a kan cewa Suratus-Shura da wannan aya take cikinta, ta sauka ne a Makka. Da duk wata sura da ke farawa da haruffa. Kowa kuwa ya san Ali bai auri Nana Fatima ba a Makka. Ko a Madinar ma sai bayan yaqin Badar. Ka ga kenan wannan aya ta girmi Hassan da Husaini da shekaru. To, ta yaya za a ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fassara wannan aya da wajabcin soyayya ga wasu makusanta da Allah bai riga ya halitta ba, balle har a san su a so su?!
Tafsirin wannan aya, da ke cikin Buhari da Muslimu, wanda aka samo daga xan Abbas ya sava ma abin da wannan xan Shi’ah ya faxa. Abin da ya zo a cikinsu shi ne, cewar da Sa’idu xan Jubairu ya yi: An tambayi xan Abbas a kan ma’anar wannan aya, sai na yi farat na ce: “Tana nufin kada ku rava ga makusantan Muhammadu ku cutar da shi”. Sai xan Abbas ya ce: “Ka yi gaugawa. Ai ba wani gida na Quraishawa face Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama nada dangi a ciki”. Ya ci gaba da cewa: “Ayar na nufin: Ba ni tambayar ku wata sakayya a kansa. Amma ina roqon ku da ku dubi zumuncin da ke tsakanina da ku”.
To, ka ji ta bakin xan Abbas; masanin Alqur’ani. Kuma mafi ilimi daga cikin Ahlulbaiti, bayan Ali Raliyallahu Anhu. Kuma wannan ita ce fassara, ba fassarar xan Shi’ar ba. Domin soyayya a cikin zumunta ya ce, ba ga zumu ba.
Abin lura a cikin wannan al’amari shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya neman wani sakamako daga kowa, a kan saqon da yake isarwa na Ubangijinsa, har abada. Ladarsa na wurin Allah. Kamar yadda ya ce: Ka ce, “Ba ni tambayarku wata sakayya a kansa kuma ba ni daga masu qaqalan faxarsa (39:36). Da kuma inda ya ce: Shin kana tambayar su wata sakayya ne, saboda haka suka zama masu jin nauyin biyan tarar? (52:40) Da kuma inda ya ce: Ka ce, “Abin da na roqe ku na wani sakamako, to amfaninsa naku ne. Sakayyata ba ta ko ina sai a wurin Allah, (54:47).
Irin togiyar da ke cikin wannan aya ita malaman lugga ke ce ma yankakkiya, saboda banbantar farkon maganar da qarshenta. Kamar yadda Allah ya ce: Ka ce, “Ba ni tambayar ku wata sakayya a kansa sai dai wanda ya so riqa wata hanya zuwa ga Ubangijinsa (25:57). Riqa wata hanya zuwa ga Ubangiji ba sakayya ce ga Manzo ba, haka ita ma qaunar sa saboda zumunta ba sakayya ce garai ba.
Amma fa kar ka zaci muna so ne mu kore wajabcin nuna soyayya ga Ahlul-Baiti. Ko kaxan. So da qaunar mutanen gidan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wajibi ne. Amma ba da wannan aya, wannan wajabci ke tabbata ba. Kuma wannan soyayya ba ita ce ladar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Tana dai daga cikin abubuwan da Allah Ya hore mu da su, kamar yadda Ya hore mu da sauran ibadodi. Duk kuwa wanda ya xauki wannan soyayya ta mutanen Babban Gida, a matsayin wani abu da zai saka wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da shi na lada, to haqiqa ya tafka kuskure, mai girma. Kuma inda a ce haka ne, to da mu ba wata sakayya ta lada da za mu samu a kan haka. Domin kuwa abin da ya cancanta da shi ne, na lada a kan isar da manzancinsa muka ba shi.
Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi wai jivintar halifofi uku na kafin Ali bai wajaba ba, ba gaskiya ba ne. Domin kuwa ai ta tabbata cewa Allah na son su. Duk kuwa wanda Allah ke so, to, ya zama wajibi a kan kowane musulmi ya so shi. Domin son wanda Allah ke so, da qin wanda Allah ke qi wajibi ne. Hasalima ma ha kanshi ne igiya mafi qarfi daga cikin yaggwan imani. Kuma su waxancan halifofin, suna daga cikin manya-manyan waliyan Allah masu taqawa, irin waxanda Allah Ya wajabta jivinta. Kai ta ma tabbata a nassin Alqur’ani cewa Allah Ya yarda da su, su kuma sun yarda da shi. Duk kuwa wanda Allah Ya yarda da shi, to, lalle ko yana son sa. Daga nan zaka gane cewa, son halifofi uku na farko da jivintar su ya fi zama wajibi a kan son Ali da jivintar sa shi kaxai. Domin wajabcin so da jivinta na tafiya ne daidai da xaukaka. Su ko sun fi shi xaukaka babu shakka.
Cewar da xan Shi’ar ya yi wai, sava wa Ali na nuna rashin son sa. Kamar yadda xa’a ga umurninsa shi ne son nasa. Daga nan ya fitar da wajabcin yi masa xa’a da zamowar sa shugaba. Sai mu ce: Idan dai har soyayya na wajabtar da xa’a kamar yadda xan Shi’ar ya ce, to, ai soyayyar ma’abuta kusancin can ta wajaba ko? Kenan su ma wajibi ne a yi masu xa’a. A kan wannan ma’auni kenan wajibi ne musulmi su naxa Fatima Raliyallahu Anha halifanci. Idan kuwa har yin hakan vata ne. To kuwa ko hakan can vata ne.
Abin da ya kamata mu sani shi ne, so da qauna ba su wajabtar da kasancewar wanda ake yi wa su shugaba nan take, ta yadda da zarar son mutum ya wajaba, sai a naxa shi shugaba. Ai son Hassan da Husaini wajibi ne tun kafin su zama shugabanni. Shi ma Ali Raliyallahu Anhu son sa wajibi ne tun Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na raye, ga shi ko bai zama shugaba ba. Amma dai wajabcin son sa na nan duk kuwa da jinkirin da shugabancin nasa ya yi har zuwa bayan kashe Usman.
Wannan na tabbatar da cewa, abin da ke tsakanin ‘yan Shi’ah da Ahlus-Sunnah daidai yake da wanda ke tsakanin Kirista da Musulmi. Kirista sun ce Masihu Allah ne. Amma Ibrahimu da Musa da Muhammadu Alaihimus Salamu ba su kama qafar Sahabban Isah Alaihis Salamu a daraja ba. Haka abin yake a nan. Domin ‘yan Shi’ah sun ce Aliyu shi ne Imami Ma'asumi, ko Annabi, ko ma dai, shi ne Allah. Amma sauran halifofi uku na farko, ba su kama qafar Ashtaru ba da makamantansa. A kan haka ne jahilcinsu da zaluncinsu suka gagari yawun alqalami siffantawa. Domin sun kasance suna godogo da riwayoyin qarya da ruxaxxun lafuzza da mummunan qiyasi, suna kuma ji da iqrarin cewa riwayoyi ne na gaskiya, kai mutawatirai ma. Kuma lafuzzan can nasu nassosa ne qwarara, ga su sarai. Kuma duk hujjar da za su kafa ta hankali, hujja ce gar.
Dostları ilə paylaş: |