Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə36/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   32   33   34   35   36   37   38   39   ...   51

4.14 Ayar: ﭽ ﰆﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﭼ الصافات: ٢٤

Xan Shi’ar ya ce: Hujjar ta goma sha huxu ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma ku tsayar da su. Don haqiqa su, waxanda ake yi wa tambaya ne (37:24). Ya ce, an samo ta hannun Abu Nu’aimi daga Sha’abi daga xan Abbas, wanda ya ce, wannan ayana nufin za a tambaye su ne a kan shugabancin Ali. Haka kuma wai, ya zo a cikin littafin: Al-Firdausi, daga Abu Sa’id Al-Khudri Raliyallahu Anhu daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

Ya ce: Idan har kuwa za a tambaye su, a kan shugabancin Ali, kenan shi ne wanda ya cancanta da shugabancin bisa wajabci. Babu kuwa wanda irin haka ta tabbata a kansa daga cikin Sahabbai sai shi. Kenan shi ne Imamu.

Bismillahi, mun fara:

Tun da har kan malamai ya haxu a kan jingina magana ga littafin Al-Firdaus da na Abu Nu’aimi, ba ya zama hujja, to, muna son marubucin ya faxa mana wata hanya, wadda wannan magana ta inganta tata. Domin ba mu kokwanto cewa, wannan magana an fesa ta ne.

Kuma takin qasar waxannan ayoyi, na takin saqa da yadda xan Shi’ar ya fassara. Domin kuwa cewa Allah Ta’ala Ya yi: Ku tara waxanda suka yi zalunci, da abokan haxinsu, da abin da suka kasance suna bauta wa; wanin Allah. Saboda haka, ku gargaxa su zuwa ga hanyar wutar Jahima. Kuma ku tsayar da su, lalle su, waxanda ake yi wa tambaya ne. Me ya same ku ba ku taimakon juna? A’a su a yau masu miqa wuya ne (37:22-26).

Ka ji abin da Allah Subhanahu WaTa’ala Ya ce. To, kuma ka gani, duk Wannan magana ta shafi mushrikai ne, masu qaryata ranar sakamako. Allah zai tambaye su ne a kan kaxaita shi da Imani da manzanninsa, da ranar qarshe. To, me ya haxa wannan da cewa za a tambaye su ne kan “Son” Ali?

Mu xauka cewa ma suna daga cikin masoyansa. Kana ganin hakan za ta amfane su da wani abu, tattare da kasancewarsu kafirai kuma mushrikai? Ko kuma kana ganin qin da suke yi masa wani abu ne, wanda suka qi Annabawan Allah da littafansa da addininsa, balle Ali?

Kuma ka sani, babu wanda zai yi qarfin halin fassarar Alqur’ani hakan can, har kuma ya jingina fassarar ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai zindiqi, mulhidi, wanda bai san girman addini ba, mai qoqarin bice hasken musulunci. Ko qasurgumin jahili, wanda bai san abin da yake faxa ba. Wai ma shin mene ne banbancin son Ali da son Xalhatu da Zubairu da Sa’adu, da Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum?! Duk xaya ne.

4.15 Ayar: ﭽ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭼ محمد: ٣٠

Xan Shi’ar ya ce: Hujjarsu ta goma sha biyar ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma lalle kana sanin su ga tuntuven harshe (47:30). Abu Nu’aimi ya riwaito da isnadinsa, daga Abu Sa’id Al-Khudri, wanda ya ce: Tuntuven harshen da Allah ke nufi a cikin wannan ayar shi ne, furta qiyayyarsu ga Ali Raliyallahu Anhu. Xan Shi’ar ya rufe maganarsa da cewa: Babu kuwa wanda haka ta tabbata gare shi daga cikin Sahabbai sai Ali. Kenan ya fi su girman daraja. Shi ne kuma Imamu.



Martani:

Da farko, muna neman ingancin wannan batu. Na biyu kuma, mu sanar da kai cewa, malaman hadisi sun qaryata wannan magana da kuka jingina ga Abu Sa’id.

Na uku: Ko da ta inganta cewa Abu Sa’id ya faxi wannan magana bisa qaddarawa, ai shi xaya ne daga cikin Sahabbai. Kan ma’abuta ilimi kuma ya haxu a kan cewa: Idan maganar wani Sahabbai ta ci karo da ta wani Sahabin irinsa, to, ba za ta iya zama hujja ba. Kuma ana sane da irin yadda Sahabbai da yawa ke jin qaiqayi a kan Ali Raliyallahu Anhu kuma bai tava kafa masu hujja da zancen wani Sahabi ba, sai dai da Alqur’ani da sunna.

Na huxu: Fassara wannan aya ta Alqur’ani da irin wannan magana, qarya ce bayyananna. Domin kuwa tuva-tuvan harshen da aka san munafukai da su, ba su qunshi furta qin Ali ba.

Na biyar: Wani abin kuma shi ne: Qyama da qiyayyar da Ali ke yi wa kafirai da munafukai ko alama ba ta kama qafar wadda Umar ke yi musu ba. Don haka ne ma suka fi cin azaba a hannun Umar fiye da Ali. Kai babu wani lokaci da za su haxu da wata azaba a hannun Ali, face qiyayyarsu da Umar ta tsananta.

4.16 Ayar: ﭽ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﭼ الواقعة: ١٠ - ١١

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha shida akan wajabcin shugabancin Ali ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Da waxanda suka gabata iyakar gabaci. Waxannan su ne waxanda aka kusantar (ga Allah) (56:10-11). Abu Nu’aimi ya riwaito daga xan Abbas, wanda wai ya ce: waxanda suka gabata a cikin ayar na nufin Ali. Kuma wai Ibnul-Magazili ya riwaito daga xan Abbas, wanda ya ce: “Yusha’u xan Nuni ya riga kowa a wajen Annabi Musa. Shi Musa ya riga kowa a wajen Haruna. Ma’abucin Yasin ya riga kowa ga Annabi Isa. Shi ko Aliyu ya riga kowa ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama”. Kuma babu wanda ya sami wannan daraja da xaukaka daga cikin Sahabbai sai Ali. Saboda haka shi ne Imamu kenan. Inji xan Shi’ar.



Martani:

Kasancewar ana samun qaryace-qaryace da yawa, a cikin abubuwan da, waxannan malamai da xan Shi’ar ya kafa hujja da su ke riwaitowa, muna neman marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan naqali. Domin Ibnu Abbas bai faxi wannan magana ba. Ko da kuma ya inganta cewa ya faxe ta, ba za ta zama hujja ba, matuqar zancen nasa ya ci karo da na wanda ya fi shi qarfi.

Kuma ai cewa Allah Ta’ala Ya yi: Kuma magabatan farko daga Muhajiruna da Ansaru da waxanda suka bi su da kyautatawa, Allah Ya yarda da su, su kuma sun yarda da shi, kuma Ya yi masu tattalin gidajen Aljanna: qoramu suna gudana a qarqashinsu (9:100). Ya kuma ce: Sa’anna mun gadar da littafin, ga waxanda muka zava daga cikin bayinmu. Kuma daga cikinsu, akwai mai zalunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsa kaitawa, kuma daga cikinsu akwai mai gabata da ayyukan alheri da izini Allah (35:32).

Magabatan farko, da waccan aya ta yi bisimilla da su, su ne fa waxanda suke bayar da dukiyarsu tun kafin qarfin musulunci, suka kuma yi jihadi. Su ne kuma mafiya xaukaka a kan waxanda ba su bayar da dukiyarsu ko suka yi jihadi ba, sai bayan xaukakar addini, kamar yadda ya ce. A cikinsu kuwa har da waxanda suka yi Bai’atur-Ridhwani, adadinsu bai kasa mutum dubu xaya da xari huxu ba. To ya za a ce wani mutum xaya ya yi wa irin wannan al’umma fintinqau?!

Kuma cewa wannan falala ta riga zuwa ga musulunci, ba ta tabbata ga wani daga cikin Sahabbai ba sai Ali, ba gaskiya ba ce. Malamai da sauran al’umma, sun qari junansu sani a kan wanda ya fara musulunta; Abubakar ne ko Ali.

Amma abin lura a cikin wannan magana shi ne; ko da Ali ya riga musulunta, an yi ittifaqi a kan cewa, yana yaro ne qarami a lokacin, wanda ba mukallafi ba. Don haka babu wani kokwanto a kan cewa musuluncin Abubakar Raliyallahu Anhu ya fi kamala da amfani. Ka ga kenan a haka, kan malamai ya haxu a kan kasancewar musuluncin Abubakar Raliyallahu Anhu marigayi ga kamala. Akwai ma waxanda suka ce ya riga Alin musulunta, ba tare da wata togiya ba. To, ta yaya za a ce Aliyu ya riga shi musulunta, alhali kuwa babu wani dalili ko hujja a kan haka?!.



4.17 Ayar:

ﭽ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﭼ التوبة: ٢٠

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha bakwai ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Waxanda suka yi imani, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihadi, a cikin hanyar Allah, da dukiyoyinsu, da rayuwarsu, su ne mafi girma ga daraja, a wurin Allah (9:20).

Sannan ya ce, Ruzainu xan Mu’awiyah ya riwaito a cikin littafin: Al-Jam’u Bainas-Sihahis-Sitta cewa, wannan aya ta sauka ne a kan Ali, lokacin da Xalhatu xan Shaibata da Abbas suka yi wani alfahari. Babu kuwa wani Sahabi da ya sami irin wannan xaukaka sai Ali. Kenan shi ne mafifici daga cikinsu, kuma Imamu. Inji xan Shi’ar.



Martani:

Martaninmu a kan wannan magana zai kasance kamar haka:

Muna neman marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan magana. Domin kuwa Ruzainu ya ambaci wasu abubuwa a cikin littafinsa, waxanda ba su da inganci.

Na biyu: Abin da ya zo a cikin Buhari ya sava wa abin da Ruzainu ya ambata. Abin da Nu’umanu xan Bashiru ya riwaito a cikin Buhari, cewa: Na kasance gindin munbarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai wani mutum ya ce: Ba zan damu da ban aikata wani aiki bayan musulunci ba, in na shayar da alhazai ruwa ba. Wani kuma ya ce: Ba zan damu da ban aikata wani aiki ba bayan musulunci, in na yi hidimar masallacin Harami. Wani kuma ya ce: Duk jihadi a tafarkin Allah ya fi waxannan abubuwa da kuka ambata daraja. Nan take sai Umar Raliyallahu Anhu ya kwatse su, ya ce: Ku daina xaukaka sautukanku gindin minbarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma ga shi yau juma’a. Amma ku bari idan an qare sallar juma’a, in shiga in yi wa Annabi fatawa a kan wannan abu da kuke savani a kansa. Nan take sai Allah Ta’ala Ya saukar da: Shin kun sanya shayar da mahajjata da rayar da masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, kuma ya yi jihadi a cikin hanyar Allah? Ba su daidai a wurin Allah (9:19). Muslimu ne ya fitar da hadisin.

Wannan ingantaccen hadisi na tabbatar da cewa, maganar Aliyu Raliyallahu Anhu ta fifita jihadi a kan hidimar masallacin da shayar da mahajjata, ta fi inganci bisa maganar waxancan Sahabban biyu da suka fifita waxannan abubuwa biyu a kan jihadi. Kenan Aliyu Raliyallahu Anhu shi ne mafi dacewa da gaskiya a cikin wannan mas’ala, a kan waxanda suka yi ja-inja da shi. Wannan ko shakka babu gaskiya ne.

Amma kuma wancan zance na fifiko ta hanyar Imani da Hijira da Jihadi, riga ce da ta shiga wuyan gaba xayan Sahabbai, waxanda suka yi imani, da hijira, da jihadi. Babu wata daraja da Ali ya kevanta da ita a nan.



4.18 Ayar Ganawa

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha takwas ita ce: Faxar Allah Ta’ala:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛﭜ ﭼ المجادلة: ١٢

Ya ku waxanda suka yi imani! Idan za ku gana da Manzon Allah, to, ku gabatar da ‘yar sadaqa a gabanin ganawarku (58:12).

Wai an samo, inji shi, daga hannun Hafiz Abu Nu’aimi zuwa ga xan Abbas, wanda ya ce: “Haqiqa wannan aya na bayyana, Allah Subhanahu WaTa’ala Ya haramta ganawa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai tare da an gabatar da wata ‘yar garawa. Amma haka ba ta sa Sahabbai suka riqa gabatar da sadaqar ba; sai kowa ya qi. Aliyu Raliyallahu Anhu ne kawai ya gabatar da ita. Babu wani daga cikin musulmi da ya yi haka bayan sa”.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: An samo a cikin tafsirin Sa’alabi, cewa xan Umar ya ce: “Wasu darajoji uku sun kasance ga Ali Raliyallahu Anhu Waxanda da zan sami xaya daga cikinsu, da ta fi soyuwa gare ni a kan garken jayayen raqumma. Na farko, Aurar masa da Fatima. Na biyu, danqa masa tuta da aka yi ranar yaqin Haibara. Na uku kuma, Saukar ayar Munajati a kansa”.

Kuma wai Ruzainu xan Mu’awayya ya riwaito daga Aliyu Raliyallahu Anhu wanda wai ya ce: “Babu wanda ya yi aiki da wannan aya sai ni. Kuma a dalilina ne Allah Ya sassafta wa wannan al’umma”. Wannan kuma na nuna kasancewarsa mafifici a kan sauran Sahabbai. A kan haka kuma shi ne mafi cancanta da shugabancin, inji xan Shi’ar fa, ba inji ni ba.



Martani

Eh, abu ne tabbatace cewa Ali Raliyallahu Anhu ya gabatar da wata ‘yar sadaqa a lokacin da buqatar ganawa da Manzon Allah ta kama shi, kamar yadda ayar ta umurta. Amma kuma sai Allah Subhanahu WaTa’ala Ya hukunci shafe ayar kafin buqatar ganawa da Manzon ta kama wani Sahabi bayan Alin, balle har ya gabatar da garawar.

Amma kuma abin lura a nan shi ne, ayar ba ta wajabta wannan sadaqa a kan Sahabbai ba, ta dai umurce su da yin ta ne idan buqatar ta same su. Ka ga kenan wanda buqatar ba ta kama ba, babu wannan sadaqa a kansa. Tunda kuwa har ganawar ba wajibi ce kansu ba, kenan sadaqar ma ba wajibi ba ce. A kan haka ba za a zargi kowa ba, idan ya yi biris da abin da ba wajibi ba. Haka kuma duk wanda ba ya da ikon gabatar da sadaqar daga cikinsu, wanda kuma tabbas da buqatar ganawar za ta kama shi, ta kuma taras da ikon gabatar da sadaqar, da ya gabatar. To, ko ganawar irin wannan ya yi hannu biyu, yana da ladar niyya. Shi kuwa wanda buqatar ganawar ba ta kama ba, balle ya gabatar da garawar ko yana da ikon yin haka, ba za a ce masa kasasshe ko naqqasasshe ba. Kai ko da wanda ganawar ta maqare ya kuma yi, amma saboda matsolanci ya kasa gabatar da sadaqar komai, ba za a yi masa kallon hadarin kaji ba, don mustahabbi ne kawai ya bari. Wannan kuma ba ya daga cikin halin Sahabbai halifofi balle a shede su da shi.

Haka kuma babu wanda zai iya ce maka yana da wata masaniya a kan kasancewar halifofin can uku halarce lokacin da wannan aya ta sauka. Abu ne mai sauqi ko da aka saukar da ita wasu daga cikinsu ba su nan. Ko kuma ta kasance babu abun sadaqar hannu a lokacin. Ko ma kai babu buqatar ganawar sam-sam, ga wasunsu.

Kada ka yi mamakin waxannan hasashe-hasashen. Domin kuwa ana da tabbacin cewa shiga shantun qadangare ayar ta yi wa duniyar Sahabbai, nan take aka shafe ta. Balle ko kace ta xauki wani lokaci mai tsawo da yake da wuya a ce buqatar ganawar ba ta kama wani daga cikinsu ba.

Da kuma za mu qaddara ta kama su xin amma kuma ba su gabatar da sadaqar ba, suka kuma ganar, hakan ba komai ba ne. domin kuwa mun riga mun yi bayani a wurare da dama cewa, aikata mustahabbi da wani zai yi, ba ya wajabta kasancewarsa mafificin daraja, kai tsaye a kan wanda bai aikata ba.

Hasali ma Tirmizi ya riwaito hadisi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ke cewa: “Ba ya kamata ga mutanen da Abubakar yake a cikinsu, wani wanda ba shi ba ya yi masu limanci”.

Kuma ai ka ga raquma dubu da halifa Usmanu ya raka wata ruduna ta musulmi da su, sun fi qarfin waccan ‘yar sadaqa da Aliyu ya yi nesa ba kusa ba. Domin kuwa ko banza ciyar da dukiya domin jihadi farilla ne. Savanin waccan ‘yar sadaqa domin ganawa, wadda kawai aka sharxanta a kan wanda buqatar ganawar ta kama; ta yadda wanda bata kama ba, sadaqar ba ta ko hau kansa ba.

Kuma harwayau ka ga a kan wasu Ansaru ne dai, Allah Ta’ala Ya saukar da: Kuma suna fifita waxansu a kan kawunansu, ko da suna da wata lalura (59:9) .

A taqaice, idan ana zancen bajinta a fagen ciyar da dukiya a kan tafarkin Allah da wasu al’ammurra na addini, ba a zancen Ali Raliyallahu Anhu. Da yawa daga cikin Muhajiruna da Ansaru sun yi masa fintinqau a fagen; sun sami darajar da bai samu ba. Domin kuwa Allah bai hukunce shi da mallakar wata dukiya ba a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.



4.19 Ayar :

ﭽ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﭼ الزخرف: ٤٥

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha tara ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma ka tambayi waxanda muka aika a gabaninka daga Manzanninmu (4:45)

Wai Abu Nu’aimi ya fitar da cewa, Allah ya tara Annabawa tare da Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama daren da aka yi Isra’i da shi. Sannan Ya ce masa: “Ka tambaye su ya kai Muhammadu cewa: A kan me aka aike ku? Wai sai suka ce: An aike mu ne don tabbatar da ba wanda ya cancanci bauta sai Allah. Da kuma iqirarin Annabcinka da shugabancin Aliyu xan Abu Xalib”. Xan Shi’ar ya shafa fatiha da cewa: Wannan magana ce ga-ta-sarai, da ke tabbatar wa Ali da shugabanci.



Martani:

Muna neman marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan magana. Amma kuma kai mai karatu, kada ka yi zaton neman da muke wa wancan marubucin da ya tabbatar mana da ingancin wannan mummunar qarya da makamantanta, sakamakon shakkar da muke da ita ne a kan kasancewar su qarya da xumi-xuminta. Ko alama ba haka abin yake ba. Muna yin haka ne, don bayar da ‘yar sanyi ga abokin tattaunawarmu. Domin da ba mu da masaniya da kasancewar maganganu nasa qarya, to, da ba mu kafa hujja da su ba, ta hanyar neman ya tabbatar da ingancinsu. Domin kuwa yin haka kamar kafa hujja ne da abin da ba a san ingancinsa ba, wanda kuwa yin haka ba ya halatta ittifaqan.

Duk wani xan makaranta da ya sanya qafarsa a cikin ilimin hadisi ya san ko shakka babu, wannan magana shegiyar nan ce ‘yar gidan Musailamu. Kuma varna ce da duk mai hankali da kishin addini ba zai gasgata ba. Babu kuma ba mai qirqira irin waxannan maganganu sai wawayen mutane marasa kunya. Ta yaya za’a tambayi Manzanni Alaihis Salamu a kan abin da ba ya cikin tushen imani?

Hasali ma gaba xayan musulmi sun haxu a kan cewa; Yau da mutum zai yi imani da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kuma bi shi sau da qafa, ya kuma rasu Annabin na raye, ba tare da ya san Allah Ya halicci wani da ake kira Abubakar ko Umar ko Usmanu ko Aliyu ba, hakan ba za ta cutar da shi da komai ba, balle ta hana shi shiga aljanna.

To, idan har wani daga cikin al’ummar Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama na da irin wannan garanti, ya za a ce yana wajaba a kan Annabawa Alaihimus Salamu su yi imani da wani daga cikin Sahabbai?! Wannan ba ta savuwa; wai bindiga a ruwa.

4.20 Ayar: ﭽ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭼ الحاقة: ١٢

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi) (6:12)

Ya ce: Sa’alabi ya faxi a cikin tafsirinsa cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Na roqi Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya sa kunnen nan ya kasance naka, ya kai Ali”. Haka kuma an samo ta hannun Abu Nu’aimi, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ya kai Ali! Haqiqa Allah Ya umurce Ni da in ja ka a jiki, in kuma karantar da kai don ka kiyaye. Saboda haka ne ma aka saukar mani da wannan aya. Kuma kai ne kunnen mai kiyayewa”.

Xan Shi’ar ya qara da cewa: babu wanda ya sami wannan xaukaka sai Ali. Saboda haka shi ne shugaba.



Martani:

Da farko muna neman bayani a kan ingancin madogarar wannan magana. Domin kuwa Sa’alabi da Abu Nu’aimdu na riwaito abubuwan da ba su iya tsayawa a matsayin hujja, bisa haxuwar kan malamai. Sannan kuma, masu ilimi sun haxu a kan cewa wannan hadisi qagagge ne.

Wannan ayoyi ba tana magana ne a kan kunnen wani mutum xaya daga cikin mutane ne ba. A’a, magana ce da ta shafi gaba xayan ‘ya’yan Adamu. Karanto daga farko ka ji. Allah ya ce: Lalle ne mu, a lokacin da ruwa ya qetare haddi, mun xauke ku a cikin jirgin ruwan nan. Domin Mu sanya shi, abin tunawa gare ku, kuma duk kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi) (69:12).

Hore ma ‘yan adam hawan jirgin ruwa, na daga cikin manya-manyan ayoyin Allah. Dubi abin da a wani wurin Allah Yake cewa: Kuma aya ce a gare su kasancewar haqiqa mun xauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lodin. Kuma muka halitta masu abin da suke hawa daga irinsa (36:41-42) Ya kuma ce: Ashe, ba ka ga lalle jirgin ruwa na gudana ba a cikin teku da ni’imar Allah, domin ya nuna muku daga ayoyinsa? Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga dukan mai haquri, mai godiya (31:31). To, ta yaya za a yi duk wannan al’amari ya taqaita ga buqatar kiyayewar kunnen wani mutum xaya daga cikin mutane?

Gaskiya ne. Kunnen Ali Raliyallahu Anhu na xaya daga cikin waxannan kunnuwa masu kiyayewa. Kamar yadda ba mai musun kasancewar kunnuwan Abubakar da Umar da Usmanu da wasunsu Raliyallahu Anhum daga cikin waxannan kunnuwa. Ka ga kenan abin bai kevanci Aliyu kawai ba. Wannan kuwa kowa ya san da shi; ba kunnen Ali ne kawai mai iya kiyaye waxancan ni’imomi na Allah ba.

Ko kana ganin kunnen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba kunne ne mai kiyayewa ba? Ko kuma kunnen Hasan da Husaini da Ammaru da Abu Zarri da Miqdadu da Salmanul-Farisi, da Sahalu xan Hunaifu, da sauran mutanen da ‘yan Shi’ah suka yarda suna da imani. Duk kunnuwansu ba su daga cikin kunnuwa masu kiyayewa?

Idan kuwa har akwai waxansu mutane da ke da irin waxannan kunnuwa masu kiyayewa, bayan Ali, to, cewa wannan falala ba ta samu ga kowa ba sai shi, wasa da hankali ne.

A haka kuma, ko shakka babu, wannan xan Shi’ah, ya yi jahilci da zalunci, don ya gina al’amurransa a kan turbar qarya saboda ya vatar da mutane. Ta kuma tabbata cewa babu wata qungiya daga cikin qungiyoyin bidi'a da ta riqi sungumin ragga a matsayin makami kamar ‘yan Shi’ah. Savanin Mu’utazilawa da makamantansu, waxanda ke da wasu hujjoji da dalilai da ke rikita hankalin da yawa daga cikin ma’abuta ilimi da hankali. Amma ‘yan Shi’ah, ba su tava mallakar wata hujja da wani ke iya gamsuwa da ita ba, face jahili da azzalumi da mai biyar son zuciya. Wanda ke karvar duk abin da ya dace da ra’ayinsa; gaskiya ne ko qarya.



4.21 Surar: ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﭼ الإنسان: ١

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da xaya ita ce: Suratul Insan. Ya ce: Ya zo a cikin tafsirin Sa’alabi, ta hanyoyi da dama, cewa: Watarana Hasan da Husaini sun kwanta rashin lafiya. Sai kakansu Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi duba su tare da gangami na xaukacin Larabawa. Sai suka ce: “Ya kai baban Hasan! me zai hana ka yi alkawarin azumi, godiya ga Allah idan ‘ya’yan nan naka sun warke?” Sai ko ya sha alwashin azumin kwana uku. Haka nan mahaifiyarsu Fatima da kuyangar gidansu Fiddhatu, su ma suka yi. Sai kuwa Allah Ya ba su sauqi. A lokacin kuwa babu qwaya balle tiya a gidan Muhammadu. Saboda haka sai Aliyu ya ranto sa’i uku na alkama. Nan take Fatima ta gurje sa’i xaya. Ta toya curi biyar na waina da shi, domin kowanensu ya samu xaya.

Bayan da Ali Raliyallahu Anhu ya qare sallar magariba tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya iso gida sai aka kawo abincin aka xora a gabansa. Haka ke da wuya, sai wani almajiri ya yi sallama, yana cewa: Ga wani miskini daga cikin talakawan musulmi. Ku taimakan da sadaqar abin ci, Allah Ya saka maku da na aljanna. Ali na jin haka, sai ya yi umurni da a xauki gaba xayan abincin can a ba shi. Haka kuwa aka yi. Su kuwa a wannan dare da yininsa, suka zauna haka nan, ba su saka komai bakin salati ba sai baqin ruwa.

Kashegari kuma Fatima ta toye sa’i guda. Sai abin da ya faru jiya ya sake faruwa da wani almajiri daga cikin bayi. A rana ta uku aka sake maimaita labarin jiya da na shekaranjiya, amma tare da wani maraya wanda ya yi masa koken an kashe babansa ranar yaqin Aqaba. Suka kwana uku ba su saka komai a bakinsu ba, ga su ko suna azumi.

Rana ta huxu na kamawa, bayan alwashin da suka sha na azumin kwana uku ya cika, sai Aliyu ya kama Hasan da hannunsa na dama, Husaini kuma da na hagu. Ya tasar wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama iska na kaxa su kamar yadda yake kaxa ‘yan tsaki, saboda tsananin yunwa. Ganin su haka ke da wuya sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wannan hali da na gan ku a ciki, shi ne abin da ya fi komai baqanta mani rai. Ku tashi mu isa gidan ‘yata Fatima in ji yadda aka yi”. Isarsu ke da wuya, suka taras da ita kwance cikin xaki fatar cikinta ta lahe ga qashin bayanta. Saboda tsananin yunwa, har idanunta sun yi kogo. Da Annabi ya gan ta cikin wannan hali, sai ya ce: “Allah ka agaje mu, yau ga mutanen gidan Muhammadu yunwa na shirin kashewa”.

Nan take sai Jibrilu ya sauka yana mai cewa: Ya kai Muhammadu, saurari abin da Allah ke taya ka murna da shi, a kan abin da ya sami mutanen gidanka. Sai Annabi ya ce: Mene ne wannan abu ya kai Jibrilu? Sai ya karanta masa:

ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﭼ الإنسان: ١

Lalle ne mudda ta zamani ta zo a kan mutum wadda bai zamo wani abin ambato ba a cikinta (75:1).

Xan Shi’ar ya ce: Wannan falala ce mai tarin yawa, da wani bai samu ba kafin Ali Raliyallahu Anhu wadda kuma ke nuna cewa shi ne mafifici a kan duk wanda ba shi ba. Shi ne kuma Imamu kenan.

A nan sai mu ce: Qanqurus qan qusu.

Martani:

A wannan karon ba mu ko buqatar a tabbatar mana da wannan tatsuniya. Mun dai gaji da waxannan riwayoyin Sa’alabi marasa kan gado. Kuma irin riwayoyinsa da na ire-irensa ba su raba gardama koda a mas’ala ta mustahabbi balle aqida, ballantana fassarar Alqur’ani da bayanin dalillan saukar sa.

Ma’abuta ilimin hadisi a matsayinsu na jagorori masu yanke hukunci a cikin wannan sha’ani, sun yi ittifaqi a kan kasancewar wannan hadisi qarya. Kuma zancensu shi ne, abin kamawa a wannan babi.

Daga cikin abubuwan da ke tabbatar da kasancewar wannan hadisi qarya har da cewa, kowa ya sani Ali Raliyallahu Anhu bai auri Nana Fatima ba sai a Madina. Bai kuma yi baiko da ita ba sai bayan yaqin Badar. Bayan haka ne kuma aka haifi Hasan da Husaini, tsakanin shekara ta uku da huxu bayan hijira. Ita kuma wannan sura ta sauka ne a Makka kamar yadda malaman tafsiri da riwaya suka haxu a kan haka. Wannan ko yana qarfafuwa da salon tafiyar surar wanda masana suna gane na surorin Makka ne.

To, ka ga kenan duk wanda ya ce: Surar ta sauka ne bayan rashin lafiyar Hasan da Husani, ya tabbata maqaryaci, don ba a halicce su ba lokacin saukarta.

Kuma yin nazarin qwaqwaf ga takin qasar wannan hadisi da lafuzzan da ke cikinsa, ya ishi mutum gane cewa tatsuniya ce da jahilai suka qirqira. Xan kalli cewar da xan Shi’ar ya yi wai, kakansu ya je duba su, tare da gangamin xaukacin Larabawa. To, duk wanda ya san tarihi, ya san cewa faxin wannan magana a Madina jahilci ne. xaukacin Larabawa da suke kafirai za su je duba shi?

Kuma don Allah dubi cewar da ya yi wai Larabawa sai suka ce: Ya kai baban Hasan! Me zai hana ka sha alwashin, don godiya ga Allah idan ‘ya’yan nan naku biyu sun sami sauqi. Alhali kuwa Aliyu ba ya karvar wani abu na addini daga Larabawan. Alwashi kuwa addini ne. A’a yana karva ne daga wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Inda ha kan wani umurni ne na xa’a ga Allah, to, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya kamata ya hore shi da shi, bisa cancanta ba waxannan Larabawa ba. Idan kuwa hakan ba xa’a ba ce, kai ka san ko sun hore shi ba zai aikata ba. To wai, ta yaya ma zai saurare su, ba tare da ya waiwayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan lamarin ba?!

Ya tabbata a cikin Buhari da Muslimu cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana irin wannan alwashi, da ya ce: Haqiqa alwashi ba ya tahowa da alheri, ana dai matse marowaci ne kawai da shi.

Idan kuwa har Aliyu da Fatima da suran mutanen gidansu ba su san da wannan magana ta Annabi ba, wadda gaba xayan Al’umma ta sani, to tasgaro ya tabbata a cikin iliminsu. To, in haka ne, ina maganar ma'asumanci ta kwana?

Idan kuwa har suna da masaniya da haka, suka kuma aikata abin da Allah da Manzonsa ba za su gode ba, to, babu wata lada da za su samu a ciki. Tunda har an hana su daga hakan; hani na haramci ko na karhanci. Runtse ido su aikata hakan kuwa, na tabbatar da rashin cikar addininsu ko hankalinsu ko iliminsu, in kun yarda.

Aliyu da Fatima ba su da wata kuyanga da ake kira Fiddatu. Kai ba su ba, ko cikin makusantan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama babu mai ita. Babu ma wata kuyanga a faxin garin Madina da aka sani da wannan suna. Babu wani ma’abuci ilimi da ya ambaci wannan kuyanga a cikin tarihin waxannan mutane.

Abin dai da ya tabbata a cikin Buhari, shi ne cewa, wani Sahabi daga cikin Ansaru ya fice wa wani baqonsa abincinsa na dare, ya lallashi qananan ‘ya’yansa suka yi barci. Shi da matarsa suka kwana wahalce. A kan haka ne ma Allah Ta’ala Ya saukar da: Kuma suna fifita waxansu a kan kawunansu, kuma ko da suna da wata lalura (59:9).

Kuma ko shakka babu, wannan yabo da Allah ya yi ma wannan Ansari, ya fi wanda ya yi a cikin ayar Suratul Insan da suke zaton ta sauka a kan Ali, wadda ta ce: Kuma suna ciyar da abin ci, a kan suna buqatarsa, ga matalauci da maraya da fursuna (76:8). Don wannan yana daidai da inda Allah Ya ce: Kuma ya bayar da dukiya, a kan yana son ta, ga mai zumunta da maraya da, matalauta (2:177).

Kuma a cikin wannan qissa da xan Shi’ar ya qaga, akwai abin da bai dace a jingina shi ga Aliyu da Fatima ba. Saboda abin ya sava wa abin da shari’a ta yi umurni da shi; wato barin qananan yara cikin lalurar yunwa har tsawon kwanaki uku. Ta hanyar sa su yin xoreri na kwanakin. Irin wannan yunwa na vata hankali da jiki da addini. Ka sani kuwa wannan bai yi daidai da qissar Ba ansaren nan ba. Domin shi dare xaya ne kawai ya bar ’ya’yan nasa, ba tare da sun ci abin ci ba, alhalin kuma ba su yini da azumi ba. Ka ga ai qananan yara na iya daure wannan, savanin kwanaki uku; yini da dare.

Wani abun kuma shi ne, cewar da xan Shi’ar ya yi a cikin wannan tatsunita wai marayan can ya ce: “Mahaifina ya rasu ranar yaqin Aqabah”. Ita ma wannan magana qarya ce bayyananna. Domin kuwa babu wani yaqi da aka yi a wannan dare na Aqabah. Illa dai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya karvi bai’ar Ansaru a wannan dare kafin a yi hijira, balle a yi umurni da jihadi.

Wannan magana na nuna cewa bayan kasancewar wannan hadisi qagagge, yana daga cikin qaryace-qaryace da jahilan mutane waxanda ba su san tarihin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba suka qago. Domin da xan Shi’ar ya ce, marayan ya ce: “Mahaifina ya rasu ranar yaqin Uhudu”. Da hakan tafi zama kusa ga gaskiya. Kuma ai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya xauke nauyin gaba xayan yaran waxanda suka yi shahada tare da shi. Saboda haka ne ma ya tava gaya wa Fatima Raliyallahu Anha a lokacin da ta roqi ya samar mata mai hidima, cewa: “Ba zan qyale marayun Badar ba, in xauki nauyin samar maki mai hidima”

.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   32   33   34   35   36   37   38   39   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin