4.22 Ayar: ﭽ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭼ الزمر: ٣٣
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da biyu ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gasgata a game da ita, waxancan su ne masu taqawa (39:33).
Ya ce: An samo daga hannun Abu Nu’aimi daga Mijahidu cewa: Wanda ya zo da gaskiyana nufin: Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama. Wanda kuma ya gasgata a game da ita na nufin Ali xan Abu Xalib Raliyallahu Anhu. Wai kuma an samo ta hannun malamin nan masanin fiqihu Bashafi’e – Ibnul Magazili – daga Mujahidu cewa, ayar na nufin: Muhammadu ya zo da gaskiya, Aliyu kuma ya gasgata shi.
Xan Shi’ar ya ciga da cewa, wannan falala ce da, Aliyu ya kevanta da ita. Shi ne Imamu kenan.
Martani:
Martaninmu a kan wannan magana zai kasance ta fuskoki kamar haka:
Fuska ta farko:
Wannan magana da xan Shi’ar ke yi, ba a cirota ta daga bakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Sannan maganar Mujahidu shi kaxai ransa, ba ta zama hujja, idan ma har ta inganta. To, ina ga ba a da tabbacin shi ya faxe ta? Tare kuma da masaniyar da ake da akan qaryar wanda ya xauko ta?.
Duk da haka kuma dai, abin da ta tabbata daga Mujahidu ya ci karo da wannan. Domin kuwa cewa ya yi: kalmar “Gaskiya” a cikin ayar na nufin “Alqur’ani”. A ya yin da ta “wanda ya gasgata” ke nufin mumini matuqar ya yi aiki da ita. Ka ga kenan shi a wurinsa ayar, gama-gari ce.
Fuska ta biyu:
Ko shi wannan tafsiri da ya tabbata daga Mujahidu, abin da ya shahara a wurin ma’abuta tafsiri ya ci karo da shi. Domin kuwa shugaban sahun masu tafsiri, wato Imamux-Xabari, ya ambaci wata riwaya, wadda ya danganta ga Ali Raliyallahu Anhu ta hanyar isnadinsa. Wadda yake cewa a cikinta: Wanda ya zo da gaskiya a cikin ayar na nufin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama. Wanda kuma ya gasgata na nufin Abubakar. Ba Xabari kawai ba, akwai ma wasu malamai da suka tafi a kan haka.
Fuska ta uku:
A taqaice dai lafuzzan wannan aya game-gari ne kai tsaye. Ba su kevanci Abubakar ko Aliyu ba. Magana xaya ita ce, duk wanda ya sami shiga qarqashin inuwarta, hukuncinta ya shafe shi. Kuma ko shakka babu Abubakar da Umar da Usmanu da Ali Raliyallahu Anhum sun fi kowa a cikin wannan al’umma cancanta da shiga qarqashin inuwarta. Amma dai ba su toshe hanyar shigar wasu ba.
4.23 Ayar:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭼ الأنفال: ٦٢
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da uku ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Shi ne wanda Ya qarfafa ka da taimakonsa, kuma da muminai (8:62).
Ya ce: An samo ta hannun Abu Nu’aimi daga Abu Hurairata, wanda ya ce: “Akwai shi rubuce a kan al’arshi cewa: Babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, shi kaxai ba ya da abokin tarayya. Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa. Na kuma qarfafa shi da Aliyu xan Abu Xalib. Wannan shi ne ma’anar zancen Allah, a cikin littafinsa da Ya ce: Shi ne wanda ya qarfafa ka da taimakonsa kuma da muminai (8:62). Wato yana nufin ya qarfafa shi da Ali. Wannan kuma na daga cikin manyan darajojin da babu wanda ya same su daga cikin Sahabbai sai shi. A kan haka shi ne shugaba (Imamu) kenan.
Martani:
Kamar kodayaushe, muna neman marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya. Domin kuwa sanannen abu ne cewa, kan malamai ya haxu a kan riwaya ba ta zama hujja don kawai an jingina ta ga Abu Nu’aimi ba.
Mun san cewa Abu Nu’aimi nada littafi mai suna: Fala’ilus-Sahaba. Amma kuma ai ya ambaci wani yanki na darajojin a farkon littafin: Hilyatul Auliya’i. Idan shi ma ‘yan Shi’ah na kafa hujja da shi, to ya riwaito wasu darajoji na Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum waxanda ke rosa duk abin da suke gina. Idan kuwa har ba su kafa hujja da abin da ya riwaito, to kada su sake dogaro da naqalinsa.
Abin da Ahlus-Sunnah ke yi kodayaushe shi ne, komawa su auna duk abin da Abu Nu’aimi da ire-irensa suka riwaito, da ma’aunin ma’abuta ilimi a wannan fanni. Ta hanyar biyar hanyoyin da ake gane gaskiya ko qaryar hadisi da su. A nan ne ake yi wa isnadi da mazajen da ke cikinsa binciken qwaqwaf. Don a gane in su amintattu ne, ko a’a. da kuma neman tabbacin saduwar mariwaitan da junansu. Sannan a bi diddigin sauran hanyoyin da za su iya qarfafa hadisin in har akwai. A lokacin da malamai ke wannan fixa, ba ruwansu da abin da aka riwaito, ya shafi darajojin Ali ne ko na waninsa. Duk abin da bincikensu ya tabbatar gaskiya, nan take za su inganta shi. Babu kuma abin da zai hana su qaryata duk abin da ya tabbata qarya.
Bayan haka, sai mu ce: Ma’abuta ilimin hadisi sun yi ittifaqi a kan cewa, wannan hadisi qagagge ne. Wallahi mu ba mu shakkar kasancewar wannan hadisi zuqi ta mallau. Kuma wallahi, Abu Hurairata bai faxe shi ba, sam. Haka abin yake a cikin duk hadisai ko maganganun da muka kushe na wannan xan Shi’ah.
Kuma ai ka ga cewa Allah Ta’ala Ya yi: Shi ne wanda Ya qarfafa ka da taimakonsa kuma da muminai. Kuma Ya sanya soyayya a tsakanin zukatansu. Da ka ciyar da abin da yake cikin qasa, gaba xaya, da ba ka sanya soyayya a tsakanin zukatansu ba, amma kuma Allah Ya sanya soyayya a tsakaninsu (8:62-63). Ka ga waxannan ayoyi da aka haxa hancinsu, sun nuna cewa, waccan kalma ta Muminai waxanda Allah Ya qarfafa Manzon da su bayan taimakonsa, adadi ne na jama’a, waxanda Allah ya sanya danqon soyayya a tsakanin zukatansu, kuma Sayyidina Ali, xaya ne daga cikinsu. Bai mallaki wasu zukata ba can daban, da yake sa soyayya a tsakaninsu. Kuma shi “tilo” ne, a yayin da waccan kalma ta muminai ta ke cikin sigar “Jam’i”. Ka ga wannan nassi ne, da kai tsaye ke nuna, Allah ba Ya nufin wani mutum xaya kevantacce. Saboda haka ba ya halatta ga wani ya shiga gaban Allah, ya ce: Ayar na nufin Ali ne, wahdahu la sharika lahu.
Abu ne sananne a kan tilas, kuma ta dubaiban hanyoyi, cewa nasarar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya samu ta yaxa addini, ba da sa hannun Aliyu ne kawai ya same ta ba. Duk da yake yana daga cikin na farko-farko a shiga musulunci, a daidai lokacin kuma addinin na cikin rauni. Ai ba don Allah Ya shiryar da wasu mutane zuwa ga imani da hijira da taimakawa ba, da kasancewar Aliyu kawai wanda ke cikinsa, ba ta taimaka masa da komai ba. Kuma hasali ko imani da hijira da taimakawar da mutane suka yi ba wai Ali ne ya sanya su ba. Ba a kuma san Ali da tsayuwa wajen kira zuwa ga musulunci a Makka ko a Madina ba, kamar yadda aka san Abubakar da yin haka. Ba a kuma cirato wani ya musulunta a farkon musulunci ta hannun Ali ba. Kai, ko bayan hijira. A tarihi ma dai babu wani Sahabi da aka ce a hannun Ali ya musulunta. Amma da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa gwamna a Yaman, ba za a yi mamaki ba idan an ce wani ya musulunci a hannunsa can. Wannan yana yiwuwa. Amma ai su ba Sahabbai ne ba. Abin da kowa ya sani ne ko cewa, akwai manya-manyan Sahabbai da suka musulunta ta hannun Abubakar, bisa ga kuma shawararsa.
Kuma Ali bai yi ja-in-ja da mushrikai irin yadda Abubakar ya yi ba, ba su kuma nuna tsoronsa irin yadda suke tsoron Abubakar da Umar ba. Kai, duk wata gudunmawa da ka san sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya tava bayar wa musulunci, to, akwai takwarorinsa daga cikin Sahabbai da suka ba da irinta ko fiye da ita. Wannan kuwa abu ne da, duk masanin tarihi ya san da shi. Sai maqaryata da ciwonsu ba ya da magani.
Amma yin qarya a irin waxannan lamurra abu ne mai haxari, saboda dangantakarsu da addini. Kuma Allah ya ce: Kuma wane ne ya fi zalunci bisa ga wanda ya qirqira qarya ya jingina ta ga Allah, ko kuma ya qaryata gaskiya a lokacin da ta je masa? (29:68).
Ya kamata kai ma ka tambayi kanka. Ya za a ce, duk gwagwarrmayar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sha, da nasarorin da ya samu, duk da taimakon wani Sahabbai ne tallintal ya same su? Ina tarin gudunmuwar da gaba xayan muminai daga cikin magabatan farko, da Muhajiruna da Ansau, waxanda suka yi masa bai’a a qarqashin bishiya, da waxanda suka rufa masu baya cikinsutura, suka ba shi? Ina waxanda suka ba da jinainansu a Badar da Uhud da sauran yaqoqa?
4.24 Ayar: ﭽ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭼ الأنفال: ٦٤
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da huxu ita ce: Faxar Allah Ta’ala da ya ce: Ya kai Annabi! Allah Ya ishe ka, kai da duk wanda ya bi ka daga muminai (3:64). Wai Abu Nu’aimi ya ce: Wannan aya ta sauka ne a kan Ali. Kuma wai daraja ce da ba wanda ya samu daga cikin Sahabbai sai Ali. Kenan shi ne Imamu. Inji shi.
Martani:
Da farko: Wannan magana ba ta inganta ba.
Na biyu kuma: Wannan magana ba ta zama hujja, ko da an qaddara ingancinta.
Abin da ayar ke nufi shi ne, Allah Ya isar wa Manzon da muminai, mabiyansa. Kuma shi ne kaxai qwal wanda Ya isa kariya ga Manzon da Muminan da ke tare da shi. Ba abin da ayar ke nufi ne ba cewa, Allah da muminai sun ishi Manzo. A’a, Allah shi kaxai ne, wanda ya isar wa gaba xayan halitta.
Fahimtar jahilci da ‘yan Shi’ah suka yi wa wannan ayar na cewa, Allah da muminai sun ishi Manzo, shi ya kai su ga qaga wannan qarya cewa muminan, Ali ne kaxai ake nufi.
To, wannan jahilci nasu na biyu ma, ya fi wancan na farko fitowa fili. Domin abu ne mai yiwuwa qwarai waccan fassara da suka yi ta farko, ta qyafta wa wasu mutane a matsayin gaskiya. Amma ta biyu, ko alama. Babu mai hankalin da zai kasa tantance gaskiyarta. Domin kuwa ba Aliyu ne kawai daga cikin halitta, ya kama wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama harkar addini ba. Da kuwa shi ne kawai ya kasance tare da shi a fagen, da addinin bai tsaya ba balle ya kawo yau.
Ai ba a ma maganar Ali a irin wannan fage. Domin kuwa ko kansa bai iya amfana wa komai ba, a lokacin da ma mafi yawan rundunar da ke bayan qasa take bayansa. Ka tuna lokacin da Mu’awiyah ya yaqe shi, da irin jaruntakar da ya nuna har ya rinjaye shi. Daxa ko duk ta hanyar da ya bi, ya dai rinjaye shi. Ko ta hanyar qarfin tuwo ko makirci da yaudara. Ai da ma yaqi xan zamba ne.
To, ka ga a hankalce, idan Aliyu Raliyallahu Anhu ya kasa isar wa kansa da komai, a irin wannan lokaci da Musulunci ya game duniya. Kuma mafi yawan mutane da ke bayan qasa ke biye da shi. Ta yaya zai isar wa Manzo da wani abu a lokacin da gaba xayan mutanen duniya ke qiyayya da shi?!
Da ‘yan Shi’ah sun ce ma na, ai Aliyu Raliyallahu Anhu ya kasa rinjayar Mu’awiyah da waxanda ke tare da shi ne, saboda rudunar Aliyun ba ta biyayya gare shi; duk lokacin da ya yi gabas sai su yi yamma. Sai mu ce masu: Idan har musulmin da ke tare shi ba su yi masa xa’a ba, yaya za a yi kafiran da ba su yarda da shi da Annabin ba, su yi masa xa’a?!
Kuma sannannen abu ne a kan tilas cewa mutane, a lokacin da suka shiga addinin musulunci, sun fi kasancewa masu biyayya ga gaskiya. Ta ya za a yi wanda ya haxa hannu da Allah a cikin aikin tsayar da addinin Muhammadu a kan qafafunsa, har aka rinjayi kafirai, mutane suka musulunta ya kasa bayar da irin wannan goyon baya don a rinjayi wata ‘yar qungiya da ta yi tawaye a kansu, waxanda adadinsu bai kai na kafiran da ke akwai ba, a lokacin da aka aiko Manzo, balle su yi qarfinsu. Tattare kuma da kasancewarsu mafi zama kusa da gaskiya fiye da su?
4.25 Ayar: ﭽ ﮨ ﮩ ﭼ المائدة: ٥٤
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da biyar ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﭼ المائدة: ٥٤
Ya ku waxanda suka yi imani, duk wanda ya yi ridda daga cikinku; ya bar addininsa, to, da sannu Allah zai zo da waxansu mutane waxanda yake so, suna son sa, masu tawali’u ga muminai, masu izza a kan kafirai. Suna yin jihadi a cikin hanyar Allah kuma ba su tsoron zargin wani mai zargi. Wannan falalar Allah ce, da yake bayar da ita ga wanda ya so. Kuma Allah Mayalwaci ne, masani (5:54)
Wai Sa’alabi ya ce: Wannan aya ta sauka ne a kan Ali Raliyallahu Anhu. Kuma wai wannan na nuna shi ne Mafifici daga cikin Sahabbai, kuma shi ne Imamu.
Martani:
Qaryar qaryace-qaryace ta qare. Domin Sa’alabin ma bai faxi wannan magana ba. Abin da ya ce a cikin tafsirinsa a matsayin fassarar wannan aya shi ne: Ali da Qatadatu da Hasan sun ce: “Ayar na nufin Abubakar da Sahabbansa”. Shi kuwa Mujahidu ya ce: “A’a, tana dai nufin mutanen Yaman”. Mujahidu bai tsaya a nan ba, sai da ya kafa hujja da hadisin Iyalu xan Gunmu, da ke cewa: “Su ne mutanen Yaman”. Ya kuma kafa hujja da wani hadisi a kan haka.
To, ka ga shi kansa Sa’alabi ya riwaito cewa Aliyu kansa ya fassara ayar da cewa, tana nufin Abubakar da jama’arsa. Ali kuwa yana cikin jama’ar Abubakar.
Waccan magana kuwa tasa, babu hujja a cikinta. Saboda haka karvarta ba ya wajabta. Don ta ci karo da wadda ta fi ta shahara da bayayyana, wato wannan da ke cewa ayar ta sauka ne a kan Abubakar da jama’arsa, waxanda ya yaqi ma’abuta ridda tare da taimakonsu. Wannan shi ne abin da aka sani, kamar yadda ya gabata. Su dai waxannan maqaryata na so ne su xauke duk wata daraja da ta zo kan Abubakar, su kai ta ga Ali. Wannan kuma na daga cikin mummunan makirci, wanda kuwa dodo ne da ba ya cin kowa sai mai shi.
Abin da ya inganta a wurin masana tarihi shi ne, Abubakar ne ya yaqi ma’abuta ridda tare da taimakon jama’arsa. Su ne suka yaqi Musailamatal-Kazzabi, wanda ya ce shi Annabi ne. Suka murqushe shi tare da magoya bayansa banu Hanifata da mutanen Yamama, waxanda a ka ce yawansu ya kai dubu xari. Suka kuma yaqi Xulaihatul-Asadi, wanda shi ma ya yi da’awar Annabci a Najadu, har wasu mutane da dama daga cikin qabilar Asadu da Tamimu da Gaxfanu suka goyi bayansa.
Haka kuma an sami wata mata da ake kira Sajahi, wadda ta yi da’awar Annabta. A qarshe kuma ta auri Musailamatul-Kazzabi kafin a kashe shi. Maqaryaci ya auri maqaryaciya kenan.
Ko shakka babu waxanda suka yaqi murtaddai, na daga cikin waxanda Allah ke so, kuma suke son sa. Kuma su ne mafi cancantar mutane da shiga qarqashin inuwar wannan aya. Haka nan su ma waxanda suka yaqi sauran kafirai na Farisa da Ruma, wato Abubakar da Umar da waxanda suka kama masu, daga cikin mutanen Yaman da sauransu, duk sun shiga cikin wannan aya. Saboda hake ne ma, aka samu riwaya cewa, an tambayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da wannan aya ta sauka, a kan su wane ne? Sai ya nuni Abu Musal Ash’ari, ya ce: “Su ne jama’ar wannan”.
Wannan abu ne sananne bisa lalura. Kuma an san shi ta hanya mutawatira cewa, waxanda suka tanka tare da xora jinkan musulunci, kuma suka tabbata cikinsa, a lokacin da mutane ke fitarsa, suka yaqi murtaddai, da kafirai, na cikin waxanda Allah ke so, suna son sa, masu tawali’u a kan muminai, masu izza a kan kafirai. Suna yin jihadi a cikin hanyar Allah kuma ba su tsoron zargin wani mai zargi. Shi kuwa Ali Raliyallahu Anhu ko shakka babu yana xaya daga cikinsu. Sai dai ba shi ne mafi cancanta da wannan siffa ba, fiye da Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum kamar yadda arangamar da ya yi da kafirai da masu ridda ba ta fi wadda suka yi da su girma ba. Kuma alherin da ya tabbatar wa addini ta hanyar wannan jihadi, bai fi wanda suka tabbatar masa yawa ba.
Tabbataccen abu dai shi ne, kowane daga cikinsu na da nagartattar rawar da ya taka da inganccen aikin da ya tavuka, da kyakkyawan Kufan da ya bari a cikin musulunci. Allah kuma zai saka masu da alherinsa, albarkacin hidimar da suka yi wa musulunci da musulmi, a matsayinsu na halifofi shiryayyu, masu shiryarwa, kuma shugabanni masu kevowa, waxanda a mulkinsu suka yi hukunci adalci da gaskiya.
Wannan ita ce magana.
Amma yau a ce waxannan shugabanni na jama’a, waxanda amfanin da suka tabbatar a cikin addini da duniya ya fi a qirga, wai, su ne kafirai ko fasiqai azzalumai. A ce kuma wani wanda abin da ya gudana a hannunsa na alheri, bai kama qafar wanda ya gudana a hannun xayansu ba, a xauke shi matsayin Allah ko abokin tarayyarsa, ko a kai shi matsayin abokin tarayyar Manzon Allah; a ce ma'asumi ne, da ba a yin imani sai an yarda da ma'asumancinsa; kuma duk wanda bai yarda da hakan ba kafiri ne. A ce kuma yau kafirai, waxanda suka yi ridda ba kafirai ba ne. Waxanda suka yaqe su sun ci haqqinsu. A lokaci xaya kuma, a ce waxannan musulmi da ke sallah biyar, su yi azumin watan Ramalana, su ziyarci xakin Allah, waxanda suka daxe da shanye ruwan imani da Alqur’ani, wai su ne kafirai, saboda sun yaqi waxancan, wal-iyazu billahi.
Kai ka san ba mai faxar wannan magana sai tantirin jahili da, qarya da zalunci da shishshigi ba su ishe shi ba.
Mu qaddara cewa, wannan aya ta sauka ne a kan Ali Raliyallahu Anhu ko akwai mai iya qarfin halin cewa ta kevance shi ne kawai, Alhali lafazinta na nuna Jama’a?.
Nazari game qumshiyar ayar na ba ka tabbacin cewa, waxannan mutane da Allah ke magana a kansu, ba mutum xaya ba ne. Kuma ko Larabcin da Allah ya yi amfani da shi ba ya bada waccan ma’ana.
Da ‘yan Shi’ah za su yi qarfin halin cewa: Waccan ayar na nufin jama’a ne, amma jama’ar su ne: Ali da magoya bayansa. To, sai mu ce: Idan har wannan aya za ta sanya wani tare da Ali, a qarqashin inuwarta, to, ko shakka babu waxanda suka yaqi kafirai da masu ridda, sun fi cancanta da shiga ciki tare da shi, a kan waxanda ba su yaqi kowa ba sai masu mayar da gaba gabas su yi sallah. Ko shakka babu mutanen Yaman waxanda suka taya Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum yaqi sun fi cancanta da shiga inuwar wannan aya a kan ‘yan Shi’ah, waxanda ba su da abokai sai Yahudawa da Nasara da Mushrikai, A daidai lokacin da ba su da abokan gaba sai magabatan musulmi.
Kuma ai ka ga ayar cewa ta yi, Allah, zai zo da wasu mutane, Yana son su kuma suna son sa (5:54). Xauki kalmar can ta ‘Wasu’ ka duba ta da kyau. Za ka tabbata cewa lafazi ne da bai kevance kowa ba; haka qofarsa take sake. Tana jiran duk wanda waccan siffa ta tabbata gare shi ya shiga, ko waye shi kuwa. Ba sai Abubakar ko Aliyu ko waninsu ba. Ka ga kenan kuskure ne a ce Ali ya fifita a kan duk wanda ya yi tarayya da shi a cikin wannan falala. Balle har hakan ta wajabta kasancewarsa Imamu.
Kai, a taqaice abin da wannan aya ke nufi shi ne: Babu wani lokaci da ridda zata bayyana; mutane su rinqa barin addini, daga yau har zuwa ranar qarshe, face Allah Ya tayar da wasu, waxanda yake so, suke kuma son sa, masu sassabci ga muminai da tsanani ga kafirai, su yaqi waxanda suka yi riddar.
4.26 Ayar: ﭽ ﭕ ﭖ ﭗﭘ ﭼ الحديد: ١٩
Xan Shi’ar ya ce: Hujjarsa ta ashirin da shida ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭼ الحديد: ١٩
Kuma waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, waxannan su ne masu kamalar gasgatawa, kuma su ne masu shahada a wurin Ubangijinsu, (57:19)
Ya ce: Ahmadu xan Hambali ya riwaito da isnadinsa daga wajen xan Abu Laila, shi kuma daga babansa, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Ya ce: Masu gasgatawa guda uku ne: Habibu xan Musa, kafinta, muminin Ali Yasin. Wanda ya ce: “Ya ku mutane! Ku bi Manzanni”. Da kuma Hizqilu, muminin Ali Fir’auna. Wanda ya ce: Yanzu kuna yarda ku kashe mutum don kawai ya ce: “Ubangijina shi ne Allah”? Na qarshensu kuma shi ne Aliyu xan Abu Xalib. Shi ne kuma mafifici daga cikinsu.
Haka wai inji xan Shi’ar, malamin nan masanin Fiqihu Ibnul-Magazili, Bashafi’e da marubucin littafin: Al-Firdausi, duk sun riwaito irin wannan magana. Ya kammala maganar tasa da cewa, wai wannan xaukaka ce da ke nuna shugabancin Ali Raliyallahu Anhu.
Martani:
Muna son ya tabbatar mana da ingancin wannan hadisi. Domin kuwa babu shi a cikin Musnadin Imamu Ahmad. Kuma ma’abuta ilimi sun yi ittifaqi cewa ko da ya riwaito shi a cikin littafinsa na Fadha’ilus-Sahabati hakan ba ta nuna cewa ya inganta a wurinsa. Domin kuwa ana da tabbacin cewa, yakan riwaito abin da ya ci karo da mutane sun riwaito, ko da kuwa bai inganta ba. Kuma duk wanda ya san abin da ake ce wa ilimi, ya san cewa ba kowane hadisi ne da Ahmad ya riwaito a cikin littafinsa na Fadha’ilus-Sahabati yake zama ingantacce ba. Kai, ko waxanda yake riwaitowa a cikin Musnad nasa, ba kowane hadisi ne ke zama ingantacce ba. Hasali ma hadisan da wannan Musnad nasa ya qunsa, hadisai ne da mutane suka riwaito ba tare da tantancewa ba. Amma ba ya riwaya daga waxanda aka yi masu shedar qarya. Saboda haka abu ne mai yiwuwa, a sami wata makama cikin wasu daga cikinsu da ke nuna raunin wasu daga cikinsu ko ma kasancewa qarya. Sai dai ana da tabbacin cewa, mafi yawansu hadisai ne na gargaru, da kuma ake iya kafa hujja da su. Kuma tabbas ne cewa, sun fi hadisan da ke cikinsunanu Abi Dawuda nagarta. Amma abin da ya riwaito a cikin Fadha’ilus-Sahabati bai shiga wannan vangare ba.
Cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Masu gasgatawa uku ne. Ya kuma taqaita hakan a kan ambaton waxancan mutane uku, magana ce da ba ta sauraruwa. Domin kuwa hadisi ingantacce ya zo da ambaton wani wanda ba Ali ba a matsayin “mai gasgatawa” ta fuskoki da dama. Kamar inda Annabi ya ambaci Abubakar da wannan suna. To, ya za a ce haka?
Misalin wannan shi ne, hadisin da ya zo a cikin Buhari da Muslimu, daga Anas, wanda ya ce: Watarana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hau kan dutsen Uhudu. Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum suka rufa masa baya. Sai dutsen ya girgiza. Annabi ya ce masa: Kwantar da hankalinka ya kai Uhudu. Ba wasu ne a kanka ba face Annabi da Siddiqi (mai gasgatawa) da Shahidai guda biyu.
Kai, ko Alqur’ani ma, Allah Subhanahu WaTa’ala Ya ambaci Sayyida Maryamu da Sunan mai gasgatawa. Ka ga cewa Annabi Ya taqaita wannan kalma a kan mutanen can uku, labari ne.
To, idan ‘yan Shi’ah na nufin cewa: Masu gasgatawa uku ne, na nufin babu wani Siddiqi bayan ukun, to, qarya ce. Domin kuwa hakan ta sava wa littafin Allah, da Sunnar Manzon Allah da haxuwar kan musulmi. Idan kuwa suna nufin hakan na nufin Siddiqancin waxancan mutane uku, shi ne mafi kamala, to, shi ma cewa haka kuskure ne. Domin kuwa wannan al’umma tamu ita ce mafi alherin al’umma, wadda Allah Ya samar don ceto mutane. To, ta yaya wanda ya gasgata Musa, da wanda ya gasgata Isah za su fi waxanda suka gasgata Muhammadu cika da kamala?
Kuma ai ka ga Allah Ta’ala cewa ya yi: Kuma waxanda suka yi imani da Allah da Manzonsa, waxannan su ne masu kamalar gasgatawa, kuma su ne masu shahada a wurin Ubangijinsu (57:19). Ka ga wannan magana na nuna cewa, duk wanda ya yi imani da Allah da Manzonsa Siddiqi ne.
Idan kuwa har kasancewa Siddiqi shi ne abin da ke sa mutum ya cancanci zama shugaba (Imamu). To wanda ya fi kowa cancantar karva wannan suna, shi ne Abubakar Raliyallahu Anhu. Domin shi ne wanda dalilai da dama suka tabbatar wa sunan, ta dubban hanyoyi. Kuma gaba xayan jama’a, babba da yaro, kowa ya yarda da hakan kai tsaye. Har ta kai maqiyan musulunci ma sun miqa wuya. To, ka ga kenan, a haka shi ne wanda ya cancanci zama shugaba. Idan kuwa kasancewarsa Siddiqi xin nan, ba ta wajabta kasancewarsa shugaba ba, to, wannan hujja da ‘yan Shi’ah ke qoqarin kafawa ta sha kara tanda.
4.27 Ayar: ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﭼ البقرة: ٢٧٤
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da bakwai ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Waxanda suke ciyar da dukiyarsu, a dare da yini, voye da bayyane (2:274).
Ya ce: An samo ta hannun Abu Na’aimi, da isnadinsa zuwa ga xan Abbas, wanda ya ce: “Wannan aya ta sauka ne kan Ali Raliyallahu Anhu. Saboda wasu dirhamomi da ya mallaka guda huxu. Ya bayar da sadaqar xaya da dare, xaya da rana. Xaya kuma a asirce, xaya a bayyane”.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Sa’alabi ma ya riwaito wannan magana. Ka ga hakan ba ta faru ga wani Sahabi ba, inji shi. Kenan Aliyu ne mafifici daga cikinsu sai ya zama shugaba.
Martani:
Martaninmu a kan wannan magana shi ne:
Mene ne ingancin wannan riwaya tukuna? Dole ne a yi bayanin yadda wannan riwaya ta inganta. Saboda kasancewarta ta Abu Nu’aimi da Sa’alabi. A qashin gaskiya ma dai, wannan riwaya qarya ce.
Sannan bayyanannen abu ne cewa, wannan aya gama gari ce. Duk wanda ya ciyar da wani abu saboda Allah, da dare ko da rana, a voye ko a bayyane, ya shiga qarqashin inuwarta. Saboda ya yi aiki da ita. Daxa Aliyun ne ko waninsa. Kuma hawa da gangararta na tabbatar da rashin hujjar wanda ya kevance wani mutum xaya da ita.
Xan Shi’ar kuma ba ya da labarin ya yi walle; domin kuwa abin da ya faxa a cikin wannan qagaggen hadisi ya yi takin saqa da abin da ayar ta qunsa. Bari ka ji: Ita ayar tana magana ne a kan waxansu lokuta biyu waxanda kowane zamani ya ke da, da kuma ciyarwa a cikinsu. Da kuma wasu halaye ko yanayoya biyu, waxanda dole ne kowane aiki ya kasance ya faru cikin xayansu; Wato dole ne idan za a bayar da labari, a ce: An yi kaza ne a daidai lokaci kaza. Shi kuwa lokacin nan, dole ne ya kasance dare ne ko rana; ba na uku. Shi kuwa aikin da aka yin, dole ne ya kasance an yi shi a voye ko a bayyane. Idan mutum ya ciyar da dukiyarsa cikin dare kuma a asirce, ya haxa abu biyu kenan, wato dare da asiri. Haka kuma idan ya ciyar da ita da rana kata, kuma quruquru kowa na gani. Shi ma ya haxa abu biyu, wato rana da sarari.
Da za mu qaddara cewa Aliyu ya ciyar, kuma a kansa ne waccan aya ta sauka. To, ai iyakar abin da ya yin bai fi ciyar da dirhami huxu ba kacal ko?! Kuma qofar aikata irin wannan aiki ai tana nan buxe hayan-hayan har ranar qiyama. Waxanda kuma ke shiga da fitowa suna komawa ta cikinta ba su qidayuwa. Babu wani musulmi da ke fatar alheri, yake kuma da iko, face ka taras ya ciyar da wani abu, da yardar Allah, wani lokaci da dare, wani lokaci kuma da rana. Wani lokacin kuma asirce, wani kuma a bayyane. Ka ga wannan ba wani abu ne da za a ce wani ya kevanta da shi ba. Balle ya zama wata siffa ta wanda ya kamata ya zama shugaba.
Dostları ilə paylaş: |