4.28 Ayoyin ﭽ ﯪ ﯫ ﯬ ﭼ
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da takwas ita ce: Abin da Ahmadu xan Hambali ya riwaito daga xan Abbas cewa: Babu wata aya a cikin Alqur’ani, wadda ke farawa da: Ya ku waxanda suka yi imani face Aliyu ne shugaba kuma liman a cikinsu, kuma jagora mafi girman daraja. Kuma wai Allah Ta’ala Ya zargi Sahabban Muhammadu a cikin Alqur’ani, a wurare da dama. Amma bai tava ambaton Aliyu face da alheri ba. Wai kuma wannan na nuna fifikonsa a kansu, da cancantar zamansa shugaba. Ka ji kai.
Martani:
Martaninmu a kan wannan magana zai kasance ta fuskoki kamar haka:
Fuska ta farko:
Muna son marubucin ya gaya mana yadda wannan magana ta inganta. Domin kuwa tabbas babu ta a cikin Musnadin Imamu Ahmad. Kuma ko da ya riwaito shi a cikin Fadha’ilus Sahaba, hakan kawai ba ta tabbatar da kasancewarsa ingantacce. Balle kuwa tabbas ne bai riwaito shi ba a cikin waxannan littafai nasa biyu. Yana dai daga cikin qare-qaren da Qaxi’iy ya yi.
Fuska ta biyu:
Ko shakka babu, wannan magana qarya ce aka yi wa xan Abbas. Domin kuwa ta tabbata ta hanya mutawatira cewa, a wajen xan Abbas xin, Abubakar da Umar su ne mafifita xaukaka a kan Ali. Kuma akwai waxansu abubuwa na Aliyun da yake qyama, har ma yake aibanta shi da su. Akwai kuma wasu al’amurra da yake ganin ko alama Ali bai kyauta ba a cikinsu. Har yake cewa, a lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya qona zindiqan da suka naxa masa rawanin ubangizantaka: “Da ni ne Ali, ba zan qona su ba, saboda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana a yi horo da wuta. Zan kawai sare kawunansu ne. Saboda cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: Kuma ku kashe duk wanda ya canza addininsa”. Buhari da waninsa ne suka riwaito wannan hadisi.
A lokacin da wannan magana ta kai kunnen Ali, sai ya ce: “Oh, Allah Ya jiqan uwar xan Abbas.”!.
Fuska ta uku:
Ce wa Aliyu ne shugaban sahun Ya Ayyuhal-Lazina Amanu ba yabo ne ba. In ko sun nace, sai mu ce, to, ga wata ayar: Ya ku waxanda suka yi imani! Don me kuke faxin abin da ba ku aikatawa? Ya girma ga zama abin qyama a wurin Allah, ku faxi abin da ba ku aikatawa (61:2-3).
To, ita ma wannan Ali shugaban sahun waxanda aka kira a cikinta? Akwai ire-iren wannan ayar da dama.
Fuska ta huxu:
Daidaitattar fahimta ita ce, wannan lafazi na waxanda suka yi imani ya haxa har da Ali Raliyallahu Anhu, duk da yake ba shi ne dalilin maganar ba. Ko shakka babu yadda lafazin ya haxa har da waninsa, ya haxa da shi. Babu wata wariya a cikin lafazin wannan aya tsakanin wani mumini da wani.
Fuska ta biyar:
Cewar da xan Shi’ar ya yi wai wasu Sahabbai sun ce: Ali shi ne shugaba kuma Imamin irin waxannan mutane, jagora kuma mafi girman daraja a cikinsu, magana ce da babu tabbas a cikinta.
To, ja ta ma hakan. Mu qaddara cewa suna nufin Ali ne farkon wanda aka yi magana da shi, ta wannan lafazi. To, ko a ha kan maganar ba ta shiga. Domin kuwa yanayin zancen na tafiya ne tare da kundume waxanda ake zancen da su, bai xaya; bai ware wani sashe, da abin da bai shafi wani sashe ba.
Iyakar abin da kuke godogo da shi a cikin wannan magana, na san duk bai fi cewar da kuka yi xan Abbas na fifita Ali a kan sauran Sahabbai ba. Tattare kuma da kasancewar wannan magana qarya, wadda aka yi ma shi, da takin saqar da maganar ta yi da abin da aka sani na zantukansa. To, mu qaddara ya ce hakan. Mu kuma kau da kai daga ban hannun makafi da ya yi da Jumhuru. Duk da haka, ba yadda za a yi hakan ta iya zama hujja.
Fuska ta shida:
Kowa ya san cewa, cewar da xan Shi’ar ya yi, wai haqiqa Allah Ya zargi Sahabban Muhammadu a cikin Alqur’ani a wurare da dama. Amma bai tava ambaton Ali ba face da alheri, qarya ce lafiyayya. Domin kuwa ba a tava jin inda Allah Ya zargi Abubakar a cikin Alqur’ani ba. Ai Alqur’ani ba a voye yake ba. Kai, ba a ma tava jin Abubakar ya sava wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, balle. Abin da ma aka riwaito daga gare shi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne abin da ya tava cewa a cikin wata huxuba: “Ya ku mutane! Ku kiyayi mutuncin Abubakar. Ku sani bai tava sava mani, da xai rana ba”.
4.29 Ayar: ﭽ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﭼ الأحزاب: ٥٦
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta ashirin da tara ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﭼ الأحزاب: ٥٦
Lalle, Allah da mala’ikunsa suna salati ga Annabi. Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi (33:56).
Ya zo a cikin Sahuhul Buhari daga Ka’abu xan Ujrata, wanda ya ce: Mun tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bayan saukar wannan aya da cewa: Ya kai Manzon Allah, ya za a yi salati gare ku mutanen Babban Gida? Domin Allah Ya riga ya sanar da mu yadda za mu yi sallama. Sai ya ce: Ku ce “Ya Ubangiji ka daxa tsira a kan Muhammadu da mutanen gidansa.
Ya kuma zo inji xan Shi’ar a cikin Sahihu Muslimu cewa, mun ce wa Manzon: “Ya Manzon Allah! Ita sallama mun riga mun san yadda za mu yi maku ita, to salati fa”? Sai ya ce: Ku ce “Ya Ubangiji ka daxa tsira a kan Muhammadu da mutanen gidansa. Kamar yadda ka daxa tsira a kan Ibrahimu da Mutanen gidansa”.
Xan Shi’ar ya kammala da cewa: Ko shakka babu kuwa Aliyu shi ne mafi xaukaka a cikin mutanen gidan Muhammadu. Saboda haka ya fi kowa cancanta da shugabanci.
Martani:
Ko shakka babu wannan hadisi, ingantacce ne. Kuma Buhari da Muslimu sun haxu a kan sa. Kuma lalle Ali Raliyallahu Anhu na daga cikin mutanen gidan Muhammadu, da ke cikin salatin.
Amma kuma wannan xaukaka ba ta kevanci Aliyun kawai ba. Balle ta zama wani abin hura hanci. Domin kuwa gaba xayan zuri’ar Hashimu, da ta haxa da Abbas da zuri’arsa da Harisu xan Abdul-Muxxalabi da zuri’arsa, duk suna cikin wannan ayari. Haka ‘ya’yan Annabi mata; Ruqayyatu da Ummu Kulsumi da Fatima, da gaba xayan matansa, duk suna cikin wannan ayari, kamar yadda ya tabbata a cikin Buhari da Muslimu, cewa Manzon ya ce: “Ya Ubangiji ka daxa tsira a kan Muhammadu da matansa da zuri’arsa”.
Kai! Ba waxannan kawai ba, duk wanda ke da wata dangantaka da Manzon Allah, a matsayin xan cikin gida, har ranar da Allah Ya naxe qasa, na cikin wannan ayarin albarka. Kar ka yi tsammanin na manta da ‘ya’uwan Ali su Ja’afaru da Aqilu, su ma suna ciki.
Ka ga sanannen abu ne sarai cewa, shigar waxannan mutane qarqashin wannan inuwa ta tsira da aminci, ba ta nufin sun fi duk wanda bai sami shiga ciki ba. Balle har hakan ta sa waninsu cancanta da shugabanci, ko ya kevanta da shi.
4.30 Ayar: ﭽ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭼ الرحمن: ١٩ - ٢٠
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin ita ce: Faxar Allah Ta’ala: (Allah) Ya gauraye tekuna biyu (Ruwan daxi da na zartsi) suna haxuwa. A tsakaninsu akwai shamaki, ba za su qetare haddi ba (55:19-20).
Ya ce: Ya zo a cikin tafsirin Sa’alabi ta hannun Abu Nu’aimi daga xan Abbas, wanda wai ya ce: Tekunan can biyu da Allah Ya garwaye na nufin Ali da Fatima. Shi kuma shamakin can da ke hana su qetare haddi, shi ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Sannan aya ta gaban waxannan kaxan kuma, wadda ke cewa: Lu’u’lu’u da Murjani na fita daga gare su (55:22) Suka ce, Lu’ulu’in da Murjani, Hassan da Husaini kenan. Wai kuma babu wani daga cikin Sahabbai da ya sami irin wannan falala sai Ali. Sai ya zama shugaba kenan.
Martani:
Martaninmu a kan wannan magana zai kasance kamar haka:
Babu mai yin wannan magana da makamantanta, sai wanda bai san abin da yake faxa ba. Kuma wannan fassara ta ‘yan Shi’ah, ko kaxan ba ta yi kama da tafsirin Alqur’ani ba; ta fi kama da renin hankali. Kuma irin wannan tafsiri na daga cikin irin tafsirin da, mulhidai da Qaramixawa da ‘yan Baxiniyyah ke yi wa Alqur’ani. Kai sharrin ma da ke cikin wannan ya fi wanda ke cikin wancan. Hasali ma irin wannan tafsiri shishshigi ne da sukar lamirin Alqur’ani da babu wata suka da kushewa da za a yi masa, wadda ta kai ga irin ta.
Amma irin wannan shishshigi a cikin tafsiri, ba baqon abu ne ga ‘yan Shi’ah ba. Kuma kaxan ma ka ji. Dubi abin da suka ce, wai kalmar Littafi Mabayyani a inda Allah ke cewa: Kuma kowane abu Mun qididdige shi a cikin Babban Littafi Mabayyani (36: 12) wai tana nufin Ali. Kuma wai kalmar Uwar littafi a inda Allah ke maganar Lauhul Mahfuz da ya ce: Kuma lalle shi haqiqa, maxaukaki ne, bayyananne ne a cikin uwar littafi, a wurinmu. (43:4) na nufin Ali, in ji su. Haka kuma wai kalmar Bishiyar da aka la’anta a inda Allah ke cewa: Da bishiya wadda aka la’anta a cikin Alqur’ani. (17:60) wai, na nufin Banu Umayyata.
Akwai irin waxannan fassarora da makamantansu da yawa a bakinsu, waxanda ba wanda zai riqa furuci da su sai wanda ba ya fatar samun gafarar Allah, bai kuma yi imani da Allah da littafinsa ba.
Akwai abubuwa da dama da ke tabbatar da wannan magana qarya ce:
Abu na farko: Ita ayar da ake magana a kanta a Makka ta sauka bisa haxuwar kan musulmi. Hasan da Husaini kuma a Madina aka haife su.
Abu Na biyu: Yi wa Ali da Fatima alkunya da tekuna, Hasan da Husaini kuma da kalmar Lu’ulu’u da Murjani. Duk abubuwa ne da harshen Larabaci ba ya xauka ta kowace fuska; daxa ga asalin kalma ko aro. To, ka ga kenan bayan qiren qaryar da xan Shi’ar ya yi wa Allah da Alqur’ani. Ya kuma yi wa harshen Larabci.
Abu na uku: Babu wani abu a cikin wannan al’amari da ya wuce irin wanda ke faruwa ga kowane xan Adam. Domin duk wanda ya auri wata mata har ta haifa masa ‘ya’ya biyu, to wannan riga na iya shiga wuyansa.
Abu na huxu: Wani abu kuma da da ke qara tabbatar da qaryar wannan xan Shi’ah, a cikin wannan baquwar fassara tasa, shi ne: Ai Allah Ta’ala Ya ambaci cewa, Ya haxa wasu koguna biyu, a cikin wata aya da Yake cewa: Kuma (Allah) shi ne Ya garwaya tekuna biyu, wannan mai daxi, mai sauqin haxiya. Kuma wannan gishiri-gishiri, gurvatacce (25:53). Ka ga da a harshen Larabaci da na qur’ani, wannan kalma na nufin; Aliyu da Fatima da wannan ayar ta tabbatar da kasancewar xayansu abin zargi. Ahlus-Sunnah da Shi’ah kuwa duk ba su yarda da haka.
Abu na biyar: Ai ka ga cewa Allah Ta’ala Ya yi: A tsakaninsu akwai shamaki, ba za su qetare haddi ba (55:20). To, da waccan aya na magana ne a kan Alin da Fatimar, kuma shamakin shi ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wanda shi ke hana xayansu ya kai farmaki ga xaya? To ka ga wannan magana ta fi kama da zargi, ba yabo ba.
Abu na shida: Ta kuma tabbata gaba xayan malaman tafsiri sun haxu a kan savanin wannan fassara ta xan Shi’ah. Kamar yadda Ibnu Jarir da waninsa suka ambata.
4.31 Ayar: ﭽ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭼ الرعد: ٤٣
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da xaya ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Da wanda yake akwai ilimin littafi a wurinsa (13:43).
Ya ce, an samo ta hanyar Abu Nu’aimi daga Ibnul Hanafiyyah, wanda ya ce: Mai ilimin littafin can shi ne Aliyu xan Abu Xalib. A cikin tafsirin Sa’alabi kuma, samowa aka yi daga Abdullahi xan Salam, wanda ya ce: Na tambayi Ibnul Hanafiyyah cewa: Wane ne wanda ke akwai ilimin littafi a wurinsa? Ya karva mani da cewa: Shi ne Aliyu xan Abu Xalib. Wannan kuwa na nuna shi ne mafi xaukaka a cikin Sahabbai. Shi ne kuma ya dace da zama Imamu, inji xan Shi’ah.
Martani:
Muna son marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan abu da ya riwaito daga xan Salami da Ibnul Hanafiyyah. Ko da an qaddara kasancewar wannan riwaya ingantatta, ba za ta iya zama hujja karvavva ba. Domin kuwa abin da akasarin malamai suka tafi a kai ya sava masa. Kai ko shakka babu dai wannan magana qarya ce ake yi wa xan Abadussalami da xan Hanafiyyah.
Wani abin da ke tabbatar da kasancewar tafsirin xan Shi’ar nan shirme, shi ne: Ai Allah Ta’ala cewa Ya yi: Ka ce, “Allah Ya isa zama shaida a tsakanina da ku, da wanda yake akwai ilimin littafi a wurinsa (13:43). Ka ga da ayar na nufin Ali shi ne mai wancan ilimi na littafi, da kenan sai Muhammadu ya kafa shi sheda wa waxanda suka kafirta, a kan duk abin da zai gaya masu.
Sanannen abu ne kuwa, ko da Aliyu ya shede shi a kan Annabci, da dukan abin da zai faxa, hakan ba za ta daxe shi amfanin komai ba, balle ya rinjayi mutane da hakan a matsayin hujja. Ko kuma shedar tasa gare shi ta zama wani dalili abin kafawa. Kuma babu ma wanda zai miqa wuya ga Muhammadun saboda ita. Domin kafiran cewa za su yi: Ya aka yi Aliyu ya san haka. Lalle haxa baki suka yi da Muhammadu. Ka ga kenan a haka, su a wurinsu Muhammadu ne ya tsaya wa kansa a matsayin sheda. Kafiran kuma na iya cewa, to ai Aliyu qanin Annabi ne, kuma yana daga cikin waxanda suka fara imani da shi, abu ne mai sauqi su haxa baki don a yaudari mutane.
Amma ka ga da Ahlul-Kitabi za su tsaya wa Muhammadu shedu, a kan Annabcinsa da duk abin da zai faxa, ta hanyar amfani da abin da suka sani daga Annabawansu, da wannan sheda za ta yi amfani. Kamar yadda da a ce Annabawan na raye suka kuma shede shi a kan haka, za ta yi. Duk abin xaya ne.
Amma ka ga saboda kasancewar wannan xan Shi’ar jahili, ya zaci wannan abu xaukaka ce ga Ali. Bai san ha kansuka ce ya yi gare shi ba, da Annabin da, sanadiyyarsa ya zama mumini. Haka kuma wannan magana suka ce ga dalilan da ke xaure wa musulunci gindi. Babu kuwa mai irin wannan magana sai zindiqi, jahili wanda ya yi nisa a cikin kogin jahilci.
Idan dai xan Shi’ar yana sane ya yi wannan cavi, to, wannan musiba ce. Idan kuwa jahilci ne ya yi masa kanta, to, musibar ta qara kauri.
Allah Ta’ala Ya ambaci sheda a kan Annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama na iya fitowa daga Ahlul-Kitabi, a wurare da dama a cikin Alqur’ani. Kamar inda yake cewa: Ka ce “Shin, kun gani, idan (Alqur’ani) ya kasance daga wurin Allah yake, kuma kuka kafirta da shi, kuma wani mai shaida daga Banu Isra’ila ya bayar da shaida a kan irinsa (46:10).
To, ko xan Shi’ar na son ne ya ce mana Aliyu na daga cikin Bani Isra’ila?!.
4.32 Ayar: ﭽ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭼ التحريم: ٨
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da biyu ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi da waxanda suka yi imani tare da shi (66:8).
Ya ce: Abu Nu’aimi ya riwaito hadisi ta hanyar Inbu Abbas, daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: Farkon wanda za a zuba wa kayan adon aljanna shi ne Annabi Ibrahimu Alaihis Salamu, a kuma danqa masa takardar shedar badaxayantaka daga wurin Allah. Bayansa sai Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama. Saboda kasancewarsa zavavve a wurin Allah. Daga nan kuma sai Aliyu ya shiga tsakiyarsu, su garzaya zuwa aljanna. Sai kuma Ibnu Abbas ya karanta waccan aya da muka ambata, wato: Ranar da Allah ba Ya kunyatar da Annabi da waxanda suka yi imani tare da shi (66:8). Ya kuma ce: Shi ne Aliyu da Sahabbansa.
Xan Shi’ar ya ce: Wannan na nuna cewa Aliyu shi ne mafifici a kan duk wanda ba shi ba. Kenan shi ne Imamu.
Martani
Da farko muna son marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya. Domin muna sane da cewa, ba ta da asali. Kuma wannan riwaya qarya ce yanke. Domin zubin maganar na nuna cewa Aliyu ya fi Annabi Ibrahimu da Muhammadu girma saboda shi ne tsa kansu; sun yi masa fikafikai. Alhali kuwa Annabi Ibrahimu da Muhammadu su ne mafifita daraja a cikin halitta. Duk kuwa wanda ya fifita Aliyu a kansu, to, gara jakin gidansu da shi.
Abin da dai ya tabbata a cikin Buhari da Muslimu daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne, cewar da ya yi: Farkon wanda za a wa ado ranar qiyama shi ne Ibrahimu. Annabi bai ambaci kansa ba, balle Aliyu a cikin wannan hadisi. Kuma ka sani gabatar da Annabi Ibrahimu da Allah Subhanahu WaTa’ala Ya yi a cikin wannan sha’ani na tufatarwa, ba ya nufin ya fi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama girman daraja kai tsaye.
Ka lura da kyau, cewa Allah Subhanahu WaTa’ala Ya yi: Ranar da Allah ba ya kunyatar da Annabi da waxanda suka yi imani tare da shi. Haskensu yana tafiya a gaba gare su da jihohin damansu, suna cewa, Ya Ubangiji ka cika mana haskenmu, kuma ka yi mana gafara. Lalle kai, mai ikon ne a kan dukan kome (66:8). A wata surar kuma Ya ce: Ranar da za ka ga muminai maza da mata, haskensu na tafiya a gaba gae su, da kuma dama gare su. (Ana ce musu): Bushararku a yau, ita ce gidajen aljanna, ruwa na gudana daga qarqashinsu suna masu dawwama a cikinsu. Wannan shi ne rabo mai girma (57:12).
Ka ga nassin ayoyin gama-gari ne da ya kundume gaba xayan muminan da ke tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. kuma hawa da gangarar zancen na tabbatar da haka. Haka ma gaba xayan fassarorin magabata na da alaqa da waxannan ayoyi, na tabbatar da gamagarancinsu.
4.33 Ayar: ﭽ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البينة: ٧
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin uku ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Lalle ne waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan qwarai, waxannan su ne mafifita alherin, halitta (98:7).
Ya ce: Hafiz Abu Nu’aimi ya riwaito da isnadinsa zuwa ga xan Abbas, wanda ya ce: Lokacin da wannan aya sauka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu: Za ka zo ranar qiyama, kai da jama’arka kuna masu yarda da Allah, kuma yardaddi a wurinsa. Maqiyanka kuma za su zo suna abin qi da qyamar gani. Xan Shi’ar ya ce: To, tunda ko har shi ne mafificin halitta, babu ko wanda ya cancanta da zama shugaba in ba shi ba.
Martani
Da farko, sai mu ce masa: Wanda bai ga uwarsa ba yana maganar kakarsa? Fara tabbatar da ingancin wannan batu, sannan ka gina son ranka a kansa. Mu dai ba mu da wani kokwanto a kan kasancewarta qaraya. Gaba xayan qungiyoyin musulmi sun haxu a kan cewa, riwayar Abu Nu’aimi in ba an tantance ta ba, to, da ita da babu uwarsu xaya ubansu xaya
Kuma kan malamai da ma’abuta sanin sirrin riwayoyi ya haxu a kan cewa, wannan riwaya na daga cikin qagaggin riwayoyi.
Wani abu kuma shi ne, wannan qagaggen tafsiri na xan Shi’ar, ya ci karo da irinsa, na waxanda ke cewa: Mutanen can da suka yi imani suka kuma aikata aikin na qwarai su ne Nasibawa, masu adawa da Ali kamar Harijawa da makamantansu. Harwayau kuma waxannan mutane na cewa: Duk wanda ya jivinci Ali, ya kafirta. Da shi da shiga qarqashin inuwar wannan aya fau-fau. Kuma hujjarsu a kan wannan magana ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Wanda bai yi hukunci ba da abin da Allah Ya saukar, to, waxannan su ne kafirai (5:44).
Suka ce: Duk wanda ya sa wasu maza su yi hukunci a cikin addinin Allah, ya yi hukunci kenan da abin da Allah bai saukar ba, kuma ya kafirta. Duk kuwa wanda ya jivinci kafiri shi ma kafiri ne. Saboda Allah Ta’ala na cewa: Kuma wanda ya jivince su daga cikin ku, to, lalle ne shi yana cikinsu (5:51) .
Suka kuma qara da cewa: Da Ali da Usmanu Raliyallahu Anhuma da duk wanda ya riqe su abin jivinta, wai riddaddu ne daga addinin Allah. Saboda abin da ya faru sanadiyyar su, bayan wucewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, wanda ma ya bayar da labari a kansa da cewa: “Wallahi za a kori wasu maza daga wurin kogina kamar yadda ake korar baqon raqumi daga mashayar ruwa. Sai in ce: Ya Ubangiji ai waxannan Sahabbaina ne. sai a karva mani da cewa: Haqiqa kai ba ka san abin da suka haddasa ba bayanka; ba su gushe ba suna fita daga addini sannu-sannu, tun lokacin da ka rabu da su”.
To, waxannan su ne waxanda suka yi hukunci da abin da Allah bai saukar ba, a kan jinainan musulmi da dukiyoyinsu. In ji Harijawa.
Hujjar da suka kafa a kan wannan hukunci da suka yi ita ce, cewar da Annabi ya yi: “Kada ku koma kafirai bayana; sashenku na saran wuyan sashe”.
Suka ce: Duk kuwa waxanda sashensu ya koma yana saran wuyan sashe, babu shakka, sun koma kafirai bayan wucewar Annabi.
Duk da kasancewar waxannan hujjoji na Harijawa da makamantansu varna tabbas. To hujjojin nan da ‘yan Shi’ah ke kafawa sun fi su zama varna, domin Harijawa sun fi su hankali da gaskiya tare da biyar sawunta. Kuma sukan kwatanta gaskiya kodayaushe. Idan ma ka ce ba su qarya, ba ka yi qarya ba. Saboda su mutane ne ma’abuta addini fai da voye. Illah dai kawai jahilci ya yi masu kanta. Wanda har ya kai su faxawa cikin halaka da fita daga addinin musulunci kamar yadda kibiya ke fita daga cikin baka.
Inda dai qarya da jahilci da biyar son zuciya suka yi sansani, sai ga ‘yan Shi’ah. Kuma mafi yawa daga cikin shugabaninsu da Ya’ayyuhan nasun cikinsu duk zindiqai ne, mulhidai. Ba su da wata sha’awa da ilimi da kishin addini. Kai!
Ba su biyar kome face zato da abin da rayukansu ke sha’awa, alhali kuwa shiriya ta daga wajen Ubangijinsu, ta je masu (53:23).
Ko shakka babu, cewar da Allah Ta’ala ya yi: Lalle ne waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na qwarai (98:7) magana ce gama-gari da ta haxe duk wanda ya siffanta da wannan sifa. To, me zai sa a kevance Shi’ah da zancen, har kuma da wajabta hakan?
Da ‘yan Shi’ah sun ce: Mun yi haka ne saboda duk wanda ba xan Shi’ah ba kafiri ne. Sai mu karva mu ce: Da akwai dalilin da ke tabbatar da kafircin wanda ba su ba, da hakan ta wadatar da ku daga wannan dogon surrutu. Idan kuwa hakan can ba ta tabbata ba, to, wannan dalili da kuka kafa ba zai amfana maku komai ba. Domin kuwa ba ya da magarzai ta fuskar naqali. Idan kuma har akwai wani dalili da za ku iya tabbatar da kasancewar duk wanda ba xan Shi’a ba kafiri, to, ba ko wannan aya ba.
Wani abu kuma da ke tabbatar da qaryar ‘yan Shi’ah a cikin wannan magana, duk bai fi tsomo xan Abbas a ciki ba. Domin kuwa sanannen abu ne ta hanya mutawatira cewa, xan Abbas na da kyakkyawar alaqa da waxanda ba ‘yan Shi’ah ba fiye da yadda yake da ita da, da yawa daga cikinsu ko ma dukkan su. Ko ‘yan Shi’ah, da yawa yakan zauna tare da su, ya ba su fatawowi, ya yi ja-in-ja da su. Ka ga da yana da imanin cewa ‘yan Shi’ah ne kaxai waccan aya ke magana a kai, a matsayinsu na kawai waxanda suka yi imani suka kuma aikata aiki na qwarai, duk kuma wanda ba su ba kafiri ne, to, da bai aikata ko wani abu mai kama da haka ba.
Idan aka lura da kyau za a ga cewa kafin wannan aya, cewa Allah Ta’ala Ya yi:
ﭽ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﭼ البينة: ٦
Lalle ne waxanda suka kafirta daga mutanen littafi da mushrikai, suna cikin wutar jahannama, suna madawwama a cikinta. Waxannan su ne mafi sharrin talikai (98:6).
ﭽ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البينة: ٧
Daga nan kuma Ya ce:
Lalle ne waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan qwarai, waxannan su ne mafifita alherin halitta (98:7).
Ka ga kenan wannan aya ta biyu, na bayyana cewa, mutanen da take magana a kansu, wasu mutane ne, da suka sha banban da waxancan na cikin waccan ayar, wato Mushrikai da Ahlul-Kitabi. Kuma ai akwai wurare da dama a cikin Alqur’ani, inda Allah Ya ambaci Waxanda suka yi imani suka kuma aikata ayyuka na qwarai. Kuma dukan ayoyin gama-gari ne. To laifin me wannan aya ta yi da za a mayar da ita kaxai, saniyar ware?
4.34 Ayar: ﭽ ﯲ ﯳ ﯴ ﭼ الفرقان: ٥٤
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da huxu ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﭼ الفرقان: ٥٤
Kuma (Allah) shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya (alaqarsa) zumunta da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance mai ikon yi (25:54).
Ya ce: Ya zo a cikin tafsirin Sa’alabi daga Ibnu Sirina, wanda ya ce: Wannan aya na magana ne a kan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Aliyu xan Abu Xalib, wanda ya aurar wa da Fatima. Saboda haka ne wannan aya ta sauka.
Xan Shi’ar ya qara da cewa: Ka ga wannan ba ta tabbata ga kowa ba sai Ali. Saboda haka ya fi kowa, kenan shi ne Imamu.
Martani:
Muna son marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya. Don ko shakka babu wannan qarya ce ake yi wa Ibnu Sirina. Ko da ta tabbata kuma ya faxe ta, to, haka kawai bata sa ta zama hujja. Domin sauran malamai sun sava masa a kan haka.
Wannan aya na cikin suratul Furqani ne. Ita kuwa wannan sura a Makka ta sauka. Kuma kan mutane ya haxu a kan cewa wannan aya da muqarrabanta na daga cikin ayoyin da suka sauka a Makka na surar, kafin Aliyu ya auri Fatima. To, ta yaya za a ce an saukar da ita ne a kan sha’anin aurensu?!
Tabbataccen abu ne cewa, wannan aya na magana ne a kan kowace zumunta da kowace surukuta; ba ta ware wani mutum ta bar wani ba.
Mu qaddara cewa ayar na magana ne a kan surukutar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali. To, wannan surukutar kawai ba ta isa tabbatar da kasancewar Ali mafi xaukaka a kan wanda ba shi ba, bisa haxuwar Ahlus-Sunnah da ‘yan Shi’ah. Domin kuwa babu xaya daga cikin halifofin huxu wanda bai da surukuta da Annabi. Tattare kuma da tabbatar kasancewar wasu daga cikinsu mafiya xaukaka a kan wasu. Ka ga inda surukutar ce za ta sa mai ita zama mafi xaukaka, da hakan ta haifar da tuqa da walwala.
Dostları ilə paylaş: |