Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə41/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   37   38   39   40   41   42   43   44   ...   51

5.4 Wakilcin Ali a Madina

Hujja ta huxu inji xan Shi’ar, ita ce kasancewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya waqilta Ali Raliyallahu Anhu ga tsare garin Madina tattare da kasancewar tafiyar da zai yi wurin yaqin taqaitacciya ce, ta ‘yan kwanuka kaxan. Don haka, wannan qwaqqwaran dalili ne ga Ali Raliyallahu Anhu ya kasance shi ne zai gaje halifar Manzon Allah bayan rasuwarsa, ba wani ba. Kuma wai Manzon Allah bai karvi ragamar shugabancin daga Ali Raliyallahu Anhu bayan ya dawo daga wurin yaqin ba, har Allah ya yi masa wafati. Wannan ma wani dalili ne da ke qara tabbatar da cancanntar Ali Raliyallahu Anhu fiye da kowa ga zama halifan Manzon Allah bayan rayuwarsa a garin na Madina da sauran garuruwan musulunci inji shi. Kuma wai wannan hukunci ne shafe zane.


Martani:

Amsarmu a nan ita ce: Ko shakka babu wannan hujja da makamantanta waina ce irin ta wake a hannun alanqosa. Ga amsoshi da martaninmu daki-daki.


Martani na Farko:

A shafi na farko na wannan martani, muna tabbatar wa ‘yan Shi’ah cewa, tarihi ingantacce ya tabbatar da cewa Sahabi Abubakar ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi nuni ga ya gaje halifarsa bayan rayuwarsa, ba Ali ba. Kamar yadda muka tabbatar a baya. Idan kuwa har ‘yan Shi’ah suka kafa kai ga qasa suka ce a’a. Sai mu tuna masu da cewa ai ‘yan’uwansu Rawandiyawa, waxanda bori xaya suke wa tsafi da su, sun tafi a kan cewa Abbas ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya waqilta don ya gaji halifarsa. Amma kuma tabbatacciyar Magana a bakin gaba xayan masana ingancin riwayoyi, ita ce da Alin da Abbas, babu wanda Manzon Allah ya yi nuni ga ya gaji halifarsa. Abubakar Raliyallahu Anhu xin dai da ba su qauna shi ne Manzon ya zava.

Idan kuma har wata riwaya ta inganta wadda ke nuna cewa, Manzon Allah bai yi nuni ga wanda zai gaje shi ba, to, ba wan ba wan kenan a wannan vangare. Abin da zai biyo baya shi ne inganci da tabbatar halifancin Sahabi Abubakar wanda al’umma ta zava bayan Annabi, zave kuwa na cancanta.
Martani na biyu:

Abin da xan Shi’ar nan ya yi na qoqarin tabbatar da cancantar Ali Raliyallahu Anhu ga maye gurbin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bayan rasuwarsa, bisa dalilin waqilta shi da ya yi a gurbinsa a lokacin da yake raye, qiyasi ne. ‘Yan Shi’ah kuwa ai ba su yarda da qiyasi ba. Amma mu da muka yarda da qiyasi, muna iya qiyastawa, mu daidaita waqilta Umar da ya yi a lokacin da yake raye, ba tare da ya yi wani nuni a kan xorewar waqilcin nasa har bayan ransa ba. Don iyakar ikon da Manzon yake da shi a kan al’ummarsa lokacin da yake raye ne, ta hanyar shatawa da tsara siyasar ta kai tsaye ko ta hanyar waqilinsa. Amma da zarar rai ya yi halinsa, to, wannan nauyi da aka xora masa, da ma kowane iri ya kau. Kamar yadda Allah Ta’ala Ya ce ta bakin Annabi Isah Alaihis Salamu: Kuma na kasance mai shaida a kansu a lokacin da nake cikinsu (5:117). Bai ce waqilina zai ci gaba da zama mai shaida a kansu ba. Ka ga wannan dalili ne a kan cewa Annabi Isa bai naxa wa al’ummarsa halifa kafin ya rasu ba. Haka kuma wannan hujja ce a kan cewa ba wajibi ba ne ga Annabawa su naxa wanda zai gaje su tun suna raye.

Qarewa da qarau ma, ta tabbata an riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tava cewa: “Iyakar abin da zan cewa shi ne, irin abin da Annabi Isah ya ce: “Kuma na kasance mai shaida a kansu a lokacin da nake raye a cikinsu (5:117)”.
Martani na Uku:

Mun yarda cewa, shugaba ya sanya waqili don kula masa da waxansu talakawansa a lokacin da yake raye wajibi ne. Sawa’un shugabancin nasa na manzanci ne ko na sarauta, kasancewar hannu xaya ba ya tanka dame. Dole ne ko shakka babu, ya waqiltar da wani ga jama’a a lokacin da baya nan. Don shi waqilin ya jagorance su a sallah, ya hore su da alheri, ya kuma hane su mugun aiki, ya karva wa mai haqqi haqqinsa idan wani azzalumi ya zalunce shi, ya hukunta wanda ya cancanci hukunci daga cikinsu bisa gaskiya da adalci. Duk a madadin wanda ya waqilta shi. Kamar dai yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan yi ga dukkan abin da baya iya zartarwa da kansa, a lokacin da yake raye. Kamar yadda ya naxa kwamandodi, don su riqa bai wa mujahidai sallah, su jagorance su a wurin jihadi, tare da gudanar da sha’anin aikinsu. Haka kuma ya naxa gwamnoni a duka garuruwan da musulunci ya ci. Amma bai ce ga wani da zai tabbata a kan wani muqami, ko ya gaji halifarsa bayan ya rasu ba.

Babu wani dalili da zai sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi haka. Ya riga ya isar da saqon Allah, kuma shi ne kaxai wanda shari’a ta wajabta wa al’umma yi masa xa’a yana raye ko bayan rasuwarsa. Amma zancen wanda zai ci gaba da jagorantar su a bayansa, wannan haqqi ne da iko nasu, su zavi wanda suke so, suke kuma ganin dacewarsa. Kamar yadda suke da ikon yin haka a cikin kowace irin farilla wadda ba ta aini ba (kamar duk wajibban da wani ke iya xauke wa wani) wadda ke buqatar mutum xaya gaban sahu daga cikin al’umma. Wannan ya isa dalili a kan rashin zaman waqilcin da aka bayar ana raye dalili a kan xorewarsa har bayan ran wanda ya tsayar da shi.
Martani na Huxu:

Naxa wakili a lokacin rayuwar shugaba wajibi ne kamar yadda Annabi ya yi.

Gaba xayan masu hankali sun yarda da wannan hujja tamu, don savanin haka ba abu ne mai yuwuwa ba ko alama. Idan kuwa har yana yiwuwa, to kuwa lalle ne mai mutuwar ya naxa gaba xayan waxanda za su jivinci al’amurran jama’a xaya bayan xaya; tun daga Sarakunan yanka har zuwa ga Dagatai da shaggun Hakimai wanda hakan kuwa na da matuqar wuya.
Martani na Biyar:

Rashin naxa magaji da Manzon Allah ya yi, shi ne abu mafi dacewa da cikar xaukaka gare shi a matsayinsa na Manzo. Allah shi ya nufe shi da haka. Kuma har koyaushe Allah kan xora shi a kan abin da yake shi ne mafifici. Kuma yanke hukuncin xorewar waqiltar tasa a lokacin da yake raye, har bayan ransa qololuwar jahilci ne.

Abin da Sayyidina Abubakar ya yi na naxa Umar a matsayin magadinsa tun yana raye, ba ya yi haka ba ne don yana da masaniyar al’umma ba za ta zave shi bayan rasuwarsa ba. Ko alama, ba haka abin yake ba. Ya yi haka ne don wata masaniya da ya kevanta da ita a matsayinsa na shugaba. Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi nuni da shi Abubakar ya gade shi bisa wata masaniya da ya kevanta da ita.
Martani na Shida:

Mu xauka cewa Manzon Allah dole ne a kansa ya naxa magadi. Sai mu ce, to, ai ko ya naxa Abubakar. don nunin da ya yi a kansa.

Kuma cewa, bayan daworsa daga yaqin Tabuka wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai karvi waqilcin da ya ba Ali ba. Ingantaccen tarihi ba zai bari mu je ko ina xauke da wannan magana ba. Domin ko ai da dawowar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya soma tafiyar da al’amurran Madina, ya karvi ragamar mulkin garin kenan. Intaha.

Ba da vata lokaci ba kuma, sai ya tura Abubakar zuwa hajji a shekara ta tara. Ya kuma tura Ali a matsayin mabiyinsa. Bayan sun dawo ne kuma ya sake naxa Ali Raliyallahu Anhu a matsayin gwamnan Yaman. Bayan haka ne kuma ya tafi hajjin bankwana, inda ya sake waqilta wani a tsaron birnin Madina. To, zai yiwu a ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana Madina, Ali na Yaman, amma kuma Alin ne halifansa a can Madinar?

Su dai ‘yan Shi’a jahilcinsu ba ya qarewa. Ba su da wata masaniya game da tarihin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da ma na sayyidina Alin.
5.5 Hadisin Wasicci

Hujja ta biyar a cewar xan Shi’ar, ita ce abin da Ahlus-Sunnah wai suka riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu: “Kai xan’uwana ne, kuma mai wasiccina, kuma halifana a bayana, kuma mai biyan bashin da ake bina”.


Martani:

Muna neman marubucin ya kawo mana ta inda wannan labari ya inganta. Don mu iya abin da muka sani babu wani littafi ingantacce na hadisi da ya riwaito shi, balle ya zama hujja. Kuma babu wani malami daga cikin malaman hadisi da ya inganta shi.

Kuma cewar da ya yi malaman Ahlus-Sunnah sun riwaito shi, idan yana nufin irin su Buhari da Muslimu, waxanda ake kafa hujja da littafansu, to yayi qarya. Ba su riwaito shi ba, balle su inganta shi. Idan kuma yana nufin irin su Abu nu'aimu sun riwaito shi a cikin Kitabul Fadha’il da irin su Mughazili da Khaxibu da Huwarizmi da makamantansu, ko kuma a cikin wasu littafai masu kawo falala. To, malamai masana sun haxu a kan cewa, fitowar wasu hadisai ko wata magana a cikin nau'in waxannan littafai, ba ya sa a kafa hujja da su ko da akan qananan abubuwa balle manya, irin sha’anin Imamah, wadda ku ‘yan Shi’ah kuka tada duniya tsaye a kan ta.

Sannan malaman hadisi gaba xaya sun haxu a kan cewa, wannan hadisi qarya ce zalla. Kamar yadda a baya kaxan malam Ibnu Hazam ya tabbatar cewa, wannan hadisi da iri-irensa zuqi ta mallau ne aka yi wa fiyayyen halitta. Kuma duk wanda ke da masaniya da ilimin hadisi komai qanqantarsa ya san haka.

Yana da kyau a sani cewa, sayyidina Ali bai biya wani bashi da ke kan Manzon Allah ba, don babu shi. Abin da ya inganta a cikin Sahihul Buhari shi ne, koda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar duniya akwai garkuwarsa a hannun wani Bayahude, a matsayin jingina. Ya jinginar da shi ne kuwa a kan awo talatin na alkama da ya karva daga hannunsa. Ka ga waccan garkuwa ita ke biyan wannan bashi. Ba a kuma san wani bashi da ake bin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bayan wannan ba.

Kuma Buhari da Muslim sun riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kada magadana su raba wani abu da na bari. Idan an cire abin da matana za su ci da haqqin ma’aikatana, to, saura sadaka ne”. Ka ga da akwai wani bashi a kansa, da sai a biya daga cikin abin da ya bari, ba Ali ya biya masa ba.


5.6 Hadisin Qulla Zumunci

Xan Shi’ar ya ce, hujja ta shida ita ce, hadisin qulla zumunci da Anas ya riwaito cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a tsakanin Muhajirrai da Ansaru a ranar da aka yi Mubahala. Sayyidina Ali na tsaye kuma Annabin na ganin sa a lokacin. Amma bai haxa shi zumunci da kowa ba daga cikin Ansaru. Sai Ali ya juya yana kuka. Da Annabi bai gan shi ba, sai ya tambayi Sahabbai, ina baban Hasan ya yi ne? suka karva masa da cewa, ya koma gida yana kuka. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci Bilal da ya je ya dawo da shi, yana son ganin sa. Bilal ya bi shi. Isar sayyidina Ali ke da wuya sai sayyida Fatima Raliyallahu Anh ta tambaye shi, me ya faru haka kake kuka? Ya karva mata da cewa, Manzon Allah ne ya qulla zumunci a tsakanin Muhajiruna da Ansaru ya bar ni bai haxa ni zumunci da kowa ba daga cikin Ansaru. Ta ce masa ita ko: “Allah ba zai bari kayi kunya ba. Wataqila Manzon Allah na nufin shi ne abokin zumuncinka”. Suna cikin haka sai suka ji sallamar Bilal. Ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu Manzon Allah na son ganin ka. Da suka iso gaban fiyayyen haliyya Annabi, ya tambayi Ali akan dalilin kukansa. Ya bayyana masa dalilin. Sai Manzon Allah ya ce masa: “Ai ina nufin ni ne abokin zumuncinka. Ko ba ka son ka zama abokin zumuncin Annabinka?” Ali ya ce: “Tabbas ina so, ya Manzon Allah”. Daga nan wai sai Manzon Allah ya riko hannun Ali Raliyallahu Anhu ya hau mimbari ya ce: ya Ubangiji! Ka sheda da ni da Aliyu ga shi mun zama jini da tsoka. Ku sani ya ku jama'a! matsayinsa a wurina, kamar matsayin Annabi Haruna ne a wurin Annabi Musa. Kuma duk wanda yake da akwai so da qauna tsakanina da shi, to, ta kasance tsakanisa da Ali. Daga nan Ali Raliyallahu Anhu ya sa kai, wai sai Umar ya bi shi yana faxin daxa ai ta qare. Daga yau ka zama abin so da qauna a wurina da wurin kowane musulmi. Suka ce, wai wannan zumunci da Annabi ya qulla tsakaninsa da Ali Raliyallahu Anhu na nuna cewa Ali ya fi gaba xayan Sahabbai wurin daraja. Saboda haka ba wanda ya cancanci ya zama halifa bayan Annabi sai shi.


Martani:

Muna buqatar marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan hadisi. Don bai faxa mana littaffin da ya ciro hadisin daga cikinsa ba, kamar yadda ya saba. Duk da yake yakan xauko hadissan ne daga cikin littafan da hujja ba ta kafuwa da su a shari’a. Kamar dai yadda ya gada ga manyan malamansa ‘yan Shi’ah, waxanda ke riwaito labarai da hadissan qarya waxanda ba su da asali. Ga shi kuwa Ibnul Mubarak ya ce: “Isnadi rukuni ne na addini. Don ba don albarkacin isnadi ba, da kowa ya tsoma bakinsa da abin da ya ga dama a cikin Addini. Idan kuma aka tambaye shi dalilin ya tsaya yana ‘yan kame-kame”.

Malamai masana hadisi dai sun tabbatar da cewa, wannan hadisi qiren qarya ne. Babu kuma malami xaya da ya ware daga wannan da'ira. Haka kuma malaman sun tabbatar da cewa, duk wanda ya qirqiro wannan hadisi ya danganta shi ga Manzon Allah, jahili ne tubran, ta yadda bai ma san yadda zai kitsa qaryar da ba za a iya gane qarya ce ba. Ko jaririn da ke rarrafe a duniyar ilimin hadisi ya tunkari wannan hadisi zai rosa shi. Za mu qara bayani nan gaba kaxan.

Babu kuma wani hadisi da ya inganta daga Annabi cewa, ya qulla zumunci da Ali Raliyallahu Anhu. Dukkan su qiren qarya ne. Annabi bai qulla zumunci da kowa ba. Kamar yadda bai qulla shi tsakanin Muhajirai wasu–wasu, ko tsakanin Abubakar da Umar, ko tsakanin Ansaru wasu–wasu a wannan lokacin ba. Amma dai abin da ya tabbata shi ne, Manzon Allah ya qulla zumunci tsakanin Muhajiruna da Ansaru lokacin da ya iso Madina. Ita kuwa Mubahala an yi ta ne ranar da wakilan qabilar Najjaru suka zo wurin Manzon Allah a shekara ta tara ko ta goma bayan hijira.

Daga cikin hadisin kansa akwai dalilin da ke bayyana zamansa qarya, kamar inda ya ce, a ranar Mubahala Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qulla zumunci a tsakanin Muhajiruna da Ansaru. Mubahala kuwa an faxi sadda aka yi ta. A dalilinta ne aka saukar da surar Ali Imran.

Saboda haka, zumuncin da Manzon Allah ya qulla tsakanin Muhajiruna da Ansaru wanda lafiyayyen tarihi ya san da shi kamar yadda muka bayyana, ya faru ne a shekara ta farko bayan hijira a gidan Banu Najjar. Tsakanin wannan kuwa da Mubahala akwai shekaru masu yawa.

Ta kuma tabbata cewa, Manzon Allah ya qulla zumunci tsakanin sayyidina Ali da Sahalu xan Hunaifu. Ya kuma qulla wani tsakanin Muhajiruna da Ansaru. Amma tsakaninsa da Ali Raliyallahu Anhu waxanda dama ‘yan’uwa ne kuma ga su Muhajirai, ai ba buqatar qulla wani zumunci.

Daga qarshe, cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Ali: “Baka son ka zama a wurina kamar yadda Haruna yake a wurin Annabi Musa? Malaman hadisi gaba xaya sun yi ittifaqi a kan cewa, ya yi wannan magana ne lokacin da zai je yaqin Tabuka, bai kuma sake maimaita ta a wani wuri ba.


5.7 Hadisin Yaqin Haibara

Xan Shi’ar ya ce hujja ta bakwai, ita ce abin da malaman Sunnah suka riwaito cewa, a lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsare mutanen Haibara tsawon kwanaki ashirin da tara, ana dakon yaqi. A lokacin tutar musulmi na hannun Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu sai ya samu rauni a idonsa xaya, har ya yi kumburi, ta yadda ba ya gani sosai balle ya yi yaqi da kyau. Ana haka sai Marhab, shugaban Yahudawa ya shelanta fara yaqi. Ganin haka, sai Manzon Allah ya umurci Abubakar da ya karvi tutar, ya canji Ali, ga kuwa sauran Muhajiruna. Abubakar ya karvi tutar ya tafi wai ya kasa tavuka kome, ya dawo kunya-kunya. Safiya na yi sai Umar ya karvi tutar, shi ma wai bai je ko ina ba, ya dawo ya labarta wa makusantansa abin da ya haxu da shi na cirjiya har ya dawo da baya. Daga nan sai Manzon Allah ya ce: Kai! Ku kira min Ali, shi xai ke iya wannan daga. Sahabbai suka ce, hala ka manta ba ya da lafiyan ido xaya? Ya ce, kai haka ne fa, ku nuna mani inda yake. Ku nuna mani wanda Allah ke so yake kuma son Allah, wanda kuma baya gudu ranar daga. Qarshe xai suka kira Ali ya zo. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi tofi a kan hannunsa ya shafi ido da kan Ali, nan take ya warke. Shi kuma ya danqa masa tuta. Ali ya yi yaqi mai tsanani har Allah ya ba shi nasara.

‘Yan Shi’ah suka ce, wai waxancan siffofi da Manzon Allah ya siffanta Ali da su alama ce ta babu wanda ya kama qafarsa cikin sauran Sahabbai. Saboda haka, shi ya fi cancanta da zama shugaban musulmi bayan wucewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.
Martani:

Muna son marubuci ya yi wa duniya bayanin yadda wannan hadisi ya inganta, a cikin wannan siga. Domin cewar marubucin ya yi malaman Sunnah sun riwaito wannan hadisi gaskiya ne. Sai dai ba haka amintattu daga cikinsu suka riwaito shi ba. Ingantattar magana ita ce, sayyidina Ali Raliyallahu Anhu bai ma halarci yaqin Haibara ba. A sanadiyar wancan kumburi da ya sami xayan idonsa. Daga baya ne kuma ya kasa daure wa zaman gida Annabi na fagen fama. Saboda haka sai ya haura takalmansa ya isa wurin. Kafin ya kai wurin ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Sahabbai dake tare da shi: “Tutar yaqinmu a gobe zan danqa ta ne a hannun wani mutun wanda Allah da Manzo ke so, yake kuma son su, wanda kuma Allah zai ba shi nasara”.

A lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke wannan magana tutar ba ta shiga hannun Abubakar ko Umar ba. Kai ko alamar karkata ga xayansu babu. Cewa an ba su ita sun kasa tavuka komai kafin haka, qarya ce tsagwaronta. Hasali ma jin waccan magana ta Manzon Allah ce ta sa sayyidina Umar ya ce: Ban tava jin ina kwaxayin shiga gaban sahun jama'a a matsayin jagora ba, sai a wannan rana. Kuma ba ni kawai ba, duk mazajen da ke wurin, kowannensu ya yi fatar ya zama shi ne Manzon Allah zai danqa wa tutar. Amma ina! Safiya na wayewa sai kawai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kira Ali Raliyallahu Anhu. Kafin ya iso daga wurin da yake, sai aka gaya masa cewa, ai yana fama da ciwon ido. Da ya iso sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa addu'a a idon nan take kuwa ya warke, ya kuma danqa masa tutar. Allahu Akbar! Rabo ya rantse sai mai shi.

Ka ga a hankalce wannan falala da Ali Raliyallahu Anhu ya samu, sakamakon biyo Manzon Allah ne da ya yi tattare da yana fama da wannan rashin lafiya. Ita kuma waccan magana da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi tun Aliyun bai iso ba karamarsa ce Sallallahu Alaihi Wasallama. Babu kuma wani lafazi a cikin hadisin da ke nuna naqasar darajar Sahabi Abubakar ko Umar. Ko alamar haka babu.

Wani abu kuma shi ne: Cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi Sayyidina Ali na son Allah da Manzonsa, su kuma suna son sa gaskiya ne. Amma hakan martani ne ga Nasibawa waxanda ke ganin akasin haka. Kuma ba za a saurara wa ‘yan Shi’ah ba, idan suka kafa hujja da wannan magana a kan fifikon Ali Raliyallahu Anhu a kan sauran Sahabbai, balle har su qara da faxar abin da suka yi imani da shi cewa, gaba xayan Sahabban sun yi ridda bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama in ban da Ali Raliyallahu Anhu da wasu kaxan daga cikinsu.

Idan ‘yan Shi’ah suka kafa hujja da waxannan maganganu, to, sai mu bar su da takwarorinsu Harijawa, waxanda ke ganin har shi Aliyun ya yi ridda, a lokacin da ya yarda da sasantawa tsakaninsa da Mu’awiyah a yaqin basasar Siffin, inda suka ce wa Ali: “Tabbas ka fita daga musulunci. Maza-maza ka dawo”.

Sannan kuma xan Shi’ar a cikin sharhin wancan hadisi da ya yi, ya ce wai, cewar da Annabi ya yi zan xamqa tutar yaqinmu ga mutum mai siffa kaza da kaza, kuma abin ya faxa hannun Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu hakan na nuna cewa, babu wani Sahabi da ke da waxancan siffofi sai fa shi Alin.

A nan muna da Martani biyu zuwa gare shi. 1) Eh, mu xauka cewa siffofin can da Annabi ya faxa da tabbacin nasara da ya ce zai samu, duk sun tabbata a kan Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu. A hankalce da la’akari da qa’idar harshen Larabci, hakan ba ta nuna ba mai waxancan siffofi a cikin Sahabbai ba sai Ali, balle a kafa hujja da hakan a kan kasancewarsa mafi cancanta da shugabanci bayan Manzon Allah, kai tsaye. 2) Idan kuma muka cije a kan cewa, ba mu yarda da cewa waccan magana ta Annabi na nufin kevance wani daga cikin Sahabbai da waxancan siffofi, koda kuwa shi Allah ya zava da karvar tutar, ba mu yi kuskure ba. Dalilinmu kuwa shi ne maganar ta Annabi, kamar kai kace ne: Zan bayar da wannan kuxi kyauta ga wani mutum mabuqaci, ko ka ce: Yau zan ziyarci wani mutum maras lafiya, ko managarci. Koko zan danqa wannan tuta a yau hannun wani mutum jarumi. Ko wani abu mai kama da haka. Gaba xayan waxannan jumloli ba su nufin kevance wani mutum da waxancan siffofi. Duk wani mabuqaci ko maras lafiya ko managarci ya shiga cikin lissafinka, illa dai sai wanda Allah ya datar kawai.

To, mu qaddara cewa zaven sayyidina Ali Raliyallahu Anhu da Allah ya yi da waccan falala ta shigar waccan tutar a hannunsa tattare da isowarsa qarshe a Haibara, hakan ya daxa xaukaka dajararsa. Ko da mun yarda da haka, to, ba ta nufin a cikin sauran Sahabbai babu wanda ya fi shi girman daraja a wannan rana. Ko alama ba haka abin yake ba.

Harwayau dai mu qara qaddara cewa, xaukakar sayyidina Ali da martabarsa sun daxa fitowa a idon musulmi a waccan rana, hakan ba ta nufin kasancewarsa “Ma’asumi” kuma wanda ko sama da qasa za su haxu sai ya gaji halifar Manzon Allah bayan wucewarsa. Kai ba Ahlus-Sunnah ba, da yawa daga cikin ‘yan Shi’ah Zaidiyyawa da wasu daga cikin Mu’utazilawa na baya-baya da wasunsu duk sun tafi a kan haka. Sun yi imani da kasancewar Ali Raliyallahu Anhu mafificin daraja a cikin Sahabbai. Amma kuma ba su ga wata illa a cikin kasancewar Sahabi Abubakar halifa ba. Don su a wurinsu ya halatta mai matsa kaiciyar daraja ya jagoranci sahun musulmi, tattare da kasancewar a cikin waxanda ke bayansa akwai wanda mudun darajarsa ya cika ya batse.


5.8 Hadisin Tsuntsu:

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta takwas ita ce labarin bandataccen tsuntsu. Wai gaba xayan malaman Sunnah sun riwaito cewa: Watarana an kawo wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kyautar bandataccen tsuntsu, sai ya buxa baki ya ce: “Ya Ubangiji! Ka kawo wani mutum mafi soyuwa a wurinka da wurina daga cikin halittarka, wanda za mu ci wannan tsuntsu tare da shi. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cikin gida yana jiran wanda Allah zai kawo. Sahabi Anas kuma wai, na zaune qofar gidan daga ciki yana cika fada. Ana haka sai Anas ya ji an qwanqwasa qofa. Da ya buxe qofar sai ya ga ashe Ali ne ya kawo jiki, sai ya ce masa: Annabi ba ya ganuwa yanzu, don yana ‘yar buqata, sai Ali ya juya. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake maimaita waccan addu’a, kuma sai ga Ali ya sake qwanqwasa qofa. Anas ya ce masa: Ashe ban gaya maka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai ganuwa, yana wata buqata ba? Sayyidina Ali ya sake juyawa. Can kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sake maimaita wannan addu’a. Sai ga sayyidina Ali ya dawo fusace, ya sake qwanqwasa qofar da qarfin gaske, har Annabi ya ji qwanqwasar ya kuma ce wa Anas ya bari Ali ya shigo.

Shigowar sa ke da wuya sai Annabi ya tambaye shi: Me ya tsayar da kai haka?” Shi kuma ya karva masa da cewa, na zo har sau uku Anas na cewa, ba ka ganuwa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya juya kan Anas ya ce masa: “Anas me ya sa ka yi haka?” Ya karva masa da cewa: “Ina sane nayi haka ya Manzon Allah. Na so ne Allah ya kawo wani mutum daga Ansaru”. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: “Kana ganin akwai wani mutum daga cikin Ansaru wanda ya fi Ali xaukaka da daraja?” Xan Shi’ar ya kammala da cewa, tun da kuwa har Ali shi ne mafi soyuwa ga Allah daga cikin halitta a wurin Allah, to, lalle kuwa shi ya fi cancanta da zama halifa a bayan Annabi.

Shi kenan. Qanqurus qan qusu!



Martani:

Tun da farko, cewar da ya yi dukkan malaman Sunnah sun riwaito wannan hadisi qarya ce muraran. Kuma muna bin sa bashin ingancin wanna tatsuniya. Domin babu wanda ya riwaito shi daga cikin masana hadisi amintattu, ballantana ya inganta shi. Amma kamar yadda gama garin malamai masu kwasar karan mahaukaciya suka riwaito ire-irensa, sun riwaito shi, shi ma. Haka kuma sun riwaito masu kama da shi a game da falalar Mu’awiyah. Har ma an wallafa littafai masu yawa a irin wannan. Amma a wurin malamai masanan fannin hadisi, da waxannan hadisan da babu duka xaya.

Kuma ma a wurin malaman hadisi, hadisin bandataccen tsuntsu tatsuniya ne. Wasu malamai ma sun tattara hanyoyin da aka ce an samo wannan hadisi ta su. Cikinsu har da Imamu Hakim An-Naisaburi da Abu Nu’aimi da Ibnu Mardawaihi da sauran su. Da aka tambayi Hakim a kan matsayin hadisin, cewa ya yi: “Bai inganta ba”. Ga shi kuwa ‘yan Shi’ah na ganin Hakim a cikin malamansu.

A bayyane ta ke cewa, cin naman tsuntsu ba wani abu ne mai girma na a zo a gani ba, har da za a yi fatar haxa hannu da mafi soyuwar halitta a wurin Allah cikin yin sa. Ai da shege da xan halas ba wanda ba a shar’anta wa cin abinci ba. Babu wani kusanci ga Allah da sayyidini Ali zai qara, ko wani ci gaba da addinin Allah zai samu, ko wani inganci da rayuwar musulmi zata qara don Ali ya ci naman tsuntsu tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan fa in an qaddara ingancin hadisin kenan.

Wannan hadisi dai bai inganta ko a addinin Shi’ah don ya yi ban hannun makafi da aqidarsu. Don su, suna ganin cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya san cewa, Ali shi ne mafifici daga cikin halittun Allah, kuma don haka ne wai, ya zave shi a matsayin halifansa. Shi kuwa wannan hadisi na nuna cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai san wanda Allah ya fi so ba.

To, a nan ko dai mu xauka cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya san wannan bayani, ko a’a. idan muka qaddara cewa, ya sani, to, me ya janyo buqatar wannan addu’a? ai da sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka kawo min Ali, don shi ne mafi soyuwa gare ka daga cikin halittunka”. Kamar yadda yake aikawa a kira masa wasu daga cikin Sahabbai. Kuma da ya ambaci Ali Raliyallahu Anhu a cikin addu’arsa, da Anas bai hana Alin ganin sa ba, da kuma bai yi waccan fata maras amfani ba ta gurin Allah ya kawo wani daga cikin Ansaru.

Idan kuwa muka qaddara cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai san Ali shi ne mafi soyuwar halittar Allah ba, wancan iqirarin nasu ya faxi. Kuma ya za a ce, mutum kamar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai san wanda ya fi so ba, tun da xan Shi’ar cewa ya yi a addu’ar: “Ya Ubangiji! Ka kawo wani mutum mafi soyuwa a wurinka da wurina daga cikin halittarka..”.

Da za ka haxa hancin ma’anar sauran hadisai da suka inganta, za ka taras sun ci karo da wannan hadisi. To, ya za a kawar da su da wannan tatsuniya?



Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   37   38   39   40   41   42   43   44   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin