Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə30/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   26   27   28   29   30   31   32   33   ...   51

Fuska ta Biyar:

Eh, gaskiya ne Allah Ta’ala ya halicci mutum da qwandar son zama cikin jama’a. Kamar yadda kuka ce. Amma cewar da kuka yi wajibi ne a samar da shugaba ma'asumi a cikin irin wannan zama, don ya hana mutane zalunci da cutar da juna, na nufin lalle ne a samar da shi a kowane gari daga cikin garuruwan duniya. To, ma’asumi nawa ake buqata kenan? Kuma har a garuruwan kafirai da mushrikkai akwai irin waxannan ma'asumai? Kenan har a Sham inda Mu’awiyah Raliyallahu Anhu yake akwai ma’asumi ko?

Na san ga wautarku za ku ce, kuna nufin ne akwai ma'asumi xaya a kowane babban birni. A sauran garuruwa kuma akwai waqilansa. To, tambayarmu a nan ita ce: Shin waqilan nan sun haxa gaba xayan garuruwan duniya ne, ko sashensu?

Idan kuka ce, ai akwai su a cikin gaba xayan garuruwan duniya. Mun san wannan irin fankamar da kuka saba da ita ce. Idan kuma kuka ce, a’a, a waxansu sassa ne kawai ake da su, to sai mu tambaye ku, don me haka za ta faru idan dai har cewar da kuka yi samar da ma'asumi wajibi ne a kan Allah ta tabbata? Babu dalilin da zai sa a kevance wasu garuruwa da wannan alheri, a bar wasu. Domin kuwa ai buqatar da suke da ita da wannan ma'asumi duk xaya ce.



Fuska ta Shida:

Muna son mu gane, shin ita wannan martaba ta ma’asumantaka ta taqaita ne ga babban kawai, koko su ma waqilan nasa ma'asumai ne? Mun san ba za ku yi kuskuren cewa su ma ma'asumai ne ba. Domin kun san za mu jefe ku da ‘Girman kai’. Domin kuwa ai ko a cikin waqillan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama babu ma'asumi ko xaya, balle daxa daga cikin waqilan Ali Raliyallahu Anhu waxanda ma tarihi ya tabbatar da irin yadda suka cutar da shi, alhali waqilan Ma’awiyah Raliyallahu Anhu ba su cutar da shi haka nan ba. To ina zancen ma’asumanci yake a nan?

Wohoho! Na san kuna iya sake salo, ku ce, ai sharaxin ma’asumantaka a kan babban kawai yake. To, haka ba za ta raba mu da ku ba. Harwayau, idan haka ne, mene ne makomar sauran mutane da ke zaune a garuruwan da ke nesa da babban birnin da ma'asumin yake? Musamman a irin lokacin da ma'asumin ba ya iya tanqwara waqilan a sakamakon kasancewarsa kasasshe? Kenan irin waxannan mutane ba za su qaru da komai ba na gallar luxufin ma'asumin. Domin kuwa wanda ke ba su sallah, yake hunkuci tsakanin su, yake karvar dukiyoyinsu a matsayin khumisi, suke kuma tsananin biyayya gare shi ba ma'asumi ba ne.

Kuna iya cewa ai gaba xayan waxannan abubuwa waqillan na yin su ne a matsayin babban nasu. Sai mu ce: Da a ce shi wannan ma'asumi naku ya yi jaruntaka da qarfin iko kamar na Umar da Usmanu da Mu’awiyah Raliyallahu Anhu ba zai iya cusa imanin tsayar da adalci a cikin zukatan gaba xayan waqilansa ba, kamar yadda shi yake yi. Iyakar abin da yake iya yi shi ne ya zavi wanda yake ganin yana iya kwatanta adalaci fiye da wasu, ya naxa shi. Idan kuwa ya kasa samun kowa sai kasasshe, kuma azzalumi, ba yadda zai yi dole shi zai naxa.

A nan ba ku da wata ta cewa, illa ku ce, idan har Allah bai halicci kowa ba sai irin waxannan rubabe-rubaben, to, ba lalle ne a kan babban ma'asumin ya nemo shi ba. Sai ya yi da abin da ya samu.

Da wannan magana taku kenan, kun yarda da cewa Allah bai halicci wani mahaluki da ke da iko a kan komai, wanda kuma ba ya kuskure ko zalunci ba. Abin da kawai Ya wajabta wa shugaba shi ne ya aikata iya abin da yake da ikon aikatawa. Kamar yadda iyakar abin da yake wajibi a kan mutane shi ne su zavi mafi zama kusa ga shiriya a matsayin shugaba, ko da kuwa akwai wata ‘yar tangarxa tare da shi ta fuskar ikon zartarwa da tsayar da adalci.

Wannan ita ce gaskiya. Domin an riwaito cewa Umar Raliyallahu Anhu yakan ce: “Ya Ubangiji a wurinka nake koken jaruntakar fajiri da kasawar nagari”.

Ka ji. Kowa kuwa ya san ba a tava yin wani shugaba a duniya kamar Umar ba. Domin kasancewarsa zuma; ga dafi ga zaqi. To, ya kake zaton yadda halin wanda ba shi ba zai kasance?

Sannan kuma, shi kasasshen ma'asumin, wanda aka tabbatar da babu shi, wa zai tsare kaiwa da komowa tsakaninsa da waqilansa, balle ya san halin da suke ciki? Waye zai tursasa su su yi masa xa’a? Idan daga cikin waxanda ya waqilta xin, wani ya yi laho ya nuna kamar na Allah ne shi, sai bayan da ma'asumin ya naxa shi ta bayyana shi kure ne; ya tattara dukiyar mutane ya haye ya nemi mafakar siyasa a wajen wasu sarakuna. Yaya wannan kasasshen ma'asumin zai yi da shi?

Ka ga a haka ta tabbata, komai irin qarfin ikon da ma'asumin yake da shi, ba zai iya tabbatar da abin da ake buqata na zaman jama’a ba, shi kaxai. To, ina ga wanda yake kasasshe kuma audugar kasuwa? Ga shi kuma a fake, a vace, ta yadda ba zai iya ce wa mutane uffan ba. Balle daxa a lokacin da ya karva sunan da masu hankali da ilimi suka yi masa na Malam-Babu?



Fuska ta Bakwai:

Rawar da ta kamata wannan ma'asumi naku ya taka, da Allah Ya sa akwai shi, ta hana masu qarfi su zalunci na qasa gare su, da qwato haqqin da suka riga suka ci na wani, da ba wa kowa haqqinsa. Duka wani yanki ne na toshe qofar zalunci, da tabbatar da adalci. Sai kuma ga shi ya kasance kasasshe kuma audugar kasuwa, ta yadda ba ya iya kare kansa daga kowane irin zalunci, qo kwato wani haqqin nasa na shugabanci ko dukiya, ko haqqin matarsa na gado. To, wanda ya kasance haka, wane irin zalunci zai iya kawarwa balle har ya sadar da wani haqqi ga mai shi? Balle daxa a irin wannan hali da aka tabbatar da rashin kasancewarsa a zahiri, yana dai can fake, ta yadda ba ya iya bayyana a wata al-qarya ko qauye don tsoron wai kada azzalumai su kashe shi. Haka yake lave fiye da shekaru 460. Alhali kuma ga duniya ta cika ta batse da fasadi da zalunci. Shi kuwa ko ya fito ya ce ga shi shi ne wane, abin ya faskara. Ka ga kenan babu yadda za a yi har abada ya iya kare faruwar wani zalunci ko ya sadar da wani haqqi ga mai shi. Kai, babu wanda ya fi su dacewa da faxar Allah Ta’ala, inda yake cewa:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭼ الفرقان: ٤٤

Ko kana zaton cewa, mafi yawansu suna ji, ko kuwa suna hankali"? Su ba su zama ba face dabbobin gida suke. A’a, su ne mafi vacewa ga hanya (25:44)

Fuska ta Takwas:

Ku sani ya ku ‘yan Shi’ah, buqatar da mutum yake da ita ta sarrafa jikinsa da ikon kansa, ta fi girma da matuqar muhimmanci bisa ga buqatar da yanayin zaman jama’a a matsayin birane suke da ita, ta samun shugaba. Amma kun ga tattare da haka Allah bai halacci ran mutum ya sa ta ma'asumiya ba. To, yaya zai zama wajibi a kansa ya halicci wani shugaba ya kuma sa shi ma'asumi?

Abin lura a wannan magana tawa shi ne, ai kun san mutum na iya fanxare wa birnin zuciyarsa ya aikata wani savo a voye. Har ya shahara da aikata wasu zalunce-zalunce da varna, amma ma'asumin da ke tare da shi bai sani ba. Ko da kuma ya sani ba yadda zai yi ya hana, tunda kasasshe ne. To, idan kuwa har Allah ya qyale shi bai yo shi, shi kansa ma’asumi ba, to, ba wata buqatar samar da wani ma’asumi don ya kula da shi.

Fuska ta Tara:

Tambaya ce za mu yi a nan. Shin kuna nufin samuwar waxannan imamai ma'asumai ta sa shiriya ta fi varna yawa a bayan qasa? Ta yadda kowane mutum zai kasance mafi zama kusa ga shiriyar, mafi kuma zama nesa daga varna, ta yadda da za a rasa Imaman babu mai iya maye gurabunsu? Koko a’a, kuna nufin kasancewarsu za ta kai qarshen sake faruwar wata varna? Ko akwai dai wani miqdari na shiriya da kuke nufin kasancewarsu ta samar?

Idan kuna nufin damen farko na wannan magana; wato shiriya ta rinjayi varna. To, ai wannan shi ne abin da mafi yawan shugabannin musulunci suka tabbatar a kwanukansu. Haka ta kasance a zamanin halifancin Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhum fiye da yadda ta kasance a zamanin halifancin Ali Raliyallahu Anhu kamar kuma yadda ta kasance a kwanukan mulkin halifofin Umawiyyawa da Abbasiyawa, fiye da yadda ta kasance sanadiyar imamai goma sha biyu xin nan naku.

Bari ma ta zancen waxannan, yadda irin haka ta kasance a zamanin mulkin Rumawa da Turkawa da Indiyawa ta fi yadda ta kasance da kasancewar Malam-na-Voye wanda kuke yi wa laqabi da Sahibuz-zamani. Kuma dama yadda matsalar take ai, babu wani shugaba da za a naxa, daga baya a qaddara gushewarsa ba tare da mamayi ba, face varnar da za ta faru a lokacin da aka qaddara gushewar tasa, ta fi wadda ka iya faruwa idan yana nan. Amma kuma duk da haka abu ne mai sauqi wani shugaba ko mutum ya fi shi kasancewa shiryayye. Kamar yadda ake jin an ce, shekara sittin qarqashin fajirin shugaba ta fi alheri bisa ga dare xaya ba shugaba.

Idan kuma kuka ce, a’a muna nufin dame na biyu na maganar, wato samuwar shiriya ta har abada tsintsa; wadda ba varna tare da ita. Sai mu ce maku: Har abada haka ba za ta samu ba, domin Allah bai shirya haka ba. Kuma ko kokwanto babu a kan cewa bai halicci dalilan da ke iya tabbatar da samuwar haka ba. Duk kuwa wanda ke jin wajabcin kasancewar haka, har ya wajabta samar da hanyoyin samuwar haka a kan Allah, lalle ne ko dai yana yaudarar kansa ne, ko kuma ya rena Allah Ubangijinsa. Domin kasancewar Allah Ya halicci abin da ke iya taimakawa ga samuwar haka, ba za ta samar da hakan ba, idan bai halicci abin da lalle sai da shi ne hakan ke iya kasancewa ba.

Wannan magana ma taku, ku sani ta taqaita a kan ayyukan bayi ne na al’ada. Abin duk da kuwa ya shafi zancen ma'asumanci, to, sai hattara. Domin kuwa ba shi ne ke da ikon samar wa kansa ganbun tsari da ikon da ke tare da shi ba. Wannan sai Allah. Kai ‘yan Shi’ah daga cikin Mu’utizilawa ma na jin hakan ta sha qarfin ikon Allah.

To, wajabta wa Allah Subhanahu WaTa’ala halitta wani mutum wai shi ma'asumi wanda zai shafe savo daga doron qasa kwata-kwata, ya fi zama varna a kan wajabta masa halittar kyawawan ayyukan bayi gaba xaya.

Fuskar ta goma:

Yanzu kuma za mu koma ga cewar da xan Shi’ar ya yi wai, da kuwa shugaban al’umma bai kasance ma'asumi ba, da hakan ta sa ta buqatuwa ga samun wani shugaban ba shi ba. Domin kuwa kuskuren da ke da yiwuwar faruwa a cikin al’umar ne, dalilin da ya sa ake da buqatar irin wannan shugaba. To, idan kuwa har shi ma akwai yiwuwar ya yi kuskure, to, sai a buqaci wani shugaba ba shi ba, don da shi da su ba a san gwani ba.



Martani:

Me zai hana ku yarda da kasancewar wasu mutane a cikin al’ummar, waxanda za su riqa faxakar da shugaban a duk lokacin da ya saki hanya bisa kuskure? Ta yadda ba za ta yiwu gaba xayan xaixaikun al’ummar su haxu a kan kuskuren ba. Wato ya kasance a duk lokacin da wani sashe na jama’a ya yi kuskure, sai shugaba ko mataimakinsa ya faxakar da su. A lokaci xaya kuma idan shi shugaban ne ya yi kuskuren, ko mataimakin can nasa, sai a sami wasu mutane su faxakar da shi. A haka sai suturar ma'asumancin ta tabbata a jikin gaba xayan al’ummar har da shugaban, ba a jikin kowane daga cikinta a xaixaice ba. Kamar yadda Ahlus-Sunnah ke cewa.

Kamar yadda hukuncin yake a cikin xaixaikun masu bayar da wani labari mutawatiri, wato kasancewa tana yiwuwa ga kowane xaya daga cikinsu ya yi kuskure a matsayinsa na tilo. Ko ma ya qiri qarya da gangan. Amma a lokacin da suka haxu wasu-wasu a kan labari xaya, al’ada ba ta yarda da yiwuwar su haxa baki a kan qarya ba. Kamar yadda abin yake a cikin sha’anin ganin jinjirin wata ko wasu qananan abubuwa. Wanda tana yiwuwa ga mutum xaya wani abu ya qyafta masa ya faxi savanin abin da yake shi ne gaskiya. Amma idan taron jama’a ya cure, hakan kan wuyata.

Haka wannan lamari yake a cikin nazarin lissafi da zane-zane. Tana yiwuwa qwarai, mutum xaya ya kasa tantance matsala xaya ko biyu a wannan fage. Amma a yayin da ma’anbuta ilimi suka haxu a zauren qara wa juna sani, suka yi wa matsalar taron dangi, yana da wuya a al’adance su kasa tantance mas’alolin kamar yadda suke asalatan

Kuma ma ai sanannen abu ne cewa, rigar ma’asumantaka ta fi dacewa da wuyan taron jama’ar da bakinsu ya haxu a kan kalima xaya. Saboda hakan ya fi zama kusa ga abin da hankali da duniya ke karva, fiye da wuyan mutum xaya. Idan kuwa har rigar ta qi shiga wuyan irin wannan taro da suka haxu a kan wani ayyanannen abu guda xaya, to bai ko kamata a iske ko sunsunar wuyan mutum xaya, wanda ya kevanta da wani abu ta yi ba. Idan kuma har ta kuskura ta shiga wuyansa har ta zauna, to lalle ne kuwa ba makawa, a iske ta daxe da zaunawa wuyan irin wancen taro har ta yi annakiya saboda jimawa; ana batun tuve ta a wanke.

Kuma idan ka duba da kyau, za ka ga hakan ta tabbatar da fin cancantar wuyan taron jama’a da rigar can ta ma'asumanci a kan wuyan tilo. Kuma hakan ya haxa har da shi shugaban, don xaya ne shi daga cikin jama’ar. Illa dai kawai ya kasa zama gudagudan ma'asumi: Wahadahu la sharika lahu. Ka ga ta haka an huta.

Amma saboda jahilcin da ya yi wa ‘yan Shi’ah kanta, sai suka wajabtar da kasancewar xaya daga cikin musulmi ma'asumi. A lokaci xaya kuma suka yardar wa gaba xayan ragowar musulmi yiwuwar faxawa a cikin kuskure, matuqar babu wani ma'asumi xaya tare da su. Amma ka ga a fahimta ta hankali, duk lokacin da kan malamai da yawa ya haxu a kan wani zance xaya, to, ya fi kasancewa mafi kusa ga zama daidai, bisa abin da wani malami tilo yake a kai can gefe. Wannan kuwa ko da savanin da ke tsakanin malaman a waxansu mas’aloli ya wuce misali. Domin kuwa idan dai ana iya kama maganar wani tilo ta zama ilimi, to kuwa maganar taron jama’a ta fi cancanta da zama haka.

Wani abin da zai qara tabbatar maka da haka shi ne, ai shugaba abokin tarayyar mutane ne a cikin gaba xayan aikinsa wanda ya shafe su, domin kuwa shi kaxai ba ya iya gudanar da wannan hidima, sai idan sun tallafa masa. Misali, ai ka ga idan ba su ba shi haxin kai ba, ba ta yadda za a yi ya iya zartar da hukunce-hukunce, ko ya tabbatar da cikar mudun haqqoqa. Ba zai iya karo da abokan gaba ba, sai da sa hannunsu. Kai, ko sallar juma’a da ta jam’i sai idan sun yarda sun bi shi, sannan zai samun ladarsu. Haka kuma ba zai karva sunan shugaba ba, sai idan sun yarda sun aikata abin da ya umurce su da aikatawa.



Fuska ta Goma Sha Xaya:

Ya kamata ‘yan Shi’ah su kwantar da hankali su sani ilimi a addinin musulunci kashi biyu yake. Babu wani abu daga cikin abubuwan da shugabanni ko sauran al’umma ke buqata na ilimi da ya fita daga cikin waxannan nau’o’a biyu: Nau’i’ na farko shi ne, ilimi gamagari, wanda ya haxa da sanin wajabcin salloli biyar, da azumin watan Ramalana da zakka da hajji, da haramcin giya, da zina da sata, da makamantansu. Nau’i na biyu kuma shi ne, kevantaccen ilimi, ko kuma ka ce, Rava-darni. Wanda ya haxa da, gane zakka ta wajaba a kan kaza ko tsayar da haddi kaza ya wajaba a kan wanda ya aikata laifi kaza, da matara kama da wannan.

Shi Nau’i na farko, shari’a ta hutar da kowa ta vangarensa. Ba ta da buqata da wani shugaba ya tsoma baki a ciki. Domin kuwa babu wani jijjige ko jigo na shari’a wanda yake wajibi ga samuwa face ka taras Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi bayaninsu filla-filla a nassance. Ko kuma ya bar wata ‘yar kafa a jikin waxanda ke da buqatar fahimtar malamai a ciki (Qiyasi). To, idan suna magana ne a kan ilimin da muka faxa kashi na farko, to, gayya ta gama aiki a nan. Idan kuwa na biyun ne suke magana, to ba sauran wahayi dangane da shi sai dai qiyasi.

Idan kuma har kuka yi qarfin halin cewa, ai akwai waxansu abubuwa da Manzon ya bari, waxanda nassi da qiyasi ba za su iya bayyanawa ba, sai ma'asumi ya sa baki. Kenan kuna son ne ku ce, ma'asumanci rabin Annabta ne! Ah, haka kuke nufi mana. Idan dai har ma'asumin naku na iya wajabta wani abu ko ya haramta wani, ba tare da ya kafa hujja da wata magana ta Annabi ba, ya zama mai cin gashin kansa kenan, ba mabiyi ga Annabin ba. Duk wanda ya kasance haka kuwa, to shi ma ya zama Annabi kenan. Amma duk wanda ya yarda da wani a matsayin halifan Annabi, to lalle kuwa ba zai raba gari da shi ba.

Haka kuma qiyasi, idan har ya tabbata hujja, to, dole ne a mayar da mutane zuwa gare shi. Idan kuwa bai tabbata hujja ba, to, lalle ne kuwa a tarar cewa Annabi ya riga ya yi cikakken bayani da nassi a kan jigoginsa.

Ko banza Allah Ta’ala ya riga ya faxa mana cewa:

ﭽ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﭼ

المائدة: ٣



A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika ni’imata a kanku, kuma Na yarda da musulunci ya zama addini a gare ku (5:3)

Ka ga wannan aya nassi ce, da ke nuna cewa addini ya riga ya gama cika. Ta yadda ba ya buqatar wata tsalma daga kowa.

Amma qananan abubuwa, ba ta yiwuwa ya kasance an daddale hukunce-hukuncesu filla-filla. Dole ne a bari ijtihadi ya yi aiki a cikinsu. Ta yadda malamai za su tantance wa kowane musulmi fuskar da zai kalla don ya dace da alqibla idan zai yi sallah, su kuma shata wa kowane alqali sifofin da ake buqata ga shedu, gwargwadon yanayin zamantakewar jama’a. Ba ta yiwuwa nassi ya qayyade irin waxannan abubuwa da makamantansu.

Tunda kuwa har haka ne, da zarar kuka yi iqirarin ma'asumancin wani shugaba a cikin irin waxannan qananan hukunce-hukunce, to, jahilcinku da girman kanku sun bayyana. Domin kuwa babu wanda ya tava iqirarin haka. Kuma ko a cikin waxanda Ali Raliyallahu Anhu ya naxa a matsayin wakilansa a waxansu yankuna, akwai waxanda yake da yaqinin mazanbata ne kuma kasasshi, ko suna da wasu ayubba na daban. Kuma shi kanshi akwai lokacin da ya yanke hannun wani, yana mai dogara a kan shedar da wasu mutane biyu suka bayar a kansa. Daga baya kuma ya gane ya yi kuskure har ya ce: "Mun yi kuskure a cikin wannan hukunci kuma da na san ba bisa gaskiya kuka yi wannan sheda ba, da na sa an yanke hannayenku".

Kai! Ko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya jin shi ma'asumi ne a cikin irin waxannan hukunce-hukunce. Domin kuwa ya zo a cikin littafin Buhari da na Muslimu cewa ya ce: "Haqiqa kun kasance kuna kawo qara gare ni. Tana kuma yiwuwa sashenku ya kasance mafi iya salon magana a kan wani sashe. To, ku iya sani fa ina hukunci ne dabra da abin da na ji. Duk wanda na ba haqqin xan’uwansa kar ya karve shi. Domin kamar na yanka masa wani yanki ne na wuta.

Fuska ta goma Sha biyu:

Muna so ne mu gane, shin wannan ma'asumanci da kuke waqe, kuke kuma jin ya tabbata ga shugaban naku, kuna nufin shi ne ke da ikon zavar ayyukan xa’a ya aikata, ya kuma nisanci na savo a ra’ayi da ikon kansa? Tattare kuma da kasancewar, ku a wurinku ba Allah ne Ya halicci ikon yi ko bari, a cikin ran ma'asumin ba? Koko kuna nufin kuma dai Allah Ya halicci iradar yin haka ne a cikinsa, ta hanyar zare ikon aikata savo daga cikin ransa?

Idan kuka ce kuna nufin maganar farkon ne, alhali kuwa ba ku yi imani da cewa Allah shi ne wanda ya halicci ikon yi ko bari a cikin kowane xan Adam ba. Kenan a cikin haqiqanin manufarku, Allah ba Ya iya halitta ma'asumi.

Idan kuma kuna nufin magana ta biyu ne, to, farkon abin da kuke tutiya na cikakken iko ga ma'asumin, a kan aikata abin da duk ya ga dama, ya roshe.

Da kuma za ku dawo ku ce, a’a muna dai nufin Allah Ya zare ikon aikata savo ne daga cikin halittar ma'asumin, to, kenan wannan ma'asumi naku na da wata halitta a cikin jikinsa ta kasawa. Kamar yadda duk yadda makaho ya so ba zai iya saka xigagga ga baqaqen qur’ani ba, daidai da irin duk yadda gurgu ya so tafiya, ba zai iya ko sawu xaya ba.

Shi ko a hankalce, duk wanda ba ya iya aikata wani abu ko barin aikata shi, to ya yi kaxan ga a hore shi da aikata abin, ko barin shi. Idan kuwa har hakan ta tabbata a kansa, kenan bai cancanci lada akan duk wata biyayya da zai yi ba, domin babu wanda ya sa shi. Kenan ma'asumi a wurinku ba ya samun ladar komai a kan nisantar ayyukan ashsha, ko aikata na madalla. Babu kuwa tavewa ko naqasar da ta kai ga wannan.

A kan haka, kenan ko farar hula daga cikin musulmi, wato musulmi hannu biyu ya fi wannan ma'asumi naku daraja a wurin Allah. Domin shi da zarar ya aikata wani laifi ya tuba, an yafe masa. Kai za a ma maye masa gurbin kowane zunubi daga cikin waxancan zunubai da suka gabata, da lada. Ka ga kenan ko a wurin waxannan ‘yan Shi’ah, sakamakon da musulmi falan xaya, zai samu ya fi alheri a kan zama ma'asumi. Wannan kuwa yana walwale waxancan maganganu nasu, matuqar walwaluwa.

Idan kuma muka dawo ga matashinyarsu ta biyu, muka qaddara wajabcin samar da shugaba ma'asumi. To, hakan ba ta hukuntar da kasancewar Ali Raliyallahu Anhu ma'asumi shi kaxai tallintal, bisa ittifaqi. Domin kuwa da yawa daga cikin ma’abuta ibada, da sufaye, da sojoji, da farar hula daga cikinsu, nada imanin cewa akwai ma'asumai da yawa a cikin shehunansu. Kamar yadda ‘yan Shi’ah ke da imanin haka a cikin imamai goma sha biyu. Da yawa ma sukan yi masu inkiya da kalmar Ash-Shaikhul-Mahfuz, tsararren malami kenan.

To, idan kuwa har za su yi irin wannan imani a kan shehunansu, tattare da imanin da suke da shi a kan cewa darajar Sahabbai ta fi ta shehunan, to kuwa halifofin can sun fi cancanta da wannan imani na ma’asunanci, ya kasance a kansu.

Kuma ka ga irin wannan wuce wuri na ‘yan Shi’ah a cikin xaukaka darajar imamansu, ya watsu qwarai a cikin wasu qungiyoyin mutane. Ta yadda za ka taras suna wuce iyaka a cikin ciccivawa da kambama shehunansu.

Misalin wannan shi ne Shi’ah Isma’iliyyah. Su ma sun yi imani da cewa shugabanninsu ma'asumai ne, kuma su ba ‘yan-sha-biyu ne ba. Ba waxannan kawai ba har ma da yawa daga cikin talakawan sarakunan Umawiyyawa, ko ma mafi yawansu suna da imanin cewa ba za a yi wa shugaba hisabi ba balle azaba ranar lahira. Kuma wai talakawa ma Allah ba zai kama su da laifin komi ba, matuqar dai hakan ta kasance ne a bisa tafarkin yin xa’a ga shugaban. Kai suna jin wajibi ne a kansu, su yi xa’a ga shugabansu a kan komai. Kuma wai Allah ne Ya umurce su da hakan.

An riwaito cewa, Yazidu xan Abdulmalik ya so ya bi sawun Umaru xan Abdulaziz a cikin mulkinsa. Sai qungiyar wasu shaihunan zamaninsa suka same shi. Suka rantse masa da Allah, wanda ba wani Ubangiji sai shi a kan cewa, da zarar Allah Ya naxa mutum ya zama shugaban jama’a, to kuwa zai karvi ayyukansa kyawawa ya yafe masa munana.

Hakan ta sa kake jin maganganun mafiya yawa daga cikin manyan mutanen waxannan za munna, cike da umurni da yin xa’a ga shugaba ba tare da wata togiya ba. Har sukan qarfafa zantukan nasu da cewa, duk wanda ya yi xa’a ga shugaba ya yi wa Allah ne. Wannan ne ma dalilin da ya sa idan mutane za su kwatanta biyayyar wani sai ka ji an ce, kamar xan garin Sham.

Ka ko ga ai mutanen Sham jama’ar Mu’awiyah ne, ba ‘yan Shi’ar Ali ne ba.

Babu wata qungiya daga cikin irin waxannan qungiyoyi da za a ce wa, dole ne su samar da wani shugaba ma’sumi, face sun karva da cewa, wannan shugaba da muke biyayya gare shi ya wadatar da mu. Ba mu da buqata da wani ma'asumi daga cikin imamai goma sha biyu, ko da kuwa Aliyu.

Idan kuma kuka ce, ai ba a la’akari da mutanen Sham domin su kangararru ne. To, sai mu ce maku: Ai waxannan mutane sun fi ku, daga ku ‘yan-sha-biyu ko har Isma’iliyyahwa. Domin kuwa shugabanni da shehunansu sun fi alheri, bisa ga wannan ma'asumi na fake wanda babu shi ma sam-sam-sam, babu kuma wani amfani da ya ke yi wa jama’a, ta kowane hali. Matsayinsu duk yadda yake ya fi naku.

Wasu ‘yan Shi’ah na kafa hujja da cewa Ali Raliyallahu Anhu ma’asumi ne wai don shi kaxai ne daga cikin halifofi aka samu waxanda suka raya cewa ma’asumi ne. Sai mu ce: To, wa ya raya hakan in ba ku ba. A cikin Sahabbai babu wanda ya yi wannan iqirari ga Abubakar da Umar da Usmanu ballantana Ali.

A taqaice dai, duk lokacin da ‘yan Shi’ah suka buxa baki suna raya cewa, imamansu ma’asumai ne, to, za ka tarar da akwai wasu su ma masu irin wannan da’awar a kan wasu mutane daban ba imaman Shi’ah ba. Ka ga kenan an rosa wannan tugufar ta ‘yan Shi’ah ta cewa su kaxai suke irin wannan da’awa. A lokaci xaya kuma an kai qarshen ruxun da suke kawowa a kan ma’asumancin Ali da zuri’arsa.



Fuska ta goma sha uku:

Dole ne ko dai samuwar shugaba ma'asumi a kowane zamani ta zama wajibi ko kuma ba wajibi ba. Idan ba ta zama wajibi ba to, iqirarin ‘yan Shi’ah ya bi shanun sarki. Idan kuwa har a kan qaddarawa hakan ta wajaba, to mun yarda. Amma ba mu amince da kasancewar Ali shi kaxai ma'asumi ba, ba tare da waxancan halifofi uku ba na kafinsa ba. Kai kasancewar wannan qaddarawa ma gaskiya, na wajabtar da kasancewar Abubakar da Umar da Usmanu Raliyallahu Anhu ma'asumai, ba da shi ba. Dalili kuwa shi ne haxuwar kan gaba xayan Ahlun-Sunah a kan fifikon Abubakar xin da Umar a kan Ali, a fagen daraja, da kasancewar su mafiya cancanta da zama ma'asumai – in har dole ne – a kan sa. Kuma a wurinsu, idan har ma'asumanci abu ne mai yiwuwa, to zai fi kusa ga halifofin uku na kafin Ali. Idan kuwa har ba abu ne mai yiwuwa ba, to rashin yiwuwarsa gare shi ta fi dacewa.

Kuma ku sani, miqa wuya da muka yi ga koruwar ma'asumanci daga waxancan halifofi uku, mun yi shi ne saboda imanin da muke da shi a kan cewa Allah Ta’ala bai halicci wani shugaba ma'asumi ba. Da kuwa za mu qaddara yiwuwar haka, to da lalle ko waxancen halifofin uku sun fi duk wanda ya zo bayansu cancanta da ita. Kuma wannan dalili ne ya sa muka kore ma'asumancinsu.

Wai ina ma ‘yan Shi’ah suka samo wannan magana ta cewa Ali ma'asumi ne? Suna iya ce mana, ai haxuwar kan malamansu ne ta tabbatar da ma'asumancin Ali. To, a nan sai mu ce musu: Kasancewar ijma’i ba hujja ba a wurinku, ta rosa wannan hujja taku. Idan kuwa har kun yarda da kasancewarsa hujja a kan wannan matsala ta ma'asumancin Ali, a matsayinta na kanwa uwar gami a cikin gaba xayan matsalolin, to, kenan idan wasu malamai suka haxu a kan kansancewar wanda ya tsare alfarmar shari’a kuma ya yaxa ta ma’asumi, haxuwar tasu ta zama hujja kenan . Amma abin da zai ba ka mamaki shi ne, ‘yan Shi’ah na kafa hujja ne da ijma'i a wannan matsala kawai. Amma a wurinsu ijma’i ba hujja ba ne. To idan kuwa har haka ne, sai sun gaya mana inda suka samo wannan magana ta kasancewar Ali ma'asumi, shi kaxai daga cikin halifofi.

Idan kuma har suka ce, a’a ai ma'asumancin nasa ya samo asali ne daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta hanya mutawatira. To, sai mu gaya masu cewa, wannan magana daidai take da cewar da suka yi shugabancin Ali bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kai tsaye, abu ne da Annabin Sallallahu Alaihi Wasallama ya nassanta kuma aka riwaito ta mutawatirar hanya. Kenan ba su da wata madogara a cikin matsalolin biyu baya ga wannan.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   26   27   28   29   30   31   32   33   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin