Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə35/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   31   32   33   34   35   36   37   38   ...   51

4.8 Ayar:

ﭽ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﭼ البقرة: ٢٠٧

Hujja ta takwas, inji xan Shi’ah, ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma akwai daga cikin mutane wanda yake sayar da kansa, domin neman yardar Allah (2:207). Sa’alabi ya ce: A lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tashi yin hijira, sai ya bar Aliyu xan Abu Xalib, don ya biya basosan da ke kansa, ya kuma mayar da ajiye-ajiyen da ke hannunsa na mutane. Ya kuma umurce shi da ya kwana a kan shimfixarsa, a daren da zai fita zuwa kogon dutse, daidai lokacin da mushrikai suka yi wa gidan nasa qawanya. Ya ce masa: Ya kai Aliyu! ka rufa da koren bargon nan nawa bahadrame, ka kwanta a kan shinfixata. Da yardar Allah babu wani mugun abin da zai same ka. Haka ko aka yi.

Nan take sai Allah Ta’ala Ya yi wahayi ga Jibrilu da Mika’ilu, cewa; haqiqa Ni na qulla zumunci tsakaninku. Na kuma hukunta shekarun xayanku su fi na xaya tsawo. Wane ne daga cikinku zai fice wa xan’uwansa waxannan dogayen shekaru? Sai kowanensu ya zavi kansa. Daga nan sai Allah Ya sake yi masu wahayi da cewa: Me zai hana ku yi koyi da Aliyu xan Abu Xalib? Na qulla zumunci tsakaninsa da Muhammadu, yau ga shi can kwance a kan shifixarsa yana fansar sa da rayuwarsa. Saboda haka ku sauka qasa ku kare shi daga maqiyansa. Sai suka sauka. Jibrilu ya tsaya wurin kansa, mika’ilu kuma wurin qafafunsa. Daga nan sai Jibrilu ya ce: Wai! Wai!! Wai!!! Lalle Aliyu xan Abu Xalib ka isa. Tirkashi! Yau kai ne Allah ke yi wa mala’iku alfahari da kai? Nan take kuma sai Allah Ya saukar da wannan aya da muka faxa a kan Ali, a daidai lokacin da Manzon ya kama hanyar Madina.

Wai kuma xan Abbas ya ce: Wannan aya ta sauka a kan Ali, a daidai lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gudu daga mushrikai zuwa kogon dutse. Wannan irin daraja da ba wanda ya samu sai shi Ali, na nuna fifikonsa a kan gaba xayan Sahabbai. Saboda haka shi ne Imamu kenan. Inji xan Shi’ar.

Martani:

Muna son xan Shi’ar ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya. Mun gaji da riwayoyin Sa’alabi marasa kan gado. Malamai magadan Annabawa sun daxe da watsar da wannan hadisi. Kuma lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hijira tare da Abubakar Raliyallahu Anhu zuwa Madina, ba nufin Quraishawa ba ne su kashe Aliyu. Suna dai neman Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne da Abubakar don su kashe. Har ma sun riga sun sanya diyyar kowannensu a matsayin goron wanda ya kashe shi. Kamar yadda hakan ta tabbata a cikin ingantattun littafan riwaya irin su Buhari.

Annabi ya umurci Aliyu ne da kwanta shimfixarsa, don su za ci cewa yana cikin gidan bai fita ba, balle su bi sawunsa. Domin ba suna nufin kashe shi a cikin gidansa ba. Safiya na yi sai suka ga ashe Aliyu ne, suka kunyata. Saboda haka ne ma ko baqar magana ba su gaya masa ba. Sai ma dai kawai suka tambaye shi inda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yake, kuma a cikin lalama. Ya ce masu bai sani ba.

Babu wani tsoro da ake ji wa Ali a lokacin daga kowa. Matsalar ta tattare ne a kan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da amininsa; su ake ji wa tsoro. Da Quraishawan can nada wani mugun nufi da Ali, da sun far masa, a lokacin da suka gan shi. Amma rashin yin haka, ya tabbatar da ba shi suke nema ba. To, ina wata fansa da ya yi wa Manzon Allah, da ransa a nan? Babu.

Wanda dai ta tabbata ya fanshi Manzon Allah da ransa; ta hanyar shiga tsakaninsa da halaka, tare da yarda da cutuwa a madadinsa shi ne Abubakar Raliyallahu Anhu. Domin shi ne a kan hanyarsu, idan ya tuna ana iya dafafo su ta baya, sai ya koma bayan Annabi. Ya kuma koma gabansa, idan ya tuna ana iya taka qaya ko wani abu. Shi ne kuma ke zuwa yana shaqo masa labarai. Ka ga idan akwai wani abu da ake tsoro na haxari, ya gwammace ya same shi, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tsira.

Mun jiya, fansarsa ya yi. To, ai ba shi kaxai ya tava fansar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. An samu Sahabbai da dama, da suka fanshe shi, da rayukansu a fagagen daga, ba kan gado ba. Akwai waxanda suka kwanta dama a gabansa. Wasu kuma aka sharce masu hannaye; kamar Xalhatu xan Ubaidullahi. Kenan da an qaddara cewa wancan abu da Ali ya yi, fansa ce ya yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ransa, to, da hakan ta kasance wani abin xaukaka da, shi da wasu Sahabbai suka yi tarayya a ciki. Balle kuwa asalatan babu wani abu da ake ji wa Aliyun tsoro.

Bayan haka kuma idan xan Shi’ar bai manta ba, ai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ce wa Ali ya yi: Ya kai Aliyu! ka rufa da koren bargon nan nawa bahadrame, ka kwanta a kan shinfixata. Da yardar Allah babu wani mugun abin da zai same ka. Kenan Annabi ya lamunce masa, ya tabbatar masa da cewa babu wani abu da zai same shi. Wannan lamuncewa ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta sa ya samu natsuwa. Ya yi baccinsa har da minshari.

Sannan wannan hadisin a karan kansa, tsatstsage yake da abubuwa bayyanannu da ke tabbatar da cewa qarya ne. Na farko: Wancan abu da ya ce ya faru ga Mala’iku, bai dace da su ba, domin varna ne. Babu wanda yunwa ko tsoro ke kamawa daga cikinsu, balle a yi tunanin yiwuwar xayansu ya fice wa xaya wani abin ci ko aminci. To, ta yaya za a ce: Allah Ya ce: Waye daga cikinsu zai fice wa xaya tsawon rayuwa? Kuma zancen qulla zumunci tsakaninsu da ya yi, abu ne marar asali a tsakanin mala’iku. Hasali ma ba ruwan wani da wani a cikinsu, aikin Jibrilu daban, bai shafi Mika’ilu ba. Na Mika’ilu daban bai shafi na Jibrilu ba. Kamar yadda ya zo a cikin Asaru, cewa Jibrilu aikinsa ya shafi wahayi ne da gudunmuwar nasara ga zavavvun Allah, a yayin da kula da arziqi da ruwan sama ke hannun Mika’ilu.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava qulla zumunci da Ali ko waninsa ba. Duk abin da aka riwaito, wanda ke qoqarin tabbatar da haka qarya ne.

Duk da hadisin da aka riwaito a cikin wannan sha’ani, tattare da rauni da varnar da ke cikinsa, iyakar abin da ke cikinsa shi ne, Annabi ya qulla zumunci da Aliyun a Madina. Abin da Tirmizi ya riwaito kenan. Amma zumuncin da ake cewa ya qulla da shi a Makka, wala. Tatsuniya ce ta kowace fuska.

To, mu koma ga maganar waxancan Mala’iku. Cewa Jibrilu da Mika’ilu sun sauko don ba da kariya ga wani, na daga cikin manya-manyan maganganu yasassu. Domin kuwa Allah mai iko ne ga kare duk wanda ya so daga cikin halittarsa, ba tare da haka ba. Lokacin da kawai aka riwaito cewa waxannan mala’iku biyu sun tava saukowa qasa, shi ne ranar yaqin Badar, ko shi don su taya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga. Sai kuma lokacin waxansu abubuwa masu girma irin waxannan. Da sun tava saukowa don bayar da kariya ga wani mutum, to da Annabi ne da amininsa, waxanda maqiya ke nema ruwa a jallo.

Ita dai wannan aya da muke cece-ku-ce a kanta, tana cikinsuratul Baqara ne. Ita kuwa surar ta sauka ne a Madina bisa haxuwar kan malamai. Ba a daidai lokacin hijirar ne ta sauka ba. Wasu kuma sun ce, ta sauka ne lokacin da Suhaibu ya yi hijira, mushrikai suka bi sawunsa. A inda ya miqa masu dukiyarsa baki xaya, ya isa Madina emti. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya jinjina masa da cewa: Cinikinka ya yi riba ya kai baban Yahaya. Wannan qissar mashahuriya ce a cikin tafsiri, saboda malamai da dama sun riwaito ta.

Game da maganar xan Shi’ar da ya ce: Babu wanda ya sami waccan xaukaka wai, ta fansar Annabi da rayuwa, sai Ali. Saboda haka wai hakan ta tabbatar da kasancewarsa mafifici. Kenan shi ne Imamu. Abin da za mu ce a nan shi ne: Idan haka ne, Alqur’ani da ijma’i sun tabbatar da cewa ko shakka babu wata xaukaka ta samu ga Abubakar Raliyallahu Anhu a lokacin hijira, wadda ba ta samu ga wani Sahabi ba. Kenan shi ne Imamu.

Dalilinmu a kan haka shi ne gasgantaccen zancen nan da ba sofanen qarya a cikinsa, wato faxar Allah Ta’ala:

ﭽ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜﭼ التوبة: ٤٠

Idan ba ku taimake shi ba, to, lalle ne Allah Ya taimake shi, a lokacin da waxanda suka kafirta suka fitar da shi suna su biyu. A lokacin da suke cikin kogo, da yake ce wa abokin tafiyarsa: “Kada ka damu. Haqiqa Allah na tare da mu (9:40).

Baya ga Abubakar kuwa, babu wanda ya sami wannan xaukaka yanke. Savanin bajintar bayar da rayuwa a matsayin kariya. Wadda ko da ta inganta cewa Ali Raliyallahu Anhu ya yi a can, to, an sami Sahabi ba guda ba, da ya yi irin wannan.



4.9 Ayar Mubahala

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta tara ita ce: Faxar Allah Ta’ala:

ﭽ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﭼ آل عمران: ٦١

To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka na ilimi, to, ka ce: “Ku zo mu kirayi ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kanmu da kanku, sa’annan kuma mu qanqantar da kai, sa’annan kuma mu sanya la’antar Allah a kan maqaryata (3:61).

Xan Shi’ah ya ce: Gaba xayan Jumhuru, yana nufin malaman Sunnah, sun naqalto cewa ‘ya’yanmu a cikin wannan ayana nufin Hasan ne da Husaini. Matanmu kuwa na nufin Fatima. A ya yin da Kanmu ke nufin Ali. Wai kuma wannan aya dalili ce a kan tabbatar shugabancin Ali. Domin Allah Ta’ala ya daidaita shi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Alhalin ko yin kat-kat-kat da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama abu ne da ba shi yiwuwa. Kenan waccan daidaitawa da aka yi musu, tana nufin shugabancin qoli. Da kuwa akwai wani wanda ba waxancan mutane da Manzon ya gayyato ba. Waxanda ke daidai da su ko fiye, a xaukaka da cancantar amsa du’ai, da kuwa Allah Ya umurci Manzon da gayyato su. Domin idan wannan lokaci ya wuce ba wani; iyakar damar kenan.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Babu wanda zai kasa tantance dalilin da ke cikin wannan aya, wanda ke tabbatar da abin da muke son tabbatarwa, sai wanda xan Lisu ya gurvata zuciyarsa, ya mamaye sasanninta. Ya kuma qawata masa son duniya, wadda kuwa samunta bai yiwuwa sai da zalunci.

Martani:

Maganar mubahala gaskiya ce. Ayar Alqur’ani ce ta faxe ta. Kuma bayan saukar ta ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kira Sayyidina Ali da Nana Fatima da Hasan da Husaini ya gabatar da su don yin ta. Labarin yana cikin Sahihu Muslim daga Sa’adu xan Abu Waqqasi. Amma wannan ba ya nuna wani dalili a kan shugabanci ko fifiko.

Cewarsa kuwa Aliyu yana daidai da Manzo, don Allah ya kira shi “kansa” kuma wai wannan na nufin shugabancin qoli, ba magana ce da take kan hanya ba. Domin kuwa babu wani dalili da ke iya tabbatar da ita. Yin wannan fassara ma na nuna ragguwar fahimta ga harshen Larabci. Duba wata aya mai kama da wannan da take cewa: Inda ma a lokacin da kuka ji shi, muminai maza da mata sun yi zaton alheri ga kan su (24:12). Kenan muminai maza da mata sun daidaita?.

Kuma ma ai wancan abu da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ba abun mamaki ko tinqaho ba ne, domin kuwa, da ma ana mubahala ne tare da gayyato makusanta. Musamman da yake su abokan mubahalar sun gayyato makusantansu ne. To, dole ne shi ma ya gayyato irinsu. Da zai gayyato waxanda ba su ba daga cikin irin danginsa na nesa, abin da ake nufi ba zai sami tabbata ba. Ko da kuwa waxannan xin sun fi waxancan girma a wurin Allah.

Haka kuma da xan Shi’ar ya ce: Da akwai wani wanda ba waxancan mutane da Manzon ya gayyato ba. Waxanda ke daidai da su ko fiye, a xaukaka da cancantar amsa du’a’i. Da kuwa Allah Ya umurci Manzon da gayyato su. Domin idan wannan lokaci ya wuce ba wani; iyakar damar kenan.

Martani:

Ai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai gayyato waxancan mutane don du’a’in da za a yi ya sami karvuwa a wurin Allah ba, saboda su. Du’a’in da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi shi kaxai, ya isa. Inda kuwa har ya kira su ne, don ana nufin du’a’in ya karvu, albarkarsu, to, da ya gayyato gaba xayan muminai ya yi fadanci da albarkarsu. Kamar yadda ya kan roqi ruwan sama a wurin Allah tare da su. Yake kuma roqon sa’ar yaqi ta hanyar fita da dattijai daga cikin Muhajirai. Kuma ai an riwaito ya kan ce wa Sahabbai: “Kuna tsammanin nasarar da kuke samu da arziqi, ba albarkacin masu rauni daga cikinku ne ba; saboda addu’o’insu da sallolinsu da ikhlasinsu?”

Kuma sanannen abu ne cewa, duk da kasancewar waxancan mutane da Manzo ya gayyato, waxanda Allah ke karvar addu’arsu, yawan bakuna a cikin du’a’i na qara mata qaimin samun karvuwa. Amma ba ana nufin ya kirasu ne, don du’a’insa ya sami shiga ba. A’a an yi haka ne don daidaitawa tsakanin iyalinsa da na waxancan. Mun kuma sakankance a tilas cewa, da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai gayyato Abubakar da Umar da Usmanu da Xalhatu da Zubairu da xan Mas’udu da Ubayyu xan Ka’abu da Mu’azu xan Jabalu da wasunsu don halartar wannan mubahala, da sun kasance mafi girman mutanen da za su karva wannan kira nasa, waxanda kuma du’ainsu zai fi na waxanda ba su ba karvuwa a wurin Allah. Amma Allah Subhanahu WaTa’ala bai umurce shi da gayyato su ba, don hakan ba za ta iya tabbatar da abin nufi ba.

Wannan abin nufi kuwa shi ne waxancan mutane, abokan mubahala, su gayyato waxanda a al’ada suke tausaya wa. Kamar ‘ya’yansu da matansu, da mazansu; waxanda kuma duk, suke mafi kusancin mutane gare su. Ka ga da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai gayyato wasu manisantansa, da sai su ma su gayyato irinsu. Kuma da mubahalar ba ta karva sunanta ba, kamar yadda za ta karva shi idan kowane vangare ya gayyato makusantansa. Domin kuwa da ma a xabai’ar xan Adamu, ya fi tsoratar wa makusancinsa wani abin qi, a kan manisancinsa. Saboda haka Allah Ya murci Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da waxancan mutane, kowa ya gayyato makusancinsa.

A haka ta tabbata babu wani dalili a cikin wannan aya da ke tabbatar da abin da xan Shi’ar ke qoqarin tabbatarwa, asalatan. Amma saboda irin halinsa da ire-irensa, irin halin Nasara na karkata da ke cikin zukatansu, sai suna kama reshe su bar tushe. Maganarsa cewa kalmar “kanmu” na nufin daidaitawa, idan aka yi amfani da ita tsakanin abubuwa biyu ta sava wa yadda ake amfani da ita a harshen Larabaci.

Ita ma kalmar matanmu a cikin ayar, ba ta kevanta ga Nana Fatima ita kaxai ba. Duk da yake ita kaxai ce Manzon ya gayyato. Amma da Zainab da Ummu Kulsum da Ruqayya na raye a lokacin, duk wadda ya gayyato a cikinsu ko su duka, na iya zama makwafinta. Abin ya tsaya a kanta ne, don babu wata sai ita a lokacin, sauran sun riga sun rasu.

Haka nan kalmar Kanmu ba ta taqaita ga Ali kawai ba. Domin sigar jam’i gare ta, kamar yadda matanmu da ‘ya’yanmu ke da. Annabi ya gayyato Hasan da Husaini ne, saboda babu wanda ke da dangantaka ta jini da shi, a matsayinsa na Annabi sai su. In da kuwa Qasim na raye a lokacin, ko wani cikin qannensa da kowanne aka kira daga cikinsu ya wadatar.

4.10 Ayar:

ﭽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﰄﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﭼ البقرة: ٣٧

Xan Shi’ar ya ce: Hujjarsa ta goma ita ce, faxar Allah Ta’ala: Sai Adamu ya karvi wasu kalmomi daga Ubangijinsa. Saboda haka, ya karvi tubarsa (2:37).

Ya ci gaba da cewa, malamin nan masanin fiqihu, Ibnul-Magazili Bashafi’e ya riwaito, da isnadinsa, daga xan Abbas, wanda ya ce: An tambayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan kalmomin nan da Adamu ya karva daga Ubangijinsa, har Ya karvi tuba a kansa. Sai ya karva da cewa: Ya roqe shi ne Ya yafe masa albarkacin Muhammadu da Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini.

Xan Shi’ar ya ce, a kan haka ne Allah Ya yafe masa. Wannan kuwa, inji shi, xaukaka ce da ba wanda ya same ta daga cikin Sahabbai, balle ya riski Aliyu a cikinta. A kan haka sai ya zama shugaba. Saboda yin kafaxa-da-kafaxa da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin yin tawassuli da shi da aka yi zuwa ga Allah Ta’ala.

Martani:

Da farko, muna neman marubucin da abin da muka saba na tabbatar da ingantacin wannan riwaya. Domin kuwa mun riga mun san cewa, kasancewar Ibnul Magazili ya riwaito magana ba ya sa ta zama hujja, bisa haxuwar kan ma’abuta ilimi.

Wannan hadisi dai Abul-Faraji Ibnul Jauzi ya ambace shi cikin: Al-Maudu’at wato kundin Hadisan Gizo da qoqi.

Alqur’ani mai tsarki kuma ya riga ya fassara waccan aya, tare da bayyana kalmomin da Adamu ya karva daga wurin Ubangijinsa, waxanda ya yi fadanci da su har aka karvi tubarsa, da cewa su ne a cikin faxar Allah Ta’ala: Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kanmu. Kuma idan ba ka gafarta mana ba, kuma ka yi mana rahama, haqiqa muna kasancewa daga cikin masu hasara (7:23).

Wannan dai ita ce fassarar magabata. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava umurtar wani da amfani da irin waxancan lafuzza a cikin du’a’i don neman gafarar Allah ba. Kai ko a cikin wani du’a’i da ba na neman gafara ba, ba a samu ya tava umurnin wani da haka ba. Hasali ma bai shar’anta wa al’ummarsa roqon Allah da irin wannan tawassuli ba. Da kuwa irin wancan lafazi karvavve ne a matsayin shari’a da ya shar’anta wa al’umarsa shi.

Babu kuma inda Alqur’ani ko Sunnah suka zo da halaccin rantsuwa ga Allah ta hanyar amfani da sunayen Mala’iku ko Annabawa. Ma’abuta ilimi da dama, irin su; Abu Hanifata da Abu Yusufa, sun bayyana fili cewa: Tawassuli ga Allah da wani mahaluqi ba ya halatta.

Wani abu kuma da ke tabbatar da kasancewar wannan magana ba shari’a ba, shi ne; kasancewar Adamu xaya daga cikin manyan Annabawa, ba ta yiwuwa ya roqi Allah yana tawassuli da wanda bai kai darajarsa ba. Ko shakka babu Annabinmu Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi Adamu girman daraja. Amma shi kuma Adamun ya fi Aliyu da Fatima da Hasan da Husaini girman daraja.

4.11 Ayar: ﭽ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﭼ البقرة: ١٢٤

Xan Shi’ar ya ce: Hujjarsa ta goma sha xaya akan wajabcin shugabantar da Ali tun fari, ita ce: Faxar Allah Ta’ala:

ﭽ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰﮱ ﯓ ﯔ ﯕﯖ ﭼ البقرة: ١٢٤

Haqiqa, Ni mai sanya ka ne shugaba ga mutane. Ya ce: Kuma daga zuri’ata (2:24).

Ya ce: Malamin nan masanin fiqihu, Ibnul Magazili Bashafi’e ya riwaito daga xan Mas’udu, wanda ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Du’ain nan ya tuqe ne a kaina da Ali. Domin babu xayanmu da ya tava yin sujada ga gunki. Saboda haka ne Allah Ya zave Ni Annabi, Ya zave Aliyu Wasiyyi. Xan Shi’ar ya ce, wannan nassi ne da ke tabbatar da shugabancin Ali.



Martani:

Da farko: Ina asalin wannan hadisi naku?

Na biyu: Ma’abuta ilimin hadisi sun daxe da soke shi

Na uku: Cewa wannan du’a’in ya tuqe ne a kan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali, maganar kawai ce. Ba ya kuma halatta a jingina ta ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Domin kuwa cike take da tuqa da walwala. Ko kafin wannan al’umma, wannan addu’ar ta shafi wasu mutane daga cikin zuri’ar Annabi Ibrahim (AS); suka zama Annabawa.

In ko yana nufin du’a’in ya tuqe a kan Muhammadu da Aliyu ne, a cikin wannan al’umma, to, kenan hakan na nufin ba yadda za a yi Hassan ko Husaini ko waninsu ya zama Imamu daga baya. Sun ko zama. Ka ga waccan magana ta tashi, bisa haxuwar al’umma. Dalilin kuwa da ya kafa da cewa, waxannan mutane, ba su tava yin sujada ga gunki ba, wata siffa ce da sauran musulmin da suka zo bayansu suka siffanta da ita.

Na huxu: Rashin tava yin sujada ga gunki, wata daraja ce da duk wanda aka Haifa a cikin musulunci yake tarayya da Ali a cikinta. Amma ai musulmi magabata na da fifiko a kan irin wannan. To, ta yaya za a xaukaka wanda aka fi, a matsayin wanda ya cancanci wannan daraja, ga kuwa wanda ya fi shi?

Na biyar: Idan ‘yan Shi’ah suka ce, Ali Raliyallahu Anhu bai tava sujada ga gunki ba, saboda ya karvi musulunci tun bai balaga ba. Kuma haka bayan ya musuluntar ma bai yi ba, tunda musulmi ne. Babu wani abin alfahari a cikin wannan. Tunda kowane musulmi haka yake. Da ma shari’a ba ta hau kan yaro ba, balle. Idan kuwa suka ce: A’a, ba muna magana ne a kan bayan musuluntarsa ba, muna yi ne kan kafin haka. To sai mu ce masu: Wannan kuma sani sai Allah. Mu dai ba mu san wannan magana ba. Kuma shi xan Shi’ar da ke faxar wannan magana ba ya daga cikin mutanen da ake shiga xaka da zancensu.

4.12 Ayar: ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭼ مريم: ٩٦

Hujjar xan Shi’ar ta goma sha biyu wai ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Lalle ne waxanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na qwarai, mai rahama zai sanya so a gare su (9:96).

Ya ce: Hafizu Abu Nu’aimi Al-Asbahani ya riwaito da isnadinsa daga xan Abbas, wanda ya ce: Wannan aya ta sauka ne a kan Ali. Kalmar “so” kuma na nufin Allah zai sa sonsa a cikin zukatan muminai. Ya ci gaba da cewa: Kuma ya zo a cikin tafsirin Sa’alabi daga Bara’u xan Azibu, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Ali Raliyallahu Anhu: Ya kai Ali! Ka ce: Ya Ubangiji! ka yanka mani wani rabo a wurinka. Ka kuma sa ni abin so a cikin qirazan muminai. Wai daga nan sai Allah Ya saukar da wannan aya.

Xan Shi’ar ya rufe maganarsa da cewa: Babu wanda ya sami wannan lamuni sai shi. Saboda haka shi ne Imamu na gaskiya.

To, mun ji. Amma ku saurara:

Dole ne tun da farko malamin ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya, kafin komai. Idan kuwa ya kasa, to, ya sani kan malamai ya haxu a kan cewa, kafa hujja da wani abu da bai kama qasa ba, abu ne yasasshe. Domin yin haka magana ce a kan jahilci, da qoqarin shiga sharu ba hanu, da shiga kokowa ba karhu, balle laya. Haka kuma Ahlus-Sunna da Shi’ah gaba xaya sun tafi a kan cewa wannan asali da xan Shi’ar ya ambata wa wannan magana ba ya amfanar da komai.

Malamai masana sirrin hadisi sun haxu a kan cawa waxannan hadisai biyu qarya ne. Kuma cewar da Allah Ta’ala Ya yi a cikin waccan ayar: Lalle ne waxanda suka yi imani, kuma suka yi ayyuka na qwarai (19:96) magana ce gama-gari, da ta shafi gaba xayan muminai. Saboda haka ba ya yiwuwa a kevance Ali da ita. Domin kuwa ta shafi waninsa. Dalilinmu a nan shi ne, ‘yan Shi’ah ba su musun kasancewar Hasan da Husaini da wasunsu daga cikin waxanda suke gani da gashi a ka, kuma duk wannan aya ta shafe su. Wannan haxuwa da aka samu, a kan ra’ayi xaya ta nuna rashin kasancewar Aliyu wanda ayar shafa kawai.

Ita kuwa cewar da ya yi wai, babu wanda ya sami irin waccan daraja daga cikin Sahabbai sai Ali, yasassar magana ce kamar ta bayanta. Domin kuwa Sahabbai su ne qarni mafi alheri. Waxanda suka yi imani suka kuma aikata aiki na qwarai daga cikinsu, su ne mafifita a kan kowa.

Sannan Alqawarin da Allah Subhanahu WaTa’ala Ya yi na sanya so ga waxanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka na qwarai, gaskiya ne. Kuma sanannen abu ne cewa, Allah Ya sanya son Sahabbai a cikin zukatan musulmi, musamman ma dai son halifofi, kuma musamman Abubakar da Umar daga cikinsu. Ta tabbata cewa, gaba xayan Sahabbai da Tabai’ai na matuqar son waxannan halifofi biyu – fiye da Ali - alhali ko su ne mafi alherin al’umma.

4.13 Ayar: ﭽ ﭲ ﭳ ﭴﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭼ الرعد: ٧

Xan Shi’ar ya ce: Hujjarsa ta goma sha uku ita ce: Faxar Allah Ta’ala:



Abin sani kawai, kai mai gargaxi ne. Kuma a cikin kowaxanne mutane, akwai mai shiryarwa (13:7).

Ya ce: Xan Abbas ya faxa a cikin littafin Al-Firdausi cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ni ne mai gargaxin, Aliyu kuma mai shiryarwa. Ta hanyarka ne ya kai Aliyu duk mai shiryuwa zai shiryu”. Ya ce, kuma Abu Nu’aimi ya riwaito irin wannan. Kuma a bayyane take cewa hadisin na tabbata da shugabanci da kasancewar Ali abin jivinta.



Martani:

Babu wani dalili da ya tabbata a kan ingancin wannan riwaya. Saboda haka hujja ba ta kafuwa da ita. Kuma ma’abuta ilimi sun haxu a kan cewa akwai qagaggun hadisai da dama a cikin littafin Al-Firdausi. Ta yadda kasancewar an samo wata riwaya daga cikinsa kawai, ba ya zama dalilin ingancinta a matsayin hadisi. Kamar yadda riwayar Abu Nu’aimi ga wata magana ba ta nuna ingancinta. Wannan maganar kuma qarya ce, bisa haxuwar ma’abuta ilimin hadisi. Saboda haka, wajibi ne a qaryata ta a kuma saka ta kwandon shara.

A zahiri wannan qagaggen hadisi na nufin ta hanyar Aliyu ne kawai mutane za su iya shiriya, ba da Annabi ba. Babu ko musulmin da zai yarda da wannan magana, balle ya faxe ta. Domin kuwa kai tsaye tana nufin an raba aikin gargaxi ne da shiryarwa a tsakaninsu; an ba kowa xaya. Wannan mai gargaxi wanda ba a shiruwa ta hanyarsa. Wancan kuma shi ne mai shiryarwa koda bai yi gargaxi ba. Shakka babu, musulmi ba zai yarda da faxin haka ba.

Allah Ta’ala Ya riga Ya Siffanta Muhammadu da cewa shi mai shiryarwa ne. A inda Ya ce: Kuma lalle kai haqiqa, kana shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya. Hanyar Allah (42:52-53) To, ta qaqa za a ce mai shiryarwa shi ne wanda ba a siffanta da haka ba, alhali ga wanda aka siffantar?!

Sannan cewa wai Annabi ya ce wa Ali: Ta hanyarka ne duk wanda zai shiriya zai shiryu. Zahirin wannan magana, babu wanda zai shiryu kenan daga cikin al’ummar Muhammadu sai ta hanyar Ali. Qarya kuwa kenan. Domin dubun-dubatar mutane sun yi imani da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sun kuma shiriya ta hannunsa, kai har ma sun shiga Aljanna, ba tare da sun ji kalma ko xaya daga bakin Ali ba. Haka kuma mutane da yawa sun shiriya ta hannun Sahabban da suka zauna tare da su, bayan cin garuruwansu da yaqi da aka yi. Suka kuma ci gaba da zama muminai ba tare da sun ji ko da kalma xaya daga bakin Ali ba. To, ta yaya zai yiwu a ce wai Annabi ya ce masa: Ta hanyarka ne duk mai shiriya zai shiryu?!

Wani abin kuma shi ne: Wasu malamai sun ce ma’anar wannan aya ita ce: Haqiqa kai mai gargaxi ne kawai. Amma mai shiriyar da kowaxanne mutane shi ne Allah Ta’ala. Wannan fassara ce mai rauni. Haka nan kuma cewar da wasu malaman suka yi ayar na nufin: Kai mai gargaxi ne kuma mai shiryarwa ga kowaxanne mutane. Ita ma fassara ce mai rauni.

Ingantattar fassara dai ita ce: Kai mai gargaxi ne kawai kamar yadda aka aiko ma kowace al’umma nata mai gargaxi wanda yake shiryar da ita. Kamar dai yadda wata ayar ta ce: Kuma babu wata al’umma face wani mai gargaxi ya shuxe a cikinta (35:24).

Wannan zancen wasu malaman tafsiri ne irin su, Qatadatu da Ikrimatu da Abud-Dhuha da Abdurrahmani xan Zaidu.

Amma waccan fassara da xan Shi’ar ya yi, ta hanyar taqaita ayar a kan Ali Raliyallahu Anhu varna ce tabbas. Musamman idan aka yi la’akari da cewa Allah Ta’ala Ya yi: Kuma a cikin kowaxanne mutane akwai mai shiryarwa (13:7). Ka ga kenan wannan na nufin, mai shiryarwa a cikin waccan al’umma, ba shi ne mai shiryarwa a cikin wannan ba. Ashe masu shiryarwa suna da yawa kenan. Idan kuwa haka ne, ta yaya za a ce Ali shi ne mai shiryarwa ga gaba xayan mutane, tun daga Annabi Adamu har ga na qarshe?!


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   31   32   33   34   35   36   37   38   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin