4.35 Ayar: ﭽ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭼ التوبة: ١١٩
Xan Shi’ar ya ce; Hujja ta talatin da biyar ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭼ التوبة: ١١٩
Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa, kuma ku kasance tare da masu gaskiya (9:119).
Ya ce, wai kenan Allah Ya wajabta mana kasancewa tare da wanda aka san mai gaskiya ne daga cikin Sahabbai. Babu kuwa mai iya kasancewa haka sai ma'asumi. Saboda haka duk yadda wanda ba shi ba ya qasura, to, ba ya fin qarfin qarya. Tunda ko har Ali, wai ma'asumi ne, to, shi ake nufi nan. Don gaba xayan halifofin huxu, shi ne kawai ma'asumi. Wai haka kuma Abu Nu’aimi ya ce a cikin wani hadisi nasa, daga xan Abbas: Ayar ta sauka ne a kan Ali.
Martani:
Kalmar Siddiqu wato gaskatau, mataki ne na qoli a layin masu gaskiya. Kenan duk “Gasgatau” mai gaskiya ne, amma ba duk mai gaskiya ne gasgatau ba. Kuma kai ka sani da yawa sun tabbatar da kasancewar Abubakar Raliyallahu Anhu gasgatau. Ka ga kenan wajibi ne ayar ta kasance tana magana ne har a kansa, ta rungume shi kam. Kai! Shi ne ma wanda ya fi cancanta da ayar ta nufa, fiye da wanda ba shi ba daga cikin Sahabbai.
Kuma idan har mun kasance tare da Abubakar Raliyallahu Anhu mun kuma aminta da ingancin halifancinsa. To, babu abin da zai sa mu yarda da kasancewar Ali shugaba ba shi ba. Ka ga kenan ayar ta yi gaba ‘yan Shi’ah sun yi baya.
Kuma wannan aya, haqiqanin gaskiya, ta sauka ne a kan Ka’abu xan Maliku da wasu Sahabbai, a lokacin da suka qi fita yaqin Tabuka. Suka kuma gaya wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama gaskiya cewa, ba su da wani uzuri a kan haka. Qarshe Allah Ya gafarta masu albarkacin wannan gaskiya da suka faxa. Maganarsu ta zo a ayar da take kafin wannan.
Kuma ko da wannan aya ta sauka a kan waxannan Sahabbai, babu wani mutum xaya da ake kaxa wa taken ma'asumanci. A kan haka ake da tabbacin cewa, cewar da Allah Ta’ala Ya yi: Tare da masu gaskiya haka xin kawai yake nufi. Don bai sharxanta kasancewar mai gaskiyar, ma'asumi ba.
Kuma ai Allah cewa Ya yi a kasance tare da “Masu” gaskiya. Ka ga wannan siga ce ta “Jam’i”. Shi kuwa Aliyu “tilo” ne, Kenan ba shi ake nufi ba.
A qa’ida ta harshe, cewar da Allah Ta’ala Ya yi, a kasance tare da masu gaskiya na iya xaukar ma’ana biyu, ko dai: Ku kasance tare da su a cikin duk abin da yake gaskiya da muqarrabanta. Wato ku yi gaskiya kamar yadda masu gaskiya ke yi, kada ku yi qarya. Ka ga sai ma’anar ta zama kamar cewar da Ya yi:
ﭽ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﭼ البقرة: ٤٣
Ku yi ruku’i tare da masu ruku’i (2:43)
Ko kuma a’a: Ku kasance tare da masu gaskiya a cikin komai; ko da ba ya da wata alaqa da gaskiya. Tirqashi.
Ma’anar ta biyun nan ba ta sauraruwa. Domin ba a cewa, wajibi ne mutum ya kasance tare da masu gaskiya har a cikin abubuwan halas na rayuwa. Kamar abinci da sha, da tufafi da makamantansu. A ce dole ya yi yadda suka yi kat-kat-kat.
A kan haka kenan ma’ana ta farko ita ce ingantatta. Babu wani umurni a cikin ayar a kan a kasance tare da wani mutum kevantacce. Ma’anar ayar dai, ita ce: Ku yi gaskiya, ka da ku yi qarya.
Yarda da wannan ma’ana a matsayin abin da ayar ke nufi, na sa a fahimci an yi wannan umurni ne saboda kasancewar gaskiya, na tabbatar da sauran ayyukan xa’a. Kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ina horon ku da, gaskiya. Saboda gaskiya na shiryarwa zuwa ga xa’a … Ka ga kenan wannan magana ta shafi duk wanda ya siffanta da gaskiya.
Mu qaddara cewa ayar na nufin a kasance tare da wanda aka “San” mai gaskiya ne. To, ai wannan kalma ta “Sani” daidai take da waccan kininta, a cikin faxar Allah Ta’ala: To, idan kun “San” su muminai ne (60:10). Ka kuwa san imanin wani ya fi gaskiya wuyar ganewa! To, idan kuwa har sharaxin na a “San” mutum da gaskiya ne kafin a kasance tare da shi, ya kuwa sava wa hankali a ce kalmar ta kevanta ga neman gane mai gaskiya kuma dole ya kasance ma'asumi. Kamar yadda ya sava wa hankali a nan, a taqaita kalmar ta “Sani” a kan tabbatuwar matan da ake magana a kansu ma’asumai.
Kuma ko da mun qaddara cewa, ayar na nufin a kasance tare da mai gaskiya, kuma lalle ya kasance ma'asumi. To, ba mu amince da ijma’in da ke cewa Ali Raliyallahu Anhu ne kawai ma'asumi ba. Ko banza kuma akwai mutane da dama waxanda suka fi ‘yan Shi’ah alqadari, da ke jin shehunansu ne wannan aya ke magana a kai. Kuma su ma duk ma’asumai ne, wai. Duk da yake lafuzzan da suke amfani da su sun sha banban da ‘yan Shi’ah. Amma dai duk da haka, ba mu yarda a ce su ba ma’asumai ba ne, Aliyu ne kawai. Ko dai a tabbatar masu da matsayin su duka, ko a hana wa kowa.
4.36 Ayar: ﭽ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﭼ البقرة: ٤٣
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da shidda itace: Faxar Allah Ta’ala: Kuma ku yi ruku’i tare da masu ruku’i (2:43).
Ya ce: An samo ta hannun Abu Nu’aimi daga xan Abbas Raliyallahu Anhu cewa, wannan aya ta sauka ne a kan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali kawai. Domin su ne farkon wanda ya yi sallah, ya yi kuma ruku’i. Ya ce: Wannan kuwa na nuna fifikon Ali, da shugabancinsa.
Martani:
Martaninmu a kan wannan magana zai kasance ta fuskoki kamar haka:
Fuska ta farko:
A wajenmu wannan riwaya ba igantatta ba ce. Kuma ga shi marubucin bai ambaci wani dalili da ke nuna ingancinta ba. Ga shi ko ma’abuta ilimin hadisi sun haxu a kan cewa wannan hadisi qagagge ne.
Da wannan ayana nufin a yi ruku’i ne tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali Raliyallahu Anhu to, da kuwa hukuncin yin hakan ya yanke a lokacin da suka rasu. Babu sauran wanda ake da buqata da ya yi ruku’i’tare da masu yin ruku’i.
Cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Ali shi ne farkon wanda ya yi sallah tare da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama maganar kawai ce. Mafi yawan mutane na ganin cewa ba haka abin yake ba. Abubakar ya riga Ali mayar da gaba gabas yayi sallah.
Wani abun kuma shi ne: Da umurnin da wannan aya ta yi, na nufin a yi ruku’i ne tare da Manzon Allah, to, ko a haka, zancen ba ya nuna cewa wanda ya yi ruku’in tare da shi, lalle ne ya zama shugaba. Domin kuwa Ali Raliyallahu Anhu bai kasance shugaba a lokacin da Manzon Allah yake Annabta ba. Tattare kuma da kasancewarsa yana ruku’in tare da shi.
4.37 Ayar: ﭽ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﭼ طه: ٢٩
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da bakwai ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
Kuma ka sanya mini wani mataimaki daga iyalaina (20:26).
An samo ta hannun Abu Nu’aimi daga Ibnu Abbas, wanda ya ce: “Watarana muna a Makka, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kama hannun Ali da nawa. Ya yi sallah raka’a huxu. Sannan ya xaga hannayensa zuwa sama ya ce: Ya Ubangiji, musa xan Imrana ya roqe ka. Ni kuma yau Muhammadu, Annabinka ina roqan ka da ka buxa qirjina, kuma ka warware mini qullin da ke ga harshena. Don su fahinci maganata. Kuma ka sanya mini wani mataimaki daga cikin iyalaina. Ya kuma kasance Aliyu xan Abu Xalib; xan’uwana xin nan. Ka qarfafa halittata da shi. Ka kuma shigar da shi a cikin al’amarina”.
Wai, kuma sai xan Abbas ya qara da cewa: “Sai na ji wani mai kira yana kira, yana cewa: Ya kai Ahmadu, haqiqa an karva roqonka”.
Xan Shi’ar ya ce: Wannan nassi ne da ke tabbatar da Imamancin Ali.
To, muna bin sa bashin tabbatar da ingancin wannan magana, kamar yadda muka saba. Kuma ma’abuta ilimin hadisi sun haxu a kan cewa wannan hadisi qagagge ne kamar takwarorinsa da suka gabata waxanda ya kawo. Kai! Yana daga cikin miyagun qaryace-qaryacen da aka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tabbas.
Kuma mafi tsawon zaman da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi a Makka, ba a haifi xan Abbas ba. Domin tarihi ya nuna cewa an haife shi ne a daidai lokacin da Bani Hashimu ke cikin kulokon batta. Kuma ko da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hijira daga Makka xan Abbas bai kai shekarun iya banbancewa tsakanin ruwa da kalanzir ba. Balle ya isa shiga sahun masu yin arwalla su bi sallah.
Mu lura a nan da cewa, xan Shi’ar ya qara wata magana da bai yi irinta ba a baya. Ita ce, cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ka kuma shigar da shi a cikin al’amarina (20:32). Ka ga a nan ya fito fili ya nuna cewa Ali na tarayya ne da Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin Annabta, kamar yadda Haruna ke tarayya da Musa. Wannan magana kuwa, irin ta waxanda ke jin Aliyu Annabi ne, ce. Kuma cewa haka kafirci ne sara. Zance kuma ne na Shi’ah Gulatu, ba Shi’ah ‘yan-sha-biyuh ba.
To, kuma ko a hakan ai, kasancewar wani abokin tarayyar wani, a cikin wani al’amari, ba ta nufin lalle ya maye gurbinsa bayansa kai tsaye. Kamar yadda kuke iqirarin wajabcin kasancewar Ali halifa kai tsaye, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Bayan kuma ya kasance abokin tarayyarsa a cikin annabta, a lokacin da yake raye, wanda hakan ta sa wannan maqaryacin xan Shi’ar qarfin halin cewa wai, wannan hadisi nassi ne ke tabbatar da shugabancin Ali.
Ka ji xanbaya. Bari ka ji, ko akwai wani abu da wannan hadisi na qarya ke nunawa, duk bai wuce kasancewar Ali, abokin tarayyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin sha’anin isar da mazancin, a lokacin da yake raye ba. Kamar yadda Haruna ya kasance abokin tarayyar Musa. Shin a shirye kake ka tsaya inda wannan nassi ya tsaya. Ka daina kafa hujja da magangaun maqaryata, da ya sassun zantukan ‘yan’uwanka mavartanata, koko?!
4.38 Ayar: ﭽ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﭼ الحجر: ٤٧
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da takwas ita ce: Faxar Allah Ta’ala:
ﭽ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﭼ الحجر: ٤٧
Kuma Muka zare duk damuwar da ke cikin zukatansu, suka zama ‘yan’uwan juna a kan gadaje, suna masu fuskantar juna (15:47).
Ya ce: An samo a cikin Musnadin Ahmad, da isnadinsa zuwa ga Zaidu xan Abu Aufa, wanda ya ce: Na shiga wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin masallacinsa. Na tayar da zancen zumuncin da ya qulla tsakanin Sahabbai. Sai Ali Raliyallahu Anhu ya ce, saura kaxan qashin bayana ya kare, nunfashina ya xauke, a lokacin da ka qulla zumunci a tsakanin Sahabbanka, Ya Manzon Allah. Idan ka yi haka ne, saboda masaniyar da kake da ita a kan cewa Allah ya yi hushi da ni, to, Allah Ya kyauta qarshenka, Ya kuma xaukaka darajarka.
Ali na sauka, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ina rantsuwa da wanda ya aiko ni Annabi, da gaskiya. Na aje wa kaina kai ne. Domin matsayinka a wurina, kamar matsayin Haruna ne a wurin Musa. Sai dai kawai babu wani Annabi bayana. Amma kai xan’uwana ne kuma magadina. Kuma za ka kasance tare da ni a cikin benena a aljanna. Tare kuma da ’yata Fatima. Kai xan’uwana ne, kuma abokin tafiyata”.
Wai daga nan kuma Annabi sai ya karanta wannan aya. Xan Shi’ar ya kammala da cewa: Wannan zumunci da Manzon Allah ya qulla da Ali, dacewa ne da zozozon da ke tsakaninsu. Kuma wannan kevancewa da Ali ya samu da zumunta da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na tabbatar da imamancinsa.
Martani:
Da farko, ina maganar ingancin wannan labari?. Muna ba da tabbacin cewa, babu wannan hadisi a inda ya faxa, ina nufin Musnadin Ahmad. Kai! Ahmad bai tava riwaito wannan hadisi ba; daxa cikin Musnad xin ko Fadha’ilus-Sahabah. Haka kuma xansa bai riwaito shi ba. Saboda haka cewar da wannan xan Shi’ar ya yi wai: An samo daga cikin Musnad na Ahamad qarya ce qwanqwasassa.
Abin da malaman hadisi suka faxa a kai shi ne, wannan hadisi na daga cikin qarairayin da Qaxi’i ya riwaito ta wata hanya daban ba ta hanyar Ahmad xan Hambali ba. Hanyar kuma duhu ce xib.
Kuma ka sani xan Shi’ar ya yi wa hadisin shan koko ne; bai ambaci cikonsa ba. Domin cikon hadisin shi ne: “Ali kai xan’uwana ne kuma magadina”. Sai Ali ya yi farat ya ce: “Me zan gada daga gare ka, ya Manzon Allah?” Sai ya karva masa da cewa: “Abin da ake gado daga Annabawan da suka gabace Ni”. Alin ya sake cewa: “Mene ne ake gado daga gare su?” Ya ce: “Littafin Allah da Sunnoninsu”.
Amma kamar yadda muka gaya maka, isnadin wannan hadisi gurvatacce ne. Domin kuwa Abdulmumini xan Abbad kawai ya riwaito shi. Yana kuma daga cikin waxanda malaman hadisi suka yi wa radan-radan. Shi kuma ya karvo shi daga Yazidu xan Ma’anu, wanda malamai ba su tantance ko waye shi ba. Wataqila ma shi ya qaga hadisin. Don ya ce, ya karvo shi daga Abdullahi xan Sharhabilu, shi ma ba a san shi ba. Sannan wai, shi kuma ya karvo shi daga wani Baquraishe da ba a faxi sunansa ba, balle a gane ko waye shi.
Ba zaka yi mamaki ba idan ka ji cewa, ma’abuta hadisi sun haxu a kan qaryata irin wannan hadisi.
Ta kuma tabbata cewa, gaba xayan hadissan da ke magana a kan qulla zumunci tsakanin Muhajiruna, wasu-wasu. Da tsakanin Ansaru, wasu-wasu duk qarya ce. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai qulla zumunci tsakaninsa da Ali Raliyallahu Anhu ba. Bai kuma qulla shi tsakanin Abubakar da Umar ba. Ko tsakanin duk wani Muhajuri da Muhajuri xan’uwansa.
Zumuncin da ya qulla tabbas, shi ne na tsakanin Muhajiruna da Ansaru. Irin wanda ya qulla tsakanin Abdurrahman xan Aufi da Sa’adu xan Rabi’u. Da kuma tsakanin Salmanul-Farisi da Abud-Darda’i. Da kuma tsakanin Ali da Sahalu xan Hunaifu.
Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hidimar qulla wannan zumunci ne a unguwar Banun-najjari. Kamar yadda Anas ya bayar da labari a cikin wani hadisi ingattacce. Ba a cikin masallacin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama aka yi hidimar ba, kamar yadda qagaggen hadisin ya nuna. A’a, cikin gida ne da wani xan Banun-najjari ya gina a anguwar tasu, aka yi wannan hidima.
Ahlus-Sunnah da Shi’ah duka ba su yarda da cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Annabi ya ce wa Aliyu: Kai xan’uwana ne kuma magadina. Domin kuwa idan xan Shi’ar na nufin gadon dukiya ne, to, hakan ba ta shiga. Domin kuwa Fatima Raliyallahu Anha ce mai wannan gado. Ko bayan ta kuwa, Ali bai gado in ga Abbas tun da matsayinsa a wajen gadon yana gaba da na Ali. Sannan Alin ba shi kaxai yake a matsayinsa na xan baffa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, akwai irin su Aqilu. Don me za a ce shi ne kaxai ke gadon ba da su ba?.
Idan kuma xan Shi’ar na nufin gadon ilimi ne da shugabanci. To, wannan ma maganar ‘yan sanda ce, da ba a shiga xaki da ita. Kuma hujjar da suka kafa da ita ta tashi, idan aka dubi faxar Allah Ta’ala: Kuma Sulaimanu ya gaji Dawuda (27:16) da kuma faxarsa: Sai ka ba ni wani mataimaki daga wajenka. Ya gaje ni (19:5-6).
Ka ga kenan, idan wannan lafazin gado na nufin gadon dukiya da ilimi da shugabanci, kenan waxannan Annabawa, sun gadar da gaba xayan waxannan abubuwa. Kamar yadda ake son a ce Ali Raliyallahu Anhu ya gade su daga wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan kuwa ko alama, ba haka abin yake ba.
A wurin Ahlus-Sunnah, Aliyu bai kevanta da gadon abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gadar na ilimi ba. Domin babu wani daga cikin Sahabbansa, wanda bai sami rabonsa gwargwado daga ciki ba. Kuma ilimi ba kamar dukiya ba ne. Ba a cewa sai an yi raba daidai a cikinsa, ta yadda wani ba zai fi wani ba. A’a, babu wata rigima a cikin sha’anin ilimi. Ba a cewa wannan ba ya da ikon sanin abin da wancan ya sani. Kamar yadda ake iya hana wani, wani adadi na dukiyar da wani ya karva.
Wani abun kuma da ke tabbatar da kasancewar wannan hadisi qarya shi ne, abin da ya inganta a cikin Buhari da Muslimu cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya qulla zumuncinsa da wani ba Ali ba. Saboda ya ce wa Zaidu: “Kai ne xan’uwanmu kuma abin jivanta gare mu”. Kuma lokacin da ya nemi auren Aishah, Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce masa: “Ashe kai ba xan’uwana ba ne?” Sai ya ce masa: “Eh, Ni xan’uwanka ne, amma ‘yarka halas ce gare ni”.
Haka kuma hadisi ya inganta Manzon ya tava ce wa Abubakar: “Sai dai muna nan matsayin ‘yan’uwan musulunci”.
Kuma duk waxannan hadisai da makamantansu, suna nan cikin ingantattun littafan hadisi. Ka ko ga hakan, na tabbatar da cewa kawai qulla zumunci irin wannan, ba ya hukuntar da zama abu xaya; kafaxa-da-kafaxa da abokin zumuncin ta kowace fuska, ko dacewa da zozozo.
To, tunda kuwa har haka ne, don me za a ce zumuncin da Annabi ya qulla da Ali, in har ya inganta, na hukuntar da imamancinsa da kasancewar mafi xaukaka daga cikin Sahabbai, alhali kuwa ba da shi ne kawai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qulla zumuncin ba?
Ta tabbata a cikin hadisai ingantattu, ta fuskoki da dama, cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Da zan yi badaxayi daga cikin mutanen duniya, to da Abubakar ne. Amma ku sani Allah Ya riga shi. Ku toshe duk qofofi in banda ta Abubakar. Kuma haqiqa, Abubakar shi ne wanda abokantakarsa da abin hannunsa suka fi amfanarmu fiye da kowa daga cikin mutane”.
To ka ga wannan magana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na nuna irin martabobin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya kevanta da su; ba tare da wani ba. Kuma a bayyane take cewa, babu wani mahaluki a bayan qasa, wanda Annabi ke so, ko ke da qima a idonsa, ko wata xaukaka, ko wani matsayi na daban a wurinsa kamar Abubakar.
Kamar yadda ya zo a cikin Buhari da Muslimu cewa, an tambayi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Wane ne mafi soyuwar mutane a wurinka?” Ya ce: “Aishah”. Aka ce: “Daga cikin maza fa?” Ya ce: “Mahaifinta”.
A cikin Buhari da Muslimu harwayau, Umar Raliyallahu Anhu ya ce wa Abubakar: “Kai ne shugabanmu, kuma mutum mafi alheri daga cikinmu. Kuma mafi soyuwa daga cikinmu a wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama”.
To, a haka, ka ga waxannan hadisai da kan ma’abuta ilimi ya haxu a kan ingancinsu, da karvar su hannu biyu-biyu; Kuma ba a sami wani masani da ya soki lamirinsu ba. Sun bayyana cewa, Abubakar shi ne mutum mafi soyuwa da xaukaka a wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama gaba da kowa.
Ka ga kenan da zumuncin da ‘yan Shi’ar ke cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qulla shi ne wannan. To, da babu wata jayayya tsakaninsu da waxannan hadisai. Amma karkata akalar tarihin da suka yi, ta hanyar ba shi wani matsayi da ba wannan ba. Ta sa waxannan ingantattun hadisai sun tabbatar da kasancewar nasu qarya.
Illa dai, abin da waxannan ingantattun hadisai ke tabbatarwa shi ne: Abubakar Raliyallahu Anhu ya fi soyuwa a wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan Ali. Ya kuma fi shi matsayi a wurinsa. Ya kuma fi duk wanda ba Alin ba. Kuma dalilan da ke tabbatar da haka ba su qidayuwa.
Ta tabbata ta hanyar kusan mutum tisi’in daga Ali Raliyallahu Anhu yana cewa: “Mafi girman daraja a cikin wannan al’umma, bayan Annabinta, shi ne Abubakar sannan Umar”. Buhari ya riwaito shi, a cikin ingantaccen littafinsa.
4.39 Ayar: ﭽ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﭼ آل عمران: ٨١
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta talatin da tara ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Kuma a lokacin da Ubangijinka Ya karvi (alqawali) daga xiyan Adamu, daga bayayyakinsu, a zuriyarsu, kuma Ya shaidar da su a kan rayukansu (Ya ce): “Shin, ba Ni ne Ubangijinku ba?” Suka ce: “Na’am, Kai ne”! Mun yi shaida!” (Ya ce): “Kada ku ce Ranar Qiyama “Lalle ne mu, mun rafkana daga wannan (7:172).
Ya ce: An samo daga cikin littafin: Al-firdausi na Ibnu Shirawaihi, riwayar da ya xaukaka ta hanyar Huzaifatu xan Yamani cewa: “Da mutane sun san ko tun yaushe aka raxa wa Aliyu sunan Sarkin Musulmi, da ba za su yi musun xaukakarsa ba; An naxa masa wannan suna ne tun ba a halicci Annabi Adamu ba”. Sai Annabi wai, ya karanta wannan aya. Wai sai mala’iku suka ce: “Tabbas haka ne”. Sai Allah Maxaukakin Sarki Ya ce: “Ni ne Ubangijinku, muhammadu kuma shi ne Annabinku, Aliyu ko Shugabanku”.
Allahu Akbar!!!
Kuma wai wannan inji xan Shi’ar nassi ne qarara da ke tabbatar da shugabancin Ali.
To, mun ji.
Martani:
Da farko dai, wannan hadisi bai inganta ba. Idan kuma xan Shi’ar na jin ba haka ba, to ga fili ga mai doki, sai ya tabbatar mana da yadda aka yi ya inganta.
Amma kar a manta fa, gaba xayan ma’abuta ilimin hadisi sun haxu a kan cewa, kasancewar mai littafin Al-firdausi kawai, ya riwaito hadisi, ba ta nuna cewa hadisin ingantacce ne. Tabbataccen abu ne cewa marubucin wannan littafi; wato Ibnu Shirawaihi Al-Hamadani Ad-Dailami ya ambaci hadissai ingantattu da dama a cikin wannan littafi. Ya kuma ambaci waxanda ba su kai su ba, har ma da qagaggu. Kuma kasancewarsa daga cikin ma’abuta ilimi da riqon addini, da rashin kasancewarsa mai yin qarya shi kansa, duk ba su hana ya naqalto abin da ya haxa da qarya da gaskiya a cikinsu. A haka sai aikinsa ya zama irin na da yawa daga cikin mutanen da suka tarkata hadisai kawai; masu kai da marar shi.
Ma’abuta ilimin hadisi sun haxu a kan kasancewar wannan hadisi qagagge ne.
Makamar maganar da ke cikin wannan aya ita ce, cewar da Allah ya yi: Shin ba Ni ne Ubangijinku ba? suka ce “Na’am. Kai ne”! (7:172) ka ga ba a ambaci wani Annabi a nan ba, balle wani shugaba.
Kuma xan dubi abin da Yake cewa a aya ta gaba: Ko kuwa ku ce: “Abin sani kawai, ubanninmu suka yi shirka daga farko, kuma mu, mun kasance zuriya daga bayansu (7:173). Ka ga kenan wannan aya na tabbatar da cewa alqawarin tauhidi ne tsintsa Allah Ya karva. Ba na Annabci ba, balle abin da ba shi ba.
Sanannun hadisan da ke cikin: Musnad da Sunan da Muwaxxa, da littafan tafsiri da wasu littafai duk, ba su qunshi wata magana mai kama da wannan ba. Da kuwa akwai ta, da gaba xayan mutane ba su yi biris da ita ba. Sai kawai a ji ta ga bakin wanda gaskiyarsa ba ta bayyana ba; hasali ma maqaryaci aka san shi?!
Wani abin lura kuma a nan shi ne: Wancan alqawari da Allah Ya karva a cikin ayar, Ya karve shi ne daga gaba xayan zuri’ar Adamu. Idan kuwa wancan tafsiri na ‘yan Shi’ah ya tabbata, kenan wajibi ne Aliyu ya kasance shugaba a kan Annabawa baki xaya; tun daga Nuhu Alaihis Salamu har ka dire ga MuhammaduSallallahu Alaihi Wasallama. Wannan kuwa magana ce irin ta mahaukata. Waxancan Annabawa sun wuce tun kafin Allah ya halicci Ali. To, ta yaya zai iya zama shugaba a kansu?.
Qololuwar abin da Aliyu ke iya zama shi ne shugaba a kan mutanen zamaninsa. Amma shugabancin waxanda aka halitta kafin sa, da waxanda za a halitta bayan sa, qarya ce da babu mai sheqa ta sai wanda bai san abin da yake faxi ba. Wanda kuma ba ya jin kunyar a kan abin zai fito bakinsa.
4.40 Ayar: ﭽ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﭼ التحريم: ٤
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta arba’in ita ce: Faxar Allah Ta’ala: Lalle Allah shi ne mataimakinsa, da Jibrilu da salihan muminai. Kuma mala’iku mataimaka ne a bayan haka (66:4). Kan malaman tafsiri, inji shi, wai, ya haxu a kan cewa Salihan muminai a cikin wannan aya na nufin Ali Raliyallahu Anhu. Kuma Abu Nu’aimi ya riwaito da isnadin zuwa ga Asma’u ‘yar Umaisu, wadda ta ce: “Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na karanta wannan aya, ya kuma kare da cewa, inji ta, wai salihan muminai xin nan na nufin: Aliyu xan Abu Xalib”.
Shi kuwa mutumin ya cika zancensa da cewa: “Kevantuwar Ali da wannan matsayi na nuna fifikonsa a kan sauran Sahabbai. Kenan shi ne Imamu. Kuma ayoyin da ke tabbatar da shugabanin nasa sun fi bakin bunu”. Ya ce: “Za mu taqaita a kan waxannan da muka ambata kar magana ta tsawaita”.
Martani:
Da farko, cewar da ya yi, kan malaman tafsiri ya haxu a kan cewa Salihan muminai a cikin ayar na nufin Ali Raliyallahu Anhu qarya ce bayyananna. Babu wata haxuwa da suka yi a kan haka. Babu kuma wani malamin tafsiri ko na hadisi da ya naqalto haxuwar kan malaman (Ijma’i) a kan haka. To, daga bakin wa xan Shi’ar ya samo ijma’in ?
Kuma littafan tafsiri cike suke maqil da savanin wannan fassara. Domin kuwa Ibnu Mas’ud da Ikrimata da Mujahidu da Dhahhaku da wasunsu, duk cewa suka yi: “Salihan muminai a cikin wancan ayar na nufin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma”. Kuma wasu malaman tafsiri irin su Xabari da wasunsu duk, sun kawo wannan magana.
Maganar kevance Ali da kasancewa Salihan muminai ba ta inganta daga bakin kowa ba, balle ta tabbata.
A bayyane take cewa cewar da Allah Ta’ala Ya yi: Da salihan muminai suna ne da ke game duk wani salihi daga cikin muminai. Kamar yadda ya zo a cikin Buhari da Muslimu cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Haqiqa mutanen gidan su wane ba mataimakana ba ne. Mataimakana kam, Allah da salihan muminai”. Kasancewar muminan kirki mataimakan manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa ba ta nufin zamansu shugabanni a kansa.
Haka kuma xan Shi’ar ya ce, ayoyin da ke tabbatar da shugabancin Ali sun fi bakin bunu, wai. Amma muna da yaqinin cewa, komai yawansu, ba za su amfane su da komai a cikin manufarsu ba. Ko da kuwa sun yi masu halin hankaka. Balle kuma mun san waxannan da ya ambata su ne tatattun abin da ke hannunsu na ayoyi. Illa dai ita qofar qarya buxe take har kullum gare su.
Da kowa zai xauki irin halinsu, da mutane da dama sun mayar masu da martani da irin qaryace-qaryacensu. Duk dai abin da kenan, kodayaushe Allah kan bice bilar qarya da mamakon ruwan gaskiya, itacen su jiqe, tokar ta bi ruwa. Boni kuma ya tabbata a kan maqaryata saboda abin da suka kasance suna aikatawa.
Dostları ilə paylaş: |