Tafarkin sunnah


Hadisin Gaisuwar Sarauta ga Ali



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə42/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   38   39   40   41   42   43   44   45   ...   51

5.9 Hadisin Gaisuwar Sarauta ga Ali

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta tara ita ce, abin da malaman Sunnah suka riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci Sahabbai su rinqa yi ma Ali gaisuwar sarauta, suna ce masa “Allah ya taimaki Sarkin Musulmi”! Kuma wai, ya qara da ce masu: “Ali shi ne shugaban musulmi, kuma limamin masu taqawa, kuma shi ne jagoran masu farin goshi a gobe qiyama”. Ya kuma ce, inji xan Shi’ar: “Ali shugaba ne ga kowane mumini bayana”. Kuma ya qara da cewa: “Ku sani, ni da Ali kamar jini da tsoka mu ke. Kuma muna da iko ga gaba xayan muminai maza da mata fiye da ikonsu akan kawunansu”.

Bisa ga wannan dalili, inji xan Shi’ar, Ali ne kaxai ya kamata ya zan shugaban musulmi a bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma waxannan hadisan yanke suna tabbatar da haka.
Martani:

Kamar koyaushe, muna neman ya ba mu tabbacin ingancin hadisan nasa. Ya faxi kuma littafan da ya cirato su. Ba kawai ya ce, malaman Sunnah sun riwaito ba. Riwaya kaxai ba ta tabbatar da hadisi in ba an bi diddigi an gano amincin mafitarsa ba. Allah kuma ya haramta qarya, musamman kuma in ta zamo a cikin addini. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi qyaci a kan wanda ya qirqira masa qarya.

To, su dai waxannan hadisan kamar na bayansu, zuqi-ta-mallau ne. waxanda ba ya halalta a ji su ga bakin wanda ya san girman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. domin waxannan sifofi da hadisan suka ba Ali sifofin Annabi ne Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma ko a bayan wafatinsa ba ya dacewa a sifanta wani da waxannan siffofi in ba shi ba. Shi ne ya cancanci wannan siffa a nan duniya da gobe kiyama.

Kuma ma sai mu ce ma xan Shi’ar: Kaffatanin musulmin da suke tare da Ali a lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke furta wannan magana – in har ya faxe ta - waxanda su ne masu farin goshin, kafirai ne a gurin ku. To, su wane ne Ali zai jagoranta?!

Tabbatattar qarya duk ba ta wuce cewa, Ali shi ne wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hukunta ya jagoranci al’ummar Sahabbai ba. Don na kusa da na nesa sun san yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke fifita Abubakar da Umar a kan sauran Sahabbai, cikinsu har da Ali. Ko kafirai ma a lokacin, sun san da haka.

Kuma cewar da xan Shi’ar ya yi, wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ali shi ne ubangidan kowane mumini bayana” qarya ce ita ma. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne ubangida kuma masoyin kowane mumini a lokacin rayuwarsa da bayan rasuwarsa. Don so da qauna na gaskiya ba su yankewa don rayuwa ta qare.

Amma cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da Ali kamar jini da tsoka ne, haka yake. Ingantacciyar magana ce, amma a cikin wani hadisi ba wannan da xan Shi’ar ya kawo ba. Ali kuwa bai kevanta da samun wannan matsayi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Domin kuwa haka ya faxa a game da Julaibibu lokacin da ya yi shahada. Kai, wata qabila ma sukutum da ake kira Ash’ariyyuna ya ba su wannan matsayin, ya ce: “Ni da Ash’ariyyuna kamar jini ne da tsoka”. Ya faxa masu haka saboda kyawon halinsu da ‘yan’uwantakar da suke yi a tsakanin junansu. To, ya za a ce Ali ya kevanta da wannan, ballantana a ce, shi ne dalilin zamansa shugaba.
5.10 Hadisin Amanoni biyu:

Hujjar xan Shi’ar ta tara daga cikin hadisai, inji shi, ita ce: Abin da malaman sunnah suka riwaito, daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Ko shakka babu zan bar maku wasu amanoni biyu da za su hana ku vacewa matuqar kun yi riqo da su: Littafin Allah da zuri’ata; iyalan gidana. Kuma ba za su rabu da juna ba har sai sun same ni a bakin tafkin Alkausara”. Da kuma wani hadisi, inji shi, da ya ce: “Iyalaina kamar jirgin Annabi Nuhu ne a cikinku. Duk wanda ya shige shi ya tsira. Wanda kuwa ya bari aka bar shi baya, to, ruwa zai ci shi.”.

Xan Shi’ar ya ce: Waxannan hadisai na nuna wajabcin saurara ma Ahlul-Baiti ga duk abin da suka faxi. To, da yake Ali ne shugabansu, ya zama tilas a kan kowane musulmi ya yi masa biyayya, ya kuma yarda da kasancewarsa halifa kai tsaye bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Martani:

A bisa al’adarmu, za mu soma neman ingancin wannan hadisi. Kuma mun san bai inganta xin ba a yadda ya kawo shi.

Lafazin da ya inganta, kamar yadda Muslimu ya riwaito a cikin ingantaccen littafinsa daga Zaidu xan Arqamu ya ce: Watarana muna bakin wani tafki mai suna Khum, a tsakanin Makka da Madina, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tashi ya yi mana huxuba, ya ce: “Bayan haka, ya ku mutane, ku sani, ni mutum ne kamar kowa. Yau manzon mutuwata na iya zuwa, ba ni da ikon qin tafiya. Ko da na tafi dai, zan bar maku wasu abubuwa biyu masu alfarma. Na farko, shi ne littafin Allah, wanda ke tattare da haske da shiriya. Ku yi riqo da littafin nan na Allah. Ku bi shi sau da qafa.” Sai ya yi ta kwaxaitar da mu, da nuna mana muhimmancin aiki da littafin Allah. In ji Zaidu. Sannan ya ci gaba da cewa: “Da iyalaina. Ina tunayar da ku Allah game da su”.

Ka ga wannan ingantattar riwaya na nuna mana cewa, littafin nan na Allah ne kawai Annabi ke umurtar mu da bi sau da qafa, kuma duk wanda ya yi haka ya tsira. Kuma ita wannan ma’ana ta yin biyayya ga littafin Allah shi kaxai, ita ce wani hadisin ya zo da ita, kamar yadda yake a cikin Sahihu Muslim daga Jabir Raliyallahu Anhu, ya ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a ranar Arafa, lokacin da yake huxubar hajjin bankwana: “Haqiqa na bar maku abin da ba za ku vace ba bayana, matuqar kun yi riqo da shi. Wannan abu shi ne littafin Allah. Za a kuma tambaye ku a kaina, me za ku ce? Sai Sahabbai suka ce: “Za mu ce, mun sheda ka isar da manzanci, ka kuma yi gargaxi ga kowa”. Daga nan sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xaga hannuwansa sama, ya rinqa dawowa da shi yana nunin Sahabbai, yana cewa: “Ya Allah! Ka zama sheda a kan haka”. Ya maimaita haka har sau uku.

Amma cewar da xan Shi’ar ya yi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Da zuri’ata; iyalan gidana. Kuma ba za su rabu da Alqur’ani ba har sai sun same ni a bakin tafkin Alkausara”. Wannan riwayar Tirmidhi ce. An kuma tambayi Ahmad xan Hambali akan matsayinta, ya ce, riwaya ce mai rauni. Wasu malamai da dama kuma daga cikin masana sun raunana shi. Amma dai da dama daga cikin malamai na cewa, iyalan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba za su haxu a kan vata ba.

To, mu a nan muka tsaya. Kuma cikin hikimar Allah, babu wani abu guda xaya da Ahlul-Baiti suka yi tarayya da ‘yan Shi’ah a cikinsa. Allah ya tsarkake su daga wannan qazamta.

Amma cewar da xan Shi’ar ya yi, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Iyalaina kamar jirgin Annabi Nuhu ne a cikinku..”. Wannan magan ba ta da wani isnadi nagartacce. Kuma littafan da ake kafa hujja da su ba su kawo ta ba. Illa dai masu bayar da tatsuniyoyi ne suka kawo ta kamar yadda suka saba. Wannan kuwa ba zai daxa wa riwayar kome ba illa rauni bisa rauni.

To, kuma a nan hadisin ya nuna cewa, iyalan Manzo ba su rabuwa da Alqur’ani. Wannan dalili ne a kan cewa, ijma’in iyalan Manzo hujja ne. Wannan ko shi ne ra’ayin wasu almajiran makarantar Ahmad xan Hambali. Kuma shi ne Alqali ya kawo cikin littafinsa AlMu’utamad. To, amma iyalan Manzo su ne, dukkan banu Hashim. Waxanda suka haxa da, ‘ya’yan Abbas da ‘ya’yan Ali da na Harisu xan Abdulmuxxalibi da sauran ‘yan gidan Abu Xalib. Ali shi kaxai ba zai amsa sunan iyalan gidan Manzo ba. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne ubangidan Ahlul-Baiti, ba Ali ba.

Wani abu kuma da ya kamata a sani shi ne cewa, Ahlul-Baiti basu bi ra’ayin ‘yan Shi’ah na fifita Ali a kan sauran Sahabbai baki xaya ba. Ibnu Abbas ga misali, duk da yake yana tare da Ali ko a yaqoqan zamanin fitina, a fili yana faxin fifikon Abubakar da Umar a kan kowa, tun ma ba a fagen shugabanci ba.

Maganar ijma’in Ahlul-Baiti ita kanta, ta ci karo da abin da ya fi ta qarfi, shi ne, kasancewar ijma’in baki xayan musulmi hujja ce da ta tabbata da Alqur’ani da tabbatattun hadisai. Su kuma Ahlul-Baiti wani vangare ne daga cikin al’umma. Don haka, duk lokacin da al’umma ta yi ijma’i sun shiga cikin sa.


5.11 Wasu Hadisan Qarya

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Hujja ta sha xaya, ita ce, hadisan da malaman Sunnah suka riwaito na wajabcin son Ali da riqonsa ubangida. Ya ce: “Ahmadu xan Hambali ya riwaito a cikin Musnadinsa cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya riqa hannun Hasan da Husaini, sannan ya ce: “Duk mai sona da ni da waxannan da mahaifansu, to, yana tare da ni, a matsayina ranar qiyama”. Kuma Ibnu Khalawaihi ya riwaito, inji shi, daga Huzaifa Raliyallahu Anhu ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke son a ba shi sandar yaqutu, wadda Allah ya halitta da hannunsa, sannan ya ce mata: kun-fa-yakunu, to, ya riqi Ali xan Abu Xalib a matsayin maigida a bayana”.

Ya ce, kuma an karvo daga Abu Sa’id Al-Khudri ya ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma Ali: “Sonka imani ne, kuma qinka nifaqa ne. farkon wanda zai shiga aljanna su ne masoyinka. Farkon wanda zai shiga wuta su ne maqiyanka. Matsayinka a wurin Allah ya kai haka. Kuma kai nawa ne, ni naka ne. amma babu Annabi bayana”.

Kuma an riwaito daga Shaqiqu xan Salamata daga Abdullahi ya ce: “Na ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana riqe da hannun Ali yana cewa: “Wannan majivincina ne, ni ma majivincinsa ne. Na qi wanda ya qi, na shirya da wanda ya shirya”. Kuma Akhxabu Khuwarizmi daga Jabir Raliyallahu Anhu ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Jibrilu ya zo min daga wurin Allah da wata koriyar takarda, an yi mata rubuta da farar tawwada cewa: Ka gaya wa halittata, haqiqa ni, na wajabta masu son Ali”.

Xan Shi’ar ya cike maganarsa da cewa, hadisai irin waxannan ba su da iyaka waxanda aka samo daga hannun ‘yan adawa. Kuma duk suna nuna fifikon Ali da cancantarsa da shugabanci.
Martani:

Ina ma dai a ce, marubucin nan namu zai iya kare kansa game da waxannan qarairayi da ya fesa ma fiyayyen talikkai?

Malamin yana cika bakinsa da faxin Ahmad xan Hambali ya riwaito, kuma ga dukkan alamu bai san banbancin hadisan da ke cikin littafan Ahmad ba. Ko ma ya san Ahmad yana da Kitabul Fadha’il wanda hadissansa galibi sun fi rauni a kan na Musnad? Kuma ko ya san baicin hadissan da Ahmad ya riwaito a cikin Musnad akwai qare-qaren da xansa Abdullahi da ya riwaito littafin ya yi? Ya kuma san Qaxi’i da ya riwaito littafin daga Abdullahi xan Ahmad shi ma ya shigar da nasa riwayoyi na daban, ba na Ahmad ba? Kuma rauni hadissan na qarshen nan yana da tsanani, kuma ba ya halalta a jingina ma Ahmad su tunda ba shi ya riwaito su ba? Iya abin da za a yi shi ne a jingina kowane hadisi a wajen riwaya ga mai shi? Anya kuwa Malam Zurqe xan Shi’ah ya san da waxannan bayanan? Sanin gaibu sai Allah. Amma dai biri ya yi kama da mutum!

Hadisin farko da xan Shi’ar ya kawo cikin hadissan Quxai’i ne na qarya. Ibnul Jauzi ya yanke masa wannan hukunci a cikin littafinsa Al-Maudu’at. Su ma dai sauran hadissan Ibnu Khalawaihi da na Akhxabu Khuwarizmi yi masu bugu guda.

Yi nazarin hadisin da ya ce, wai: Maqiyan Ali ne farkon wanda zai shiga wuta. Kana tsammanin Harijawa su riga Abu Jahli shiga wuta, da su Fir’auna da Abu Lahabi da sauran tsararrakinsu na mushrikai?. Sannan cewa, masoyan Ali ne farkon masu shiga aljanna. Za su riga Annabawa da Manzanni ne? Ko yana nufin su ma Annabawan da Manzanni za su shiga aljanna ne albarkacin son da suke ma Ali kafin son Allah da son sauran masoyansa na daga Annabawa da Manzanni?
5.12 Hadisin Kafirta Wanda ya Sava ma Ali

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Hujja ta sha biyu daga cikin hadissai ita ce: Hadisin da Akhxabu Khawarizim ya riwaito daga Abu Zarril Gifari daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Wanda duk ya yi jayayyar halifanci da Ali kafiri ne. Don kamar ya kai wa Allah da Manzonsa yaqi ne. Duk kuma wanda ya yi shakkar matsayin Ali shi ma kafiri ne”. Kuma an riwaito daga Anas Raliyallahu Anhu ya ce: Watarana ina zaune wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai na ga Ali tafe, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ni da wannan da ke tafe hujjar Allah ne akan al’ummata ranar alqiyama”. Kuma an samo daga Mu’awiyah xan Haidah Alqushairi inji xan Shi’ar, cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Ali: “Duk wanda ya mutu yana qiyayya da kai, ya mutu a matsayin Bayahude ko Kirista”.


Martani:

Su dai riwayoyin Akhxabu Khawarizim ba abin da mai hankali zai ce in ya duba su, sai dai ya ce, tsarki ya tabbatar ma Allah! Su kuma waxannan hadisai da malam Zuqa ya kawo ba su ko yi kama da hadissan da ke qamshin gaskiya ba.

Irin waxannan ruvavvun tatsuniyoyi ba su isa su girgiza imanin da musulmi duka ke da shi game da Muhajiruna da Ansar waxanda suka yi wa sayyidina Abubakar mubaya’a ba. Ga su ko Allah gwanin sarki ya tsarkake mana su sau tari a cikin Alqur’ani. Duba yadda ya bayyana mana yardarsa da su inda yake cewa:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭼ التوبة: ١٠٠



Kuma magabatan farko daga Muhajirai da Ansarai da waxanda suka biyo bayansu da kyautatawa, duk Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi. Kuma ya yi masu tanadin Aljanna waxanda qoramu ke gudana a qarqashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan shi ne babban rabo.

Kuma da za mu qaddara cewa, waxannan hadissai na qarya sun inganta. To a kaikaice hakan na tabbatar da suka ne ga shi Ali Raliyallahu Anhu da tabbatar da zamansa kafiri, wanda ya qaryata Allah da Manzonsa, wal iyazu billahi. Kamar yadda ingancin nasu ke kafirta sauran Sahabbai, saboda wai sun yi jayayyar halifanci da shi.

To, mun ji. Amma shi Ali Raliyallahu Anhu bai tava aiki da waxannan hadissan qarya ba, don a wurinsa Sahabbai gaba xaya musulmi ne masu imani. Mafi sharrin waxanda ya yaqa su ne Harijawa, amma kuma bai kafirta su ba. Ya kuwa yaqe su mafi muni yaqi. A maimakon haka ma sai ya haramta dukiyoyinsu da waxanda aka kama daga cikinsu. Kai kafin ma su gwabza yaqin sai da ya gaya masu cewa: “Ba za mu hana ku shiga masallatanmu ba, ba kuma za mu hana ku dukiyar al’umma da ke hannunmu ba”. Kai ba ma waxannan ba, ko Ibnu Muljamu da ya soki Ali kafin ya cika abin da ya ce: “Idan na rayu, ni ke da alhakin jinina”. Amma bai ce masa kafiri ba.

Haka nan waxanda ya shaya daga da shi Ali a yaqin basasar Raqumi, riwayoyi sun tabbatar da cewa ya hana a bi wanda ya juya baya daga cikinsu, ko a ganimanci dukiyoyinsu, ko a ribace qananan yaransu da matansu. Tattare da kasancewar su kafirai idan waxancan hadisai sun inganta. Daga nan za mu san cewa, Ali Raliyallahu Anhu shi ne farkon wanda ya qaryata waxannan hadisai.

Bari ma ka ji, duk waxanda suka shaya daga da sayyidina Ali a yaqin basasar Siffin, bai xauke su kafirai ba. Hasali ma shi ke yi wa waxanda aka kashe daga cikinsu sallah, yana kuma cewa: “Waxannan ‘yan’uwanmu ne da suka yi mana tawaye. Muna fatar takobi ya tsarkake su”. Yana nufin fatarsa ga Allah ya gafarta masu kuskurensu na rashin yi masa mubaya’a albarkacin a zub da jininsu. Ka ga da ya xauka su kafirai ne da bai yi masu sallah ba, ballantana ya ce hakan.

A nan dai ba muna son magana a kan kafircin wani ne ba. Muna son ne a fahimci cewa, duk yadda aka kixa aka kuma raya, waxancan hadisai na nan a matsayinsu na qaryar banza, wadda aka jingina ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. A kuma gane cewa, sun yi ban hannun makafi da addinin musulunci. Wanda kuwa duk ya yarda da su waxannan hadisan to, ya kwana da sanin kafirta gaba xayan Sahabbai har da Ali. Haka kuma wanda ya yi imani da Allah da rana ta qarshe ba zai yarda harshensa ya furta waxannan hadisai yana mai jingina su ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duk wanda kuwa ya yi haka babu shakka ya keta mutunci da alfarmar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Don haka mun tabbata cewa wani zindiqi ne mulhidi ya qaga waxannan hadisai. Allah ya la'ani wanda ya yi wannan xanyen aiki don ya hargitsa aqidar musulmi, ya ci zarafin magabata, waliyyan Allah. Kai wanda ya yi hakan ma qyacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ishe shi inda yake cewa: “Allah ya yi tanadin masauki a gidan wuta ga duk wanda ya yi mani qarya da gangan”.
5.13 Matsayin Hadissan Shi’ah

Xan Shi’ar ya ce: Idan muka ga ‘yan adawa sun riwaito irin waxannan hadisai, to ya wajaba a kanmu mu karve su daga gare su, ballantana ma muna da dubunsu a taska, waxanda muka riwaito daga amintattun malamanmu na hadisi. Haramun ne mu yi kunnen uwar shegu da su.

To, abin da za mu ce a nan shi ne: Ba mu aminta da waxanda ‘yan Shi’ah suka aminta da su a matsayin malaman hadisi ba, Iyakar mariwaitanku su zamo kamar jahilan mariwaitan Sunnah. Kuma tunda har malamai masana sun tabbatar da cewa waxanda suka riwaito waxancan hadisai maqaryata ne, to ba ya ko halatta ga ‘yan Shi’ah su ci gaba da aiki da abin da hadissan suka tabbatar, tattare da kasancewarsu mafiya qarya da jahilci a kan waxancan.

Kuma za mu gitta ma maganarsa tambayoyi kamar haka:

'Yan shi’ah ina kuka samu wata hujja da ke iya tabbatar da cewa waxanda suka riwaito waxannan hadisai a zamanin farko, amintattu ne? Don kuwa babu wani xan Shi’ah na waxannan za munna a yau, da ya riski xaya daga cikin waxancan magabata nasu, ba su kuma san komai na haqiqanin tarihinsu ba; ba su kuma da littafai da ake iya dogara a kansu don banbancewa tsakanin amintattu daga cikin magabatan nasu da vata gari. Haka kuma ba su da wani isnadi da zai taimaka masu ga sanin mazajen riwayoyin. Ta wannan fuska ma Yahudawa da Nasara sun fi ‘yan Shi’ah makama, don abin da ke hannun waxannan na ilimi da ya shafi addininsu, a cikin littafan da Hilalu da Shammas suka rubuta masu, na da kafar shan iska don babu wani abu a hannun sauran mabiyan addininsu da ya sha banban da wancan da ke hannunsu. Savanin 'Yan Shi’ah. Babu wani abu da ke hannunsu face sauran musulmi na da gudumar rosa shi kodayaushe. Su kuwa ba su san komai a kan sauran musulmi ba. Kuma tabbataccen abu ne ta hanyoyi da dama kuma tabbatattu cewa, 'yan Shi’ah maqaryata ne na qarshe, tun zamamim Sayyidina Ali har kawowa yau.

Amma ka ga malaman hadisi a duniyar Sunnah, sun riwaito hadissai daga Harijawa duk da irin qyamar da suke yi ma su, da tarin ingantattun hadissan da aka samo daga wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a kan vacin aqidar Harijawan. Wasu hadissan nasu ma na cikin littafin Buhari A cikin Muslim akwai hadissai goma da ya riwaito daga wurin su. To, ka ga wannan sheda ce daga malaman Sunnah ga Harijawa a kan cewa, duk da bidi’arsu da ake qyama da hadissan da suka bayyana cewa, su halakakku ne, amma ba maqaryata ba ne. Ku kuwa, kowa ya sani, soja da farar hula, cewa cikakkun maqaryata ne. Shi ya sa ba hadisin ko xayanku a ingantattun littafai. Allah ya tsarkake su daga wannan.

Duk mai hankali da adalci ya san haka. Amma duk wanda zuciyarsa ce limaminsa, to, ganin idonsa ba zai yi masa fa'ida ba. Duk kuwa wanda Allah ya vatar babu wani mai iya shiryar da shi.
Zango na Shida

Daga Cikin Dalilan Shi’ah:

Xabi’u Goma Sha Biyu Na Ali

Xan Shi’ar ya ce: Mataki na huxu a cikin dalilan da ke tabbatar da shugabancin Ali, shi ne xabi’unsa da suka nuna cancantarsa waxanda sun kai goma sha biyu.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Aliyu Raliyallahu Anhu ya kasance mafi tsentseni da gudun duniya daga cikin mutanen zamaninsa, ba Sahabbai kaxai ba. Ya kuma fi kowa ilimi da jaruntaka.

Daga nan sai xan Shi’ar ya kawo wasu karamomi da waxansu martabobi na Ali, ya kuma kafa hujja da su a kan kasancewarsa mafifici a kan Sahabbai.


6.1 Zuhudunsa

Ya ce: Martabarsa ta farko ita ce: Gudun duniya. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne kawai ya tsere masa a wannan fage.

Amsarmu a nan ita ce: Wannan magana ba gaskiya ba ce. Waxanda suka san ingantaccen tarihin Sahabbai, sun tabbatar wa duniya da cewa, waxanda suka fi kowa zuhudu na shari’ah daga cikin Sahabbai, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ne Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma.

Dalilansu kuwa su ne: shigar Abubakar Raliyallahu Anhu musulunci ke da wuya ya qaras da gaba xayan dukiyarsa saboda Allah, don dama shi mai arziki ne. bayan kuma ya zama halifa, hakan ba ta hana shi shiga kasuwa don neman abin sakawa bakin salati, shi da iyalinsa ba, ta hanyar saye da sayarwa. Har dai watarana Umar ya haxu da shi xauke da barguna a kansa zai je cin kasuwa. Umar xin ya qalubalance shi a kan haka. Abubakar Raliyallahu Anhu ya karva masa da cewa: Kana zaton zamana halifa zai hana in fita don nemo wa iyalina abinci?. Daga nan Umar ya shawarci Abu Ubaidata da sauran Muhajiruna a kan yanka wa halifa Abubakar albashi daga cikin dukiyar baitulmali. A qarshe aka yanka masa albashin darhami biyu a kowace safiya. Amma duk da haka gogan naka, sai da ya sa Umar da Abu Ubaidata suka sha billahillazi, a kan zaman wannan xan kuxi halas gare shi, sa'annan fa ya fara karva.

Harwayau kuma dai halifa Abubakar bai tsaya nan ba, sai ya haxa hancin dukiyar can tasa gaba xaya ya zuba ta baitulmali. Da ajalinsa ya qarato kuma sai ya umurci 'yarsa Aishah da cewa, kada su ci ko sisi daga cikin albarkar da dukiyar can tasa ta yi a sakamakon zamanta cikin baitulmali. Ya ce wannan kan haqqin musulmi ne. A qarshe, bayan rasuwarsa abin da ya bari gado shi ne, wani gwado, da farashinsa bai kai dirhami biyar ba, da wata kuyanga ‘yar habasha, wadda ke shayar da xan autansa. A wata riwaya aka ce, bawa dai ne Bahabashe aka samu da wani raqumin xibar ruwa, su ne suka zama dukiyar gadonsa. Nan take sayyida Aishah Raliyallahu Anha ta aika da su wurin Umar Raliyallahu Anhu bisa wancan umurni na mahaifinta. Isar dukiyar ke da wuya sai Sahabi Abdurrahman xan Aufu ya ce wa Umar: Ni a ganina bai kamata a raba iyalin Abubakar da wannan dukiya ba. Umar dai ya qi karva yana mai cewa: “Na rantse da Ubangijin Ka'aba tun da Abubakar ya kalli cin wannan dukiya laifi tun yana raye, ba yadda za a yi ko ni in tara kaina gare ta bayan rasuwarsa”.

Bisa wannan dalili ne malamai suka ce: Ko shakka babu Ali Raliyallahu Anhu mai gudun duniya ne, amma gudun duniyar Abubakar Raliyallahu Anhu ya fi nasa. Bisa dalilin kasancewarsa mai tarin dukiya tun farkon musulunci, amma ya ba ta baya, ya miqa ta ga hidimar addini don neman yardar Allah. Ga kuma yadda ya kasance bayan ya zama halifa.

Amma shi kuwa Ali Raliyallahu Anhu kamar yadda xan Zanjawaihi ya ce, talaka ne a farkon musulunci, shi ake taimakawa ba ya iya taimakon kowa. Bayan haka ne ya sami dukiya wadda ta haxa da gonaki da itacen dabinai da sadaqoqi. Kuma ko da ya yi shahada yana da kuyanga goma sha tara da matan aure huxu. Wannan kuma duk halal ne, Alhamdu lillahi. Amma dai bai yi umurni da a mayar da komai daga cikin wannan dukiya zuwa baitulmali ba. Duk da yake babu wata illa a cikin rashin yin hakan don halaliyarsa ce. Bayan rasuwar tasa ne ma xansa Hasan ya gaya wa mutane a cikin wata huxuba da ya yi cewa: Mahaifina bai bar zinari ko azurfa ba. Ya dai bar dirhami xari bakwai. Ko su da ya sami dama da ya yi sadaka da su kamar yadda ya saba.

Kuma Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Na kasance a lokacin rayuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ni kan xaura dutse a cikina, saboda tsananin yunwa. Amma ga shi yau ni kan fitar da kusan dinari dubu Arba'in a matsayin zakka. A wata riyawa aka ce dinari dubu huxu.

Ko alama, ba a haxa Ali da Abubakar Raliyallahu Anhu a fagen gudun duniya, duk da yake dukansu masu gudun duniyar ne.

Shi kuwa Ibnu-Hazmi cewa ya yi: Na ji wasu na cewa, wai Ali shi ne mafi gudun duniya a cikin Sahabbai. Duk wanda ya faxi wannan magana maqaryaci ne, kuma jahili. Dalili kuwa shi ne: Idan dai har gudun duniyana nufin kakkave rai daga sha’awar kaxe-kaxe da waqe-waqe da dukiya, da abubuwan jin daxi, da karkata ga ‘ya’ya da tara fadawa, wanda bani zaton akwai wata ma’ana ga kalmar zuhudu wadda ta wuce wannan. To, idan ta tabbata hakan, to, ta fuskar kakkave rai daga sha’awar dukiya, ko shakka babu halifa Abubakar ne shago a wannan fage.

Duk wanda ke da masaniya da ingantaccen tarihin Sahabbai ya san cewa, ko da halifa Abubakar ya musulunta baya rasa kuxin da suka kai dinari dubu arba’in, amma ya saxaukar da su kacokan saboda Allah. Ya yi haka ne kuwa ta hanyar fansar bayi muminai masu rauni, waxanda kafiran Makka ke azabtarwa, saboda kawai sun yarda da Allah. Kuma bai yi haka ba don su qare shi da komai da qarfinsu, illa dai da zaran ya ga ana azabtar da bawa ko baiwa don sun yarda da Allah Subhanahu WaTa’ala sai ya fanshe su ya ‘yanta su. Haka ya ci gaba da yi, har abin da ya rage hannunsa, a dai dai lokacin da za su yi hijira tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, bai fi dirhami dubu shida ba. Haka Sahabi Abubakar ya qulle waxannan kuxin, ya bi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai bar wa iyalinsa ko anini ba. Qarshenta kuma a can Madinah ya kashe su gaba xaya wajen xaukaka Kalmar Allah. Aka wayi gari Abubakar bai mallaki ko sisi ba, sai wata tsohuwar Abaya da yake fama da ita wadda yake shinfixawa in dare ya yi ya kwanta sama, idan kuma rai ya kai ita zai rufa a jikinsa ya fita neman abinci.

A dai dai lokacin da wasu Sahabbai suka mallaki manya – manyan gonaki da lanbuna da tarin dukiya ta halal. Ka ga sai dai wanda duk ya ba da baya ga irin wannan dukiya ya ciyar da ita wajen xaukaka kalmar Allah, ya fi wanda ya aje wata don Allah, gudun duniya.

Ya ci gaba da cewa: Ko bayan da Abubakar ya zama halifa, tarihi ya tabbatar da cewa bai aje kuyanga ko xaya ba. Bai kuma tara mahaukaciyar dukiya ba. Qarshen ta ma kafin ya rasu sai da ya qiddidiga xan abin da yake karva daga baitulmali a matsayin albashi, don ciyar da iyalinsa, ya yi umurni da a cire kwatankwacinsa daga cikin dukiyarsa a mayar baitulmali. Ita wannan dukiya da yake batun xiba a kai baitulmali, ya same ta ne, ta hanyar tara abin da ake ba shi na ganimar yaqoqan da ya halarta a tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, wanda kuma ya ci gaba da juyawa har zuwa lokacin da ya zama halifa ya fara xaukar albashi.

A irin wannan nau’i na zuhudu ne, na nisantar dukiya da ababen jin daxi halifa Abubakar ya yi wa sauran Sahabbai fintinqau; ba Aliyu ba, ba waninsa ba. Abu Zarri da Abu Ubaidata ne kawai, za’a iya kwatantawa da shi a wannan fage, daga cikin mazajen farko na Muhajiruna don su, sun xore da abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar su a kai na irin wannan zuhudin. Bayan waxannan biyu sai ko halifa Umar shi ma ya kwatanta irin wannan zuhun na Abubakar Raliyallahu Anhu Amma ko alama Aliyu Raliyallahu Anhu bai kai ga Umar ba a wannan fage, balle daxa ga shi uban tafiya, watau Abubakar.

Amma shi kam sayyidina Ali, ya tara dukiya amma ta halal. Ko da ya mutu kuma yana aure da mata huxu, haxe da kuyangi goma sha tara waxanda ke jiran ‘yanci da farin ciki a daidai lokacin da ake kuka da baqin cikin mutuwarsa. Haka kuma ya bar bayi da barori da dama, da ‘ya’ya ashirin da huxu; maza da mata, da dukiya da kayayyaki masu tarin yawa, waxanda magadansa suka samu kansu a cikin sahun manyan mawadata daga cikin attajiran wancan lokacin. Wannan magana ba a voye take ba, ta shahara matuqa, ko ‘yan aji xaya a ilimin hadisi da tarihin musulunci sun san ta. Ina Ali ina Abubakar a wannan fage?!

Ta vangaren abin da ya shafi qalahucin ‘ya’ya da tariyar mabiya. Tarihi ya tabbatar da cewa, tattare da halifa Abubakar nada ‘ya’ya da makusanta irinsu Xalhatu xan Ubaidullahi, xaya daga cikin Muhajiruna na farko kuma na gaba-gaba a sahun ma’abuta daraja da xaukaka a cikin kowane fage a tarihin musulunci. Da kuma irin su xansa Abdurrahman.

Ga kuma irin darajar abokantakar da ke tsakaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama mai daxaxxen tarihi. Da kuma kasancewarsa Sahabin da ya fi kowane Sahabi ladar hijira, qafarsa qafar Annabi. Da kuma sauran darajojinsa waxanda ko rana ba ta fi su zama sarai ba idan ta fito. Amma duk da waxannan muqamai da mata kai da halifa Abubakar ya kevanta da su, bai naxa xaya daga cikin waxannan makusanta nasa, a matsayin gwamna ba, a jahohin musulunci irin su Yaman, duk kuwa da irin faxin da take da shi da tarin aikin yi da ke cikinta. Ga kuma irin Oman da Hadramauta da Baharaini da Yamama da Xa’ifa da Makka da sauran yankunan hijaz. A tsawon halifancinsa, Abubakar bai kai ko xaya daga cikinsu a waxannan garuruwa ba, a matsayin ma’aikaci. Ba kuwa don rashin cancantarsu ba. A’a, ya yi haka ne don saunar talalaviya ta kwashe shi ya kasa tsawata masu saboda kusancinsu zuwa gare shi.

Wannan godabe na Sahabi Abubakar Raliyallahu Anhu shi ne wanda Umar Raliyallahu Anhu ya bi a lokacin da ya zama halifa. Duk da faxin daular musulunci a wannan lokaci, Umar bai kai xaya daga cikin makusantansa, bani Adiyyi xan Ka’abu a matsayin gwamna a ko xaya daga cikin biraren ba, har kuwa da waxanda shi ne da kansa ya ci su da yaqi irin su, Sham da Masar da gaba xayan daular Farisa zuwa khurasana, sai fa Nu’manu xan Adiyyu. Yana cikin dangin sayyidina Umar, da yake qaddara ta riga fata, har Umar ya naxa shi gwamna a Masar, amma kuma tun ba a je ko ina ba ya tuve shi.

Ba kuwa don komai Umar ya qi saka banu Adiyyi cikin sha’anin mulki ba illa zuhudu. Domin idan cancanta ce, babu wata qabila ko zuri’a daga cikin Quraishawa da ta fi su cancanta. Don ko a lokacin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi hijira su gaba xaya suka kwashe, qwansu da kwarkwatarsu suka bi shi, ba su bar kowa daga cikinsu a Makka ba. A cikin waxannan dangi kuwa akwai fitattun magabata, irin su: Sa’idu xan Zaidu, xaya daga cikin Asharatul Mubassharuna Bil Jannah, da Abul Jahmi xan Huzaifa da Ma’amaru xan Abdullahi da Abdullahi xan Umar. Allah ya yarda da su baki xaya.

Irin wannan zuhudu ne harwayau, ya hana halifa Abubakar naxa xansa Abdurrahman a matsayin magadinsa, tattare kuwa da kasancewar xan nasa Sahabi. Haka kuma Umar bai naxa xansa sarauta ba a lokacin da yake raye, bai kuma naxa shi matsayin yarima mai jiran gado ba. Tattare kuwa da shi xan nasa na xaya daga cikin Sahabbai masu daraja kuma zavavvu, ya kuma cancanci halifanci. Kai har ma wasu sahhabai sun fara tattaunawa da amincewa a kan ya gaji mahaifinsa Umar. Ka ga ko naxa shi xin ya yi babu mai tayar da qayar gaba balle ta baya. Amma namijin duniyar bai yi hakan ba.

Amma ka ga shi Sahabi Ali Raliyallahu Anhu naxa shi ke da wuya sai ijtihadinsa ya nuna masa dacewar naxa makusantansa. Ya naxa Abdullahi xan Abbas gwamna a Basra, Ubaidullahi xan Abbas a Yaman, Qusamu a Makka da Ma’abadu a Madina. Duk waxannan qannensa ne su huxu, ‘ya’yan baffansa Abbas. Ya kuma naxa xan yarsa Ummu Hani’i xiyar Abu Xalib a matsayin gwamnan Khurasana. Sai kuma agolansa Muhammad xan Abubakar, ya naxa shi gwamnan Masar. Haka kuma Ali Raliyallahu Anhu ya aminta da mubaya’ar da mutane suka yi wa xansa Al-Hassan a matsayin yarima kafin cikawarsa.

Ba muna musanta cewa, Hassan ya cancanci zama halifa bayan Ali Raliyallahu Anhu ba. Ko kuma kasancewar Abdullahi xan Abbas ya cancanci zama gwamnan Basra ba. Kai, xan Abbas xin ma da an naxa shi halifa ya yi daidai. Amma manufa a nan ita ce, ba ka haxa zuhudun waxanda suka hana ‘ya’yansu da ‘yan’uwansu sarauta alhalin sun cancance ta, da zuhudun wanda ya naxa makusantansa kodayake sun cancanta xin.

Dubi irin Xalhatu xan Ubaidullahi, nagartaccen Sahabi, xaya daga cikin Asharatul Mubassharun Bil Jannah. Ba abin da ya hana Abubakar ya yi masa gwamna in ba don kusancinsu ba. Haka ma Sa’idu xan Zaidu, ko shakka babu ya kai matuqa a fagen dacewa da sarauta, kuma shi ma yana cikin Asharatul Mubassharun Bil Jannah. Amma Umar bai naxa shi ba, don zuciyarsa na cewa, ana barin halas don kunya.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   38   39   40   41   42   43   44   45   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin