6.1.2 Ali Ya Rabas Da Duniya
Xan Shi’ar ya ce: Haqiqa Ali ya saki duniya saki uku. Saboda ya kasance ba ya da abinci sai tsakin alkama, wanda ya kan rufe don kada Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma su zuba masa miya a ciki. Kuma baya da tufafi sai masu kaushi da gajarta. Rigar ma da yake sakawa ta sha dashi har ta gaji, ta yadda har aka wayi gari yana tunanin yadda zai kama ta ya dasa. Haka kuma maxaurin takobinsa da takalmansa duk na tsawo ne.
Xan Shi’ar ya ce: Akhxabu Khuwarizim ya riwaito daga Ammaru wanda ya ce: Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana cewa: “Ya kai Aliyu! Haqiqa Allah ya yi maka wani irin ado mafi soyuwa gare shi, wanda bai tava yi wa wani daga cikin bayi irinsa ba. Ga shi ya dai saka ka mai gudun duniya kuma maqiyinta, ya kuma sanya ka mai qaunar talakawa, wanda hakan ta sa suka yarda da kai a matsayin shugaba kamar yadda ka yarda da su a matsayin mabiya. Ya kai Aliyu! Ka sani farin ciki ya tabbata ga duk wanda ya so ka, ya kuma yi gaskiya a kanka, haka kuma boni ya tabbata a kan duk wanda ya qi ka, ya kuma yi maka qarya. Waxanda duk suka so ka, suka kuma yi gaskiya a kanka su ne ‘yan’uwanka a cikin addininka, kuma masu tarayya da kai a cikin al’amarinka. Su kuwa waxanda suka qi ka, suka kuma yi maka qarya, Allah ya yi alqawarin tabbatar da su a gurbin maqaryata”.
Haka kuma suwaidu xan Gafalata ya ce: Na shiga wurin Ali Raliyallahu Anhu da la’asariyyar nan, na taras da shi zaune ya rungume kwanon madara mai zafi, ta yadda har qanshinta na bugun hancina saboda tsananin gumin da ke fitowa daga cikinta. Yana kuma riqe da gurasa wadda a jikinta nake hangen dusar alkama. Yana yi yana gutsurar gurasar da hannunsa. Idan haka ta buwaya sai ya karya ta da guwayyunsa ya jefa cikin kwanon madarar. Da na shigo sai ya ce mani: matso ka xanxana irin abin da muke kalaci da shi. Sai na ce masa, ai ina azumi ne. Sai shi kuwa ya karva mani da cewa: Na ji manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “Duk wanda azumi ya hana shi cin wani abinci da yake sha’awa, Allah ya yi alqawarin ciyar da shi abincin Aljanna, ya kuma shayar da shi abin shanta”. Daga nan ni kuma sai na juya ga wata kuyanga tasa da ke tsaye wajena, na sassauta murya na ce mata: Amma dai baki kyauta ba ya ke Fiddahatu. Ba ki gudun Allah ya kama ki da alhakin wannan dattijo? Irin yadda kika yi masa gurasa haka da alkama da ba a surfe ba? Sai ta karva mani da cewa: “Wallahi ba laifina ba ne”. Shi ne ya sharxanta mana rashin surfe duk alkamar da za mu yi masa abinci da ita. Sai sayyidina Ali ya ce: Maganar me kake yi da ita? Na gaya masa. Sai ya ce: “Na fanshe shi da uwata da ubana, wanda ba a tava surfe ma abinci ba, bai kuma tava jera kwana ukku yana qoshi da gurasa ba har ranar da Allah ya karvi rayuwarsa”. Ali kuma ya sayi gwado biyu, ya ce Qambar ya zavi xaya, shi kuma ya xauki xayan. Ya kuma ga hannun rigarsa ya rufe yatsarsa sai ya datse hannun rigar.
Haka kuma Dhiraru xan Damrata ya ce: Watarana na shiga wurin Mu’awiyah bayan rasuwarsarkin Musulmi Ali sai ya nemi in ba su labarin siffofin Ali. Sai na ce: Tuba nake Allah ya taimake ka. Sai ya nace a kan lalle sai na yi hakan. Na ce, to, tunda haka ne, Allah ya taimakeka! Na rantse har da Allah halifa Ali sarari ne mai qare gudun doki. Antaru ne sarkin qarfi. Shafe zane ne a fagen magana. Kuma a duk lokacin da zai yi hukunci ya kan yi adalci, marmaron ilimi na vuvvuga dama da hagunsa, kuma harshensa shi ne maqerar hikima. Ya kasance mai qyamar duniya da qawace-qawacenta.
Ya kuma fi miqe qafa da walwala a cikin dare, kuma lokacin da yake shi kaxai. Sarki musulmi Ali ya kasance mutum mai kaifin basira da zurfin tunani, ya fi kuma sha’awar tufafi masu kaushi da abinci maras taushi. Idan muna tare da shi baka iya gane wa ye sarki wa ye bafade? Don babu wata tambaya da za mu yi masa face ya bamu amsarta. Idan kuma muka gayyace shi zuwa gidajenmu ko wata harka zai tafi kamar kowa. Amma wallahi tattare da irin wannan kusanci da muke da shi, da shi, babu xayanmu da ba ya shakkar yi masa magana, saboda kwarjininsa.
Mutum ne mai girmama ma'abuta addini da jawo talakawa a jiki. Ba ya cin zarafin masu qarfi ba ya kuma zaluntar masu rauni. Hakan kuma ba ta sa masu qarfi zaton zai xaure masu gindi a kan varna, ko masu rauni su yanke qauna daga samun cetonsa. Idan rantsuwa da Allah na tava ganin shi yana cewa: “Ya ke duniya! Ki ruxi wani, ni har abada ba ni son ki ba ni qaunarki. Na sake ki saki ukku, wanda babu kome a ckinsu. A sane nake da cewa, shekarunki taqaitattu ne, haxarinki kuma mai yawa ne, rayuwa kuma a cikinki qasqanci ce”. “Kaico! Mun shiga uku.. Ga guzurinmu xan kaxan, tafiyarmu mai nisa, hanyoyinmu na cikinsunqurmin daji”.
Ina kawowa nan, sai Mu'awiyah ya fashe da kuka, yana cewa: “Allah ka yi rahama ga baban Hassan. Wallahi yadda ka siffanta shi xin nan haka yake”. “Ya kake jin baqin cikin mutuwarsa ya kai Dhirar?” Sai na ce masa: “Kamar baqin cikin matar da aka yanka jinjirinta, tana ji tana gani. Kai, irin kukan uwar Musa da ba ji ba gani.
Martani:
Ba mu da ja game da abin da ya shafi gudun duniyar Ali. mun yarda da haka; bamu da wata shakka a ciki. Amma bamu yarda ya fi Abubakar da Umar a wannan fagen ba. Kai ko da waxannan hikayoyi da ya kawo ba su nuna haka.
Amma kasancewar Ali Raliyallahu Anhu ya saki duniya saki uku, mu mun yarda da shi, don gaskiya ne. Kuma wannan maganar ta shahara daga wurinsa. Amma ba ta nuna cewa ya fi duk wanda bai ce haka ba gudun duniya. Domin kuwa Annabinmu da Annabi Isah xan Maryam da wasunsu basu faxi irin wannan magana ba. Tattare da cewa sun fi Ali Raliyallahu Anhu gudun duniya. Hasali ma dai ai ba wajibi ba ne idan mutum na gudun duniya sai ya faxa wa duniya haka da bakinsa, ya ce: “Ni mai gudun duniya ne”. Wanda kuma ya yi qarfin halin faxin hakan ba lalle ba ne ya kasance hakan.
Don haka, wannan maganar da ita da babu duk xaya. Faxar ta bai tabbatar da aiki, rashin faxar ta bai hana samun sa.
Haka kuma cewar da marubucin ya yi wai sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ba ya da abinci sai gayan tsakin alkama. Wannan ma ba ya zama dalili a kan fifikonsa, saboda abubuwa biyu:
Na farko: Ko shakka babu wannan magana qarya ce.
Na biyu: Ko da ta inganta, babu yabo a cikinta. Domin kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne shugaban masu gudun duniya, amma duk abin da ya tari gabansa da shi yake aiki. Bai tava cewa ba ni son wannan ba, ko lalle ne sai an samo mani wancan. Da za a kawo masa naman kaza ko na bisashe, shi zai ci. Kamar yadda idan alawa ko zuma ko wani 'yayan itace ya tari gabansa, da shi zai yi kalaci. Idan ma bai sami komai ba, da yunwa zai kwana.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance idan aka kawo masa abin ci ko abin sha, kowane iri ne, idan yana sha'awarsa zai ci, idan kuwa baya sha'awarsa zai bar shi, ba tare da wani zargi ko suka ba. A sakamakon wannan ne watarana yakan xaura dutse a cikinsa don yunwa. Wani lokaci ma a kanshare wata xaya ko biyu ba a hura wuta gidansa ba.
Kuma kasancewar maxaukan takobin Ali Raliyallahu Anhu da takalminsa na tsawo, kamar yadda xan Shi’ar ya faxa, ba gaskiya ba ne. Koda kuma ya zama gaskiya, to ba abin yabo ba ne a gare shi. Domin kuwa an riwaito cewa, takalmin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na fata ne, maxaukan takobinsa kuma na zinari da azurfa. Kasancewar su mawadata, da yawaitar fata a wurin su na sa qin amfani da ita fatar ya zama ba abin yabo ba. An kuma riwaito Manzon Allah na amfani da takalminta.
Kamar yadda Abu Umamatal-Bahiliyyu ya ce: Haqiqa wasu mutane da ke linzamin doki da tsawo su ke kuma hawan qarqashin dawaki sun ci manyan garuruwa da yaqi. Buhari ya riwaito wannan. Mai maganar na bayyana halin musulmi ne kafin nasara.
Hadisin Ammar da ya kawo dai yana cikin hadissan qarya. Haka ma hadisin Suwaidu xan Gaflata ba daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ba.
Amma labarin tufafin da Aliyu ya saya sananne ne. Labarin Dhiraru xan Dhamrata kuma, an riwaito shi. Sai dai babu wani abu daga cikin ko xayansu da ke nuna cewa, Ali Raliyallahu Anhu ya fi Abubakar da Umar Allah ya yarda da su gudun duniya. Hasali ma, duk wanda ya san tarihin Sayyidina Umar da adalcinsa da zuhudunsa, da yadda ya kauce ma naxa makusantansa ga muqamai da tauye rabon xansa daga cikin arzikin qasa daga na takwarorinsa da ya yi. Haka ita ma ‘yarsa ya rubuta mata qasa ga na takwarorinta. Da irin yadda ba ya shan romo da babge, tattare da kasancewarsa wanda ya rarraba taskokin Kisran Farisa da Qaisar na Roma. Mafi yawan arzikin da Ali ya yi rabo daga cikin sauran na Umar ne. Amma duk da haka, Umar ya rasu ana bin sa bashin dirhami dubu tamanin. Ka ga ta fuskoki da dama, hakan na tabbatar da cewa, Umar Raliyallahu Anhu na gaba da Ali Raliyallahu Anhu wajen gudun duniya. Daman dai shi Abubakar Raliyallahu Anhu a wannan fage, ya zarce su duka.
6.1.3 Zuhudu Bai Zama Hujja!
Xan Shi’ar ya ce: A taqaice, tunda har babu wanda ya kama qafar Ali a zuhudu, balle wanda ya wuce shi, ta tabbata shi ne gwarzo a fagen. Haka kuma na tabbatar masa zama shugaba, don ba ya yiwuwa a gabatar da wanda bai kai shi ba a kan sa.
Martani:
Amsarmu a nan ita ce: Mun riga mun tabbatar da cewa, Ali Raliyallahu Anhu bai fi Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma gudun duniya ba. Wannan kenan, kuma ko da ta tabbata cewa, ya fi sun, to, ai ba lalle ne sai wanda ya shahara a fagen zuhudu ba, ya fi kowa cancanta da shugabanci. Balle kuwa tarihi ya tabbatar da akasin haka, don dukiyar da Ali Raliyallahu Anhu ya mallaka ta tsabar kuxi da kuyangi, da wadda muqarrabansa suka mallaka Abubakar da Umar basu mallake ta ba, haka ma muqarrabansu.
6.2 Yawan Ibadarsa
Xan Shi’ar ya ce: Bayan wannan kuma Ali ya kasance mafi yawan ibada daga cikin mutane. Domin babu ranar da ba ya azumi, babu daren da ba ya qiyamul laili. Shi ne wanda ya koya wa mutane sallar dare da nafilolin rana. Kuma idan aka tara ibadun da yake yi, da addu’oi irin waxanda aka riwaito daga gare shi, ba za a iya qare su ba, sai wani sarki ya ci ya fita. Don bai tava kasa yin raka'a dubu ba cikin kowane dare da yini. Sallar dare ba ta tava wuce shi ba, ko da kuwa daren yaqi.
Kuma wai in ji, xan Abbas ya ce: Na ga Ali Raliyallahu Anhu watarana a fagen fama yana kirdadon rana. Sai na tambaye shi dalilin yin haka. Ya karva da mani da cewa: Ina kirdadon ta ne in gani in ta yi zawali don in yi sallah. Sai na ce masa: Sallah na yiyuwa a irin wannan halin? Shi kuwa ya ce mani: To, ai don tabbatar da sallah muke yaqin.
Ka ga kenan inji xan Shi’ar mawuyacin halin da ake ciki na yaqi bai shagaltar da Ali Raliyallahu Anhu daga tsayar da ibadar sallah a farkon lokacinta ba.
Kuma wai, saboda tsananin kulawarsa da ibada, idan ana son cire wani makami na qarfe daga cikin jikinsa, sai a bari sai ya kabbarta sallah, don da zarar ya fuskanci Ubangiji, to ba ya jin kira ko jifa; duk abin da zai same shi na raxaxi ba ya jinsa, haka kuma dai Aliyun ne Raliyallahu Anhu ya jefi tsuntsaye biyu da dutse xaya, a lokacin da ya yi sadaka da wani abu, alhali yana cikin ruku’i. A kan haka Allah Subhanahu WaTa’ala ya saukar da wata aya. Wai kuma akwai wani lokaci da aka kwashe kwanaki uku da sai an sauke sanwar abinci a gidan Ali Raliyallahu Anhu sai kawai ya rungumi tukunyar ya yi sadaka da abincin baki xaya. A kan haka ne ma Allah ya saukar Suratul Insan wadda ke farawa da:
ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﭼ الإنسان: ١
Haqiqa wata mudda ta zamani ta zo a kan mutum. Suratul Insan:1
Kai babu wani lokaci da yanayi, dare da rana, zahiri da baxini wanda Ali Raliyallahu Anhu bai yi sadaqa a cikinsa ba. Ayar da ta umurci Sahabbai da gabatar da wata 'yar sadaka kafin su gana da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Ali Raliyallahu Anhu ne sanadin saukarta, don tun kafin ta sauka ya yi hakan. Bayin kuma da ya 'yanta sun kai dubu, na qashin kansa. Ya kuma kasance a lokacin da aka sa masu linzamin tattalin arziki yana aikin lebaranci ya bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kyautar jingar.
Xan Shi’ar ya kammala da cewa: Wannan kasancewar ta Ali Raliyallahu Anhu mafi yawan bautar Allah Subhanahu Wa Ta’ala daga cikin mutane, na tabbatar da kasancewarsa mafi cancanta da zama halifa kai tsaye, bayan wucewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Martani:
Duk wanda ya san tarihin Sahabban Manzon Allah, ba ya musun cewa, waxannan labarai qaryayyaki ne kawai aka qirqira. Tattare da haka kuma babu wani abin yabo a cikinsa ga Ali Raliyallahu Anhu kamar yadda muka tabbatar da haka a cikin qaryayyakin da suka gabata.
Abu na farko dai, cewar da ya yi Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu na azumtar kowace rana da sallatar kowane dare, qarya ce yake yi masa. Don faxar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ta inganta inda ya ce: Amma ni, ni kan yi azumi, ni kan kuma sha. Ni kan yi sallar dare, ni kan kuma yi barci. Ina kuma auren mata. Duk kuwa wanda ya bar sunnata baya tare da ni.
Haka kuma Buhari da Muslim sun riwaito a cikin ingantattun littafansu cewa, Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya buga mana qofa, ni da Fatima a wani dare ya ce: Ba za ku tashi ku xan tava sallar dare ba? Sai na ce masa: Ya Manzon Allah! Ai ka san rayukanmu a hannun Allah suke. Idan ya yi nufin za mu tashi, sai ya tayar da mu. Sai ya juya yana buga cinyarsa yana cewa: Kuma mutum ya kasance mai yawan jayayya [ 18:54].
Ka ga wannan hadisi ya tabbatar mana da cewa Ali Raliyallahu Anhu yakan yi barcinsa a wani dare. Don ga shi har abin ya xauki hankalin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ya zo ya qwanqwasa masa qofa don ya tashi, ka kuma ji amsar da ya ba shi, wadda ta sa shi ya koma yana maimaita faxar waccan aya.
Kuma cewar da xan Shi’ar ya yi, daga wajen Ali Raliyallahu Anhu mutane suka kwaikwayi sallar dare, da nafilolin rana. Idan yana nufin akwai waxansu mutane kevantattu da suka koyi wannan ibada daga wajen Ali, to, ai wannan ba abin tinqaho ba ne, don babu xaya daga cikin Sahabbai da wasu mutane ba su koyi irin waxannan ibadu daga wurinsu ba. Idan kuma marubucin na nufin gaba xayan duniyar musulmi a wurin Ali Raliyallahu Anhu ne ta koyi qiyamullaili, to, qaryarsa ta sha qarya. Domin kuwa qasashen da Umar da Usmanu suka ci da yaqi, mafi yawansu, irin su Sham da Masar da qasashen yamma, duk jama’arsu na yin sallolin dare da nafilolin rana, duk da cewa ba su tava haxuwa da Ali ba. Haka kuma sauran Sahabbai suka kasance, duk suna gudanar da waxannan ibadodi tun zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma shi ne ya koya musu su. Amma idan aka ce mutanen Kufa ne, ‘yan Shi’ah, suka koya daga wajen Ali Raliyallahu Anhu, to, ko ba haka abin yake ba ana iya yarda.
Amma dai mu abin da muka sani na haqiqa shi ne mutanen Kufa sun koyi irin waxannan ibadodi ne daga wurin Abdullahi xan Mas'udu Raliyallahu Anhu da wasu Sahabbai, waxanda suka saba da mutanen Kufar, kafin Ali Raliyallahu Anhu ya sadu da su. Kuma ko da shi Aliyu ya isa Kufa, bai taras da su jahillan sallah ba. Mutane ne masu yawan ilimi da riqo da addini tun kafin wannan lokaci. Shi kuwa xan Mas'udu da sauran Sahabbai da ke tare da shi a qufa kafin wannan lokaci na zuwan Ali Raliyallahu Anhu, faxin suna da ilimi da riqo da addini bai ko taso ba.
Cewar kuma da marubucin ya yi wai, addu’oin da aka riwaito daga wurin Ali, na xaukar dogon lokaci kafin a gama su, saboda tsawonsu, wannan ma qiren qarya ne. Don mafi yawan addu’oin ba su da wani isnadi da ke danganta su ga shi Ali Raliyallahu Anhu. Kuma irin matsayin da yake da shi, da yanayin rayuwarsa da ta sauran Sahabbai a wancan lokaci, duk sun sava wa, abubuwan da addu'oin suka qunsa. Kuma ai addu'oin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ne mafificin abin da musulmi zai roqi Allah da shi. Su ne kuma zavavvun mutane daga cikin wannan al'umma na farko da na qarshe ke roqon Allah da su.
Ita ma cewar da ya yi Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu na sallah ra'aka dubu a cikin yini da dare, qarya ce, bata kuma xaukaka darajar Ali da komai ba. Dalili kuwa shi ne, waxannan raka'oi sun yi wa lokacin yawa. Sai fa in ba da natsuwa ake yin su ba. Kuma ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, tattare da kasancewarsa mafi qwazon mutane a wajen bautar Allah, bai tava wuce raka'a arba'in ba. Shiriyarsa kuwa ita ce mafi daidaitar shiriya. Tuna da nauyin jama’a da ya ke bisa kansa, to, yaushe ya sani sukunin yin waxannan raka'oi, ya kama gudanar da shugabancin jama'a da na iyalan gidansa, sai fa idan qoton kurciya ya ke yi. Wannan kuwa irin sallar munafukai ce, wadda Allah ya tsarkake Ali Raliyallahu Anhu daga yin irinta.
A daren yaqin Siffin kuwa, abin da ya inganta daga Ali Raliyallahu Anhu shi ne, ya yi zikirin da Manzon Allah ya naqalta wa Fatima na lokacin kwanciya. Ali ya ce: Tun lokacin da na ji wannan zikiri daga wajen Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ban tava wasa da shi ba. Waxanda ke tare da shi suka ce: Har cikin qurar yaqin siffin? Ya ce: Eh, na tuna shi a qarshen daren, sai na faxe shi.
Haka kuma labarin da xan Shi’ar ya bayar na salon fitar da makamin qarfe daga jikin Ali, shi ma qarya ne. Babu inda aka samu wani qarfe ya tava ratsa jikinsa. Haka zancen sadaka a cikin sallah, duk shegiyar xarin ce. Idan ka kalle ta da idon basira, za ka taras cin mutumcin Ali ne. Domin da ace yin haka abu ne karvavve a idon shari'a, to, da ya zama abin wajabtawa ga musulmi su yi haka. Da kuma an wayi gari musulmi na yin haka, kuma an taras da musulmin wancan lokaci sun yi. Wato, suna sallah suna rabon sadaka. Amma da ya zama ba a samun wani jigon musulmi da ya yarda da yin haka ba, to, mun wadatu da rashin zaman hakan ibada. Kai makaruhi ma ne.
Ita ma dai maganar gabatar da ‘yar sadaka sahunsu guda waccan.
Idan muka koma kan cewar da ya yi, wai Ali ya ‘yanta bawa dubu na qashin kansa. Shi ma wannan qarya ce da ba ta sauraruwa sai ga kidahuman jahillai. Ina Ali Raliyallahu Anhu ya ga bayin qashin kansa da suka kai wannan adadi, ko ma rabi? Wace sana’a ce ya yi ya samu waxannan kuxi? Mutumin da duk rayuwarsa an san inda ta qare wajen taimakon addini, ta fuskar jihadi da sauransu.
Ita ma cewar da malam Zurqe ya yi wai, Ali Raliyallahu Anhu kan yi aikin lebara a cikin tungarsu har ya taimaka wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kuxin jingarsa, qarya ce kamar sauran. Ga dalili:
Na farko: A wancan lokaci babu mai fita daga cikin tungar, balle ya tafi wata. Babu kuma wanda zai xauke shi qwadago ko da ya fita xin. Don mushrikai sun riga sun yi game ta kai a kansu.
Na biyu: Abu Xalib, a wancan lokaci shi ne yake xauke da nauyinsa shi kansa Ali xin.
Na ukku: Nana Khadijah ita ma a wancan lokaci, attajira ce, tana kuma tsaye iya qoqarinta a kan ciyar da dukiyarta.
Na huxu: A tarihi ba a tava jin lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya yi aikin qwadago ana Makka ba. Kuma a wannan lokaci shi, qaramin yaro ne, wanda matsayinsa bai wuce na matashi ko babane ba. Saboda haka yana cikin waxanda ake taimaka wa a cikin tungar. Ko dai ya zan Annabi ke taimaka masa, tun da a hannunsa ya ke, ko kuma babansa Abu Xalib ke xauke da xawamiyarsa. To, ta ina zai taimaka ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a wancan lokaci?
6.3 Fifikonsa a Fagen Ilimi
Xan Shi’ar ya ce: Abu na uku shi ne, kasancewar Ali Raliyallahu Anhu wanda ya fi kowa ilimi daga cikin mutane bayan Manzo Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Amsarmu a nan itace: Ahlus-Sunnah dai ba su yarda da wannan magana ba. Suna kuma hani daga faxinta. Abin da kan malaman Sunnah ya haxu a kai shi ne, wanda ya fi kowa ilimi daga cikin mutane bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne Abubakar, sannan Umar na rufa masa baya.
Wannan maganar ta malaman Sunnah kuwa ba akan ruwa aka gina ta ba. Domin a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama babu wanda ke zartar da wani hukunci, yayi huxuba, ya bayar da fatawa matuqar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na ga wuri, sai Abubakar. Kuma babu abin da ya tava shige wa mutane duhu a addininsu sai Abubakar ya warware masu matsalarsa. Ga ‘yan misalai a gurguje:
-
Sahabbai sun shiga ruxani a kan rasuwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, ya rasu ko bai rasu ba. Abubakar ne ya ba su tabbacin rasuwarsa.
-
Sun kuma shiga ruxani a kan inda ya kamata a rufe shi. Abubakar ne ya bayyana masu inda za a rufe shi; a xakin Aishah Raliyallahu Anha bisa qwaqqwaran dalili.
-
Haka kuma sun shiga ruxani a kan halaccin yaqar waxanda suka hana zakka, Abubakar Raliyallahu Anhu ya bayyana masu halaccin yi haka.
-
Abubakar Raliyallahu Anhu ya bayyana masu ma’anar ayar da ke cewa: Lalle za ku shiga masallacin harami, in Allah ya so kuma masu natsuwa. Suratul Fathi: 127 a lokacin da ba su gane ta ba.
-
Sannan ya bayyana masu manufar maganar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya ce: “Allah ya bai wa wani bawansa zavi tsakanin duniya da lahira”.
-
Shi ne kuma ya fassara masu abin da kalmar “kalalatu” ke nufi a cikin Alqur’ani.
Da wasu abubuwa masu dama ban da waxannan. Kuma a duk lokacin da Abubakar ya yi wa Sahabbai irin wannan qarin haske, babu mai musanta masa daga cikinsu.
Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu kansa, ya kasance yana riwaya daga Abubakar xin kamar yadda wasu daga cikin Sahabbai suke yi. Ya zo a cikin littafai huxu na Sunan daga Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Na kasance a duk lokacin da na ji wani hadisi daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama Allah zai amfanar da ni da abin da ya so ya amfanar da ni, daga gare shi, amma a duk lokacin da wani ya ce min Manzon Allah ya ce: kaza. To, lalle ne in nemi ya rantse kafin in yarda da shi. To, Abubakar ya faxa min, ya kuma yi gaskiya. Abin da ya faxa mini shi ne, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Babu wani musulmi da zai aikata wani zunubi sa’annan ya yi alwala, ya yi sallah raka'a biyu, ya roqi gafarar Allah Ta’ala face Allah ya gafarta masa”.
A taqaice dai, kan malaman Sunnah ya haxu a kan cewa, Abubakar shi ne ya fi kowa tarin ilimi bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Ita kuwa cewar da ya yi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Aliyu ne mafi sanin hukunci a cikinku”. Da cewarsa wai, sanin hukunci na lizimta zama mafi ilimi da addini. To, wannan hadisi bai tabbata daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Don ba shi da wani isnadi da ake iya kafa hujja da shi ta tsayu da qafafunta. Hadisin ma da Tirmidhi da Ahmad suka riwaito ta ingantaniyar hanya ya fi wannan qarfin isnadi, inda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wanda ya fi kowa sanin Halal da Haram daga cikinku shi ne: Mu'azu xan Jabalu.
Idan ma aka yi kyakkawan nazari za a tarar cewa, mu'azun Raliyallahu Anhu Sahabin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa wannan sheda ta naqaltar sanin Halal da Haram, shi ya kamata a ce ya fi kowa iya hukunci daga cikin Sahabbai ba Aliyu ba. Domin kuwa sanin Halal da Haram shi ke sa iya hukunci. Qari a kan haka ma shi ne, ita waccan shedar da xan Shi’ar ya ce Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Ali Raliyallahu Anhu, babu wani daga cikin malamai fitattu da ya riwaito ta, ko da kuwa da isnadi mai rauni, balle ingantacce. Amma sanannen abu ce cewa, waxanda suka riwaito ta shaharrarun maqaryata ne.
Shi kuwa hadisin da ‘yan Shi’ar kan kafa hujja da shi mai cewa: Wai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ni ne birnin ilimi, Aliyu kuma qofarsa”. Ba ya da tushe, tattare kuwa da kasancewar Tirmidhi ya riwaito shi. Ibnul Jauzi ma ya ambace shi a cikin littafensa. Ya bayyana zamansa qarya ta duk hanyoyin aka riwaito shi. Ya kuma qara da cewa, ba ma sai an tafi nesa ba. Ana iya tabbatar da haka, ta hanyar duba gangar jikin hadisin. Domin idan aka ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne birnin ilimi, kuma qofarsa qwara xaya ce tal, hakan za ta rosa addini. Saboda haka kan musulmi ya haxu a kan cewa ba zai yiwu ilimin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zo ma al’umma ta hannun mutum xaya ba. Dole ne ya zo ta hanyar taron jama'a waxanda abin da suka faxa ke iya zama ilimin ga ko da na nesa balle na kusa.
Da ‘yan Shi’ah za su ce mana, idan aka samu mutum xaya “ma'asumi” dole ne a karvi maganarsa. Sai mu ce masu, to, batun tabbatar da ma’asumancin nasa fa? Shi xin ne da kansa zai ba mu tabbacin ma’asumi ne? Wannan matsala ba a kai qarshenta. Don kuwa, ba ku iya tabbatar da cewa, wani imami ma’asumi ne sai ta maganarsa. Maganarsa kuma ana amsar ta ne don yana ma’asumi. To, ya kenan?
A qarshe kuma ko da ta tabbata cewa, birnin ilimi, ba ya da wata qofa sai Ali kawai, to, hakan ba ta tabbatar da zamansa ma'asumi, balle ta tabbatar da ingancin wani abu da zai faxi a kan addini, ta yadda ba za'a iya qalubalantarsa da hujja ba.
A haka dai ta tabbata cewa, wani babban zindiqi ne jahili ya qirqira shi, don zaton haka da ya yi na iya zama yabo ga Ali Raliyallahu Anhu. Dama kuma ta irin wannan hanya ce zindiqai ke sukar lamirin addinin musulunci a kaikaice. Don ai ka ga mutum xaya ne ya bayar da wannan hadisi.
Bari ma ta zancen komai in ka so, karon da wannan hadisi ya yi da tarihi, ya isa tabbatar da zamansa qarya. Domin ai babu wani birni a duniyar musulunci wanda ilimin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai kai gare shi ba. Ba kuwa Aliyu ne ya kai shi duk biranen ba Raliyallahu Anhu.
Dostları ilə paylaş: |