8.1 Wai Abubakar ba Shi da Lafiya
Xan Shi’ar ya ce: na farko: Abubakar ya tava cewa: Ni fa ina da wani iska da yake bijiro mani. Saboda haka idan kun ga na yi aikin hankali, to, ku kama mani. Idan kuwa na kama daji, to ku kevo ni. Xan Shi’ar ya ce, ka ga shugaba ne ya kamata a ce ya kankamta talakawansa. Ba su su kankamta shi ba.
Martani:
Lafazin da aka riwaito daga bakin Abubakar Siddiqu Raliyallahu Anhu cewa ya yi: “Akwai wani Shexani da ke bijiro mani (yana nufin a lokacin fushi). Idan da kuka ga ya bijiro mani, to, ku nisance ni don kar ku ji a jikinku”. Kuma ya ce: “Ku bi ni matuqar na bi Allah. Idan kuwa na sava masa, ban cancanci ku bi ni ba”.
Wannan magana da Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi ita ce mafi girman abin da za a yabe shi da shi. Kamar yadda za mu qara bayani da yardar Allah.
Malamai dai sun bayyana cewa, irin wannan shexani da ke bijiro wa Abubakar Raliyallahu Anhu yana bijiro wa kowane xan Adam a lokacin da ya ke cikin fushi. Saboda haka ne Abubkar ya ji tsoron ya cutar da wani daga cikin talakawansa a irin wannan lokaci. Shi ya sa ya hore su da kama kansu a duk lokacin da suka gan shi a cikin fushi. Kamar yadda aka samu cewa, ya zo a cikin Buhari, daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kada alqali ya yanke hukunci tsakanin mutum biyu alhali yana cikin hushi”.
Wannan hani da Annabi ya yi, na yin hukunci a lokacin fushi, shi ne abin da Abubakar ya yi la’akari da shi; ya qudurta cewa ba zai tava yin hukunci yana fushi ba. Saboda haka ya nemi kada su kusanto shi balle su kawo masa qara, su kuma nemi ya saurare ta a irin wannan yanayi. Wannan kuwa na tabbatar da irin yadda Abubakar Raliyallahu Anhu ke biyayya ga Allah Subhanahu WaTa’ala da Manzonsa.
Babu kuma wani xan Adam da fushi ba ya bijiro wa; har kuwa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayinsa na shugaban ’yan Adamu. A kan haka ma aka riwaito yana cewa: “Ya Ubangiji ka san ni mutum ne; ina fushi kamar yadda kowane mutum yake yi. Saboda haka ina roqon ka yi mani tabbataccen alqawari, irin yadda ka saba, na gafarta wa duk wani mumini da na yi wa ba daidai ba, ta hanyar sosa ransa da wata ‘yar magana, ko sa a yi masa bulala bai ji bai gani ba, a kan fushi. Ka yafe masa ka kuma kusantar da shi zuwa gare ka ranar Qiyama a dalilin haka. Buhari da Mislimu sun fitar da shi a cikin ingantattun littafansu daga Abu Hurairata.
Haka kuma cewar da halifa Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi: Idan na tsaya a kan gaskiya to, ku taimake ni. Idan kuwa na saki godabenta, to, ku yi mani hannunka mai sanda. Wannan magana na nuna cikar adalci da tsoron Allah da Abubakar Raliyallahu Anhu yake da su. Kuma wajibi ne ga kowane shugaba ya yi koyi da shi a cikin haka. Kamar yadda yake wajibi a kan talakawa su taimaki shugabansu a duk lokacin da ya hau godaben gaskiya, su qara masa qwarin gwiwa a kan xa’a ga Allah Ta’ala. Idan kuma ya saki godaben, ya faxa kurakurai, su kamo sandarsa su xora shi a kan gaskiya. Idan ya faxa zalunci da gangan, su hane shi gwargwadon ikonsu. Idan kuwa mai son gaskiya ne irin Abubakar, ba su da wani uzuri da zai sa su bar shi a kan zalunci. Idan kuwa sai an yi hasara mai yawa wadda ta fi zaluncin da suke son hana shi yi, to, ba a ce su tunkuxe qaramin sharri koda za su janyo babba ba. Don haka, sai su qyale shi, su bar shi da Allah, su bari a zauna lafiya.
Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi wai shugaba ne ake da buqatar ya kankamta talakawansa, ba su su kankamta shi ba. Wannan magana na da gyara, ta fuskoki biyu:
1) Abin da muka yarda da shi, shi ne: Dole ne a samu taimakon juna a kan xa’ar Allah da jin tsoronsa, tsakanin shugaba da talakawa. Ba a wayi gari kowanensu na xaure wa xaya gindi a kan varna da shisshigi ba. Ana so ne su kasance tsakaninsu kamar yadda kwamandan runduna yake da dakarunsa. Kamar kuma yadda limamin sallah da jagoran hajji suke da mabiyansu. Tunda kuwa har Manzo ya riga ya iyar da manzanci; addinin musulunci ya kammala ya yaxu ta fanninsa, kuma duk wanda zai kasance shugaba a kan musulmi, ba da wani sabon addini zai jagorance su ba, ka ga shi da su kowa na da buqata da juna.
Neman sanin gaskiya wajibi ne a cikin kome, a manyan mas’aloli da qanana. Don haka, da shi da su sai su qoqarta. Idan hukunci ya bayyana an huta, sai a yi aiki da shi. Idan kuwa shugaban ne ya riga fahimtar mas’alar, to, sai ya bayyana masu. Su kuwa lalle ne su saurare shi. Idan kuwa aka yi kunnen doki; kowa bai gane ba, to sai su taru a teburin shawara har Allah ya yi masu gamo da katar.
Idan aka yi sa’a ana cikin haka, wani daga cikin talakawan ya gane bakin zaren mas’alar, to, sai ya bayyana wa shugaban. Idan kuma aka sami banbancin ijtihadi tsakaninsu da shi, to nasa ne abin rinjayarwa da xauka. Don kuwa ba ya halatta su tashi baran-baran.
2) Maganar da sayyidina Abubakar ya yi a kan sha'anin shugabanci, ta qara masa girma da xaukaka a idon al'umma. Tarihi ya tabbatar da cewa wannan al'umma ba ta girmama mahaluki ba, bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama irin yadda ta girmama Abubakar Raliyallahu Anhu. Ba ta kuma yi wa wani xa'a ba kamar yadda ta yi masa. Al'ummar kuwa ta yi wa Abubakar wannan xa'a ne don qashin kanta; ba don wani abu da suke kwaxayin samu ko suka samu daga gare shi ba, ko wani zalunci da suke tsoron ya far masu daga gare shi.
Dama a duk lokacin da jama'a suka yi mubaya’a ga shugaba a qashin kansu, kamar yadda Sahabbai suka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a qarqashin bishiya. To, za ka taras sun yarda da girmansa da cancantarsa. Wannan shi ya sa a duk lokacin da wani xan canjin yawu ko wata tankiya ta shiga tsakanin Sahabbai, a zamanin halifa Abubakar Raliyallahu Anhu a kan wata mas'ala ta addini, to, da zarar ya shiga ciki ya yi masu bayani, za su saurare shi, su kuma miqa wuya ga hukuncin da ya yanke. Abubakar Raliyallahu Anhu ne kuma kawai ke da irin wannan matsayi, sai ko Umar da ya rufa masa baya, da Usman da ya rufe qofar.
Amma ka ga Ali Raliyallahu Anhu ba kaxan ya kai ruwa rana da su ba; ya yaqe, suka yaqe shi. A qarshe kuma ba wanda ya tayar da doron bayan wani. To, wane shugaba ne daga cikinsu ya karva cikakken sunan shugaba? Wane ne daga cikinsu ya samu damar tsayar da addini, ya dawo da murtaddai bisa godabe, ya yaqi kafirai, kuma muminai gaba xaya suka karve shi? Na bar maka amsar.
Ko shakka babu, ba wanda zai daidaita waxannan shugabanni da wancan sai mai tayayyen hankali da raggancin addini.
8.2 Wai Mubaya’ar Abubakar ba ta yi ba
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta biyu ita ce maganar Umar da ya ce: “Mubaya’ar da aka yi wa Abubakar ta kasance girshi ce, amma Allah ya kare musulmi daga sharrinta. Kuma duk wanda ya sake yin irinta ku kashe shi”.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Cewar da Umar ya yi "ta kasance girshi ce" yana nufin ba da son mutane aka yi ta ba. Kuma ya ce Allah da ya kare musulmi daga sharrinta. Sannan ya yi umurni da a kashe duk wanda ya sake yin irinta. Wannan ka ga yana wajabtar da suka ga Abubakar.
Martani:
Abin da Umar ya faxa yana cikin Buhari da Muslimu, wanda aka riwaito daga xan Abbas, a cikin wata huxuba da inda yake cewa: “Na sami labarin wasu na cewa: Wallahi da zaran Umar ya mutu ni ga wanda zan wa mubaya’a. To, kada wani ya kuskura ya yi hujja da cewa, an wa Abubakar mubaya’ar a kan girshi. Ba shakka haka ne. Amma kuma Allah Ya kare musulmi sharrinsa. Yau kuma daga cikinku babu wanda mutane ke iya danqa kansu gare shi kamar Abubakar. Duk wanda ya kuskura ya yi mubaya’a ga wani mutum ba tare da shawarar sauran jama'a ba sai ya gwammace bai yi ba, don su duka za a kashe su; da shi da wanda ya wa mubaya’a”.
Sannan sai Umar ya soma ba da labarin yadda aka wa Abubakar xin mubaya’a bayan cikawar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.. A ciki yake cewa: “... Sai Abubakar ya ce: Na yarda ku zavi xaya daga cikin waxannan mutane, ku yi masa mubaya’a. Da faxin haka sai ya kama hannuna da na Abu Ubaidata, muna a tsakiyarsa. Duk abin da ya faxi bai dame ni ba sai wannan. Don wallahi na fi son a sare kaina, - in ba zunubi - a kan in shugabanci mutanen da Abubakar yake cikinsu. Wannan shi ne tunanina a wancan lokaci. Kuma har yanzu haka nake ji, ban san abin da rai zai yi tunani kafin mutuwa ba.”
Ma'anar wannan magana ta Umar shi ne mubaya’ar da aka yi wa Abubakar Raliyallahu Anhu ta zo ne kwaram, ba tare da wani shiri a kanta ko quduri da aka tsara ba. Kamar yadda shi Umar xin ya faxa da bakinsa. Kuma yanayi ne kawai ya wajabta zaven Abubakar a lokacin da aka yi shi ba don an shirya hakan ba. Mutane ne kawai suka taru, suka kuma yi masa ita. Saboda sun san ya fi kowa cancanta da ita a lokacin. Ba ni kuma sa ran akwai wani mutum da jama'a za su taru su tabbatar da cancanta da dacewarsa irin yadda suka taru a kan Abubakar. A kan haka duk wanda ya nemi yi wa wani mutum mubaya’a ba tare da yardar sauran musulmi ba, ya jawo rarraba mai wajabta a kashe shi.
Kuma Umar ba addu’a ce yake yi, Allah ya kare musulmi daga sharrin mubaya’ar ba. Yana ba da labari ne cewa, Allah ya kare, ba abin da ya faru don an yi ta ba shiri. Kuma kan malamai ya haxu a kan haka.
8.3 Wai Halifofi Uku Jahilai ne!
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta uku ita ce, qarancin ilimin halifofi uku kafin Ali, ta yadda har suke dogara gare shi a cikin mafi yawan hukunce-hukunce.
Martani:
Babu shakka wannan magana na xaya daga cikin manya-manyan qaryace-qaryace. Don ba a tava jin lokacin da Abubakar ya nemi qaruwa da wani abu na ilimi daga Aliyu ba. Hasali ma Ali ne ta tabbata ya yi karatu wurin sa. Don ga riwayarsa nan daga Abubakar xin a cikin littafai ana karantawa.
Haka kuma qaruwar da Ali Raliyallahu Anhu ya yi da Umar ta fuskar ilimi ta fi wadda Umar ya yi daga gare shi. Shi kuwa Usman duk da kasancewar tarihi ya tabbatar da cewa, bai kai ilimin Abubakar da Umar ba, amma bai tava buqatuwa zuwa ga Ali ba a cikin wata harka ta ilimi. Akwai ma lokacin da wasu mutane suka kai qara ga Ali game da ma'aikatan zakka na wasu gwamnoni a zamanin Usmanu. Sai shi Alin ya aika wa Usmanu Raliyallahu Anhu da littafin da ke magana a kan Zakka. Sai Usmanu ya ce a koma masa da shi. Don bamu da buqata da shi.
Wannan magana ta Usmanu kuwa gaskiya ce. Domin Kuwa faralin zakka da yadda ake fitar da ita, da kuma rabonta duk ta hanyoyi huxu aka same su. Hanyar da ta fi kowace inganci daga cikinsu ita ce takardar da sayyidina Abubakar Raliyallahu Anhu ya rubuta wa Anas xan Maliki sadda ya sa shi wannan aiki. Tana cikin littafin Buhari. Kuma da ita ne mafi yawan malamai suke hujja. Hanya ta biyu kuwa itace, littafin Umar.
Amma littafin da aka riwaito daga Ali Raliyallahu Anhu wanda shi ne na ukku, akwai abubuwa a cikinsa da babu wani malami da ya karve su. Kamar cewar da ya yi: Zakkar awaki ashirin da biyar ita ce, xaya bisa biyar 1/5 na akuya. Ko shakka babu wannan hukunci yayi ban hannun makafi da abin da ya zo ta hanya mai cikakken inganci (tawaturi), daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Saboda haka, wannan abu da aka riwaito daga Ali ko dai ya kuskure ne, ko an shafe shi.
Littafi na Huxu shi ne littafin da Amru xan Hazmu Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rubuta masa shi ne a lokacin da ya aika shi zuwa Najrana.
Kuma littafin Abubakar Raliyallahu Anhu shi ne na qarshe a cikinsu. To, ya mai hankali zai ce ga Ali ne suke komawa wajen warware matsalolin ilimi? Ai ko alqalan da Ali ya naxa irin su Shuraihu da Abidatus-Salmani da makamantansu suna shari’a ne da abin da suka sani kuma suka karanta na ilimi ba sai daga wajen Ali Raliyallahu Anhu ba.
8.4 Kuma Wai Halifofi Sun yi Abin Kunya!
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta huxu ita ce abubuwan da, waxannan halifofi suka aikata na abin kunya waxanda muka riga muka anbaci mafi yawansu.
Martani:
Mu ma ai mun riga mun mayar da martani a kan waxannan zarge-zarge a dunqule da kuma xaixaice. Kuma mayar da martani game da zargin waxannan halifofi uku, ya fi sauqi da samun karvuwa ga masu ilimi da hankali, bisa ga mayar da martani a kan masu zargin Ali Raliyallahu Anhu. Kuma duk wanda ke da ilimi da adalci, ya kuma yi la’akari da bayanan da muka yi a baya, ba zai yi gangancin sukar waxancan Sahabbai ya wanke Ali Raliyallahu Anhu ba, a cikin gaba xaya matsalolin. Duk kuwa lokacin da ya yi qarfin halin tsalkake Ali da wanke shi, to, za ka tarar, waxancan halifofi uku sun fi cancanta da wannan wankan tsalki a kan sa. Kamar yadda a duk lokacin da ya ci zarafinsu, duk mai basira zai fahimci cewa cin zarafi ya fi dacewa da Ali Raliyallahu Anhu in har yana dacewar.
Kuma harwayau da ‘yan Shi’ah za su ce sun kakkave hannayensu daga waxancan soke-soke da cin zarafi da suka yi wa halifofin can dattijai, to su sani soke-soke da cin zarafin da suka yi wa Ali Raliyallahu Anhu na nan tabbace, ba za su kuvuta daga gare su ba. Idan kuma sun ci gaba da rungume maganganun na sukar halifofin, hakan ba za ta rage halifofi da komai ba. Don mun riga mun bayyana kasancewar su qarya, mun kuma walwale ta da gaskiya.
8.5 Wai Halifofi Uku Sun Bauta ma Gumaka
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta biyar itace faxar Allah Ta’ala da ya ce:
ﭽ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﭼ البقرة: ١٢٤
Alkawarina ba zai sami azzalumai ba [2:124]
Wai Allah Ta’ala na nufin alqawarinsa na halifanci ba zai je ga hannun azzalumai ba. Duk kuwa kafiri azzalumi ne, domin Allah Ta’ala ya ce a wani wurin:
ﭽ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﭼ البقرة: ٢٥٤
Kuma kafirai sune azzalumai [2:254].
Martani:
Sanannen abu ne cewa addinin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kai da ma sauran Annabawa da Manzannin da Allah ya aiko, sun zo da cewa, ingantaccen imani na share gaba xayan zunubai da ma kafirci idan imanin ya biyo bayan sa. Kamar yadda Allah Ta’ala ya ce: Ka ce wa waxanda suka kafirta idan sun hanu, za a gafarta musu abin da ya riga ya shige [8:38]. Kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa a cikin hadisi ingantacce: “Lallai ne musulunci na karkare abin da ke gabaninsa”. A cikin wani lafazin kuma cewa yayi: “Musulunci na rosa duk abin da ya kasance gabaninsa. Kuma Hijira na rosa duk abin da ya kasance gabaninta. Kuma Hajji na rosa duk abin da ya kasance gabaninsa”.
A tantagaryar gaskiya ba duk wanda aka haifa da layar musulunci a wuya ba ne, ya fi wanda ya musulunta da kansa girman daraja. A’a, ai nassoshi masu tarin yawa sun tabbatar da cewa, mafi alhairin mutane su ne waxanda suka rayu zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kuma mafi yawansu, sun shiga musulunci ne bayan a da sun kasance kafirai. Amma tattare da haka sun fi qarni na biyu; waxanda aka haifa cikin musulunci, girman daraja a wurin Allah. Amma ‘yan Shi’ah ba su yarda da hukuncin da Allah Ta’ala da Manzonsa suka yi a wannan mas’ala ba, kuma kan magabata ya haxu a kai, hankullan masu hankali suka karva. A wajen ‘yan Shi’ah Azaru (mahaifin Annabi Ibrahimu) ya yi imani. Haka mahaifan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kakanninsa, da baffansa Abu Xalib duk sun yi. A daidai lokacin da suke kafirta waxanda suka yi imani da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama imani na gaskiya kuma suka saxaukar da rayukansu a bayansa.
Kafin Allah Ta’ala ya aiko Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama babu wani mutum daga cikin Quraishawa da yake mumini; mazansu da mata, manya da qanana, halifofi ukku da shi Alin kansa. Duk ba muminai ba ne a wannan lokacin. Ba ta yiwuwa kuwa a ce manyan mutane kawai ke bautar gumaka daga cikinsu. Yaran ma, Aliyu da takwarorinsa duk ita suke yi.
Kan musulmi ya haxu a kan cewa, duk wanda ya dubi musulmi ya ce masa kafiri, bisa dalilin cewa ai kafiri ne kafin wannan rana. To, irin wannan mutum shi ne kafirin. Wannan kenan. To, balle daxa wanda ya dubi mafi xaukaka daga cikin halitta ya ce masu kafirai, ta la’akari da tsohon tarihinsu. Wal’iyazu billahi.
8.6 Wai Abubakar ya Nemi Yin Murabus
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta shidda ita ce cewar da Abubakar ya yi, ku yi mani murabus don ba ni ne mafi alheri daga cikinsu ba. Inji shi.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Da ta tabbata Abubakar imamu ne, da bai nemi a yi masa murabus ba. Don faxin haka ba ya halatta gare shi.
Martani:
Kamata ya yi marubucin ya bayyana ingancin wannan magana. Idan kuwa ba zai iya ba, to ya sani ba duk abin da aka riwaito ne gaskiya ba. Kuma saqar duk da aka kitsa a kan zance da bai inganta ba, ita ma hakan.
Abu na biyu: Idan ta tabbata cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu ya faxi wannan magana, babu mai ikon ce masa don me? Domin kuwa babu wani dalili da zai hana a yi masa murabus xin matuqar ya nemi hakan don wani dalili na qashin kansa. Mu dai ba mu da wata masaniya a kan ya nemi murabus ko bai nema ba, balle mu ga wurin vata lokaci a kan wannan batu.
8.7 Kuma Wai Abubakar ya yi Nadama!
Xan Shi’ar ya ce: Dalili na bakwai shi ne abin da Abubakar ya faxa a lokacin rasuwarsa cewa: Da ma dai a ce na tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko Ansaru na da haqqi a halifanci?
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Wannan na nuna cewa, shi kansa Abubakar na jin mubaya’ar da aka yi masa haramtatta ce. Ko banza kuma shi ne fa wanda ya rufe bakin Ansaru a ranar Saqifa, lokacin da suka ce, a naxa halifofi biyu; xaya daga cikinmu, xaya kuma daga cikinku. Sai Abubakar ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Kada a wuce Quraishawa a zaven shugabanni.
Martani:
Gaskiya ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Kada a wuce Quraishawa a zaven shugabanci. Amma duk wanda ya ce Abubakar siddiqu ya yi kokwanton wannan magana, ko wai bai natsu da shugabancin da aka zave shi yi ba, haqiqa ya fesa qarya.
Haka kuma duk wanda ya ce wai, Abubakar Raliyallahu Anhu ya ce: ya yi nadama a kan bai tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama matsayin Ansaru a cikin halifanci ba, shi ma haqiqa maqaryaci ne. Tarin nassosan da ake da su a tarihin musulunci, a kan wannan matsala, waxanda kuma suka inganta daga bakin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba za su bari Sahabbai su yi kokwanton wani abu a cikin al’amarin ba. Balle har wani daga cikinsu yayi da-na-sanin wani abu a kai.
Wannan na tabbatar da kasancewar wannan riwaya ba gaskiya ba.
8.8 Wai Abubakar ya Faxa Gidan Fatima ba Sallama!
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta takwas ita ce, abin da Abubakar ya faxa lokacin da yake jinyar ajali: “Wai ni kaina! Da na sani da ban faxa gidan Fatima ba sallama ba. Da kuma lokacin da muke gidan bani Sa’idah na kuma hannun xayan mutane biyu, ya zama shugaba in zama wazirinsa”.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Wannan magana na tabbatar da cewa, lalle Abubakar ya faxa gidan Fatima, lokacin da Sarkin Musulmi Ali Raliyallahu Anhu da Zubairu da wasu Sahabbai ke ganawa a ciki.
Martani:
Babu wata sukar lamiri da za ta karvu, sai idan lafazinta na da isnadi ingantacce, a kuma taras da sukar a cikinsa varo–varo; ba sai an yi lalabe da tawili ba. Idan xayan waxannan sharuxxan suka kasa samuwa a cikin lafazi, to, ba maganar suka a cikinsa sai dai wani abu.
Ahlus-Sunnah na da yaqini da masaniyar cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu bai cutar da Aliyu da Zubairu Raliyallahu Anhu da komai ba. Kai ko Sa’adu xan Ubadata, Sahabin da ya qi yi wa Abubakar mubaya’a, bai haxu da wata cutarwa daga Abubakar ba.
Qololuwar abin da masu faxa suka faxa shi ne, wai, Abubakar Raliyallahu Anhu ya leqa gidan Fatima ba da izini ba da nufin ya ga ko akwai wata dukiya ta musulmi a ciki, don ya xanka ta ga waxanda suka cancanta. Daga baya kuma yayi tunanin cewa, ko barin su aka yi da ita daidai ne, don ya halatta a ba su wani abu daga dukiyar gwamnati. Amma babu wani mai hankali da ilimi, da ya ce Abubakar ya faxa gidan har ya cutar da waxancan bayin Allah kai tsaye. Wannan magana ce irin wadda jahillai da maqaryata ke yawo da ita, jahillan masana kuma na gasgata su. Irin waxanda ke yayata cewa, wai Sahabbai sun rosa gidan Fatima, suka dake ta a ciki har ta faxi.
Gaba xayan musulmi kuwa, sun haxu a kan cewa, duk waxannan maganganu shaci-faxi ne kawai, irin waxanda sai idan an xauki mutum a matsayin dabba, sannan ne ake tallata masa su.
Kuma marubucin ya manta ya faxa mana isnadi tare da ingancin cewar da ya yi wai, Abubakar Raliyallahu Anhu ya yi fatar ba a yi masa mubaya’a ba. To, idan ma ta tabbata cewa ya faxi hakan, to kuwa alama ce ta irin zuhudu da tsentseni da tsoron Allah da yake da su.
8.9 Wai Halifofi Sun Fice Daga Rundunar Usamatu!
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta tara ita ce: Cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi watarana: Ku shirya rundunar Usmatu. Ya daxa maimatawa tare da qarfafa son ganin an aiwatar. Kuma daga cikin waxanda ya umurta da tafiya a cikin rundunar wai, akwai Abubakar da Umar da Usmanu. Amma kuma wai bai Umarci Aliyu Raliyallahu Anhu da hakan ba. Ya kuma yi haka ne don hakan ta ba Aliyun damar zama halifa bayansa, ba tare da waxancan Sahabbai uku sun hana shi ba, tunda ba su nan. Amma kuma wai ba su bi umurnin ba, inji xan Shi’ar.
Martani:
Muna son marubucin ya tabbatar mana da ingancin wannan riwaya. Don babu wanda ya riwaito da isnadi sananne. Babu kuma wani daga cikin masana riwaya da ya inganta ta. Kuma sanannen abu ne cewa, ba a kafa hujja da riwayoyi, sai bayan an gama gane ingancinsu. Idan kuwa aka ce ba za a tsare mutuncin wannan qa'ida ba, to kowa fa na da baki yana kuma da ra'ayi.
Malaman riwaya kam sun haxu a kan cewa, wannan magana qarya ce. Domin kuwa Abubakar da Usmanu ba su kasance cikin rundunar Usamatu ba. Wanda kawai ake jin ya kasance cikinta shi ne Umar Raliyallahu Anhu.
Kuma dalilai mutawatirai sun tabbata daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, ya halifantar da Abubakar ya ci gaba da ba Sahabbai sallah. Haka Abubakar xin ya riqe wannan aiki har Allah ya yi wa Manzon Allah rasuwa. Shi ne kuma ma ya jagoranci sallar safe, a ranar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama zai rasuwa. Yana cikin bayar da sallar, sai Manzon Allah ya xaga labulen qofarsa ya kalli Abubakar Raliyallahu Anhu gaban sahu, ya yi murmushi ya koma. To, ya za a ce bayan wannan nauyi da ya xora masa, kuma ya umurce shi da biyar rundunar Usamatu?
Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi nufin naxa Ali Raliyallahu Anhu a matsayin Yarima mai jiran gado, waxannan Sahabbai uku ba za su musa masa ba. Da kuma qaddarar Allah za ta sa su yi masa musu, da sauran Sahabbai sun shawo kansu. Don gaba xayansu ba su saba da savawa ko bari a sava wa umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Ba ka ganin aqalla kashi xaya cikin uku na musulmi sun tallafa ma Ali wajen yaqar da ya yi ma Mu’awiyah alhalin ba shi da wani nassi da ya sa shi yin haka? Ya kake zato da Ali na da nassi na zama halifa tun farko, amma waxancan suka amshe masa? Nawa ne daga cikin Sahabbai za su mara masa baya a wannan hali?
Da kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na nufin Ali Raliyallahu Anhu ya gaje halifarsa bayan wucewarsa, to, da kuwa shi zai danqa wa limancin sallah, tun yana raye. Amma bai yi haka ba. Sai ya danqa ma Abubakar Raliyallahu Anhu. tana da wuya ma ya yi haka don bai tava sa Abubakar qarqashin Aliyu ba.
8.10 Wai Abubakar Bai Tava Jagoranci a Zamanin Manzon Allah ba!
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma ita ce kasancewar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava shugabantar da Abubakar a kan kulawa da wani aiki ba. Sai dai ya shugabantar da wani a kansa.
Martani:
Wannan magana ba gaskiya ba ce. Ai ma shugabancin da Annabi ya sa Abubakar Raliyallahu Anhu babu wanda ya tava sa wa yin irinsa a tarihi, wato jagorancin aikin hajji. Ya kuma sa shi wani shugabancin ba wannan ba.
Malaman Sunnah da na Shi’ah gaba xaya sun haxu a kan masaniyar cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tava shugabantar da waxansu Sahabbai; waxanda darajarsu ba ta kai ta Abubakar ba, irin su: Amru xan Asi da Walidu xan Uqbata da Halidu xan Walidu. Ka ga haka na tabbatar wa mai hankali cewa, kodayake Manzon Allah bai naxa Abubakar gwamna a wani yanki na musulmi ba, amma bai yi haka don darajarsa ba ta kai ta waxannan da ya naxa ba.
Rashin naxa sarauta ba ya nuna shi ba wata tsiya ba ne. Wa ya sani ko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi haka ne, don zamansa tare da shi zai fi amfani ga shi Annabin, bisa ga a ce yana can wata nahiya? Kuma yadda yake da buqata da shi a nan Madina, ta fi yadda yake da ita gare shi, idan yana can wurin sarauta. Kuma ai Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma matsayin mataimaka suke ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Ka ga ba buqatar su yi nisa, don da su ne ake xinkin duniyar musulunci.
Dostları ilə paylaş: |