Tafarkin sunnah


Wai Manzon Allah ya Tuve Abubakar Daga Amirul Hajji!



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə48/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51

5.11 Wai Manzon Allah ya Tuve Abubakar Daga Amirul Hajji!

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha xaya ita ce, tuve Abubakar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi daga aikin sa da ya yi ya isar da Suratu Bara’ati, ya maye gurbinsa da Ali.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Ka ko ga duk wanda ya kasa iya xaukar nauyin isar da sura xaya ko sashenta, ya za a yi ya dace da shugabancin qoli, wanda ya tattara nauyin isar da hukunce-hukunce zuwa ga gaba xayan al'umma?!
Martani:

Kan ma'abuta ilimi ya haxu a kan cewa wannan magana qarya ce.

Yadda al'amarin yake kuwa shi ne: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya naxa Abubakar Raliyallahu Anhu don ya jagoranci aikin hajjin shekara ta tara. Bai kuma tuve shi ba, shi kuma bai dawo don qashin kansa ba kafin a qare. Ya jagoranci aikin a shekarar kamar yadda aka umurce shi, kuma Ali Raliyallahu Anhu na xaya daga cikin tawagarsa; a bayansa yake sallah, ba ya wani motsi sai da izinin Abubakar xin. Idan kuma ya hana shi qetara kara ba zai yi ba, ko ba ya kusa. Haka kuwa sauran waxanda ke tare da shi suka kasance.

Wannan shi ne sanannen abu kuma mutawatiri a wurin ma'abuta ilimi. Ba a sami ko da mutum biyu daga cikinsu ba, waxanda kalmominsu suka sava a kan cewa Abubakar ne Raliyallahu Anhu ya jagoranci wannan aikin a wannan shekara. To, ta yaya yau da rana tsaka wani zai gaya mana cewa wai an tuve shi?

Gaskiya ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tura Ali ya iske Abubakar Raliyallahu Anhu can don ya shedi warware alqawarin da ke tsakanin musulmi da mushrikai. Dalilin yin haka kuwa shi ne, babu lokacin da za su qulla ko su kwance alqawari da wata qabila daga cikinsu, face akwai wani mutum daga cikin qabilar wanda zai tabbatar da haka, kuma ba su yarda da waqilcin kowa.

Babu shakka wannan xan Shi’ar, kamar sauran malamansa, sun fi kowa jahiltar tarihin Manzon Allah da abubuwan da suka tuzgo daga gare shi na qashin kansa, da waxanda yau da gobe ta wajabta masa. Alhali kuwa ko kurtu a fagen ilimin tarihi ya san waxannan abubuwa, don inganci da bayyanarsu ya kai matuqa. Amma duk da haka sai ‘yan Shi’ah su yi wa al'amurran shan koko; su rage abin da suke so, su qara wanda suke so.

Duk da yake shi wannan xan Shi’ar sawun varawo ne ya taka; ko da aka haife shi shehunansa sun riga sun yamutsa hazo a fagen tarihin musulunci. Shi kuma da ya zo sai kawai ya hau ba tare da ya tankaxe ya rairaye ba, balle ya kai ga tsagwaron gaskiyar da ma'abuta ilimi manya da qanana suka sani a yanke.

Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi, shugabancin qoli ya tattara nauyin isar da gaba xayan hukunce-hukunce ga al'umma, magana ce vatatta. Ai al'umma sun riga sun gama naqaltar hukunce-hukuncen addini daga bakin Annabinsu Sallallahu Alaihi Wasallama. Ba wata buqata da suke da ita ga shugaba, face irin wadda suke da ita ga malamai takwarorinsa. Babu kuma wani daga cikin musulmi da ba zai iya isar da saqon wata sura ta Alqur’ani daga Manzon Allah ba, balle a ce Sahabi guda irin Abubakar Raliyallahu Anhu wai bai isa a sa shi isar da irin wannan saqo ba. Ba ya kamata, balle ya halatta, wani ya zaci cewa, ba wanda Annabi ke iya aikawa ya isar da saqon wata sura ta Alqur’ani sai Ali. Ai riwayar wani sashe na Alqur’ani ba ta tabbata da inganta sai ta hanya mutawatira. Amma kasancewar an ji shi daga bakin mutum xaya, ba ta wadatarwa.


8.12 Kuma Wai Umar Bai Iya Hukunci ba!

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha biyu ita ce, cewar da Umar ya yi: Lalle Muhammadu bai mutu ba. Wannan na nuna irin qarancin iliminsa. Ya kuma tava yin horo da jefe wata mata mai ciki. Aliyu Raliyallahu Anhu ya hana zartar da hukuncin. Sai umar ya ce: “Ba don Aliyu ba da Umar ya halaka”. Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, akwai hukunce-hukunce da dama da Umar ya yi kwava a cikinsu.


Martani:

Ya tabbata a cikin Buhari da Muslimu cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Haqiqa kowace al'umma da ta gabace ku na da waxanda ake labarta ma a cikinta. Idan akwai wani xaya a cikin al'ummata to Umar ne”.

Annabi bai yi wa Ali Raliyallahu Anhu irin wannan sheda ba.

An kuma riwaito yana cewa: “Na yi mafarkin an zo mani da wani qoqo da ke xauke da nono, na sha har na ga kamar yana vuvvuga ta qunbar hannuna. Sai na ba wa Umar sauran abin da ya rage”. Sai Sahabbai suka ce: Da me ka fassara shi ya Manzon Allah? Ya ce: “Da ilimi”.

Ko shakka babu Umar shi ne mafi yawan ilimi a cikin Sahabbai bayan Abubakar Raliyallahu Anhu.

Amma zaton da Umar ya yi cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai rasu ba, ai wani abu ne na xan lokaci. Daga baya ta bayyana gare shi cewa ya rasu. Da yawa kuma irin hakan kan faru ga wasu mutane; su yi zaton wani bai rasu ba, daga baya kuma da kamar awa xaya ko fiye ta tabbata cewa ya rasun. Shi kansa Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu akwai al'amurra da dama da haqiqarsu ta bayyana gare shi savanin yadda ya xauke su a farko, fiye da yadda wannan ta faru ga Umar. Akwai ma kai, hukunce-hukunce da dama da ya yi wa gurguwar fahimta, har kuma ya rasu yana kanta. Amma wannan bai sa aka ce shugabancinsa ya gurgunta ba. Kamar fatawar da ya yi a kan matar da aka xaura ma aure a kan bashi, kuma har ta mutu ba a yanka mata sadakin ba. Da wasu mas’aloli masu kama da haka, sanannu a wurin ma’abuta ilimi.

Ita kuwa mai cikin can, dama tun farko Umar bai san tana da shi ba. Saboda haka ya yi umurni da jefe ta don ta yi zina. Ganin haka sai Ali ya faxakar da shi. To, a kan haka ne ya ce: Ba don Aliyu ya gaya min tana da ciki ba da na sa an jefe ta. Da na kashe abin da ke cikin ta ba da sani ba.

Wannan shi ne abin da umar ya ji ma tsoro.

Kuma duk aje wannan. Ai ba abin kunya ba ne mutun ya qaru da wani ilimi daga bakin wanda ya fiya xaukaka da sani. Domin kuwa ai Annabi Musa Alaihis Salamu ya qaru da sanin wasu mas’aloli guda uku daga Haliru Alaihis Salamu. Haka kuma Annabi Sulaiman Alaihis Salamu ya qaru da sanin labarin Balkisu daga bakin Hudahuda.
8.13 Wai Umar ya Qago Sallar Asham

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha uku ita ce kasancewar Umar wanda ya qago sallar Asham a cikin jam’i, bayan kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ya ku mutane! Ku sani, yin sallar nafila a cikin jam’i, a daren watan Ramadana bidi’a ne. Kuma sallar walaha bidi’a ce. Kuma komai qanqancin Sunnah ta fi zama alheri bisa ga bidi’a kome yawanta. Kuma ku saurara! Kowace bidia’a vata ce. Kuma kowace vata godabenta na zuwa wuta”.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Amma duk da wannan magana ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai ga Umar ya fito watarana da dare, a cikin watan azumin Ramalana ya ga fitilu sun haskake masallatai. Ya ce: Mene ne haka? Aka ce masa: Ai mutane ne suka taru don yin sallar alkareji, sai ya ce: Bidi’a ce, amma madallah da ita.
Martani:

Abin da za mu ce a nan kafin martani shi ne, ba a tava samun qungiya daga cikin qungiyoyin bidi’a da vata, wadda ta kai ga qungiyar ‘yan Shi’ah tsananin rashin kunya da qarya ga Manzon Allah ba, da aron bakinsa a ci masa albasa. Duk da yake a cikinsu, akwai waxanda ba su san abubuwan da qungiyar tasu ke kai qarya ne ba. Jahilcin irin waxannan kuwa ya wuce la haula.

To, sai martani. Kamar kullum muna cajin marubucin ba samar wa wannan magana tasa madogara, kuma ta zan qwaqqwara.

Shi dai wannan hadisi masana sun daxe da sa jan biro a kansa. Ko ba komai shi wannan hadisi ba shi a cikin ko xaya daga cikin kundayen hadisi na malamai na da da na yanzu.

Tabbaccen abu ne cewa, tun a zamanin rayuwar Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallama mutane na wannan sallah. Kuma shi kansa Sallallahu Alaihi Wasallama ya jagoranci musulmi sallar ta asham tsawon wasu kwanuka a cikin watan azumi, kuma bai daina yin wannan sallah da jama’a ba sai don abin da ya bayyana na jin tsoron a wajabta ta. Ganin haka ya sa musulmi suka ci gaba da yin abarsu bayan yankewar wahayi da cikawarsa Sallallahu Alaihi Wasallama.

Umar Raliyallahu Anhu ya kira wannan sallah da suna bidi’ah babu shakka. Amma ai duk musulmi sun fahimci abin da yake nufi da kiran ta bidi’ah in ban da ‘yan Shi’ah. Wannan shi ya sa ma suke yin ta a duk faxin duniyar musulmi.

A qa’idar harshen Larabci, duk abin da aka fara gudanarwa ko yi, sunansa bidi’ah ba tare da kula da hukuncinsa ba. Ita kuwa bidi’ar da shari’a ta qyamata, ita ce abin da aka aikata ba bisa wani dalili na shari’ar ba. Irin wannan bidi’ah ita ce vata. Kuma ba ita Umar yake nufi ba.

In da haxuwa a cikin masallatai don gudanar da sallar asham abu ne da shari’a ta qi, da Ali ya hana shi a lokacin da ya zama Sarkin Musulmi. Amma kasancewar ya ci gaba da abin da shi Umar xin ya tabbatar, ta nuna cewa abu ne mustahabbi. Kai, an ma riwaito daga bakin Aliyun yana cewa: “Allah ya haskaka qabarin Umar kamar yadda ya haskaka masallatanmu da sallar alkareji”.


8.14 Wai Musulmi Sun Haxu a Kan Kashe Halifa Usman!

Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta goma sha huxu ita ce: haxuwar kan gaba xayan musulmi a kan kisan halifa Usman fiye da yadda suka haxu a kan shugabancinsa da na Abubakar da Umar. Wai, saboda ya aikata wasu abubuwa da ba su halatta ba.


Martani:

Tabbas, wannan magana qarya ce shahararra. Babu wani mutum a birnin Madina, da sauran biranen musulunci da bai goyi bayan shugabancin Usman, suka yi masa mubaya’a ba. A kan haka ne ma Imamu Ahmad da wasu malamai suka ce, haxin kan da aka samu a kan halifancin Usmanu ba a same shi a kan sauran ba.

Su ko waxanda suka kashe halifa Usman wasu ‘yan tsirarun mutane ne. Ga abin da xan Zubairu yake cewa a kai: “Sun mamayi Usmanu kamar yadda ‘yan fashi ke yi daga wajen gari. Qarshe Allah ya sa aka samu sa’ar kashe mafi yawan su, saura kuma suka sulale cikin duhun dare”.

To, kuma wani abu mai jan hankali a nan shi ne, yawan waxanda suka yi allawaddai da Ali Raliyallahu Anhu; suka yaqe shi, sun ninka waxanda suka kashe Usmanu yawa nesa ba kusa ba. Qarewa da qarau ma, an samu wasu daga cikin sojojin Aliyu xin da suka yi masa tawaye, suka kafirta shi; suka ce masa: “Ka fita musulunci. Saboda haka ba za mu sake yi maka biyayya ba sai ka sake musulunta”. Daga qarshe kuma suka zamo ajalinsa.

Dubun dubatar hanyoyi da riwayoyi sun tabbatar da cewa, kan gaba xayan musulmi ya haxu a kan yi wa Usmanu mubaya’a; babu wani daga cikin musulmi da ya zama saniyar ware. Savanin mubaya’ar Abubakar Siddiqu, wadda aka sami Sa’adu xan Ubadata ya kafa kai a qasa ya ce, ba zai yi ba. Haka kuwa ta tabbata, domin tarihi ya tabbatar da cewa, har wannan Sahabi ya kwanta dama bai haxa hannu da Abubakar Raliyallahu Anhu da sunan mubaya’a ba. Har halifa Umar wannan Sahabi bai yi wa mubaya’a ba, wanda a lokacin halifancinsa ne Allah ya karvi rayuwarsa.

Sa’adu xan Ubadata bai qi yi wa Abubakar mubaya’a don wata illa da yake gani a cikin yin hakan ba, ba a kuma tava jin wata mugunyar magana ta fito daga bakinsa zuwa gare shi ba, bai kuma tava musa cewa, halifan shi ne mafificin daraja a cikin gaba xayan Sahabbai ba. Abin da ya faru ai shi ne, ya nemi ayi halifofi biyu; xaya daga cikin Ansaru, xaya kuma daga cikin Muhajiruna. Hakan ta ci tura, shi kuma ya cije.

Nassin da Abubakar Raliyallahu Anhu ya kafa hujja da shi wanda ya kixe shawarar Sa’adu, in da ya ce: “A zavi shugabanni daga cikin Quraishawa”, nassi ne tabbatacce. An samo ta hanyoyi da dama cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce haka. Ka ga ra’ayin da Sa’adu ya riqa kuskure ne. Sa’adu Raliyallahu Anhu kuwa ya zaci ra’ayinsa daidai, zato kuwa ba ya kawar da haqiqa. Kenan qin yin mubaya’ar da ya yi ba daidai ba ne.

Ita ko mubaya’ar da aka yi wa Usmanu, duk da kasancewar musulmi a lokacin sun yawaita sosai, sun kuma watsu a birane da karkaru. Wannan duk bai hana qwansu da kwarkwatarsu yi masa mubaya’a ba. Amma in da gizo yake saqa duk bai fi halifancin Ali ba. Da yake qaddara ta riga fata, sai aka sami kusan rabin musulmi a lokacin suka qi yi masa mubaya’a. Kuma da ya soma yaqi da mutanen Sham, al’umma mai xinbin yawa, har daga cikin waxanda suka yi masa mubaya’a xin suka canza sheqa zuwa wurin Mu’awiyah kamar xan’uwansa Aqilu da makamantansa. Har kwanan gobe kuwa, magoya bayan halifa Usmanu masu sukar lamirin Ali na kafa hujja da wannan a kan cewa, bai karva sunan halifa ba. Amma tattare da haka, hujjarsu ba ta xara ta ‘yan Shi’ah da kome ba. Hujja ce mai raunin gaske wadda ke tabbatar da cewa, kisan da aka yi wa Ali na gilla ne. In ko haka ne, to, ina ga kisan da aka yi wa Usman?


9.0 Zango Na Tara

Rashin Cancantar Abubakar ga

Halifanci a Wurinsu
9.1 Rashin Samun Ijma’i a Kansa

Xan Shi’ar ya ce: Fasali na Shida mai kore hujjojin Ahlus-Sunnah a kan shugabancin Abubakar. Ya ce: Sau da yawa sukan ce wai kan musulmi ya haxu a kan shugabancinsa. Amsata a nan zuwa gare su ita ce, babu wani haxin kan da aka samu a kan haka. Domin kuwa, inji xan Shi’ar, wasu mutane daga cikin bani Hashim, da manyan Sahabbai, irin su Salmanu da Abu Zarri da Miqdadu da Ammaru da Huzaifatu da Sa’adu xan Ubadata da Zaidu xan Arqamu da Usamatu xan Zaidu da Khalidu xan Sa’idu xan Asi da xan Abbas, duk waxannan ba su goyi bayan zaman Abubakar halifa ba.

Kai, hatta da mahaifin Abubakar xin bai goyi bayansa ba. Don a lokacin da ya ji labarin cewa, an naxa halifa, cewa ya yi, wa aka naxa? Aka ce masa: “Xanka”. Sai ya ce, ya ‘yan bayin Allan nan biyu suka yi? Yana nufin Ali da Abbas. Aka ce masa, ai duk lokacin da ake hidima su suna can suna xawainiyra jana’izar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, sun kuma yarda da kasancewar xanka mafi yawan shekaru daga cikin Sahabbai. Wai sai ya ce, ni na tsofe masa.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Kuma gaba xayan banu Hanifata ba su yarda da shugabancinsa ba. A kan haka ne ma suka qi kai masa zakkah. Hakan ta sa ya jefe su da kalmar riddah, a qarshe kuma ya yaqe su, ya ribace su. Umar Raliyallahu Anhu ya qalubalance shi a kan haka, kuma bayan zamansa halifa ya mayar masu da gaba xayan mutanensu da dukiyarsu da aka ribata. Duk inji xan Shi’ar.


Martani:

muna godiya ga Allah da ya nuna wa duniya cewa, da waxancan mutane da suka yi ridda, da waxannan ‘yan Shi’ar xan juma da xan jumai. Malamai da almajirai kowa ya tabbatar da haka. Wanda ke da shakka ko sassauci a kan haka can da, to, yau kansa ya waye. Allah ya tona wa ‘yan Shi’ah asiri, sun bayyana da bakinsu. Qiyayyar da suke yi wa Allah da Manzonsa da zavavvun bayin Allah da masoyansa ta bayyana. Haka kuma Allah zai ci gaba da tona masu asiri domin kuwa duk wanda Allah ya saukar wa fitina, ba wani mai iya kare shi.

Duk wanda ke da masaniya da tarihin musulunci, da zarar ya ji wannan magana zai yanke xayan hukunci biyu ne; ko dai mai faxinta ya kasance mafi jahilcin mutane da tarihin Sahabbai, ko kuma duk ya fi su qarfin halin faxin qarya. Amma ni, a zatona, jahilci ne ke damun wannan marubuci da sauran ‘yan Shi’ah. Don haka suke cirato duk tunkuvar da suka ci karo da ita a cikin littafan magabatansu.

Mafi girman jahilci da vatan da ke cikin wannan magana duk bai fi sanya banu Hanifata da ya yi ba a matsayin mutanen kirki waxanda ke iya cika sahun musulmi har a kira haxuwarsu ijma’i. Kuma wai, sai bayan da suka qi yin bai’a ga Abubakar ne suka kuma qi kai masa zakkah lokacin ne ya raxa masu sunan Ahlur Riddah ya kuma yaqe su, ya ribace su. Alhali kuwa babu wanda bai san cewa, banu Hanifata sun karva kiran Musailamatul Kazzabi ba, a lokacin da ya yi da’awar annabta a qasar Yamamata.

Wannan al’amari na da’awar annabta da Musailamatu ya yi da biyarsa da banu Hanifata suka yi, abu ne da yake zahiri, ya kuma fi qarfin wani abu ya hana a san shi. Yaqar banu Hanifata kuma da sauran waxanda suka yi ridda da halifa Abubakar ya yi, na xaya daga cikin girman darajojinsa a idon na farko da na qarshen wannan al’umma. Su kuwa banu Hanifata su ne mafi girman waxanda suka yi ridda a tarihin musulunci a wancan lokaci. Kuma halifan bai yaqe su a kan sun qi fitar da zakkah ba. Ya dai yaqe su ne saboda sun karva kiran Musailamatu. Kuma yawansu kamar yadda ake faxa zai kai kusan mutum dubu xari.

Wani kuma abin da ke tabbatar da kasancewarsu ba musulmi ba, shi ne wata kuyanga wadda aka kamo daga cikinsu wadda Ali Raliyallahu Anhu ya sa xaka, wato Haulatu xiyar Jafar al-Hanafiyyah mahaifiyar Muhammadu ii. A kan wannan aiki na sayyidina Ali, wasu malamai suka kama matan da suka yi ridda a sa su xaka. Domin da a ce banu Hanifata musulmi ne masu alfarma da kiyaye ta ke wajaba, Ali ba zai sa xaya daga cikin matansu xaka ba ballantana ya sadu da ita har a haifi Muhammadu ii ba.

Haka nan ita ma cewar da xan Shi’ar ya yi, wai Umar ya qalubalanci Abubakar a kan yaqin riddah, qarya ce babba. Domin kuwa Sahabbai kacokam sun yi ittifaqi a kan yaqar Musailamatu da jama’arsa. Amma akwai wata qungiya daga cikin qabilar wadda ke waqar ita musulma ce, amma kuma suka qi fitar da zakkah. Wannan qungiya ce a farkon al’amari Umar ke ganin bai kamata yaqi ya haxa da su ba. Ya ci gaba da nacewa a kan wannan ra’ayi nasa har sai da Abubakar Siddiqu ya lurar da shi, ya kuma tabbatar masa da wajabcin yaqarsu, sannan ya yarda ya ba da gari. Wannan qissa sananna ce.

To, mu qaddara ma wannan yaqi an yi shi ne da manufar karvo Zakkah, kuma hakan ta zamo abin kunya gare su, to, abin kunyar zai fi sauqin tabbatuwa a kan wani wanda ba su ba. Idan ya wajaba a ba Ali uzuri a kan yaqinsa, to, ba Abubakar da Umar uzuri ya fi zama dahir. Domin kuwa yaqe-yaqen da Ali ya yi, ya yi su ne don a yarda da shugabancinsa, ya ci gaba da mulki a kan rayuka da dukiyoyin musulmi. To, ta ya ya za a ce yaqe-yaqe na addini ne, amma waxanda Abubakar ya yi, bayan an yarda da shugabancinsa ba addini ba?

Su kuwa manyan Sahabban da xan Shi’ar ya ce, sun qi yi wa Abubakar bai’ah, har da lissafa sunayensu xaya bayan xaya, qarya ce yake yi musu idan ka cire Sa’adu xan Ubadata. Su kuwa sauran, mubaya’ar da suka yi wa Abubakar da Umar ta fi qarfin wani ya musa ta. Domin kuwa gaba xayan masana hadisi da iliminsa, da masana Sirah da nagartattun zantuka, da sauran dangogin ma’abuta ilimi na jiya da yau, sun yi ittifaqi a kan wannan bai’ah. Saboda ma tsananin yarda da gamsuwa da shugabancin Abubakar da Usamatu xan Zaidu ya yi, shi ya sa wa Abubakar laqabin Halifatu Rasulillahi. Iyakar sunan Abubakar kenan a bakin Zaidu. Ya kuma yi masa wannan suna ne gaf da za shi fita zuwa yaqi.

Haka kuma gaba xayan waxanda xan Shi’ar ya ambaci sunayensu, babu wanda bai yi wa Abubakar bai’ah ba. Sai dai shi Khalidu xan Sa’idu ne koda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wafati yana gwamna, amma sai ya ce: Wakilcin da na yi wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya isa, ba zan iya zama wakilin wani bayansa ba. Nan take kuma ya yi murabus, kuma Abubakar ya karvi murabus xinsa. Kuma ko shakka babu, Khalidu na daga cikin Sahabban da suka yarda da halifancin Abubakar. Abin da kawai ya tabbata daga bakunan da ba sa qarya shi ne, baya ga Sahabi Sa’adu xan Ubadata babu wani Sahabi; babba ko qarami wanda bai yi wa Abubakar mubaya’a ba.

Duk da kasancewar mubaya’ar Ali ga Abubakar ta xan so ta sami ‘yar tangarxa, malamai sun yi ittifaqi a kan cewa, ya dai yi masa mubaya’ar. Haka ma bani Hashim babu mutum xaya daga cikinsu da bai yi mubaya’a ga Abubakar ba. Wasu dai suna cewa ne, Ali bai yi mubaya’ar ga Abubakar ba sai bayan wata shida. Wasu kuma suka ce wan shekara. Ala ayyi halin dai sun yi masa ba a kan tilastawa.

Haka kuma gaba xayan mutane sun yi wa Umar bai’ah idan ka cire Sa’adu. To, uwa uba Usmanu. Shi ba a sami mutum xaya da ya ce ba da shi ba a cikin bai’arsa.

Haka shi ma duk abin da xan Shi’ar ya faxa dangane da Abu Quhafata, mahaifin Abubakar, malamai sun yi ittifaqi akan zamansa qarya. Amma dai yadda haqiqanin abin ya ke shi ne, Abu Quhafata tsoho ne tuguf. Yana kuma zaune ne a garin Makkah. Ya musulunta ranar da aka buxa garin, kuma daga bisani Abubakar ya zo da shi wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ga yadda kansa da havarsa suke taf da farin gashi kamar taffa, sai ya ce: “Ai da ka bar wannan dattijon gida sai mu same shi can”. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi haka ne kuwa don girmamawa ga Abubakar.

Don haka, cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Sahabbai sun ce wa Abu Quhafata, lalle xanka shi ne mafi yawan Sahabbai ga shekaru, qarya ce zaharan. Sahabbai irin su Abbas Raliyallahu Anhu sun tsofe ma Abubakar.

Maganar kore ijma’in da xan Shi’ar ya yi a kan halifancin Abubakar, ba ta samun gindin zama a fagen ilimi, bisa ga dalilai kamar haka:


  1. Duk waxanda xan Shi’ar ya kawo in banda Sa’adu xan Ubadata sun yi mubaya’ar. Haka kuma mun ga yadda wata qungiya daga cikin banu Hashim suka qi yin mubaya’ar a farkon al’amari, amma bayan wata shida ta yi ba tare da an tilasta ta ba, ko don tsoron wani abu ko kwaxayin wani.

Rashin mubaya’ar mutum xaya ko wata qungiya ‘yar tsurut, ba zai rage ijma’in da ake buqata a tabbatar da shugabancin shugaba da komai ba. Shugabanci wani al’amari ne na wajibi. Kuma abu ne mai sauqi qwarai wani ya qi goyon bayan wani a kai, saboda wani abu da yake kimshe a cikin ransa. Kamar yadda ya faru ga Sa’adu.


  1. Ko da mun qaddara cewa, gaba xayan Sahabban can da xan Shi’ar ya zana, ba su yi wa Abubakar bai’a ba. Kai ko da yawansu ya xara hakan can sau biyu, hakan ba zata hana shugabancin Abubakar tabbata ko karva sunansa ba. Domin kuwa haxin kan da ake nema a cikin sha’anin shugabanci, shi ne na manyan mutane, irin waxanda ba a qulla kome ko kwance shi, sai tare da su. Su ne kuma jama’ar da ake nufi da hadisin da ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Na hore ku da shiga jama’a, domin hannun Allah na tare da su”.




  1. Ijma’in da al’umma suka yi a kan yarda da amincewa da halifancin Abubakar ya fi wanda suka yi a kan yi wa Ali mubaya’a, nesa ba kusa ba. Domin kuwa kashi xaya cikin uku na al’umma ko qasa ga haka kaxan ko fiye, ba su yi masa mubaya’a ba. A maimakon haka ma, sai suka yaqe shi. A yayin da kuma kashi xaya suka sa masa ido da sha’aninsa; ba su yaqe shi ba, basu yaqi wani tare da shi ba. Akwai kuma waxanda suka yi masa mubaya’ah, an samu waxanda suka sulale suka yaqe shi. A kan haka, idan har ya halalta a yi suka ga shugabancin wanda wasu daga cikin al’umma ba su yi wa bai’ah ba, to, shugabancin Ali ya fi cancanta nesa ba kusa ba, da haka.


9.2 ‘Yan Shi’ah ba su Yarda da Ijma’i ba

Xan Shi’ar ya ce: Asalatan, Ijma’i ba ya zama dalili a tsurar ruwan zatinsa. Dole ne ya kasance waxanda suka haxu suna da wani dalili na hankali ko nassi. Ba su kuwa da ko xaya. A hankalce babu wani dalili da za su togu da shi. Kuma ko a wurinsu Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar duniya ne ba tare da ya bar wasicci a kan wanda zai gaji halifarsa ba. Saboda haka wannan ijma’i nasu kuskure ne. koda kuwa an tabbatar da shi ba zai inganta ba. Kuma duk abin da aka gina a kansa vatacce ne, kuma rosasshe, inji xan Shi’ar.


Martani:

Cewar da ya yi ijma’i ba ya zama dalili a karan kansa. Idan yana nufin ba ya wajaba a yi biyayya ga wani umurni da waxanda suka yi ijma’in suka bayar, sai idan xa’a ne ga Allah da Manzonsa, to, wannan gaskiya ne, kuma zance ne ingantacce. Amma kuma ya sani wannan ba zai rage mu da komai ba. Domin ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ya wajaba a yi masa xa’a ne don komai ba sai don kasancewar umurninsa na tabbatar da umurnin Allah. Biyayya ga Manzo na wajaba ne saboda yi masa ita yi wa Allah ne. haka kuma a duk lokacin da muminai suka haxu a kan wani abu karvavve ga shari’a, to, wajibi ne sauran musulmi su yi masu xa’a. domin yi masu ita yi wa Allah ne da Manzonsa. Kamar yadda a nassance yake wajibi musulmi su kai koke-kokensu ga Manzo, saboda yin haka kamar kai wa ne ga Allah. Domin shi Manzon ba ya hukunci da son zuciya; sai da abin da Allah ya saukar. To, haka al’amarin yake a cikin miqa wuya ga abin da al’umma ta haxu a kai na alheri, daidai yake da miqawa ga Allah Subhanahu WaTa’ala.

Idan xan Shi’ar na nufin ijma’i na iya zama gaskiya idan ya dace da nassi ko akasin haka, idan nassi bai zo da abin da ya qunsa ba. Idan haka yake nufi, kamar yadda muke kyautata zato,to, ya sani ya rosa kansa. Domin kuwa wannan manufa tasa na suka ne ga ijma’i kowane iri. Kuma kamar yana so ne ya ce, abu ne mai yiwuwa al’umma ta haxu a kan vata da kuskure.

To, ka ga kenan, muna iya ce wa xan Shi’ar, kar ya manta da cewa, sun tabbatar da kasancewar Ali halifa kuma ma’asumi, da wasu abubuwa masu kama da wannan na shikashikan Imamiyyah ne, ta hanyar ijma’i. sanannen abu ne cewa, ba su da wata manufa a ginshiqan addininsu kamar yadda suke faxa da bakunansu, wadda ta fi hankali da ijma’i, waxanda riwayoyin da suka yo ke take wa baya.

A duk lokacin da suka tashi irin wannan magana, sukan ce, a hankalce, dole ne ya kasance mutane na da shugaba kuma ma’asumi, wanda nassi ya tabbatar. Sai su ce kuma, kan malamai ya haxu a kan cewa, babu wani ma’asumi mai irn wannan siffa sai Ali. da irin wannan kwancikwalato ne suke qoqarin tabbatar da hujjojinsu.

Tun daga nan muna iya ce masu, idan dai har ijma’i ba ya zama hujja, to, duk hujjojin da kuka kafa a kanshikashikan addininku ta hanyar ijma’i sun sha qasa.

Da kuwa xan Shi’ar zai dawo ya ce, sun yarda da kasancewar ijma’i hujja, to, hakan zata qara tabbatar da mazhabar Ahlus-Sunnah ne kawai. Ka ga yardarsu ko rashin ta da kasancewar ijma’i hujja duk xaya.

Idan kuma xan Shi’ar ya ce, ai mu bamu tava godogo da ijma’i ba, balle mu kafa shi hujja a kan wani abu na shikashikan mazhabarmu. Abin da kawai muke dogara a kansa shi ne hankali da abubuwan da muka naqalto daga shugabanninmu ma’asumai. To, sai mu ce masa, waxannan riwayoyin naku ma basu zama hujja don ba ku iya tabbatar da ma’asumancin wani daga cikin Imaman sai in Manzo ya yi masa shaidar haka. Tunda kuwa ba a samun wannan, to, ba sauran hujjar da ta rage maku ko guda.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin