9.3 Wai Kuma Al’umma ba ta Haxu Kan Abubakar ba!
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, kuma ai ijma’i na karva sunansa ne da yardar gaba xayan al’umma. Sanannen abu ne kuwa, hakan ba ta faru ba. Kan gaba xayan mutanen Madina ko wani yanki nasu bai haxu a kan haka ba. Kuma ta tabbata cewa, kan mafi yawansu ya haxu a kan kashe Usman.
Martani:
Zancen haxuwar kai a kan shugabanci. Idan marubucin na nufin irin haxuwar kan da shugabanci ba ya iya tabbat sai da shi. To, ai ana nufin haxin kan mutane masu qarfi ne da yardarsu kawai. Ta yadda tare da goyon bayansu shugaba zai iya zartar da manufofin shugabanci, koda kuwa yawansu bai fi yatsun hannu ba. Matuqar dai sauran jama’a na shaya masu, to, koda su kaxai suka yi wa shugaba bai’a ta tabbata. Wannan shi ne abin da Ahlus-Sunnah ke kai. Ita ce kuma mazhabar manyan malaman musulunci irin su Ahmad xan Hambali.
Wannan hukunci bai haxa da zaqaquran magana ba, Ahlul Kalam. Su a nasu gani akwai adudda daban-daban da kowanensu ke ganin sai bai’ah ta samu kafin ta karva sunanta. Wannan aiki nasu kuwa shuka ce bisa kan faqo.
Idan kuwa xan Shi’ar na nufin ijma’i na haxuwar kai a kan cancantar wane, ko duka sun cancanta, amma wane ne ya kamata ya kasance farko, saura su biyo baya. To, abu biyu ake la’akari da su a cikin irin wannan. Ko dai haxuwar kan gaba xayan al’umma ko ta mafi yawa. Idan ka haxa da amincewar masu gari, abubuwan sun zama uku kenan. Babu kuwa wanda halifancin Abubakar bai samu ba.
Shi kuwa Usman wani yanki ne na mutane kawai suka haxa kai a yi masa kisan gilla. Yawansu daga cikin al’umma bai taka kara ya karya ba.
9.4 Wata Suka ga Ijma’i
Xan Shi’ar ya ce, babu wani daga cikin Sahabbai da ya fi qarfin yin kuskure. Domin ba su da wata alfarma da ke iya kare su daga faxar abin da ba gaskiya ba a lokacin da suke zartar da wani hukunci.
Martani:
Sanannen abu ne cewa, a duk lokacin da mutane suka haxu a kan wani abu, to, wata siffa ta samu gare su, wadda babu ta ga xaixaikunsu. Saboda haka ne ma ba ya halatta a daidaita hukuncin mutum xaya da na taron jama’a. domin kuwa a duk lokacin da mutane suke xaixaice, to, yana yiwuwa qwarai a taras da wani kuskure ko qarya, ya tusgo daga bakin xayansu. Amma a duk lokacin da kansu ya haxu yana da matuqar wahala kuskure ko qarya su fito bakinsu, a matsayinsu na masu magana da harshe xaya.
Idan kuwa har tana yiwuwa kan jama’a ya haxu a kan kuskure, to, zancen tabbatar Ali ma’asumi, kamar yadda ‘yan Shi’ah ke gani, ya tashi. Domin kuwa ta hanyar ijma’i ne suka gano cewa, shi ma’asumi ne. kuma idan sharaxin yiwuwar kasancewar ijma’i kuskure ya tabbata, kenan tana yiwuwa qwarai ya kasance akwai wani ma’asumi a cikin al’umma ba Ali ba. Magana ta qare.
Ka ga kenan wannan suka da xan Shi’ar ya yi ta rosa gaba xayan abin da suka dogara a kansa na kasancewar shugaba ma’asumi. Da zarar kuwa ma’asumancin Ali ya roshe, to, mazhabar Shi’ah ta bi ruwa kenan. Haka kuma ko yarda suka yi da kasancewar ijma’in hujja, ba za ta hana ruwan ya cinye mazhabar tasu ba. Duk yadda aka kaxa ko aka raya dai, mazhabar tasu sai labari.
9.5 Kuma Wai Zaven Abubakar ya Sava ma Nassi
Xan Shi’ar ya ce: Mun riga mun bayyana nassin da ya tabbatar da shugabancin Sarkin Musulmi Ali. duk kuwa waxanda suka riqi ijma’i suka bar wannan nassi sun yi kuskure. Domin kuwa duk abin da aka haxu a kansa savanin abin da nassi ya qunsa, aikin banza ne.
Martani:
Mun riga mun warware duk wata magana da ke cewa, dole ne Ali ya zama halifa kafin halifofi uku da suka gabace shi. Domin kuwa gaba xayan nassosan da suka tuzgo a kan shugabanci na tabbatar da halifancinsu ne kafin shi. Kuma amon ijma’i a kan haka ya game duniya. hujja ne kuma yankakka, ba naji-naji ba. Musamman kuma da aka sami nassosa da dama suka mara masa baya. Da wani labari zai tuzgo ya tunni wannan ijma’i, to, sai a tuhumce shi don ya tabbata zakka. Lalle ne kuma a qarshe a taras cewa, labarin qanzon kurege ne.
A qa’ida, ba ta yiwuwa ingantaccen nassi ya ci karo da lafiyayyen ijma’i. domin kuwa kowanne daga cikinsu hujja ce yankakka. Su kuwa yankakkun hujjoji, amanar da ke tsattsage da cikannansu ta dalilai da ke tabbatar da ingancinsu ba su bari su yi kabra da juna. Da wata ‘yar hayaniya za ta faru tsakaninsu sai dai a sasanta su amma ba dai rabuwa ba.
Ta tabbata cewa, ingantaccen nassi da lafiyayyen ijma’i duk sun tabbatar da halifancin Abubakar. Shi kuwa nassin da ‘yan Shi’ah ke cewa akwai a kan halifancin waninsa, tuni gayya ta qare aiki kansa; mun gama gane qarya ce a cikin ruwan sanyi. Muna kuma da dalilai masu yawa da ke tabbatar da haka.
9.6 Suka ga Hadisin Koyi da Abubakar da Umar
Xan Shi’ar ya ce: Hujja ta biyu ita ce: Abin da suka riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, wai, ya ce: “Ku yi koyi da mutum biyu bayana: Abubakar da Umar”.
Ya ce: Babu wanda ya riwaito wannan hadisi. Koda kuwa ta tabbata an riwaito shi, to, ba ya nufin mutanen biyu su zama halifofi bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. domin kuwa koyin da ake yi da malaman fiqihu bai tilasta kasancewarsu halifofi. Kuma ma ai Abubakar da Umar sun sassava a cikin hukunce-hukunce da dama, ta yadda ba ya yiwuwa a yi koyi da su baki xaya. Ga shi kuma hadisin ya ci karo da wani hadisin da suka riwaito inda suka ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Sahabbaina kamar taurari su ke; duk wanda kuka koyi yi da shi kun shiriya”. Amma kuma duk da haka kan al’umma bai haxu a kan cancantar gaba xayan Sahabban da shugabanci ba.
Martani:
Kan gaba xayan malaman hadisi ya haxu a kan kasancewar hadisi na farko mafi qarfi a kan hadisin da ‘yan Shi’ah ke ta waqen akwai game da shugabancin Ali. Hadisin abu ne sananne, da littafan malaman hadisi da ake dogaro da su irin su Abu Dawuda da Tirmidhi da Ahmad sun riwaito shi.
Amma nassi a kan shugabancin Ali babu wani malami da ya riwaito shi. Kai qarewa ma dai, masana hadisi sun yanke masa hukuncin rashin asali. Akan haka ne ma baban Muhammad Ibnu Hazam yake cewa: Ba mu tava samun wata riwaya a kan wannan nassi da ake waqe ba, face mun taras da ita wofintacciya. Kuma ba a san wanda ya riwaito ta ba sai wani baqon haure a cikin riwayar hadisi, wai shi Abul Hamra’i.
A haka, babu dalilin da zai sa ayi qarfin halin yin suka ga wannan hadisi na koyi da Abubakar da Umar a daidai lokacin da ake qoqarin inganta wancan nassi da ake waqen akwai a kan halifancin Ali.
Tabbas, akwai dalili a cikin wannan hadisi da ke tabbatar da shugabancin waxannan Sahabbai biyu. Domin cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, a yi koyi da mutum biyu bayansa. Ka ga hakan ta tabbatar da cewa, daga shi sai su. Ya kuma yi umurni da a yi koyi da su. Da kuwa su azzalumai ne ko kafirai, Wal iyazu billahi ba zai yi horo da ayi koyi da su ba. Har abada azzalumi ba zai cancanci zama abin koyi ba, saboda Allah Ta’ala ya ce:
ﭽ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﭼ البقرة: ١٢٤
Alqawarina ba zai sami azzalumai ba. 2:124.
Da yake Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni da koyi da su, ya kuma ba da labarin kasancewarsu a bayansa, wannan ya zamo hujja a kan cewa, su halifofi ne nagartattu kuma abin koyi a bayansa.
Ita kuwa cewar da xan Shi’ar ya yi wai, Abubakar da Umar sun sassava a cikin hukunce-hukunce da dama, don haka ba ta yiwuwa a yi koyi da su a lokaci xaya. Wannan magana ba gaskiya ba ce. Tarihi ya tabbatar da cewa, ba a tava jin bakunansu sun sava a kan wani hukunci savawa ba. Sai dai xayansu ya kasance reshe a kan xaya, ta yadda zai kaxaita da riwayoyi biyu; xaya tasa, xaya kuma ta xayan. Hakan ma kan faru ne kawai a cikin wasu ‘yan taqaitattun abubuwa kamar hukuncin gadon kaka tare da ‘yan’uwan mamaci. Umar na da riwayoyi biyu akan wanna mas’ala, amma xaya zancen Abubakar ne.
Ita kuwa cewar da ya yi, wai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Sahabbaina kamar taurari suke..” hadisi ne mai rauni. Imamul Bazzar ya ce: Wannan hadisi bai inganta daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Kuma ba ya cikin kowane littafi na hadisi da ake dogaro a kansa. Kuma a hadisin babu lafazin “a bayana” wadda ta zo a wancan hadisin. Ka ga kenan, koda ya inganta ba maganar halifanci yake yi ba.
9.7 Wai Hijirarsa Tare da Annabi ba Daraja ba ce!
Xan Shi’ar ya ce: Dalili na uku shi ne: Abubuwan da suka tuzgo na darajojin Abubakar, kamar ayar da ta sauka a kan zamansu tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin kogo, da kuma cewar da Allah Ta’ala ya yi: Kuma mafi taqawa zai nisance ta 92:17. Da kuma inda yake cewa: Ka ce wa waxanda aka bari daga qauyawa za a kira ku zuwa ga waxansu mutane masu tsananin yaqi.. 48:16 Sai Ahlus-Sunnah suka ce wai, Abubakar ne zai yi kiran. Kuma ya kasance tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin dabi ranar yaqin Badar, ya kuma ciyar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Shi ne kuma wanda Annabin ya gabatar don ya yi wa mutane sallah a madadinsa.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Babu wata daraja ko fifiko da Abubakar zai kevanta da su, don ya kasance tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin kogo. Domin kuwa abu ne mai yiwuwa ya tafi da shi ne don kada asirinsa ya tonu. Haka kuma ita waccan ayar da ake kafa hujja da ita akan falalarsa, malamai ba su fahimce ta daidai ba. Ai ayar tana qoqarin fitowa da nakkas xin Abubakar ne. domin cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, “kar ka sami damuwa”. Hakan na nuna irin fargaba da qarancin haqurin da yake da su da kuma rashin yaqini da Allah Ta’ala. Bai kuma gamsu da kasancewa kafaxa-da-kafaxa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wannan hali ba. Bai kuma karvi hukuncin Allah da qaddararsa ba. Abin da zai tabbatar maka da hakan inji xan Shi’ar, shi ne, da a ce damuwar da Abubakar ya samu, ya same ta ne saboda Allah da Annabi bai yi qoqarin raba shi da ita ba. Idan kuwa ya raba shi da ita ne, don ya raba shi da savon Allah, to, abin da Ahlus-Sunnah ke son tabbatarwa da ayar na falala da xaukaka ya zama qasqanci da qaranci kenan.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa, kuma ai a duk lokacin da ka ji Alqur’ani ya yi zancen saukar da natsuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama to, za ka taras cewa, ya haxa har da muminai. Nan ne kawai bai ambace su ba. Wannan kuwa babbar naqasa ce da babu irinta.
Ita ko ayar da ta ce: Kuma mafi taqawa zai nisance ta 92:17 tana nufin Abud Dahadahi ne, wanda ya saye wa maqwabcinsa wani iccen dabino. Sanadi kuwa shi ne, ya ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na ta fama da mai iccen ya fansar ma maqwabcin na Abud dahadahi da shi, shi kuwa Manzon ya lamunce masa wani icce a aljanna, amma mai iccen ya qi. A kan haka ya saye iccen ta hanyar musayarsa da wata qatuwar gona tasa, ya cika gurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da shi na yin sadaqa da itaciyar ga maqwabcin nasa.
Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Haka nan ita ma ayar da suka kafa hujja da ita a kan kiran qauyawa zuwa yaqar wasu mutane masu qarfi, ba ta nufin Abubakar ne zai yi kiran. Allah Ta’ala na magana ne da waxanda suka qi fita yaqin Hudaibiyyah, amma da aka samo ganimar Haibara sai ga yawunsu na zuba. Sai Allah Ta’ala ya katse masu hanzari da cewa, Ka ce ba za ku bi mu ba 48:15. Hakan ta faru ne saboda Allah ya kevance ganimar Haibara ne saboda waxanda suka halarci yaqin Hudaibiyyah. Su ne waxanda Allah ke magana da su a waccan aya. Wato, za a kira su zuwa ga yaqar wasu mutane masu tsananin yaqin tsiya. A qarshe kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gayyace su zuwa ga yaqe-yaqe da dama kamar yaqin Mu’uta da Hunainu da Tabuka da wasunsu. Ka ga kenan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne mai kiran ba Abubakar ba.
Kuma tana ma iya kasancewar mai kiran Aliyu ne. domin shi ne wanda ya yaqi hutsaye da kangararru da ‘yan tawaye ya sa suka daidaita sahu. Hakan kuwa kamar ya musuluntar da su ne. Domin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ya kai Aliyu! Duk wanda ke yaqi da kai yana yaqi da ni ne”. Duk kuwa wanda ke yaqi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kafiri ne. Haka kuma, inji xan Shi’ar, kasancewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin dabi a ranar yaqin Badar ba wani abin xaukaka ne ga shi Abubakar xin ba. Saboda kewar da ake cewa ya xebe ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin abu ne da hankali ba zai karva ba. Saboda kewar da yake xebewa da mahaliccinsa ta ishe shi; ba ya buqatar wani mahaluki. Abin ma kawai da ake iya fassara taren tasu da shi a lokacin duk bai fi a ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya zaunar da shi a wurinsa ba, don gudun ya sake maimaita ababen kunyar da ya aikata a waxansu yaqe-yaqe ta hanyar raki da gudowa. Saboda haka ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai hore shi da rungumar yaqi ba. Kuma ai ko alama wanda ke zaune a inwa bai kai darajar wanda ke can yana rabkewa da maza don tabbatar da kalmar Allah ba.
Ya kuma ci gaba da cewa: Ita kuma cewar da Ahlus-Sunnah suka yi wai, Abubakar ya xauki nauyin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama qarya ce. Abubakar talaka ne na qarshe; ba ya da komai, balle mahaifinsa. Saboda talaucinsa ne ma, ko abin da zai ci sai ya je yawon kwaraka a gidan Abdullahi xan Jud’an. Ka ga in da Abubakar mawadaci ne, da mahaifinsa zai fara rufa wa asiri kafin wani. Ko a lokacin jahiliyyah shi ba kowa ba ne baya ga malamin qananan yara. Bayan da musulunci ya bayyana kuma sai ya kama sana’ar xinki. Zamansa halifa ne musulmi suka hana shi wannan sana’a, sai ya ce masu, to, da me zai rayu? Sai suka yanka masa albashin dirhami uku kulli yaumin daga cikin baitil-mali.
Wani kuma dalili a kan kasancewar waccan magana ta Ahlus-Sunnah qarya, inji xan Shi’ar shi ne, Sayyida Khadijah ta riga ta yarde wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama biyan gaba xayan bukatunsa daga cikin dukiyarta tun kafin hijira. Kuma a lokacin ba a fara yaqe-yaqe ba, balle a ce yana da buqata da kayan yaqi da abinci mai yawa. Bayan kuma da aka yi hijira, ko veran masallaci bai yi fatarar Abubakar ba, balle ya xauki nauyin wani. Kuma da ta tabbata cewa, ya xauki nauyin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da aya ta sauka a kan haka. Kamar yadda ta sauka a kan Aliyu a cikinsuratul Insan.
Sanannen abu ne kuma, inji xan Shi’ar, cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne mafi girma daga cikin waxanda Sarkin Musulmi Ali ya xauki nauyi. Amma dukiyar da Ahlus-Sunnah ke raya cewa Abubakar ya ciyar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, tattare da yawanta, rashin saukar wata aya ko wata sura ta Alqur’ani a kan haka na tabbatar da kasancewar zancen nasu qarya.
Ya kuma ci gaba da cewa: Haka kuma cewar da suka yi wai, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wakilta Abubakar ya ba mutane sallah, ba haka abin yake ba. A’ishah ce, Bilalu na qare kiran sallah sai ta yi kangamas ta umurce shi da ya gabatar da Abubakar a gaban sahu. Da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya farko daga magagin zazzavi, sai ya ji kabbara na tashi ana sallah. Sai ya ce, waye ke bayar da sallah? Su A’ishah suka ce: Abubakar ne. Sai ya ce: “Ku kama ni in fita”. Fitarsa ke da wuya tsakanin Aliyu da Abbas sai ya kama kafaxun Abubakar, ya janye shi daga Alqibla, ya ci gaba da bayar da sallar da kansa.
Xan Shi’ar ya ce: Wannan shi ne matsayin dalilan Ahlus-Sunnah. Buqatarmu a nan ita ce, masu hankali su dibi waxannan bayanai da idon basira. Kada wani son zuciya ya hana su tsayawa bisa gaskiya, su manta abubuwan da suka ji daga uwaye da kakanninsu. Domin kuwa Allah Ta’ala ya yi hani daga haka. Kada wani abu na duniya ya hana su sadar da gaskiya ga mai ita ko hana ma mai wani haqqi haqqinsa.
Wannan shi ne qarshen abin da muka yi nufin tabbatarwa a cikin wannan matashiya. Inji xan Shi’ah.
Martani:
Darajojin Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma abubuwa ne da ko makaho ba ya buqatar hannunka mai sanda kafin ya tantance su. Fifikon da waxannan dattijai ke da shi ya riga ya tabbata. Abin da ko ‘ya Shi’ah ke qoqarin yi shi ake ce wa canza ma tuwo suna. Ka ga kuma da haka sun faxa cikin faxar Allah Ta’ala da ya ce:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛﭜ ﭼ الزمر: ٣٢
Wane ne mafi zalunci fiye da wanda ya yi wa Allah qarya, ya kuma qaryata gaskiya a lokacin da ta je masa?
Da kuma faxarsa:
ﭽ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﭼ يونس: ١٧
Saboda haka, wane ne mafi zalunci a kan wanda ya qirqira ma Allah qarya, ko ya qaryata ayoyinsa? Haqiqa, masu laifi ba su cin nasara.
‘Yan Shi’ah kenan. To, bari mu dawo a kan maganganunsa. Mu fara da cewar da ya yi, babu wata daraja da kasancewar Abubakar tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin kogo ke nunawa.
Amsarmu a nan ita ce, nassin Alqur’ani ya tabbatar da akwai wannan falala da daraja. Duk wanda ya duba shi da idon basira zai gan su bayyane. Xauki ayar ka sake dubawa. Ai Allah cewa ya yi: Kada ka yi baqin ciki, lalle ne Allah yana tare da mu 9:40. ka ga anan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayar da bayanin kasancewar Allah Subhanahu Wa Ta’ala tare da shi da Abubakar, kamar yadda ya kasance tare da Musa da Haruna inda yake cewa: Lalle ni, ina tare da ku, ina ji, kuma ina gani. 20:46.
Bayan wannan kuma Buhari da Muslimu sun riwaito, a cikin hadisin Anas daga Abubakar Siddiq Raliyallahu Anhu ya ce: “Na ga qafafun mushrikai dabra da kanunmu, a lokacin da muke cikin kogo. Sai na ce, ya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama! Da xayansu zai sunkuyar da kansa ya dubi qafafunsu, tabbas da ya gan mu”. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa: Ya kai Abubakar! Me kake zato ga mutum biyun da Allah ne na ukunsu?!
Qari a kan cewa, malaman hadisi kaf sun yi ittifaqi a kan ingancin wannan hadisi, sun kuma karve shi hannu bi-biyu, ta yadda ba a samu mutum biyu daga cikinsu da bakinsu ya sava ba a kansa. Alqur’ani ya daxa tabbatar da ma’anarsa da waccan aya.
Wannan aya da wancan hadisi na daxa tabbatar da qololuwar yabo ne ga Abubakar. saboda sun nuna cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar da imanin da Abubakar ke da shi, irin wanda ke sa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya kawo xaukin nasara ne ga Manzonsa a cikin wannan hali. Kuma Allah ya bayyana wadatuwar da Manzon ya yi da shi daga kowace irin halitta, a inda yake cewa:
ﭽ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﭼ التوبة: ٤٠
Idan baku taimake shi ba, to, haqiqa Allah ya taimake shi a lokacin da waxanda suka kafirta suka fitar da shi, a lokacin da suke su biyu a cikin kogo.. 9:40
A dalilin wannan aya ne, Sufyanu xan Uyainata da wasu malamai suka ce, tabbas Allah ya ga laifin gaba xayan halitta saboda wannan hali da Annabinsa ya shiga, suna ji suna gani, sai fa Abubakar ne kawai ya tsira daga zargin. Suka kuma ce, duk wanda ya xauki waccan tare da Abubakar ya yi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wancan hali ba bakin kome ba, ya kafirta, saboda ya qaryata Alqur’ani. Su kuwa wasu malamai irin Abul Qasim As-Suhaili cewa suka yi: “Abubakar ne kawai aka tabbatar ya samu wannan daraja”.
Idan kuwa muka dubi cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Abubakar: “Me kake zato ga mutane biyun da Allah ne na ukunsu?” za mu ga cewa, yadda wannan lafazi yake a bayyane haka ma’anarsa take. Domin kuwa ko a cikin halifofi babu wanda ya karva sunan Halifatu Rasulillahi sai Abubakar. Daga Umar sunan ya canza ya koma Amirul Muminina.
Daga cikin darajojin Abubakar a lokacin da yake cikin kogon dutse, waxanda Alqur’ani yake bayyanawa, akwai busharar da Allah Ta’ala ya yi wa Manzonsa ta nasararsa da taimako, a daidai lokacin da zai tavar da gaba xayan halitta, sai fa wanda ya tsare.
Yin wannan bushara ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a daidai lokacin da Abubakar ke tare da shi, na nuni zuwa ga wata xaukaka da shi Abubakar xin ke da ita a sakamakon haka. Kamar yadda Allah Ta’ala ke cewa: A lokacin da kafirai suka fitar da shi.. 9:40.
Mutum xaya ko shi ne qarancin abin da ake iya samu ya raka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, don babu rabin mutum.
Sannan kuma Allah Ta’ala ya ce: A lokacin da yake ce ma abokinsa: “Kada ka yi baqin ciki. Haqiqa Allah na tare da mu”.. 9:40. Wannan sai ya nuna abokin nasa na matuqar tausayawa da son taimaka masa. Hakan kuwa sai ta sa shi cikin damuwa da baqin ciki. Daman kuma abin da kan sami mutum kenan a lokacin da wani abin qi ya sami masoyinsa. Amma ko halaka ya ga maqiyinsa zai yi ba zai yi ko gezun ba.
A kan haka, da a ce Abubakar ba masoyin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba ne, kamar yadda ‘yan Shi’ah ke son nunawa, ba zai sami wata damuwa ba, balle Manzon ya lallashe shi. A maimakon haka ma sai ya qume daxi da farin cikinsa.
Idan kuwa har ‘yan Shi’ar suka yi qoqarin kixe wannan bayani namu da cewa, ai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai san Abubakar na qinsa a zuci ba, ganin irin yadda ya bayyana damuwarsa akan halin da suka shiga. Sai mu ce masu, to, cewar da Manzon ya yi fa: Lalle ne Allah na tare da mu.. ta nuna cewa, idan shi bai san abin da ke cikin ran Abubakar ba, to, Allah ya sani. Don ga shi wannan aya ta ba mu labarin cewa, Allah na tare da su; su biyu, zai kuma taimake su. Ka kuwa ga ba ya halatta ga Manzon ya ba da labarin kasancewar taimakon Allah gare shi da mumuinai, ya kuma jefo wani munafuki a ciki. Ko alama ba zai yi haka ba. Domin tsararre ne shi, daga yin qari ko ragi ko kuskure a cikin isar da saqon Allah. Kuma ba ya faxar kome daga wurinsa sai gaskiya.
Ko mafi raunin hankali daga cikin mutane ba zai kasa fahimtar irin halin da ya kamata a ce Abubakar ya sami kansa a cikin wannan tafiya ba. Domin kuwa wanda yake yi wa rakiya ya gudo ne daga mutanensa, waxanda ke neman kashe shi saboda qiyayya. Kuma danginsa na gida basu iya taimakonsa da komai. Ka ga dole ne duk wanda zai riqa a matsayin aboki a cikin wannan tafiya ya kasance soyayyarsa da shi ta shafe ta kowa. Hakan kuwa ta tabbata, don ya nuna masa irin baqin cikin da yake ciki a kan halin da ya shiga. Amma kuma sai duk hakan ta zama busar iska; ya kasance yana qiyayya da shi a zuci? Bayan kuma shi ya sakankance har ga Allah cewa, shi masoyinsa ne?
Ko shakka babu, babu wanda zai yi haka sai mafi wauta da jahilcin mutane. Allah kuwa ya qasqanta duk wanda ya jingina irin wannan wauta da jahilci ga Manzonsa, kuma mafi cikar halittarsa hankali da ilimi da gogewa.
Ita ma cewar da xan Shi’ar ya yi, wai abu ne mai yiwuwa ya kasance Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi tare da Abubakar ne don tsoron kada asirinsa ya tonu, Quraishawa su yi sukuwar sallah a kansa, magana ce da ba ta sauraruwa, saboda waxannan dalilai:
-
Abin da duniya ta sani, kuma Qur’ani ya tabbatas shi ne, Abubakar masoyin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, ba mqiyinsa ba. Maganar Allah kuwa ta fi ta kowa.
-
Dubun dubatar hanyoyi na ga-ta-sarai sun tabbatar da kasancewarsa masoyin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kuma wanda ya yarda da lamarinsa, ya kuma fi kowa zama tare da shi. Wannan magana tabbatatta ce fiye da yadda labarin Antaru da jaruntarsa ya tabbata, da hatimu da kyautarsa, da soyayya da jivintar da Ali ke da su zuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. irin wannan kokwanto na ‘yan Shi’ah game da soyayyar da Abubakar ke yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ba ya da banbanci da irinsa da Harijawa ke yi game da Ali. to, wannan ma da sauqi. Don an sami wasu ‘yan Shi’a na musun kasancewar qaburburan Abubakar da Umar a cikin xakin Annabi. Wasu daga cikin ‘yan ta’addarsu ma na musun waccan tafiya da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi tare da Abubakar. Wannan feshin qarya ba abu ne farau ba a wurin waxannan mutane, domin kuwa jini da tsokarsu da qarya suka tofo. Hakan ta sa kodayaushe suke qoqarin musanta abin da duniya ta gama tabbatar da kasancewarsa gaskiya, tare da qoqarin tabbatar da abin da duniya da lahira an yarda da kasancewarsa toka.
-
Cewar da xan Shi’ar ya yi, tana yiwuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi da Abubakar ne don kada Quraishawa su kama shi, na nuna yadda ‘yan Shi’ah suke cike da baqin cikin wannan bawan Allah. Dalilin da ya sa har suke fita hayyacinsu wajen canza alherinsa ya koma sharri. In ba haka ba ai a lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita daga Makka, kuma labarin ya game gari kamar wutar daji, suka kuma aika da dakarun da ke sintiri a kan godabbu, da alqawarin lada mai tsoka ga duk wanda ya zo da xayansu a raye ko mace. To, wanda haka ta faru a kansa ana cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na tsoron faruwar wata kisisina daga wajensa? Shi kansa alqawarin bayar da diyya ga duk wanda ya kawo koda gawar Abubakar na nuna suna da masaniyar alaqar da ke tsakaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kamar yadda kuma hakan ke kore duk wata shakka cewa, ko yana da wata alaqa da su ta voye.
-
Fitar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi tare da sayyidina Abubakar ta kasance ne a talatainin dare. To, wace buqata gare shi ta tafiya tare da Abubakar don gudun tonon asiri? Na san xan Shi’ar zai yi fararat ya ce, ai qila ya faxa masa ne shi kaxai cewa, zai tafi. Sai mu ce: To, me ya sa ya faxa masa in har yana shakkar sa? Kuma ko me ya sa ya sirranta masa haka xin ma? Ai yana iya tafiya a lokacin da Abubakar xin bai sani ba, kamar yadda ya fita sauran jama’ar gari ba su sani ba. Kuma koda ta kasance sun kitse fitar da lokacin yin ta, ai abu ne mai sauqi idan har Abubakar xin na so ya qi fitar a tare da shi, ya kuma tona asirrin. Kai! Allah waddaran maras hankali. Abubakar xin ne fa ya nemi izinin yin hijra shi kaxai daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, amma Manzon ya dakatar da shi, har sai da Allah ya yi masu izinin fita tare, sannan ya kira shi ya sanar da shi. A sabili da haka ma sai da Abubakar ya fashe da kuka don murna, kamar yadda ya tabbata a cikin Buhari da Muslim.
-
Tsawon lokacin da suke zaune a cikin kogo, Abdullahi xan Abubakar ne ke kai musu labarin Quraishawa. Kuma tare da su akwai Amru xan Fuhairata. Ka ga abu ne mai sauqi da maganar xan Shi’ar gaskiya ce, Abubakar ya umarci xansa ko Amru da gayyato Quraishawa domin su kama Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
-
A lokacin da maqiya suka biyo su har bakin kogo, ga qafafuwansu Abubakar na gani, ai yana iya yin kangamat ya fito don tona asirin. Sanin kowa ne babu maqiyin da ba ya fatar Allah ya nuna masa ranar da zai zama sanadiyyar halakar maqiyinsa. To, in da Abubakar ya fito ya bar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi kaxai kuwwarka banza, sai abin da ake son duk ya faru tare da haxin kan Abubakar xin ya faru. Amma Allah ya tsare Abubakar daga wannan mugun nufi nasu.
Dostları ilə paylaş: |