Tafarkin sunnah



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə50/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51

9.8 Gaba ta Koma Baya

Cewar xan Shi’ar, wai, ayar da Allah Ta’ala ke cewa: Kada ka yi baqin ciki, lalle ne Allah yana tare da mu 9:40 wai, tana nuna naqasar Abubakar ne ba xaukakarsa ba. Hasali ma tana tona asirin da ke cikin birnin zuciyarsa ne na firgita da tsoro da qarancin haquri da rashin cikakken yaqini da Allah, da kuma rashin gamsuwa da yin kafaxa-da-kafaxa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.


Martani:

Maganar nan ta xan Shi’a ta warware abin da ya fara faxa na cewa, wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita da Abubakar don kada ya bar baya da qura. Idan har Abubakar maqiyin Manzon Allah ne a voye, to, babu abin da zai sa ya samu wata damuwa ko baqin ciki. A maimakon haka ma sai dai ya yi farin ciki tare da samun cikakkar natsuwa, musamman a lokacin da maqiyan Manzon suka biyo bayansu, har kuma suka iso dabra da kogon, kuma shi Abubakar xin yana ganin qafafunsu kamar za su taki kansa.

Ka ga idan har waccan magana ta farko gaskiya ce, sai xai ya ce masu, kai ar! Ku taho ga shi.

Waccan magana tasu dai ta rosa wannan, cewar da suka yi munafuki ne ta gushe, kasancewarsa mumini ta tabbata. Alhamdu lillahi Rabbil Alamina.

A nan yana da kyau mu yi bayanin cewa, babu munafiki ko xaya daga cikin Muhajiruna waxanda Abubakar yake cikin na gaba-gabansu. Babu wanda zai yi hijira daga cikin kafiran Makka, ya bar garinsu da dukiyarsa don ya taimaki maqiyinsa. Duk wanda ya yi hijra daga cikinsu ya yi ta ne a zavin ransa kuma don ya tsira da addininsa kamar yadda Allah ya shede su da haka. Ba mu ce ba a samun munafukai ba, amma sai a cikin xaixaikun qabilun Ansaru da suka shiga musulunci don jin tsoron mamayarsa.

Da wannan magana imanin Abubakar ya tabbata. Shi kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tun da ba wawa ba ne ko jahili, ba zai zavi abokin tafiya ba sai wanda yake shi ne mafifici daga cikin muminai. Musamman dai irin wannan tafiya mai tsananin haxari da rashin makama. Saboda haka ne ma tasiri da girman wannan hijira a zukatan musulmi ba su misaltuwa. Wannan dole ne, domin kuwa duk tubalin da aka ce za a gina tarihi da shi lalle ne ka taras da labarinsa ya haxe duniya. kamar yadda muka faxa dole ne, wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai yi wannan tafiya da shi ya kasance wanda ransa ya fi kwantawa da shi a kan kowa.

Wannan kawai ya ishi Abubakar Siddiqu abin tinqaho da zama amalen Sahabbai. Domin babu xaya daga cikinsu da ya sami irin wannan xaukaka. Haka kuma na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da kasancewarsa mafi girma a idon Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga cikinsu.

To, mu koma ga cewar da xan Shi’ar ya yi, wai, wancan rarrashi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Abubakar na kawai tabbatar da naqasarsa ne, ba xaukaka ba. Sai mu ce, wace naqasa yake nufi cikin biyu 1) Share imani daga zuciyar Abubakar kwatakwata. Ko 2) Rashin kammalar darajarsa, don yana tare da wanda ya fi shi cika da kamala?

Idan xan Shi’ar na nufin ma’ana ta farko ne, to, ya ci tuwon gigi. Domin ko Allah Ta’ala ya gaya wa Annabinsa cewa: Kada ka yi baqin ciki saboda su, kuma kada ka kasance a cikin quncin rai daga abin da suke yi na makirci 16:127. Ya kuma ce wa muminai: Kuma kada ku yi rauni, kuma kada ku yi baqin ciki, alhali ku ne mafiya xaukaka 3:139. Ya kuma ce: Kuma lalle ne, haqiqa mun ba ka (ayoyi) bakwai waxanda ake karantawa da Alqur’ani mai girma. Kada ka miqa idanunka zuwa ga abin da muka jiyar da su daxi game da shi, nau’i-nau’i a gare su, kuma kada ka yi baqin ciki a kansu 15:87-88.

A cikin waxannan ayoyi Allah ya hana Manzonsa da muminai baki xaya baqin ciki. Ashe kenan ba ta nufin wanda aka hana xin ba ya da imani.

Idan kuwa xan Shi’ar na nufin ma’ana ta biyu, wato, daraja da xaukakar Abubakar a wannan hali ba su kai na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ba, wannan gaskiya ne. babu kuma wani Ahlus-Sunnah da ke musun haka. Amma dai ba ta nufin Aliyu ko Umar ko Usmanu sun fi shi xaukaka. Haka ba za ta yiwu ba, domin babu xaya daga cikinsu da ya kasance tare da Annabi a wancan lokaci. Kai koda sun kasance tare da shi xin , hakan ba za ta sa su fi Abubakar girman daraja da xaukaka ba. Domin kuwa abin da yau da gobe suka tabbatar shi ne, a duk lokacin da qura ta musqe, tsanani ya yi tsanani, Abubakar ne ke zama zakara a fagen yaqini da haquri fiye da su. Haka kuma idan aka sami wani tajin-tajin, ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gindaya wani abu, Abubakar ne kan gaba kodayaushe wajen tabbatar da natsuwa da yaqini ta hanyar yin abin da zai faranta ran Manzon da nisantar abin da ba ya so.

Wannan magana bayyane ta ke ga duk wanda ya bibiyi diddigin tarihin waxannan Sahabbai, a lokacin rayuwa da bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Haka kuma abin da ya faru na natsuwa da jaruntaka da jajircewar Abubakar lokacin da suke cikin dabi tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ranar yaqin Badar da na Hudaibiyyah, duk ba a voye suke ba. To, ta yaya za a ce ya yi raggon kaya a waxannan lokuta?

Bayan wannan kuma, tsayin dakan da Abubakar ya yi ya yaqi waxanda suka yi ridda da waxanda suka yi watsi da rukunin zakkah, da yadda ya kwantar da hankalin muminai lokacin wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, da shirya rundunar Usamatu na daga cikin abubuwan da ke bayyana fifikonsa.

Babu wani daga cikin Ahlus-Sunnah da ke musun fifikon Abubakar a kan Umar da Usmanu. Kuma gaba xaya suna da yaqinin cewa, Ali bai fi waxannan ukun cika da kamala ba. Duk wanda ya leqa tarihin Umar da Usman zai tabbatar da sun fi Ali haquri da juriya da rashin firgita a lokacin sabkar musibu. Dubi lokacin da ‘yan tawaye suka yi wa gidan halifa Usmanu qawanya; suka hana shi shaqat. Suka ce, lalle sai ya yi murabus ko su aika shi lahira. Bai yi murabus xin ba, bai kuma bari a yaqe su ba. Ba batun ya bayar da umurni ga wasu su kare shi ake yi ba. Haka dai aka yi cirko-cirko har suka haura suka saka shi motar shahada ya isa wurin Ubangijinsa, yana mai cike da haquri da dattaku. Ashe wannan ba mafi girman jaruntaka ne ba?!

Amma ka ga shi Ali, tarihi ya tabbatar da cewa, haqurinsa bai kai na Usmanu ba. Domin kuwa da yawa yake kasa hanqurin ‘yan matsalolin da yake fuskanta daga dakarunsa, balle na abokan gaba. Savanin yadda Abubakar da Umar da Usmanu suka shanyen dafin duniya.

Kuma xan Shi’ar ya ce, wai ayar na nuna irin raki da qarancin haquri da yaqini, da rashin yarda da yin kafaxa-da-kafaxa da Annabi, da rashin amincewa da hukuncin qaddara da ke ga Abubakar. To, mun ji taka. Saurari tamu:

Zahiri take cewa ayar ta yi gabas xan Shi’ar ya yi yamma. Cewa kada a aikata abu ba ya nufin an riga an aikata. Iyakar abin da hanin ke nunawa shi ne, kada a aikata abin ko can gaba. Kamar yadda Allah Ta’ala ya ce wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama: Ya kai Annabi ka ji tsoron Allah, kuma kada ka yi xa’a ga kafirai da munafukai 33:1. Ka ga hakan ba ta nufin Annabi ba ya tsoron Allah, ko kuma yana xa’a ga waxannan mutane.

Mu qaddara cewa, Abubakar ya sami damuwar ya kuma yi baqin cikin, shi ya sa Annabi ya rarrashe shi. Ya yi haka ne don fargaban kada mushrikai su riske su su kashe Annabi, dashen musulunci ya yanqwane. Saboda haka kullum fatarsa ita ce, ya fanshi ran Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama koda shi nasa rai zai salwanta. Kamar yadda bayan fitarsu daga kogon yake kai wa da komowa gaba da bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suna kan hanya. Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tambaye shi dalili sai ya karva masa da cewa, ina shiga gabanka ne idan na tuna yiwuwar ka taka koda qaya ce. Idan kuma na tuna cewa, wani abu na iya kawo maka farmaki ta baya, sai in koma can. Ahmadu xan Hambali ya riwaito shi.

Haka kuma a lokacin, Abubakar bai yarda da zamansa katkatkat da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Amma ba da irin ma’anar da xan Shi’ar ke nufi ba. Abubakar bai yarda su mutu tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, kamar yadda bai yarda Manzon ya mutu ya bar shi a raye ba. Ya dai fi gurin ya fanshi ran Manzon da nasa ran da iyalinsa da dukiyarsa.

Ba ga Abubakar kawai ba, haka ya kamata kowane musulmi ya kasance tsakaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Kai hakan ma wajibi ne. Ka ga a wannan fage Abubakar Siddiqu ya xaga tuta. Ko banza Allah Ta’ala ya ce: Annabi ne mafi cancanta ga muminai bisa ga su kansu 33:6. Ya kuma zo a cikin Buhari da Muslim daga Anas daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Xayanku ba zai zama mai cikakken imani ba har sai na kasance mafi soyuwa gare shi fiye da ‘ya’yansa da iyayensa da mutane baki xaya.

Wannan baqin ciki da Abubakar ya yi, na nuna tsabar so da qauna da yake yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, da irin yadda yake shirye ya saxaukantar da rayuwarsa saboda shi, fai da voye. Wannan kuwa shi ne mafi qarfin imani.

Mu koma ga cewarsa, wai, hakan na nuna qarancin yaqinin Abubakar. Wannan magana varna ce gungumamma. Rarrashin ba ya nufin rashin koda irin wannan haquri da aka umurce shi da yi, balle wanda ba shi ba. Domin ai ka ga Alqur’ani da Sunnah sun wajabta wa musulmi xaukar qaddara, amma duk baqin cikin da mutum zai yi azuci, ba ya kore kasancewarsa mai haquri. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Haqiqa Allah ba ya kama kowa da laifi don zubar hawayen idaniya ko kukan zuci. Sai dai yana kama mutum da laifin abin da harshensa ya faxa, ko ya yi masa rahama a kansa”.

Ita ma cewar da xan Shi’ar ya yi wai, rarrashi na nuna rashin yaqinin da Abubakar yake da shi, ba magana ce da ke sauraruwa ba. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa, Annabawa sun yi baqin ciki a kan wasu abubuwa. Amma ba wanda zai ce hakan na nuna rashin yaqininsu da Allah sai shakiyyi. Allah ya bamu tarihin irin baqin cikin da Annabi Yaqubu ya yi. Kuma hadisi ya tabbatar da cewa, a lokacin da Ibrahimu xan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu, Manzon ya ce: “Idanunmu na zubar da hawaye, zuciyarmu na quna, amma duk da haka ba za mu faxi komai ba sai abin da Ubangiji ke yarda da shi. Tabbas muna baqin cikin rasuwar Ibrahim”.

Ko sahkka babu haka ta faru, tattare da cewa, Allah Ta’ala ya hana Manzon nasa yin baqin ciki inda yake cewa: Kuma kada ka yi baqin ciki a kansu 15:88.

Ita ma cewarsa wai, ayar na nuna raki da rashin yardar Abubakar da hukunci da qaddarar Allah, magana ce ta rashin fahimta.


9.9 Babu Shakka Abubakar ya Damu

Mutumin ya ce: Da a ce baqin cikin da Abubakar ya yi a lokacin, xa’a ne ga Allah, da Annabi bai taka masa burki ba. Idan kuwa savo ne, shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana shi, to, xaukakar da suke hange ta zama qasqasci kenan.


Martani:

Babu wanda ya ce don Abubakar ya yi baqin ciki ne kawai ya samu waccan xaukaka. Babu wanda ya ce haka. Xaukakar dai na nan cikin abin da Allah ya ce: Idan ba ku taimake shi ba, To, haqiqa Allah ya taimake shi a lokacin da kafirai suka fitar da shi suna su biyu a cikin kogo, a lokacin da yake ce wa abokinsa: Kada ka yi baqin ciki. Haqiqa Allah na tare da mu. 9:40.

Kasancewar Abubakar Raliyallahu Anhu wanda Allah ya azurta da fita tare da Annabi a wannan mawuyacin hali, ba tare da wata kwana ko gardama ba, shi ne abin da ya tabbatar da xaukaka da daraja ga baban A’ishah.

Ita kuwa cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa: Haqiqa Allah yana tare da mu 9:40 na nuna irin karvuwar da ya samu ne ga Manzon, da irin yadda ya yarda da qurbaninsa na so da qauna, ya kuma sami cikakkar natsuwa a cikin haka. Ko shakka babu, wannan irin gagarumar gudunmawa a irin wancan yanayi na tabbatar da cikar imani da tsoron Allansa. Wannan kuwa babbar daraja ce.

Bayan wannan kuma, horon da aka yi wa Abubakar da kada ya razana, na iya zama taimako gare shi na kauce wa faxawa cikin kogon damuwa. Domin kuwa ga al’ada baqin ciki kan mamayi mutum ne bai da wan ceto; ba kuma tare da ya shirya wa tahowarsa ba. Hakan kuma kan faru musamman a lokacin da babu wani sanadari da zai qarfafa masa guiwa ga hana wutar baqin cikin kamawa. Idan ko aka samu irin wannan sanadari kamar yadda ya samu ga baban A’ishah Raliyallahu Anhu to, qaryar baqin ciki ta qare.

Da ka dubi sigar waccan aya, za ka ga haka qarara. Domin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa mutumin nasa: Kada ka yi baqin ciki bai tsaya nan ba, sai da ya qara tsattsage sanadarin da cewa, Haqiqa Allah yana tare da mu. Ka ga ya cire masa tsoro a zuci, ya kuma damqa masa garkuwa a hannu. Irin haka kuwa ne kawai ke kare mutum daga allobar baqin ciki. Rashin haxuwar hancin waxannan abubuwa biyu wuri xaya ke sa mutum ya motsa kawai, ya ji shi tsamo-tsamo cikin ambaliyar sunu da tasko. Ballantana kuma, hanin da aka yi wa Abubakar daga yin wannan baqin ciki, ba yana nufin har ya riga ya yi xin kafin rarrashin ba. A’a, an dai rarrashe shi ne don ganin duk wani dalilin da ke sa mutum faxawa cikin baqin ciki ya haxu a kansa.

To, a irin wannan hali, koda yin baqin cikin savo ne, hakan ba zata cutar da mu da kome ba. Domin kuwa rarrashin da aka yi masa, ya karva sunansa na rarrashi da qarfafa guiwa, kai har ma jaje. Ka ga abin ya zama qaddara kenan ba savo ba. Ko tafi ma duk waxannan dalilai ba haka suke ba, ai baqin ciki kan riski mutum ne ba tare da ya shawarce shi ba. Ka ga a irin nan ba zancen savo.

To, kuma duk aje komai ma, babu wani mai cikakken hankali a duniya da zai zauna da mutum tsawon lokaci, irin yadda Annabi ya zauna shekaru kusan goma tare da Abubakar a Makka face ya gane mutumin nan masoyinsa ne ko maqiyinsa. Amma a ce har kawowa cikin wannan haxari Annabi bai san matsayin tarensa da Siddiqu ba, ai ka ga wannan mummunar suka ce ga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama.

Bayan kuma duk wannan ma, duniya ta san cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu babban masoyin Annabi ne tun daga lokacin da aka aiko masa da manzanci har zuwa rasuwarsa. Shi ne farkon wanda ya yi imani da shi, ya kuma gayyato wasu mutane suka yi. Ya saxaukantar da dukiyarsa wurin fansar waxanda suka bayar da gaskiya irin su Bilalu da makamantansa. Haka kuma Abubakar yana fita tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokutan hajji don kiran wasu qabilu zuwa ga imani. Babu ranar da ba ya zuwa gaban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama; in ba da safe ba da rana. Irin cutuwar da Abubakar ya yi a hannun kafiran Makka saboda kawai ya yi imani, sai wanda ya ji ko ya gani.

Da zarar an dubi wannan matsayi, za a tabbata cewa, taka irin wannan rawa da Abubakar ya yi sai wanda so da qaunar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suka keta naman jikinsa. Wannan kuma na nuna cewa, ba kawai zatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ya samu karvuwa ga Siddiqu ba, a’a, har manzancin da ya zo da shi. Saboda haka ne ma ya qi mutanensa, ya kuma yi gaba-da-gaba da aradu. A qarshe ma hakan ce ta sa ya ciyar da gaba xayan dukiyarsa ga muminai mabuqata.

Amincin da ke tsakanin Siddiqu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai qare ba sai da mai raba masoya ta raba su. Ba a tava jin ya cutar da shi koda da kalma xaya ba, balle qoqarin kashe shi kai tsaye ko ta hanyar ba shi wata cimaka, duk da kasancewarsa masu kevantuwa da shi dare da rana.

Sannan kuma idan aka dubi matsayin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na wanda Allah ke ba kariya, hakan na wajabta Allah ya sanar da shi abin da ke kimshe cikin zuriyar Abubakar na qiyayya da mugun nufi in har akwai su. Kamar yadda ya sanar da shi abin da ke cikin ran Abu Azzata na niyyar fatattaka shi alhalin ya zo yana bayyana imani. Hakanan kuma Allah ya sanar da shi abin da ke cikin ran Alhajabi ranar yaqin Hunainu lokacin da aka yi nasara a kan musulmi. Kuma Allah ya sanar da Manzon nasa abin da ke cikin ran Umairu xan Wahabu na son halaka shi a lokacin da Umairun ya zo Makkah a matsayin wanda ya musulunta. Ga shi kuma a lokacin yaqin Tabuka Allah ya sanar da shi mugun nufin da munafukai suka yi na kwance tamantakar taguwarsa.

Waxannan xaixaikun mutane kenan fa da saduwarsu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta xan lokaci ce. Ina ga Abubakar Raliyallahu Anhu wanda suke tare dare da rana gida da daji? A lokacin yaqin Badar ma shi kaxai aka bari tare da shi. Amma wai duk da haka a ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai san Abubakar na qin sa a zuci ba, abin da ko mai ‘yar qaramar qwaqwalwa na iya ganewa cikin xan qanqanen lokaci! Duk wanda ya zaci haka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da amininsa bai raga wa musulunci da musulmi ba. Mai irin wannan tunani kuwa koda ya yi haka ne akan jahilci da qoqarin bayyana irin son da yake ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama to, bai kamata qarancin iliminsa na addini ya hana shi gane cewa, ‘yan Shi’ah fa suna hannun riga ne da musulunci.

Wani abin mamaki kuma shi ne, cewar da ya yi wai, babu inda Alqur’ani ya ambaci saukar natsuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama face ya ambaci muminai tare da shi a cikinta in ba nan ba. Wai kuma babu naqasar da ta kai wannan. Marubucin yana qoqarin ya nuna Allah ya yi irin wannan magana a wurare da dama cikin Alqur’ani, alhali kuwa abin ba haka yake ba.

Natsuwar ma da Allah ya ce ya saukar a kansa, wa ya ke nufi? Manzo ne ko Abubakar? Malamai sun qari junansu sani. Kuma cewa, Abubakar ake nufi na qarfafa da xabi’ar lafuzzan da ayar ta zo da su. Domin lamirin “shi” ya rufa ma sunan Abubakar baya ne kai tsaye. Ta fuskar ma’ana kuwa, malamai suka ce, Abubakar ne ke da buqatar agajin natsuwa ba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Shi kam ai tasa natsuwar har ta yi oba. Kuma idan muka fahimci maganar a matsayin saukar da natsuwa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, to, ba kome. Kuma tun da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama xin ne ya ce masa a matsayinsa na xan rakiya: Haqiqa Allah yana tare damu, hakan na nufin duk natsuwa da agajin da za su sauka ga shi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayinsa na uban tafiya, to, sun haxa har da abokin tafiyarsa.
9.10 Abubakar ne Dai Ayar ke Nufi

Xan Shi’ar ya ce: Cewar da Allah Ta’ala ya yi: Kuma mafi taqawa zai nisance ta wai Allah na nufin Abud-dahadahu ne, kuma ya kawo qissar da ya jingina saukar wannan aya gare ta.


Martani:

Surar da wannan aya take cikinta gaba xaya ta sauka ne a Makka, kamar yadda malaman tafsiri da sauransu suka amfanar. Shi kuwa labarin Abud-dahadahi ya faru ne a Madina, domin shi kansa Ba’ansare ne da bai zauna da Annabi ba sai a Madina. Kuma a Madina kawai ake da gonakin da wannan labari da ya kawo ke iya faruwa a kansu. To, ina alaqarsa da wannan ayar? Sai dai mu ce hukuncinta ya haxa da shi. Wannan ita ce rinjayayyar magana.

Mu koma ma ayar mu gani. Allah Ta’ala cewa ya yi: Kuma mafi taqawa zai nisance ta 92:17 . Kuma a wata ayar Allah ya ce: Haqiqa mafificinku daraja a wurin Allah shi ne wanda yake mafificinku a taqawa 49:14. ka ga daga ma’anar waxannan ayoyi muna iya fahimtar cewa, duk wanda ya kasance mafificin taqawa a cikin al’umma to, dole ne ya shiga cikin wannan aya. Babu ko wani malami da ya tava cewa, Abud-dahadahi ne mafificin taqawa a cikin wannan al’umma koda ko malamin xan Shi’ah ne. Amma kan al’umma ya haxu bisa ga cewa, Abubakar ne yake da wannan matsayi.

Idan wanda ke ciyar da dukiyarsa don neman ya tsalkaka shi ne mafificin taqawa, kuma mafificin girma a cikin halitta shi ne mafificinsu taqawa, to lalle kuwa shi ne mafificin daraja.

To, wane ne mafi taqawa da ya zo a wannan aya? Ahlus-Sunnah sun ce, Abubakar. A yayin da ‘yan Shi’ah suka ce, Ali. Dalilai da dama kuwa na nuna cancantar Abubakar da zama wanda wannan aya ke nufi. Ga wasu daga cikinsu:
Na Farko:

Cewa Allah ya yi: Wanda yake ba da dukiyarsa yana tsalkaka 92:18. Wanda tarihi ya tabbatar da ciyarwarsa ga musulunci kuwa, shi ne Abubakar. Amma shi Ali abin da tarihi ya nuna shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ne ke xauke da nauyinsa tun lokacin da ya xauko shi daga wurin mahaifinsa Abu Xalib, a sakamakon wata yunwa da aka yi a Makka. Ya ci gaba da rayuwa a matsa kaicin hali har zuwa lokacin da ya auri Fatima. Ko bayan wannan aure mai albarka Aliyu bai fita daga gandun gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayinsa na wanda Annabin ke tallafa ma ba.

A sane muke, da Allah ya hore masa abin ciyarwar da ya ciyar. Wannan magana da muke faxi sananna ce qwarai ga Ahlus-Sunnah da ‘yan Shi’ah.
Na Biyu:

Cewar da Allah Ta’ala ya yi: Alhali babu wani mai wata ni’ima wurinsa, wadda ake neman sakamakonta 92:19 na nufin Abubakar Raliyallahu Anhu ba Ali ba. Abin da ke tsakaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ni’ima ce ta imani, wato, ba don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba da Abubakar Siddiqu bai tsere wa wuta sanadiyyar yin imanin ba. Biyan bashin irin wannan ni’ima kuwa sai dai Allah; ba mutum ba. Amma abin azzikin da ake iya mayar da hannun baiwa a kansa, shi ne ni’imar abin duniya. Bukin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Abubakar kuwa na addini ne. Wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa bukin ni’imar abin duniya shi ne Ali.


Na Uku:

Abubakar ne wanda ba shi da wani dalili na kashe dukiyarsa saboda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai dalilin imani. Ba kamar yadda Abu Xalib ya taimake shi saboda zumunta ba. Taimako da hidimar da Abubakar ya wa musulunci ya yi su ne kawai don neman yardar Allah Ta’ala. Kamar yadda Allah ya shedi hakan da cewa: Face don neman yardar Ubangijinsa mafi xaukaka. To, haqiqa zai yarda da sakamakon da za a ba shi 92:20-21.


9.11 Shi wannan Ayar ke Nufi

Xan Shi’ar ya ce: Cewar da Allah Ta’ala ya yi: Ka ce wa waxanda aka bari daga qauyawa 48:16 na nufin waxanda ba su fita zuwa yaqin Hudaibiyyah ba. Amma kuma suka so fita zuwa samun ganimar yaqin Haibara. Wai, sai Allah Ta’ala ya hane su, inda ya ce: Ka ce ba za ku bi mu ba 48:15 ya ci gaba da cewa wai, Allah ya yi haka ne saboda ya kevance ganimar Haibara kawai, don waxanda suka halarci yaqin Hudaibiyyah. Daga baya kuma Allah Ta’ala ya ce: Ka ce wa waxanda aka bari daga qauyawa za a kira ku zuwa ga waxansu mutane masu tsananin qarfin yaqi 48:16 kuma wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kira su bayan haka zuwa ga yaqoqa da yawa kamar yaqin Mu’utah da na Hunainu da Tabuka da sauransu.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Ka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne wanda ya yi kiran ba Abubakar ba. Tana kuma iya yiwuwa ayar ta kasance tana nufin Aliyu ne wanda zai yi kiran. Domin shi ne bayan haka ya yaqi fanxararru da kangararru da ‘yan tawaye. Dawowa da ya yi da su kuwa ga yi masa xa’a dawowa ne da su a cikin musulunci, domin sun kafirta kafin hakan. Hakan na tabbata ne, inji shi, idan muka dubi faxar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya ce: “Ya kai Ali, duk wanda ya yaqe ka ya yaqe ni ne”. Ya ce: Ka ga duk wanda ya yaqi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tabbas kafiri ne.
Martani:

Wasu daga cikin malamai sun riga sun kafa hujja da wannan aya da ta gabata a kan halifancin Abubakar Raliyallahu Anhu da wajabcin yi masa xa’a. Malaman kuwa sun haxa da, Imamus Shafi’i da Ash’ari da Ibnu Hazam da wasu ba su ba. Hujjar da suka kafa a kan wannan fassara ita ce faxar Allah Ta’ala da ya ce: To, idan Allah ya mayar da kai zuwa ga wata qungiya daga cikinsu, sa’annan suka neme ka izini domin su fita, to, ka ce, ba za ku fita tare da ni ba har abada, kuma ba za ku yi yaqi tare da ni ba a kan wani maqiyi 9:83.

Malaman suka ce, da wannan aya ne Allah Ta’ala ya umurci Manzonsa da ya gaya wa waxancan mutane da suka fita yaqin Hudaibiyyah cewa, tunda haka ne, to, ku yi ta zama, har abada ba zan sake neman fita yaqi tare da ku ba, ko kun so hakan.

Suka ce kuma, harwayau dai wannan aya ta tabbatar mana da cewa, wanda zai sake kiransu zuwa ga yaqi, ba Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne ba. Sai dai wani bayansa. Ka ko ga ba kowa bayansa sai waxannan halifofi da aka sani. Su ne suka kira mutane zuwa ga yaqar Farisawa da Rumawa waxanda sun fi kowa cancantar waccan siffa da aya ta faxa ta cewa Masu tsananin qarfin yaqi 9:16. Kuma su ne kafiran da waxancan halifofi uku suka yaqa a kansu musulunta.

Daga wannan ingantattar fassara sai a fahimci cewa, makamar wannan aya ita ce: Za a kira ku zuwa ga waxansu mutane masu tsananin qarfin yaqi, domin ku yaqe su ko kuwa su musulunta. Ka ga idan aka fahimci ayar a haka, sai siffar waxancan mutane ta tsananin yaqi ta fito tare da umurnin da aka ba waxancan jemagu na su yaqe su ko su musulunta.

Malaman suka qara daddale wannan fassara tasu da cewa, ba ta yiwuwa ko kaxan a kira mutane zuwa ga waxancan yaqe-yaqe da aka yi da mutanen Makka bisa cewar xan Shi’ar dab da qarewar shekarar nasara. Domin kuwa ai su ne aka so su fito ayi yaqi a Hudaibiyyah. Koda kuwa ana hangen cewa, ba dukansu ne mutanen wannan wuri ba, tabbatacciyar magana dai ita ce, duk jirgi guda ya xauko su.

Wani dalilin kuma da malaman suka kafa shi ne, su mutanen da aka yaqa a wannan shekara, basu fi waxancan da suka qi fita tare da Annabi tsananin yaqi ba; dukansu Larabawan Hijaz ne, dabarun yaqinsu kuma kala xaya ne. kuma ma irin wuyar da mutanen Makkah da maqwabtanta suka gana wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabbansa a wajen yaqin Badar da Uhudu da Handaqu ta fi waccan da suka sha a hannun waxancan qabilun a shekarar yaqin Hudaibiyyah, da waxansu yaqe-yaqe da ba waxannan ba. Ka ga kenan sai dai a kira su zuwa ga yaqar wani jinsi na mutane ba waxannan ba.

Shi kuwa Annabi ya ce ma Ali: “Duk wanda ya yaqe ka ya yaqe ni”, hadisi ne da bai isa a kafa hujja da shi ba. Domin kuwa ko isnadinsa xan Shi’ar bai ambata ba. Kuma ta tabbata a wajen malaman hadisi cewa jabun hadisi ne.

Idan kuma muka koma ga cewar xan Shi’ar, wai, tana yiwuwa mai wancan kiran ya kasance Ali ne ba xaya daga cikin halifofin uku ba. Saboda wai shi ne ya yaqi tsageru da kangararru da ‘yan tawaye. Wato, yana nufin rundunar da ya kara da ita a bayan A’isha Raliyallahu Anha da ta mutanen Sham da ke bayan Mu’wiyah. Sannan Harijawa da ya yaqa a Harura. To, wannan magana ta xan Shi’ar ba ta bisa hanya saboda la’akari da abubuwa da dama.

Waxannan mutane da Ali ya yi yaqi da su ba su fi ‘yan’uwansu da ke gida tsananin yaqi ba. Kuma ma sanannen abu ne cewa, mutanen da ya haxu da su a yaqin basasar Raqumi ba su kai yawan dakarunsa ba. Ba zance Harijawa ‘yan-aware ake yi ba, waxanda rundunarsa ta ninka su fiye da biyu. Haka kuma ta fi waxanda ya haxu da su a Siffin. Duk waxannan jama’a da ya yaqa a waxannan lokuta ba su xara ‘yan’uwansu na gida da komai ba a fagen qarfin yaqi balle har Alqur’ani ya siffanta su da kasancewa haka.

Amma sanannen abu ne cewa, mutanen bani Hanifata da Farisawa da Rumawa sun fi waxancan mutane da Aliyu ya yaqa tsananin qarfin yaqi. Irin yadda rayuka suka salwanta a cikin rundunar da Abubakar ya yaqi waxancan isassun qabilu da ita, ko kaxan ba su salwanta hakanan a rundunar Ali ba a yaqinsa da Larabawa. Dubi yaqin da halifa Abubakar ya yi da jama’ar Musailama, su Farisawa da Rumawa ba ma maganarsu ake yi ba. Domin babu wani mai cikakken hankali da ke musu, ko shakkar kasancewar su mutane masu tsananin yaqi, idan sun gamu da abokan gaba fiye da yadda Larabawa za su yaqi junansu wa-su-wa-su. Wuyar da musulmi suka sha a hannun Larabawa kafirai a farkon musulunci, ba ta kasance saboda tsananin yaqinsu ba, ta dai kasance ne saboda rashin yawan muminai da raunin da suke da shi a lokacin. Amma ko kaxan kafiran na Makka ba su yi tsananin yaqin Farisawa da Rumawa ba.

Kuma abin da kowa ya sani ne, Aliyu bai kai wa kowa goron gayyar yaqi daga cikin mutanensa ba, don yaqar mutanen Raqumi da Harijawa. Hasali ma koda ya iso birnin Basrah bai iso da niyyar yaqi ba, kamar yadda Xalhatu da Zubairu ba su zo da ita ba, qaddara ce kawai ta riga fata. Su ko Harijawa saboda rashin yawansu, wani sashe ma na rundunarsa na iya gamawa da su nan take. Saboda haka, ko mutum xaya daga cikin Larabawan qauyen Hijaz bai gayyato don yaqarsu ba.

Koda kuma mun qaddara cewa, wajibi ne a yi wa Aliyu xa’a a cikin yaqe-yaqen da ya yi da waxancan mutane ‘yan’uwansa. To, ai ya sava wa hankali a ce Allah Ta’ala ne ya yi umurni da a bi shi wajen yaqar masu mayar da gaba gabas su yi sallah, don neman su yi biyayya ga shugabancinsa, amma bai yi umurni da yin biyayya ga waxanda ke yaqar kafirai tuburan don neman su yi imani da Allah da Manzo ba. Ko ko mu xauka cewa ma waxanda Ali ya yaqa xin kafirai ne, to, ai kafircinsu bai fi na wanda shi asalatan bai tava alwalla ba balle ya kabbarta. Hasali ma fito-na-fito ya yi da Manzon ya kuma qaryata Alqur’anin da ya zo da shi. Ko shakka babu zunubin irin wannan mutum na farko shi ne mafi girma. Kuma ladar da za a samu a cikin qoqarin ya shigo musulunci ta fi wadda za a samu ga na biyun girma.

Haka kuma koda za mu yarda da cewa, waxanda Ali ya yaqa an xauka sun yi ridda ne su ma, kamar yadda ‘yan Shi’a ke cewa. To, ai sanannen abu ne cewa, riddar wanda har ya kai ga imani da akwai wani Manzo wanda ba Muhammadu ba kamar mabiyan Musailamu, ta fi nauyi bisa ga wanda wani shugaba ne kawai bai yarda da shugabancinsa ba, amma yana nan a matsayinsa na wanda ya yi imani da manzancin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama.

Ala ayyi halin, babu wani zunubi da za a ce waxanda Aliyu ya yaqa na da shi, face wanda mutanen da halifofin can uku suka yaqa ke da shi ya fi girma. Kamar yadda babu wata lada da daraja da za a ce waxanda suka taimaka wa Ali a waxancan yaqe-yaqe sun samu, face waxanda suka taimaka wa halifofin can uku a cikin nasu yaqe-yaqen sun samu mafi girma. Wannan ma idan mun qaddara kasancewar waxanda Ali ya yaqa kafirai, wanda kuwa tabbas ba haka ba ne. Duk ma wanda ka ji haka a bakinsa, to, ka tabbata ko cikin ‘yan Shi’ah bara-gurbi ne. Amma masu sauran hankali da tunani cikinsu ba su faxar haka. Ga shi kuma an riwaito ta hanyoyi da dama daga Aliyu da mutanen gidansa cewa, waxanda suka yaqe shi ba kafirai ba ne.

Duk wannan dawara da muke yi za ta samu gindin zama ne, idan mun yarda da cewa, waxancan yaqe-yaqe da Ali ya yi karvavvu ne a idon musulunci, wanda ko ba haka ba ne. Domin kuwa magabata sun tambayi kansu, shin waxannan yaqoqa daidai suke da yaqar ‘yan tawaye irin waxanda shari’a ta wajabta a yaqa? Ko kuwa ba irinsa ba ne?

Abin da manyan Sahabbai da Tabi’ai suka tafi a kai shi ne, yaqin basasar da Ali ya yi da magoya bayan A’ishah Raliyallahu Anhu da wanda ya yi da magoya bayan Mu’awiyah Raliyallahu Anhu a Siffin duk ba yaqi ne da Allah ya yi umurni da yi ba. Kuma da Allah ya sa bai yi yaqe-yaqen ba da haka ta fi zama alheri. A wajen waxannan magabata waxannan yaqe-yaqen fitinnu ne kawa, wato basasa. Wannan ra’ayin kuwa shi ne akasarin malaman Hadisi da na Fiqihu suke a kai.

Ita kuma wannan aya da muke ta magana a kanta ba ta nufin yaqi a bayan Ali kai tsaye. Domin yaqin da ya yi ba da kafirai ya yi shi ba. Kuma ai ka ga ayar cewa ta yi: Ku yaqe su ko su musulunta. Ka ga ko duk waxanda Ali ya yaqa sun riga sun musulunta gabanin yaqinsa. Kuma daga cikin waxanda ma ya far ma, akwai waxanda ba su yarda suka yi yaqin da shi ba, ba su kuma yaqi kowa tare da shi ba, sai suka kama kansu. To, kuma kan haka ko waxanda suka yaqe shi xin ba a ce musu kafirai. Kuma Alqur’ani da Hadisi da haxuwar kan Sahabbai har da Aliyun, duk sun tabbatar da haka. Ga abin da Allah Ta’ala ke cewa:

ﭽ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﭼ الحجرات: ٩

Kuma idan jama’a biyu ta muminai suka yi yaqi, to, ku yi sulhu a tsakaninsu. Sai idan xayarsu ta yi zalunci a kan xaya, to, sai ku yaqi wadda ke yin zaluncin har ta koma zuwa ga umurnin Allah. To, idan ta koma sai ku yi sulhu a tsakaninsu da adalci, kuma ku daidaita, lalle Allah na son masu daidaitawa 49:9.

Ka ga duk da yaqin da ya wanzu tsakanin waxannan qungiyoyi na musulmi, Allah bai tuve masu rigar imani ba. In don tawaye kuwa, da rashin miqa wuya ga wani shugaba, ba zai fitar da mutum daga sahun musulmi ba. Haka kuma a cikin ayar Allah Ta’ala ya gaya mana ci gaba da kasancewarsu ‘yan’uwa. Ka kuwa san ‘yan’uwantaka ba ta kasancewa tsakanin mumini da kafiri, sai dai tsakanin musulmi tsintsa.

Amma ka ga wannan xan Shi’ar kamar bai san da akwai wannan aya ba, ba mu ce bai yarda da ita ba. Sai ga shi kai tsaye ya kafirta waxancan mutane. Har kuma da cewa, wai yaqarsu da Ali ya yi, ya yi ne don ya dawo da su cikin sahun musulmi. Har ya kafa hujja da wai Annabi ya ce, wanda ya yaqi Ali ya yaqe shi.

Babu abin mamaki da ta kaicin da ya kai cijewar da ‘yar Shi’ah suka yi a kan wannan yasasshen ra’ayi suna masu dogaro da wannan yasasshen hadisi. Hadisin da ko bayan rashin madogararsa ya sava ma ingantattun maganganun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da aka sani cewa, barin yaqi a cikin fitina ya fi alheri a kan yin sa, da kuma yabon da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wanda ya sasanta tsakaninsu.



Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   43   44   45   46   47   48   49   50   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin