Tawassali



Yüklə 184,14 Kb.
tarix28.10.2017
ölçüsü184,14 Kb.
#17730

Nuruddeen Ibn Muhammad

(Darus-thaqalain)

064-328677, 07028041972,

08037761798, 08098001766,

e-mail: darusthaqalain@yahoo.co.uk





TAWASSALI
GABATARWA

Bismillaahir Rahmanir Rahiim, wasallallahu alan-Nabiyyi Muhammad wa Aalihix-xayyibiinax-xaahiriin.


Haqiqa Al-qur'ani mai Girma ya kawo siffar haqiqanin yadda Tawassali (Kamun-qafa) yake, a inda Ubangiji Maxaukaki yake faxawa Muminai cewa:

"يا أيها الذين آمنوا اتقوا الله وابتغوا إليه الوسيلة وجاهدوا في سبيله لعلكم تفلحون"

Ma'ana:
"Yaku waxanda suka yi imani kuji tsoron Allah, sannan ku nemi mai yi muku iso zuwa gare shi (Allah) kuyi jihadi akan tafarkin Sa ko kun sami dace" (suratul-ma'idah: 35).


Haqiqa wannan Ayar mai girma ta ambaci tsoron Allah da jihadi daga cikin abubuwa na shari'a da za'a iya kamun-qafa (Tawassali) dasu zuwa ga Ubangiji.
Shin akwai wata hanyar kamun-qafar (Tawassali) daban wacce shari'a tayi kira gare ta, ko kuwa an bar al'amarin ne kawai ga mutum abisa ikonsa ya zavi wata hanyar daban ta kamun-qafa (Tawassali) domin samun kusanci ga Ubangiji?
Abin da yake a fili valo-valo shine haqiqa hanyar da Bawa zai iya kamun-qafa (Tawassali) da ita domin samun kusanci zuwa ga Ubangiji qofa ce buxaxxiya da za'a iya yin ijtihadin ta. Ta yadda kusanci ga Ubangiji da hanyoyin tabbatar da shi na buqatar shiryarwa ne daga Ubangiji. Domin wannan shine abinda shari'a tayi bayani akai, kuma ta bada Nassi akai, ta kuma kawo a cikin Qur'ani da Sunnah. Don haka dukkanin Kamun-qafar (Tawassali) da ba shari'a ce ta bada Nassi akansa, ba a kevance ba ko a tattare to wani sashe ne na Bidi'a da Vata.
Imam Ali Amirul-Muminina (alaihis-salam) yayi nuni zuwa ga Kamun-qafar (Tawassali) da zai kusanta Bawa da shi zuwa ga Ubangiji, da faxin sa:
" إن أفضل ما توسل به المتوسلون إلى الله سبحانه وتعالى, الإيمان به وبرسوله والجهاد في سبيله. فإنه ذروة الإسلام, وكلمة الإخلاص فإنها الفطرة, وإقامة الصلاة فأنها الملة, وإيتاء الزكاة فإنهما فريضة واجبة, و صوم شهر رمضان فإنه جنة من العقاب, وحج البيت واعتماره فإنهما ينفيان الفقر ويرح ضان الذنب. وصلة الرحم فغنها مثارة في المال, ومنشأة في الأجل, وصدقة السر فإنها تكفر الخطيئة, وصدقة العلانية تدفع الميتة السوء وصنائع المعروف فإنها تقي مصارع الهوان.

Ma'ana:
"Mafi kyawun abin da masu Tawassali za suyi Tawassali (Kamun-qafa) dashi zuwa ga Allah Ta'ala, Imani da Allah da Manzon sa da Jihadi akan Tafarkinsa, yin hakan kaiwa ne qololuwa a Musulunci, tare da yin Tsantseni wanda shine matakin farko, hakanan da yin Sallah akan lokacin ta cikakkiya don kuwa shine Imani, da bada Zakka don ita farilla ce kuma wajiba, da azimtar watan Ramadana saboda kuvuta ne daga uquba, sannan aikin Hajji dana Umara domin suna kore rashi kuma suna wanke Zunubai, da sada Zumunci don yana havaka dukiya da qara tsawon Rai, hakanan da yin Sadaka a voye domin tana kare mutum daga aikata kuskure, da yin Sadaka a fili shi kuma yana kare mutum daga mummunar mutuwa, da aikata ayyuka kyawawa don yana kare mutum daga mutuwar qasqanci".
Al-qur'ani mai Girma yayi nuni akan halayya kyakkyawa abar so ga Musulmai, inda Ubangiji yake cewa:
"ولو أنهم إذ ظلموا أنفسهم جاءوك فاستغفروا الله واستغفر لهم الرسول لوجدوا الله توابا رحيما" (النساء: 64)

Ma'ana:
"Da ace zasuyi aiki mummuna kuma suzo gurin ka (suna Kamun-qafa) su tuba ga Allah sannan Manzon (Allah) ya nema musu gafara to da Allah zai gafarta musu ya jiqan su" (Suratun-nisa' :64).


Irin wannan aiki abin yabawa na yanayin rayuwar Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) tsakanin Musulmi bazai qidanyu ba. A bayan Ubangiji Ta'ala yana cewa:
"ولا تحسبن الذيت قتلوا في في سبيل الله أمواتاً بل أحياء عند ربّهم يرزقون" (آل عمران: 169).

Ma'ana:
"Kada ku zaci waxanda aka kashe su akan tafarkin Allah matattu ne a'a rayayyu ne a gurin Ubangijin su yana azurta su" (Aali Imarana: 169).


Don haka ne Tawassalin ya zamo wani Ibada da ya kasance ana aikata shi har bayan wafatin sa (Sallallahu alaiHi wa AliHi) har wala iyau, wanda Musulmai sun fahimci halascin hakan kuma suka kasance suna aikatawa bayan wafatin sa, kamar yadda wasu daga cikin masu Tafsiri suka tafi akan haka (duba Tafsirin Malam Ibn Kathir 1\532).
Don haka babu wani hani ga neman alaqa da Ubangiji tare da neman gafarar Zunubai daga gare shi. Ko kuma neman biyan buqata ta duniya da lahira ta hanyar Tawassali (Kamun-qafa) da Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi), ya nema musu gafara saboda la'akari da kusancinsa ga Allah da samuwar sa mai Girma a gare shi. Wannan hanya ce da shari'a ta yaba kuma Qur'ani ya nuna.
Don qarin bayani sai mu bi wannan bahathi (Bincike) cikin waxannan alamomi masu zuwa:
NA FARKO: Tawassali a mahangar Masana Yare (Lugha) da Masana Al'ada, Yanayi da Amfani (Isxilaah).

NA BIYU: Ra'ayuyyuka kan hukuncin Tawassali.

NA UKU: Halascin Tawassali a cikin Qur'ani.

NA HUDU: Tawassali a cikin Hadisan Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi).

NA BIYAR: Tawassali a cikin Tarihin Musulmi.

NA SHIDA: Tawassali a gurin Ahlul-Baiti (Alaihimus-salam).

NA BAKWAI: Tattaunawar masu tunani kan halascin Tawassali da yarda da shi ga Shari'a.

NA FARKO


TAWASSALI A LUGA DA ISXILAAHI
Yazo a cikin "Lisaanul-Arab": wasiila a gurin Sarki. To wasila anan tana nufin: Matsayi (Daraja), haka nan dai tana nufin: Kusanci, "wa wasala fulaan ilallahi wasilatan" wato anan kenan idan mutum ya aikata aiki ya kusanta shi ga Alllah. "Al-waasilu": anan shine mai kwaxayi ga Allah. Lubaidu yace:
"أرى الناس لا يدرون ما قدر أمرهم *** بلى كل ذي رأي إلى الله واسل"

Ma'ana:
"Naga mutane ba su san qimar lamarin su ba *** E, dukkanin wani mai Ra'ayi ga Ubangiji yake kwaxayi"


"wa Tawassala ilaihi bi wasiilatin" ma'ana: "Sai yayi Kamun-qafa gare shi da tsani" "izaa taqarraba ilaihi bi amalin" ma'ana: "yayin da ya kusance shi da wani aiki", yayi tsani gare shi da kazaa: ya kusance shi da girmamawa wacce take tare da kulawa a gare shi. "Al-wasiilatu" anan tana nufin: Isuwa, da Kusanci, wanda jam'in ta shine: "Al-wasaa'il", Allah Ta'ala yana cewa:
"أولئك الذين يدعون يبتغون إلى ربهم الوسيلة أيهم أقرب" (لسان العرب لابن منظور جزء 11 مادة وسل).
Ma'ana:
"Waxannan waxanda suke kira suke neman kusacin Ubangijin, waye cikinsu yafi kusaci gare Shi"
Hakanan sauran litattafai na Qamus sun qoqarta wajen kawo misalai akan "Wasiilah", da cewar ma'anarta na daga cikin abubuwan da fahimtar su yake a fili, kuma haqiqar ta bata buqatar xaukar wani abu wanda shine zai zamo kamar wani tsani zuwa ga wani al'amarin daban da zai zamo shine maqasudi ko abin nema, ita ta sava ta yanayin savawar qudurai.
Wanda duk ya nufi yardar Allah Ta'ala, yana Kamun-qafa da kyawawan ayyuka wanda dasu yake neman yardar sa. Wanda yaso ziyarar Xakin Allah mai tsarki yana Kamun-qafa da abinda zai kai shi zuwa gare shi (Attawassul fis-shari'atul-islamiyya, Malam Ja'farus-Subhaani: 17).
Malam Ibn Kathir akan Tawassul yana cewa: shine mutum ya sanya wani tsani tsakanin sa da Ubangiji don ya biya masa buqatar sa ta sanadin wannan tsanin da yayi Kamun-qafa dashi. (Tafsir Ibn Kathir: 1\532).

NA BIYU
RA'AYUYYUKA AKAN HUKUNCIN TAWASSALI


Amma kafin mu fara kawo dalilai akan Tawassali da shari'ancin sa sannan tattaunawa akansa ya kamata mu xauko wasu ra'ayuyyukan da aka ruwaito su a game da Tawassali waxanda suke nuna Halasci da kuma Hani.
RA'AYI NA FARKO: HANI DAGA YIN TAWASSALI
Malam Albaani yace akansa (Tawassali) yana xaukar sa daga vata, a cikin littafinsa (Attawassul Anwaa'uhu, Ahkaamuhu), sannan a gabatarwar (Sharhux-Xahaawiyyah) yace: haqiqa Magana kan Tawassali ba magana ce da ta shafi Aqida ba.
A cikin masu hanin akwai Muhammad bn Abdul-Wahhab, inda yake cewa: "yayin da mushirikai suka ce maka (Yana nufin sauran Musulmai ba Wahabiyawa ba) "Alaa inna Auliyaa'ullaahi laa khaufun alaihim walaa hum yahzanun" (Surati Yunus: 62) ko kuma suka ce Ceto gaskiya ne, ko kuma suka ce Annabawa suna da wani babban matsayi a gurin Allah, ko suka ambaci wata magana ga Annabi da yake nuna shi akan vacin sa (Yana nufin Ceto da …..) wanda kai baka gane ba, (Ai ba zaka iya yin bayanin sa ba) to ka gaya masa cewa: haqiqa Allah ya ambata a cikin Littafinsa; waxanda zuciyoyin su suke kan vata suna barin abinda yake hukuntacce ne suyi riqo da abubuwa masu rikitarwa" (Kashfus-Subuhat na Malam Muhammad Abdul-Wahhab: 60).
Hakanan dai daga masu tafiya akan hanin akwai Malam Abdul-Aziz bn Abdullahi bn Baaz, inda yake cewa: "Wanda ya roqi Annabi ya nemi ceton sa to ya vata Musuluncin sa" (Mukhaalafatul-Wahaabiyyah lil-Qur'ani was-Sunnah li Umar Abdus-Salam: 20, wanda aka ciro daga AL-aqiidatus-sahiihah wa nawaaqidul-Islam li Abdul-Aziz bn Abdullah bn Baaz).
RA'AYI NA BIYU: MAGANA AKAN HALASCI
Malam Shaukaani Az-zaydii ya tafi akan halascin Tawassali a cikin littafin sa (Tuhfatuz-Zaakiriina) da faxin sa cewa: "yana Kamun-qafa zuwa ga Allah Maxaukakin Sarki da Annabawansa da Salihai" (Tuhfatuz-Zaakiriina lis-shaukaanii:37).
Hakanan Malam Samhuudii As-shaafi'ii, yayin da yace: "Ana iya yin Tawassali da shi (Sallallaahu alaiHi wa AaliHi) da neman wani al'amarin daga gare shi, da nufin Shi (Sallallahu alaiHi wa AaliHi) yana da iko wajen sanadin biya masa buqatar sa da ceton sa a gurin Ubangijin sa, sai ya zam ya dawo yana neman addu'ar sa duk da dai lafazin ya sava. Akwai wani faxin da yake cewa akan sa "Ina roqon rakiyar ka a Aljanna…….bawai yana nufin sa ba ne (Sallallahu alaiHi wa AliHi) sai dai kawai ya zamo masa sanadi kuma mai ceto". (Wifaa'ul-wafaa' bi akhbaari darul-Musxafaa lis-Samhuudii:2\1374).
Sannan dai Malam Ibn Taimiyya ya ciro daga Malam Ahmad bn Hanbali a cikin (Mansikul-Marwazii) yin Kamun-qafa da Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da addu'a a gare shi. Hakanan dai ya ciro daga Malam Ibn Abid-Dunyaa da Malam Baihaqiy da Malam Xabaraaniy ta hanyoyi daban-daban waxanda akayi musu shaida da inganci (Attawassul wal-wasiilah: libni Taimiyya:144 – 145).
Cikin masu ra'ayi akan halascin akwai Malam Shaafi'ii, shi abinda yace: "Ni ina neman albarka da Abi Haniifah sannan naje qabarin sa kowace rana, duk lokacin da naji ina da wata buqata nakan yi Sallah raka'a biyu sai nazo qabarin nasa na roqi Allah buqata ta a gare shi, nan kusa sai ta biya" (Taariikhu Bagdaad: 1\123 'babi maa zakara fii maqaabiru Bagdaad').
Akwai dai daga cikin waxanda suka tafi akan halascin Malam Abu Aliy Al-khilaal Shaikhul-Hanaabilaa, inda yace:"Babu wani abu da ya tava taso mini naje qabarin Musa bn Ja'far (Alaihis-salaam) nayi Kamun-qafa da shi sai Allah ya yassare mini abinda nake buqata" (Taariikhu Bagdaad: 1\120 'babi maa zakara fii maqaabiri Bagdaad).
Amma mabiya Mazahabin Ahlul-Baiti (Alaihimus-salam) su cewa sukayi: ya halasta yin Tawassali da Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi), da A'immah (Alaihimus-salam), a wajen biyan buqatu da yaye qunci bayan mutuwar su, kamar yadda ya halasta ma yayin da suke raye. (Al-Baraahiinul-Jaliyyati fii daf'i tashkiikaatil-wahaabiyya, Sayyed Muhammad Hasan Al-qazwiinii Al-Haa'irii: 30).
RA'AYI NA UKU: SAVANI TSAKANIN NAU'O'IN TAWASSALI
Wannan ra'ayin na Malam Ibn Taimiyya ne, sai dai zamu taras wani ra'ayi ne mai rikitarwa a vangaren Maganar kan Tawassalin. Wani lokacin sai a taras yana tsakanin rashin halasci da kuma halasci sannan da kasuwa ta uku. A waxannan kason nasa ta fagen Kamun-qafa an halasta biyu an haramta na ukun. Yace: furucin Tawassali na buqatar ma'anoni guda uku:

  1. Kamun-qafa da biyayyar Annabi da Imani da shi. Wannan shine tushen Imani da Musulunci, wanda kuwa yaqi hakan, to kuwa kafircin sa a bayyane yake a gurin dukkanin Al'uma.

  2. Kamun-qafa da addu'arsa da cetonsa: abin nufi anan Annabi shine wanda yake addu'a yake ceto kai tsaye – wanda kuwa ya zamanto ne a cikin yana raye, kuma zai kasance ranar tashin Alqiyama ana Kamun-qafa da cetonsa. Dukkanin wanda ya qaryata wannan ya kafirta yayi ridda sai ya tuba, idan ya tuba shike nan idan kuwa yaqi to a kashe shi yana mai ridda.

  3. Kamun-qafa da cetonsa bayan mutuwarsa: da yin rantsuwa da Zatin Allah wanda wannan yana daga cikin abin da aka faras daga baya. (duba cikin: Attawassul wal-wasiilatu: 13, 20, 50.)


NA UKU: HALASCIN TAWASSALI ACIKIN QUR'ANI MAI GIRMA
Annabawa da Salihai sunyi Magana akan cewar haqiqar Tawassali tamkar Ibada ce da shari'a ta shar'anta, wacce ba zata tava fita daga sahun shari'a ba. Al-qur'ani mai tsarki ya kawo mana abubuwa da daman gaske waxanda mutane sukayi Kamun-qafa dasu da Annabawa da Waliyyai domin kusanci zuwa ga Allah Ta'ala; wanda yakasance tabbacin hakan na daga bayan yin addu'o'insu sai biyan buqatun su. A cikin waxannan abubuwa waxanda nassi yazo da su cikin Al-qur'ani akwai:
A – Allah yana cewa:
"وأبرئ الأكمه والأبرص وأحيي الموتى بإذن الله" (آل عمران : 49)

Ma'ana:
"Ina warkar da Makafi da masu Mele ina raya matattu da izinin Allah" (Aali Imraan :49)
Anan zamu samu mutane suna Kamun-qafa da Annabi Isah (Alaihis-salam), sai dai wannan Kamun-qafar basa ganin cewar daga Imanin su ne suke ganin Annabi Isah yana da wata dama ba damar Ubangiji ba. Sai dai kurum don gundarin Imanin su, cewar Annabi Isah yana da wata dama da zai iya warkar da marasa lafiya da izinin Allah, domin kasantuwarsa yardajje a gurin Ubangiji. Don haka ba za'a ce wannan Shirka ne ba. Domin kuwa Shirka shine yin quduri da yin Imani da cewar Annabi Isah yana da wata dama da ta kevantu da Allah, wanda babu xaya daga cikin Musulmi da yake da qudurin hakan.
B – Allah Ta'ala yana cewa :
"قالوا يا أبانا استغفر لنا ذنوبنا" (يوسف : 97)
Ma'ana:
"Suka ce ya Babanmu nema mana gafara" (Yusuf : 97)
Haqiqa 'Yayan Annabi Ya'quba basu nemi gafara daga Ya'quba ba domin gujewa tsarin (qudrah) Ubanngiji ba, sai dai sun sanya Ya'quba (Alaihis-salam) ne ya zamo musu wani tsani wajen neman gafara don zamowar sa makusanci kuma mai daraja a wajen Ubangiji. Wanda bayanin a sarari yake da bayanin da Annabi Ya'quba yayiwa 'Yayayen sa:
"قال سوف استغفر لكم ربي إنه هو الغفور الرحيم" (يوسف : 98)

Ma'ana:
"Yace da sannu zan nema muku gafara gurin Ubangijina, haqiqa Shi mai gafara ne mai jin qai" (Yusuf : 98)
C – Allah Ta'ala yana cewa:
"ولو أنهم إذ ظلموا أنفسهم جاءوك فاستغفروا الله واستغفر لهم الرسول لوجدوا الله توابا رحيما" (النساء: 64)

Ma'ana:
"Da za'a ce sun aikata zunubi suka zo maka suna neman Allah ya gafarta musu kuma Annabin (Muhammad) ya nema musu gafarar da sun sami Ubangiji mai karvar tuban (su) mai jinqan (su)" (Annisaa': 64)
Wannan ayar tana nuni ne akan karvar neman tuban Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ga Musulmai masu tuba, domin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) mai girman daraja ne a gurin Allah Maxaukakin Sarki.
Hakanan dai har ila iyau a lokaci guda tana tabbatar da muhimmancin zuwan Al'uma gurin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) domin neman gafara a garesu. (Ka duba cikin : Mukhaalafatul-wahaabiyyah : 22, na Umar Abdus-Salam).

SIFFOFIN TAWASSALI KAMAR YADDA QUR'ANI YAZO DASU
Allah Maxukakin Sarki ya nunawa Muminai yadda Tawassali yake a cikin Al-qur'ani, sannan ya halasta Tawassali ta fuskoki daban-daban. A kusa zamu kawo fuska cikakkiya ta kala-kalan Tawassali yardajje ga shari'a a cikin Qur'ani:
A – TAWASSALI DA SUNAYEN ALLAH MAXAUKAKIN SARKI
Allah Ta'ala yana cewa:
"ولله الأسماء الحسنى فادعوه بها وذروا الذين يلحدون في أسمائه سيجزون ما كانوا يعلمون" (الأعراف: 180)

Ma'ana:
"Kyawawan Sunaye suna ga Ubangiji don haka ku ambace shi da su ku rabu da waxanda suke rubxe sunayen Sa (Ubangiji) zasu sami sakamako da abinda suke aikata"
Wannan Aya tana wassafa dukkanin Sunayen Ubangiji da kyawawane babu wani bambamci, sannan akayi umarni da addu'a ta tafarkinsu.
Yayin da Bawa yake ambaton sunayen Sa (Ubangiji) waxanda suka tattare dukkanin Alheri da Kyawu da JinQai da Gafara da Xaukaka sannan Bawa ya fuskanci Ubangiji yana neman Gafara daga Zunubai da biyan buqatu, Ubangiji Ta'ala yana amsa addu'ar mai Tawassali da Sunayensa.
B – TAWASSALI DA KYAWAWAN AYYUKA
Haqiqa kyawawan aiki ana qidaya su daga cikin abubuwan da ake Tawassali da su a Shari'a wanda Bawa yake Kamun-qafa dasu ya sami kusanci zuwa ga Ubangiji Maxaukakin Sarki. Yayin da Tawassali ya kasance gabatar da wani abu ne ga Fadar Ubangiji don samun yardarSa, to babu makawa akan cewa Kyakkyawan aiki abin izna ne wajen mafi kyawun Tsanin da Bawa ke riqo dashi don bijiro da tabbacin buqatun sa. Ubangiji Maxaukakin Sarki yana cewa:
"وإذ يرفع إبراهيم القواعد من البيت وإسماعيل ربّنا تقبّل منّا إنّك أنت السميع العليم* ربّنا واجعلنا مسلمين لك ومن ذرّيتنا اُمّة مسلمة لك وأرِنا مناسكنا وتب علينا إنّك أنت التواب الرحيم" (البقرة: 126- 127).
Ma'ana:
"Yayin da (Annabi) Ibrahim da (Annabi) Isma'il suka xauki haramar gina Xakin Allah(Annabi Ibrahim yace) Ubangiji ka karvi wannan aiki namu haqiqa kai Mai Ji ne kuma Masani* Ubangiji ka sanya mu daga Masu miqa-wuya gareka, hakanan Ka sanya Zuriyar mu daga Al'umma mai miqa-wuya gareka, Kuma ka nuna mana guraren ibadar Hajjinmu, Ka yafe Mana Haqiqa Kaine Mai yafewa mai Jinqai" (Al-Baqarah: 127 – 128).
Wannan Ayar anan ta qarfafa dangantaka tsakanin Kyakkyawan aiki – wanda shine gina Xaki – da kuma addu'ar da ya kasance yana son tabbatarwar sa shi Annabi Ibrahim (alaihis-salam) – wato shine karvar ayyuka Kyawawa – kuma ya zamo a Zuriyarsa al'umma mai miqa-wuya (Musulma).
Kamar yadda faxinsa Maxaukaki yake qarfafa hakan:
"الذين يقولون ربّنا إننا آمنّا فاغفر لنا ذنوبنا وقنا عذاب النار" (آل عمران: 16)

Ma'ana:


"Waxanda suke faxin: Ubangiji haqiqa munyi Imani ka gafarta mana zunubanmu kuma ka tserar damu daga azabar Wuta" (Ali Imrana: 16).
Haqiqa zaka gani wani Tausayi ne neman gafarar saboda zuwan "F" inda yace "Fagfir lanaa" akan maganarsa: "mu munyi Imani" (Innanaa Amannaa) wannan "F" xin ta rabawa tana nuni ne akan dangantaka tsakanin Imani da neman Gafara.
C – TAWASSALI DA ADDU'AR MANZO (S)
Al-Qur'ani yayi nuni akan matsayin Manzo (sallallahu alaiHi wa AliHi) da Girman sa da Qimarsa gurin Allah Maxaukakin Sarki, da bambamcinsa tsakanin sa da sauran mutane, da faxinsa:
"لا تجعلوا دعاء الرسول بينكم كدعاء بعضكم بعضاً" (النور:63).

Ma'ana:
"Kada ku xauka addu'ar Manzo a tsakaninku kamar addu'ace a tsakankaninku" (An-Nur: 63).


Hakanan dai Qur'ani yayi nuni har wala iyau akan Manzo (sallallahu alaiHi wa AliHi) shine kaxai mai baiwa Duniya aminci. Da faxinsa:
"وما كان الله ليعذبهم وأنت فيهم وما كان الله معذبهم وهم يستغفرون" (الأنفال: 33)

Ma'ana:
"Kuma bazai tava yiwuwa (Ubangiji)ya azbtar dasu ba alhalin kana cikin su, kuma Ubangiji ba zai zamo mai azabtar dasu ba alhalin suna neman gafara" (Al-Anfal: 33).


Sannan zamu samu Al-Qur'ani a wasu guraren da dama yana gwama ambatonsa Maxaukaki da sunan Manzo (sallallahu alaiHi wa AliHi) kuma yana danganta musu aiki iri xaya. Yana faxin:
"وسيرى الله عملكم ورسوله ثم تردون الى عالم الغيب والشهادة" (التوبة:94).

Hakanan yace:



"وما نقموا إلاّ أن أغناهم الله ورسوله من فضله" (التوبة: 74)

Ma'ana:
"Haqiqa Ubangiji da Manzon sa za suga aikin ku, sannan ku koma zuwa duniyar Gaibu da Shaida" (Taubah: 94).


"Ba wani abu suka qi ba illa Ubangiji da Manzonsa su wadatasu daga Falalarsa (Ubangiji)" (Taubah: 74).
Da wasun waxannan Ayoyin waxanda suka zo da sunan Manzon tsira tare da na Ubangiji Maxaukakin Sarki. Idan har ya zamanto wannan shine matsayin Annabi Muhammadu (Sallallahu alaiHi wa AliHi) a wajen Ubangiji to tabbas bazai qi karvar addu'arsa ba za'a amsa addu'arsa. Hakanan mai riqo da addu'arsa ya zamanto yana riqo ne da wani Asasi mai qarfi.
Don haka zamu samu Ubangiji Maxaukaki yana umarnin masu zunubi daga Musulmi da yin riqo da addu'arsa, ya nema musu Gafara a zamansa, ya roqi Ubangiji don ya gafarta musu har ila iyau don ya zamanto Istigfarinsa akan su wani sanadi ne na saukar rahamarsa da karvar tubansu. Maxaukaki yana cewa:
"وما أرسلنا من رسول إلاّ ليطاع بإذن الله ولو أنّهم إذ ظلموا أنفسهم جاءوك فاستغفروا الله واستغفر لهم الرسول لوجدوا الله تواباً رحيما"ً (النساء: 64).

Ma'ana:
"Bamu aiko wani Manzo ba sai don ayi masa biyayya da izinin Ubangiji, da ace zasuyi aiki mummuna kuma suzo gareka suna neman gafarar Ubangiji, Manzon ya nema musu gafara to da Ubangiji ya karvi tubansu" (Nisa'i: 64).


A wannan ma'anar Ubangiji yake cewa:
"وإذا قيل لهم تعالوا يستغفر لكم رسول الله لوّوا رؤوسهم ورأيتهم يصدّون وهم مستكبرون" (المنافقون: 5).

Ma'ana:
"Kuma yayin da aka ce musu kuzo Manzon Allah zai nema muku gafara sai su karkatar da kawunansu sai ka gansu sunqi suna masu girman kai" (Munafiqun: 5).



D – TAWASSALI DA ADDU'AR XAN'UWA MUMINI
Ubangiji yana cewa:
"والذين جاءوا من بعدهم يقولون ربّنا اغفر لنا ولاخواننا الذين سبقونا بالإيمان ولا تجعل في قلوبنا غلاًّ للذين آمنوا ربّنا إنك رؤوف رحيم" (الحشر: 10).

Ma'ana:
"Kuma waxanda suka zo a bayansu suna faxin Ubangiji ka gafarta mana da 'Yan'uwanmu waxanda suka rigaye mu da Imani kuma kada ka sanya Qyashi a zukatanmu ga waxanda suka yi Imani, Ubangiji kaine Mai Rangwame Mai Jinqai" (Hashr: 10).


Yayin da Aya mai girma take nuna cewar Muminai na baya suna nemawa waxanda suka gabacesu gafara daga 'Yan'uwansu. Wanda wannan yana nuna cewar addu'ar Xan'uwa abisa haqqin Xan'uwansa wani lamari ne da ake buqata kuma karvavve.


E – TAWASSALI DA ANNABAWA DA BAYI NA GARI KANSU
Wannan vangaren ba vangare ne irin wanda ya gabata ba wanda shine Tawassali da addu'ar Manzo. Amma shi Tawassali ne da Zatin Annabawa da Managartan Bayi da sanya su wani tsani wajen karvar addu'a da yabo ga matsayin da suke xauke dashi ga Ubangiji Maxaukaki.
Idan ya kasance muna Tawassali da addu'ar Manzo ga Ubangiji a matsayin tsani zuwa gareshi. To a wannan vangare muna sanya Shi kansa Manzonne da Karamarsa tsani zuwa ga Ubangiiji Ta'ala. Wannan sananne cewa haqiqa Tsani "Wasiilah" shine addu'ar da take vuvvugowa daga wannan Mutum wanda Ubangiji ya Girmamashi ya Xaukakashi ya xaga muqaminsa kamar yadda yake cikin faxinsa Ta'ala:
"ورفعنا لك ذكرك" (الإنشراح: 4).

Ma'ana:
"Kuma Muka xaukaka ambatonka" (Inshirah: 4).


Sannan aka umarci Musulmi da girmamashi da xaukakashi, inda Ubangiji yake cewa:
"فالّذين آمنوا به وعزّروه ونصروه واتّبعوا النور الذي أنزل معه اُولئك هم المفلحون" (الأعراف: 157).
Ma'ana:
"Hakanan Waxanda sukayi Imani da shi kuma suka Yabe shi (Xaukaka shi) suka Taimaka masa sannan suka bi Hasken da Ubangiji ya saukar tare da shi Waxannan su suka rabauta" (Al-A'raf: 157).
Idan har ya kasance Tikitin amsar addu'a shine Shi kansa kaxai abin kwatance da kuma Muqaminsa wajen Ubangiji. To abinda yafi shine Bawa yayi Kamun-qafa da shi kamar yadda yake Tawassali da addu'arsa. Wanda kuwa ya gamsu da halascin na farko kuma yaqi gamsuwa da halascin na biyun to haqiqa ya raba abubuwa biyun da suke a haxe ne gam.
Wanda wannan nau'in na Tawassali na taimaka masa abinda aka ruwaito cikin Sunnar Annabi ta hanya ingantacciya shine abinda Ginshiqai cikin Ahlul-Baiti suka faxa.

F – TAWASSALI DA ALFARMAR SALIHAI DA GIRMANSU DA MATSAYINSU
Haqiqa abin la'akari ga Tarihin Musulmai shine samun su cike da irin wannan yanayin na Tawassali. Abin nufi cewar su suna Tawassali da Matsayin Salihai da Girmansu ga Ubangiji da Alfarmarsu gareshi.
Malam Muslim ya ruwaito daga Ma'azu xan Jabal (Allah ya yarda da shi) yace: Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yace: "Shin kasan menene haqqin Ubangiji akan Bayi? Yace: sai nace: Ubangiji ne da Manzonsa suka Sani, Yace: Haqiqa haqqin Ubangiji akan Bayi shine su bauta masa kada suyi tarayya da shi da wani. Sannan yayi tsawon Sa'a xaya, sannan yace: ya Mu'azu nace: na'am Ya Manzon Allah fata nagari gareka, shin kasan haqqin Bayi ga Ubangiji idan suka aikata haka? Yace: sai nace Ubangiji ne da Manzonsa suka sani, yace: shube kada Ubangiji yayi musu Azaba"
Don haka sai gashi Qur'ani mai girma ya kawo mana Tarihin Annabawa da Salihan Bayinsa cikin Tawassalinsa. Sannan ya kawo mana wani adadi na nau'o'insa da Shari'a ta yarda da shi. Hakanan samuwarsa baya keve shi da addu'a kaxai, da ya bambamta tsakanin Zatin Annabi da addu'arsa, ai lallai sai ya haxa da Zatin Annabi har wala iyau.

NA HUXU: TAWASSALI CIKIN HADISAN ANNABI
An ruwaito Hadisai masu tarin yawa da suke halasta Tawassali da Annabi (Sallallahu aliHi wa AliHi) ko kuma da Waliyyai Salihai.
1 – An karvo daga Usman xan Hunaif yace: haqiqa wani mutum Makaho ya zowa Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yace masa: ka roqar mini Ubangiji ya yaye mini makantar nan. Sai (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yace: idan kaso a jinkirta maka hakan shi yafi alheri gareka, in kuma kaso na yi maka addu'ar. Sai yace: kayi addu'ar, sai ya umarce shi da yin Alwala ya kyautata ta yayi Sallah raka'a biyu, yayi addu'a da wannan Addu'ar:
"اللهم إني أسألك وأتوجه إليك بمحمّد نبي الرحمة. يا محمّد إني قد توجهت بك إلى ربي في حاجتي هذه لتُقضى . اللهم فشفّعه فيَّ " (سنن ابن ماجه: 1/144 الحديث 1385 ومسند أحمد: 4/138 ح 16789 ومستدرك الصحيحين للحاكم النيسابوري: 1/313 والجامع الصغير للسيوطي: 59 ومنهاج الجامع: 1 / 286)

Ma'ana:


"Ubangiji ina roqonka kuma na fuskantoka da Muhammadu Annabin Jinqai. Ya Muhammadu na sanya ka gaba zuwa Ubangijina akan ya biya min Buqata ta wannan. Ubangiji ka ceceni don Shi"
Wannan Hadisin babu wani savani wajen ingancinsa har Malam Ibn Taimiyya ma ya xauke shi akan ingantaccene kuma yace: wanda ake nufi da Abu Ja'far wanda yake cikin Sanadin Hadisin shine Abu Ja'far Al-Khaxmiy kuma shi "Thiqatun" Yardajjene.
Amma Malam Rufa'iy cewa ya yi: Babu kokonto akan wannan Hadisin ingantaccene kuma ya Shahara. Domin ya tabbata a cikinsa – babu shakku babu kokonton – dawowar ganin Makahon da addu'ar Manzon Allah. (At-Tawassul na Subhaniy: 69, wanda ya ciro daga At-tawassaul (da Sadun) ila haqiqatit-Tawassul na Malam Rufa'iy: 158).
Hakanan Malam Nisaa'iy da Malam Baihaqiy da Malam Xabaraaniy da Malam Tirmiziy da Malam Haakim cikin Mustdrik xinsa duk sun ruwaito wannan Hadisin. (Sunanut-Tirmiziy: 5/135 Hadisi na 3578, Sunanul-Kubrah na Malam Nisaa'iy: 6, 169, Hadisi na 10495).
Da wannan Hadisin yake tabbatar da Shar'anci Tawassali, ta inda muka samu Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya sanar da Makaho yadda zaiyi Tawassali zuwa ga Ubangiji da Manzonsa Annabin Rahama. Kuma ya cece shi da biya masa buqatarsa. Kuma abinda ake nufi, Annabi shine shi kansa Annabin bawai addu'arsa ba, da fuskantar Ubangiji da Alfarmar Annabi da Tsaninsa.
2 – Axiyyatul-Aufiy ya ruwaito daga Abu Sa'iidul-Khudriy cewar Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yace: Wanda ya fita daga gidansa zuwa yin Sallah kuma yace:
"اللّهم إني اسألك بحق السائلين عليك، واسألك بحق ممشاي هذا، فإني لم أخرج اشراً ولا بطراً ولا رياءً ولا سُمعة، خرجتُ اتقاء سَخَطك وابتغاء مرضاتك، فأسألك أن تعيذني من النار وأن تغفر لي ذنوبي، إنه لا يغفر الذنوب إلا أنت" (سنن ابن ماجة: 1/256 الحديث 778 باب المشى الى الصلاة).

Ma'ana:
"Ubangiji ina roqon ka da Alfarmar masu roqon ka, hakanan ina roqonka da Alfarmar wannan tafiya tawa, domin ni ban fito don wani Wasa ko mai Girman kai ko mai Riya ko Alfahari ba. Na fito ne domin nisantar fushinka da neman yardarka. Ina roqonka ka kare ni daga shiga Wuta, kuma ka yafe mini Zunubai na, domin haqiqa babu wani mai yafe Zunubai sai Kai"


To Ubangiji zai karva masa don Alfarmarsa, kuma zai sanya Mala'iku Dubu Saba'in su nema masa Gafara.
Haqiqa wannan Hadisin yana nuna halascin Tawassali zuwa ga Ubangiji da Alfarmar Waliyyan sa Salihai, da Matsayinsu da Muqaminsu gurin Ubangiji. Kuma ya sanya waxannan Tsani kuma masu Ceto wajen biyan buqatarsa da amsar addu'arsa.
3 – Daga Anas xan Malik yace: yayin da Faximah bint Asad ta mutu Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya shiga gareta ya zauna dai-dai kanta yace: "Ubangiji ya jiqanki ya Wacce take Babata bayan Mahaifyata ya yabeta yayi mata Likkafani da RigarSa, sannan Mazon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya kira Usaamata xan Zaidu da Abu Ayyubal-Ansaariy da Umar xan Haxxaabi da wani Hadimi Baqi don su haqa Qabari. Yayinda suka kai "Lahdi" wato Uwa Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) sai ya karva ya ci gaba da haqan da kansa, kuma ya fitar da qasar da kansa, bayan ya gama ya shiga Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya kishingixa a ciki, sannan yace: Ubangijin da yake rayawa yake kashewa kuma shine Rayayye ba ya mutuwa, ka gafartawa Babata Faxima bint Asad, ka yalwata mata Qabarinta, don Alfarmar Annabinka da Annabawan da suka zo kafin Ni". (Kashful-Irtiyab: 312, wanda ya ciro daga Wafaa'ul-Wafaa' da Durun-Niyyah: 8).
4 – An ruwaito daga Sawaadu xan Qaarib yayiwa Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) Qasida da Qasidarsa wacce yake Kamun-Qafa a cikinta da Annabi yake cewa:
وأشهد أن الله لا ربّ غيرهُ***وأنك مأمون على كلّ غائبِ

وانك أدنى المرسلين وسيلة***الى الله يابن الأكرمين الأطائبِ

فمرنا بما يأتيك يا خير مُرسل***وإن كان فيما فيه شَيبُ الذوائبِ

وكن لي شفيعاً يوم لا ذو شفاعة***سواك بمغن عن سواد بن قاربِ

(الدرر السنية : 27، والتوصل الى حقيقة التوسل: 300، فتح الباري: 7/137)
Ma'ana:
Na shaida hakiqa Ubangiji babu waninsa,

Kuma haqiqa Kai amintacce ne ga dukkan wanda baya nan.


Haqiqa kuma Kaine mafi kusancin Manzanni wajen Kamun-Qafa,

Zuwa ga Ubangiji Ya Xan Masu girman Tsarkaka.


Umarce mu da abinda yake zuwar maka Ya Mafificin Manzanni,

Koda kuwa ya kasance zai kawo Furfura ga gashin gaban goshi (don wahala).


Zamo mini Mai-Ceto ranar da babu Mai-Ceto,

Kamar ka don Waqen Sawaadu xan Qaarib.



NA BIYAR: TAWASSALI CIKIN TARIHIN MUSULMAI
Haqiqa Tarihin Musulmai ya gudana a lokacin Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yana Raye da bayan Wafatin Sa abisa yin Tawassali da Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da Waliyai da neman Ceto don Alfarmarsu ga Ubangiji. Don haka ga irin Samfirin wanna Sirah:


  1. Haqiqa Abubakar bayan Wafatin Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi), yace: "Ka ambacemu Ya Muhammad a gurin Ubanngijinka don mu kasance cikin Zuciyarka".




  1. Haafiz Abu Abdullahi Muhammad Ibn Musan-Nu'umaaniy ya faxa cikin littafinsa Misbaahuz-Zalam: cewar haqiqa Haafiz Baban Sa'iidus-Sam'aaniy ya ambaci daga cikin abinda muka ruwaito daga gareshi daga Aliyyu Xan Abu Xalib (Alaihs-salam), yace: "Wani Balarabe yazo mana bayan mun binne Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da kwana uku, ya faxa kan Qabarin Manzo (Sallallahu alaiHi wa AliHi) yayi buxu-buxu da Qasar Qabarin a Kansa, sannan yace: ya Manzon Allah, nace munji faxinka, kuma na sami Sani ne daga Ubangiji Maxaukaki sannan mun sami Sani ne daga gareka. Hakanan yana daga cikin abinda aka saukar: "Da za'ace sun zalunci kansu suzo wajenka su nemi Gafarar Ubangiji ……." To haqiqa ni na zalunci kaina kuma nazo ka nema mini Gafara, sai akaji kira daga cikin Qabarin akace: haqiqa an Gafarta maka" (Wafaa'ul-Wafaa' na Samhuudiy:2/1361).



  1. Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ya kasance ya sanar da wani mutum akan yayi addu'a kuma ya roqi Ubangiji, sannan yayi Magana da Annabi yayi Kamun-Qafa da shi sannan ya roqi Ubangiji ya karvi Cetonsa, da yace: "Ubangiji mun kasance muna Kamun-Qafa gareka da Annabinka Annabin Jinqai, Ya Muhammadu Ya Manzon Allah ina Kamun-Qafa da kai zuwa ga Ubangijina abisa biyan buqata ta, Ubangiji ka ceceni domin sa" (Majmuu'atur-Rasaa'il wal-masaa'il na Ibn Taimiyya: 1/18).




  1. Yazo cikin Ingataccen littafin Malam Buhari cewar Umar xan Haxxaabi ya kasance idan sunyi farin rashin Ruwan sama, Abbas bn Abdul-Muxxalabi (R.A) yakan yi roqon ruwa yace: "Ubangiji mun kasance muna Kamun-Qafa gare ka da Annabinka kuma ka shayar damu, yanzu ma muna Kamun-qafa gareka da Baffan Annabin ka ka shayar damu. Yace: kuma a shayar dasu". (Sahiihul-Bukhaariy: baabi Salaatul-istisqaa': 2/32 Hadisi na 937).



  1. Mansur Al-Abbas ya tambayi Maalik bn Anas – Imamin Malikiyya – yadda ainihin Ziyarar Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) take da yin Tawassali da shi ….. sai yace: "Ya Abdullahi na fuskanci Alqibla nayi addu'a ne, ko kuma na fuskanci Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ne? Maalik ya faxa cikin jawabi: kar ka xauke fuskar ka gare Shi, domin shine tsaninka kuma tsanin Babanka Adam har izuwa Tashin Qiyama?! Na'am fuskance shi ka nemi ceto da shi Ubangiji zai cece ka. Ubangiji Maxaukaki yana cewa: "Da za ace sun zalunci kansu ……." (Wafaa'ul-Wafaa' na Samhuudiy: 2/1376).




  1. Shaafi'iy ya ambaci waxannan Baitukan guda biyu a Waqen sa yana mai Tawassali da Alayen Ma'aiki (Sallallahu alaiHi wa AliHi):


آل النبي ذريعتي*** وهم اليه وسيلتي

أرجو بهم أُعطى غداً***بيدي اليمين صحيفتي

(الصواعق المحرقة: 274)

Ma'ana:

Alayen Annabi sune Tsani na *** Da su nake Kamun-Qafa gare Shi (Ubangiji)



Fatana dasu shine Gobe Qiyama abani *** Littafina a hannun dama na

Daga waxannan Dalilai da Shaidu na Tarihi, waxanda na Magabata ne zamu iya cewa: Haqiqa Annabawa da Salihan Bayinsa ana kawo su akan Tsanuka ne na Shari'a wanda Ubangiji ya samar da faxinsa:


" يا أيّها الذين آمنوا اتّقوا الله وابتغوا إليه الوسيلة" (المائدة: 35)

Ma'ana:
"Yaku waxanda kuka yi Imani kuji tsoron Allah kuma ku nemi Mai-yi-muku-iso (Wasiila) gareshi"


Wasiila anan ta qunshi Mustahabbai ba za a qidanya ta wajen bada Wajibai ba da barin abubuwan Haram.

NA SHIDA: TAWASSALI A GURIN AHLUL-BAITI (A.S.)
Haqiqa Imaman Ahlul-Baiti (Alaihimus-salam) sun kawo da yawa akan Tawassali da Qur'ani da Waliyan Allah da wasunsu. Wanda idan ka koma cikin litattafan Imamiyya da litattafan Hadisan su da litattafan Addu'o'insu zaka taras abune wanda yake a fili valo-valo wanda bai yiwuwa ayi kokonto akai. Gareka Samfurin wasunsu:


  1. Haarith bn Mughiirata yace: naji Abu Abdullahi [Husain] (Alaihis-salam) yana faxin: "lallai idan xayan ku zai roqi Ubangijinsa wani abu daga buqatun Duniya sai ya fara da Yabo ga Allah Maxaukakin Sarki da tsarkake shi, sannan da yin Salati ga Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi) sannan ya tanbayi buqatar tasa" (Bihaarul-Anwaar: J-93 Kitaabuz-zikri wad-du'a'u babi 17 Hadisi-19).

  2. An karvo daga Abu Ja'far (Alaihis-salam) yace: Jaabirul-Ansaari yace: nace da Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa Alihi): me zakace akan Aliyyu bn Abu Xalib? Sai yace: wannan kainane. Nace: me zakace akan Hasan da Husein? Yace: su biyun Rainane, Faxima kuwa Mahaifiyarsu 'Yata yana baqanta mini duk abinda ya baqanta mata kuma yana faranta mini duk abinda ya faranta mata. Allah ka shaida ina faxa da duk wanda yake faxa da su, da aminci da duk wanda ya aminta da su. Ya Jaabir idan kana son ka roqi Ubangiji ya amsa maka ka roqa da Sunayensu domin sune mafi soyuwar Sunaye a gurin Ubangiji Maxaukakin Sarki.

  3. Daga Annabi (Sallallahu alaihi wa Alihi): "Ubangiji ina fuskantoka da Muhammadu da Alayen Muhammadu kuma ina fuskanto su gareka kuma ina gabatar dasu ga buqatata" (Bihaarul-Anwaar: Hadisi-94, Babi-28).

  4. Hakanan Imam Aliyy Amirul-Muminiina (Alaihis-salam) yana faxa cikin addu'arsa: "…… da alfarmar Muhammadu gareka, da alfarmarka Maigirma garesu kayi Salati garesu kamar yadda ka saba kuma ka bani mafi darajar abinda ka baiwa masu roqonka daga Bayinka da suka gabata Muminai, da mafi darajar abinda ka baiwa waxanda suka rage daga Muminai" (As-sahiifatul-Ulawiyyah lis-Samaahiijiy:51).

  5. Imam Abu Abdullahil-Husein (Alaihis-salam) na faxa a cikin addu'ar Arfa: "…. Ubangii mun fuskanto ka – cikin wannan Maraicen wanda ka wajabta, ka kuma girmama – ga Muhammadu Annabinka Manzonka kuma Zavavvenka daga Halittunka" (Iqbaalul-Aa'maal na Ibn Xaawus: 2/85).

  6. Imam Zainul-Aabidiina (Alaihis-salam) ya faxa cikin addu'arsa ta kamawar Watan Ramadan: "….. Ubangiji ina roqon ka don alfarmar wannan Watan da alfarmar wanda yayi Ibada cikinsa – daga farkonsa zuwa qarshensa – daga Mala'ikun da kusantasu ko Annabin da ka aiko ko Bawa na gari da ka kevance shi ……" (As-sahiifatus-Sajjaadiyya: Du'a' raqum 44).



NA BAKWAI: JAYAYYAR MASU INKARIN HALASCIN TAWASSALI DA SHAR'ANTAWAR SA
Sukace: baya yiwuwa ayi Kamun-Qafa da matattu, wanda wannan mummunan aiki ne a hankalce, don rashin samun damar mamaci wajen biyan buqata, yin Kamun-Qafa da shi yin Magana da abinda babu shi. (Duba cikin Minhaajus-Sunnah, na Ibn Taimiyya).
Haqiqa wannan iqrarin abin yarwa ne kuma yayi karo da Al-Qur'ani, ga Ayoyi nan misali waxanda suke kore mamaci akan cewar babu shi.


  1. Misalin faxinsa Maxaukakin Sarki:

"ولهم رزقهم فيها بكرة وعشيّا" (مريم: 62).

Ma'ana:
"Kuma suna da abinci a cikinta, safe da maraice" (Maryam: 62).
Wannan vangaren ya sauka ne akan alfarmar Muminai, yayin da aka bayyana nau'in kulawa gare su cikin Duniya da Lahira.


  1. Wacce kuma tafi fitowa fili daga ciki, faxinsa Maxaukakin Sarki:

"النار يعرضون عليها غدوّاً وعشيّاً ويوم تقوم الساعة أدخلوا آل فرعون أشدّ العذاب" (غافر: 46)


Ma'ana:
"Ana gifta su a kan Wuta safe da maraice, kuma da ranar da Alqiyama zata zo, (ace musu) ku shigar da mutanen fir'auna mafi tsananin azaba".
Inda Ubangiji maxaukakin Sarki yake bayyana sakamakon da masu yin savo da kafirai za su samu a cikin rayuwar bayan mutuwa (Barzakhu) kafin tashin qiyama. Ta inda ake nuna samuwarsu rayayyu bayan mutuwa, kuma kafin tashin qiyama. Kuma haqiqa tashin alqiyama an ambace shi ne bayan bijiro da su akan wuta safe da maraice.
To idan ya tabbata cewar mutuwa ba gushewa ba ce, a'a wata rayuwar ce, to shin zai iya yiwuwa samun saduwa da mamaci ko kuwa bai yiwuwa? Da da'awar cewa ita rayuwar barzakhu tana hana saduwa da shi.
Yazo a cikin Qur'ani maigirma – a bisa qari akan abinda aka samu cikin sunnar Manzo (S) – wanda yake nuni akan yiwuwar saduwar mutumin da yake samamme a cikin wannan duniyar rayayye da mutumin da yake rayuwa a Barzakhu, daga cikin waxannan hujjojin akwai:


  1. A cikin kiran da Annabi Salihu yayiwa mutanensa zuwa bautar Ubangiji, da umarninsa Ubangiji garesu akan kada su nufi wannan Mu'ujiza tasa da cutarwa – itace Taguwa. Wanda bayan sun soke taguwar, sun yi girman kai ga umarnin Ubangijinsu Allah yace:


"فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ (78) فَتَوَلَّى عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَةَ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ وَلَكِنْ لَا تُحِبُّونَ النَّاصِحِينَ (79)" الأعراف.

Ma'ana:


"Sai tsawa ta kama su, kuma suka wayi gari a cikin gidajensu gurfanannu. Kuma ya juya garesu, sannan yace: Ya mutanene haqiqa na isar muku da manzancin Ubangijina, kuma na yi muku gargaxi, sai dai ku bakwa son masu gargaxi".
Mu duba muga yadda Ubangiji ya bada labari ta yankakkiyar fuska akan tsawar ta halaka mutanen Annabi Salihu (A) suka wayi gari a gidajensu gurfanannu. Haka nan kuma bayan haka ya bada labarin Annabi Salihu ya juya garesu yana faxa musu: "Ya mutanene haqiqa na isar muku da manzancin Ubangijina, kuma na yi muku gargaxi, sai dai ku bakwa son masu gargaxi". Wanda maganar Annabi Salihu garesu tazo ne bayan halaka da mutuwa ta riske su.


  1. Annabi Shu'aibu (A) ya yi Magana da mutanensa bayan halakarsu da faxinsa maxaukakin Sarki:


"فَتَوَلَّى عَنْهُمْ وَقَالَ يَا قَوْمِ لَقَدْ أَبْلَغْتُكُمْ رِسَالَاتِ رَبِّي وَنَصَحْتُ لَكُمْ فَكَيْفَ آَسَى عَلَى قَوْمٍ كَافِرِينَ (93)" الأعراف.

"Sai ya juya garesu, kuma yace: Ya mutanena haqiqa na isar muku da manzancin Ubangijina, kuma na yi muku gargaxi, to yaya zan yi baqin ciki a kan mutane kafirai".
Haka nan maganar Annabi Shu'aibu (A) ga mutanensa, ya yi ta ne bayan halakarsu. Wanda wannan ya tabbatar da yiwuwar saduwa dasu. Da kuma basu zamo halakakku ta sanadin tsawar ba sun ji maganar Annabi Salihu da Annabi Shu'aibu (A) ba, to menene ma'anar maganar tasu garesu?!
Don haka bai yiwuwa a fassara shi a hakan, domin Magana ce ta tausayi, kuma ya savawa zahiri, kuma bai inganta ba ta fuskar Usulul-tafsiiriyyah.
Amma Hadisai tsarkaka da suke nuni akan yiwuwar samun saduwa da rayuka matattu, akwai daga ciki:


  1. Abin da aka ruwaito daga Annabi (S) ya tsaya ranar yaqin Badar ya yiwa mushrikan da aka kashe Magana.

Daga Anas xan Maalik, yace: Sahabban Manzon Allah (S) sun ji Manzon Allah (S) cikin tsakiyar dare yana cewa: Ya ku mutanen Badar, ya Utbah xan Rabii'ah, ya Shaybah xan Rabii'ah, ya Umayyah xan Khalaf, ya Abuu Jahal xan Hishaam, da wasu adadan daga cikinsu, shin kun taras da abin da Ubangijinku ya yi muku alqawari da gaskiya? Haqiqa ni na sami abin da Ubangiji na yayi mini alqawari da gaskiya. Sai Musulmi suka ce: Ya Manzon Allah (S), kana Magana ne da mutanen da suka bushe ne? sai yace: Haqiqa baku fisu jin abin da na faxa musu ba, sai dai su ba zasu iya bani amsa ba. Wannan hadisin yazo cikin Buhari:5/7, da Siiratu Ibn Hishaam: 2/639.




  1. Haqiqa Musulmai – abisa bambamcin mazahabarsu – suna yin sallama ga Manzon Allah (S) a cikin qarshen sallarsu suce: "Assalamu alaika ayyuhan-Nabiyyu wa rahmatullaahi wa barakaatuhu", wanda haqiqa sunnar Annabi tabbatacciya ce gareshi yana raye da bayan mutuwarsa, kuma babu wani yankewa ga sallarmu da alaqarmu da Annabi (S).

Wanda ita wannan sallamar tana nuni ne akan samuwar alaqa da ruhinsa (S) kai tana ma nuna samuwarsa ne a wajen.




  1. Haka nan kuma yazo daga gareshi (S): "Dukkanin wanda ya ziyarce ni bayan wafati na, kuma yayi sallama gareni, zan mayar masa da sallamar sau goma, kuma Mala'iku goma zasu ziyarce shi suna sallama gareshi, haka kuma duk wanda yayi sallama gareni a cikin xaki, Ubangiji zai dawo mini da ruhi na har na yi masa sallama". Ka duba cikin Sunani Abu Daawud: 2/218, da Kanzul-ummaal: 10/38, da Xabaqaatush-shaafi'iyyah na Sabakiy:3:408.




  1. Manzon Allah (S) yace: "Duk wanda ya ziyarce ni bayan mutuwa ta, to kamar ya ziyarce ni ne ina raye ……." Ka duba cikin Kanzul-ummaal: 5/135, hadisi na – 12372.

Idan har ya tabbata samun saduwa da mutumin da yake rayuwa a Barzakhu, to shin ya halasta neman wani abun gareshi da kuma kamun-qafa gareshi na biyan buqatu, ko kuwa yin hakan shirka ne da Allah dalilin faxinsa Maxaukakin Sarki: (Innal-amra kullahu lillaahi) Aali-imraan:154. "Tabbas dukkan lamari ga Allah yake".


Tabbas dukkanin lamari ga Allah yake kuma da ikonsa, kuma da yardarsa komai yake faruwa, sai dai haqiqa hakan baya kore tabbacin ceto ga Annabawa da Waliyyai anan duniya da lahira bayan izini daga Allah. Kamar yadda hakan bai kore tabbatar da halitta ba, da kuma rayar da matacce da warkar da marar lafiya ga Annabi Isa (A) ba bayan izini daga Allah maxaukakin Sarki!
Hakanan dai-dai lokacin da abubuwa suke gudana akan doron sababin shari'a, muke samun Annabin Musa (A) yana cewa: "Qaala hiya asaaya atawakka'u alayhaa wa ahushsha bihaa alaa ghanamiy wa liya fiihaa ma'aaribu ukhraa" (Xaaha:18). "Yace: Shi sandana ne, ina kaxar ganye da shi na gutsutstsurasu ga dabbobi na, haka nan ina da wasu buqatun da shi".
Annabawa tare da Isimar (Kariya) da Allah yayi musu ace suna neman taimakon wanin Allah, har abisa haqqin Manzon Allah (S) aya ta sauka take cewa: "Yaa ayyuhan-Nabiyyu hasbukallaahu wa manittaba'aka minal-mu'miniina" (Al-anfaal:64) "Ya kai Annabi, Allah ya isar maka, da wanda ya bika daga muminai".
Wanda kuma gundarin zahirin abin da ayar ke nunawa shine samuwar Annabi ya nema daga Allah da Muminai kamar irin yadda Annabi Isa (A) ya nema daga Hawariyawa inda yake cewa: "Man ansaariy ilallaah" (Aali-imraan:52). "Su waye mataimakana zuwa ga Allah". Haka nan da irin neman Annabi Musa (A) ga Xan'uwansa Haaruuna, inda Allah ya amsa da faxinsa: "Sanashuddu adhudaka bi-akhiika" (Qasas:35). "Zamu qarfafi qarfinka da Xan'uwanka".
Sannan kuma zamu samu Allah maxaukakin Sarki ya taimaki bayinsa da faxinsa: "In tansurullaaha yansurkum" (Muhammad:7). "Idan kun taimaki Allah, zai taimakeku". Da faxinsa: "Wallaziina aawaw wa nasaruu ulaa'ika humul-mu'minuun" (Anfaal:74). "Kuma da waxanda suka bada masauki, kuma suka yi taimako, waxannan sune muminai".
Wanda kuma da za ace mun san cewar neman taimako da kamun-qafa ga wanin Allah halastacce ne domin shi da izinin Allah ne da ikonsa bawai kevantacce ne ba, to menene fuskar neman taimako ga mamaci, tare da cewar haqiqa tabbaci shine neman taimako da Annabi ko Waliyyi halin yana raye ba yana mace ba? Wanda haqiqa Sahabbai basu tava inkarin kamun-qafa da Annabi ba a halin yana raye da halin yana mace.
KAMUN-QAFA DA ANNABAWA DA SALIHAN BAYI BAYAN MUTUWARSU
Yana daga cikin tarihin Musulmai kamun-qafa da Annabi bayan mutuwarsa (S).


  1. Yazo a cikin littafin Musnad na Ahmad: "Ya Ubangiji ina roqonka da haqqin masu roqonka, da haqqin wannan matafiyar tawa, domin ni ban fito don wani Wasa ko mai Girman kai ko mai Riya ko Alfahari ba. Na fito ne domin nisantar fushinka da neman yardarka. Ina roqonka ka kare ni daga shiga Wuta, kuma ka yafe mini Zunubai na, domin haqiqa babu wani mai yafe Zunubai sai Kai" (Musnad Ahmad: 3/21, da Sunani Ibn Maajah: 1/356.

A cikin wannan Hadisin akwai dalili valo-valo akan halascin kamun-qafa da Salihai su kansu, bawai da addu'arsu ba, domin shi furuci ne gamamme da ke xauke da dukkanin masu roqo daga 'Ya'yan Adamu (A) har zuwa ranar qiyama, kai ya qunshi Mala'iku da Muminan Aljanu. Bai yiwuwa taqaitashi da masu roqo na wannan lokacin ko kuma daga rayayyu, domin babu abinda yake nuna hakan a cikin wannan Hadisin, hakan wanda ya fitar da shi bai kevance hakan ba har wala iyau. (Azziyaarah wattawassul, Saa'ibu Abdul-hamiid:142).




  1. Yazo a cikin Turmiziy da Nisaa'iy: "Ya Ubangiji ina roqonka kuma ina kamun-qafa gareka da Annabinka annabin Rahama, Ya Muhammad Ya Manzon Allah ina kamun-qafa da kai zuwa ga Ubangijina a cikin buqata ta domin ya biya mini ita, ya Ubangiji ka karva domin Shi".

Wannan tana daga cikin addu'o'in da Musulmai suke kamun-qafa (Tawassali) da Annabi (S) bayan mutuwarsa.




TATTAUNAWAR IBN TAIMIYYA CIKIN HUKUNCINSA GA WANNAN ADDU'AR
Savani ya faru tsakanin Ibn Taimiyya da masu kwaikwayonsa (Mabiyansa) daga cikin Salafiyya da Wahabiyawa akan mas'alar Tawassuli (Kamun-qafa) da Annabawa da Salihai a bayan mutuwarsu, a inda shi ya tafi akan rashin kamun-qafar da mamata, don haka ga maganar tasa kafin muzo tattaunawar:
Babu a cikin kamun-qafa addu'a da ababen halitta, hakanan babu neman taimako da abin halitta, domin haqiqa ana addu'a ne da neman xauki da Allah, sai dai akwai roqon da ake ace da alfarmarsa, kamar yadda yazo cikin Sunani Ibn Maajah, daga Annabi (S) ya ambata a cikin addu'ar mai fita sallah yace: "Ya Ubangiji ina roqon ka da haqqin masu roqonka ……". A cikin wannan Hadisin yayi roqo da haqqin masu roqo gareshi …. Kuma Allah maxaukakin Sarki ya sanya haqqi akansa ….(har zuwa inda yace) sai wata tawaga tace: babu cikin wannan halascin kamun-qafa da shi bayan mutuwarsa ko kuma baya gurin, kai ana yin tawassali da shine a halin yana raye kuma yana wajen …
Sannan ya xauka yana samun rinjaye da wannan ra'ayin na qarshe, inda yake cewa: shi wannan kamun-qafar da shi su sun kasance suna roqonsa ne akan ya roqa musu, suyi addu'ar tare da shi, suna kamun-qafa da cetonsa da addu'arsa. A inda ya bada misali akan hakan da Hadisin wani Balarabe da yake cewa: Ya Manzon Allah! Dukiyar ta halaka kuma hanya ta toshe, ka roqa mana Allah ya riqa mana ita.
Yace: wannan ya kasance tawassalinsu ne da Shi yayin roqon ruwa ko waninsa, don haka yayinda Manzon Allah (S) ya mutu sai suka riqa kamun-qafa da Abbas (R) ….. hakanan kuma dai Mu'awiya xan Abu Sufyaan, ya roqi ruwa da Yaziidu xan Aswadul-Jarshiy, yace: Ya Ubangiji muna neman cetonka da zavinmu, ya Yaziidu xaga hannuwanka zuwa ga Allah ………
Sannan ya cika da faxinsa: kuma ba a sami wani daga cikin Malamai wanda ya ambaci cewar yana shar'anta kamun-qafa da roqon ruwa da Annabi da Salihi ba bayan mutuwarsa hakanan da idan baya wajen. Kai hakanan bai ce Mustahabbi ne ba hakan cikin roqon ruwa ne ko kuwa cikin neman xauki ko wanin hakan daga cikin addu'o'i. (Ziyaaratul-qubuur wal-istinjaadi bil-maqbuur: 37 – 43.
Cuxanya da dungu da karo valo-valo ne cikin mafi yawancin maganganun Ibn Taimiyya, a wannan maganar zamu fara da tona irin waxannan gurare, kafin kaiwa ga dalilai ga mai nema.


  1. Ya cuxanya tsakanin kamun-qafa da Annabi (S) da tsakanin kamun-qafa da alfarma, kuma bambamcin a fili yake a cikin faxinka: "Ya Muhammadu, ya Manzon Allah ina fuskantoka zuwa ga Allah" da kuma tsakanin kace: "Ubangiji da alfarmar Masu roqonka" ko "Ubangiji da alfarmar Muhammadu (S)". A farko ya fuskanta da kamun-qafa da shi, na biyu kuwa ya fuskanta da kamun-qafa da haqqinsa da alfarmarsa da muqaminsa ne. Waxannan nau'uka biyu ne na kamun-qafa da Annabawa da Salihai da suke shiga wannan vangaren, haka kuma ya riqi na farkon akan na biyun, wanda kuma riqo ne ba ingantacce ba.




  1. Anan ma Malamin yayi cuxanya kamar yadda yayi a baya tsakanin fuskantar Annabi (S) da tsakanin addu'a daga gareshi. Wanda bambamcin a bayyane yake, ba a voye yake ba cewar ya aikata hakan ne domin yin dungu, ba komai ba. Hakan ne ya sanya ka ganshi yayinda yake nuni da Hadisin Balarabe yazo da qashin bayan Hadisin ya bar faxin nasa wanda muka gabatar da shi baya kaxan: "Ya Manzon Allah mu muna neman cetonka a gurin Ubangiji" wanda kuma Manzon Allah (S) ya bashi garantin hakan.




  1. Ya doki kansa da kansa (Tanaaqud) a wajen cirowa daga Malami, sannan ya nemi majingina zuwa ga keta addu'ar zuwa ta roqon ruwa da watar ta domin yin dungu ga tunani ba komai ba, domin ya dawo ya haxe dukkanin siffofin nau'o'in addu'a (Ba Mustahabbi ne ba hakan cikin roqon ruwa ne ko kuwa cikin neman xauki ko wanin hakan daga cikin addu'o'i). Domin ya ciro faxin Malamai daga farko da suke faxin halascin kamun-qafa da Annabi (S) a cikin yana raye da bayan mutuwarsa, sannan ya komo yana cewa: bai ambaci mutum xaya daga cikin Malamai ba da yake shar'anta Kamun-qafa da roqon ruwa da Annabi (S) da Salihan bayi ba bayan mutuwarsa!! Don haka ne anan muka zo abin da yake tauye da'awarsa wannan xin da dalilan da shi ya tabbatar ingancin wasunsu, kuma bai ambata ga xaya vangaren tabbaci ko rashin tabbacin ba.

Mun faxa kuma muna daxa tabbatarwa akan cewa Ibn Taimiyya bai sami wani nassi ba da yake tabbatar masa da hanin kamun-qafa da Annabi (S), sai gashi ya vige yana xaukar wasu nassukan da bai kamata a xauke su ba. Zamu ganshi anan yadda yake juya bayansa ga nassi tabbatacce gareshi ta yanayin da babu wata qura tare da shi:


Yana cirowa daga hanyar da ya san ingancinta daga babban Sahabi Uthman bn Hunayf cewar shi yana koyar da mutane kamun-qafa da Annabi (S) a zamanin Uthman xan Affaan, sannan yana cetonsa da labaru makamanta daga salafu.
Yana cewa: Malam Baihaqiy ya ruwaito cewa wani mutum ya kasance yana juyawa da buqatarsa zuwa ga Uthman xan Affaan, shi kuwa Uthman bai kulawa da shi, sannan baya duban buqatar tasa. Sai wannan mutumin yaje gurin Uthman xan Hunayf yakai masa kuka, sai Uthman xan Hunayf yace: kazo da abin alwala kayi alwala, kaje Masallachi kayi sallah raka'a biyu, sannan kace: "Ubangiji ina roqonka kuma ina fuskanto ka da Annabinmu Muhammad Annabin Rahama, ya Muhammadu, ina fuskanto ka zuwa ga Ubangijina domin ya biya min buqata ta", sannan ka ambaci buqatarka. Wannnan mutumi ya tafi ya aikata hakan, da yazo gurin Uthman xan Affaan masu tsaron qofa suka shigar da shi wajensa ya zaunar da shi tare da shi akan tabarma, sai yace: menene buqatarka? Ya faxa nan take ya biya masa.
Mutumin ya fita ya tafi wajen Uthman xan Hunayf, yace masa: Allah yayi maka sakayya da alheri, ba shi da niyyar ya kalli buqata ta ko ya saurare ni har sai da kayi masa Magana a madadina. Sai Uthman xan Hunayf yace: ni ban yi masa Magana ba, sai dai naji Manzon Allah (S) wani marar lafiya yazo masa ya kawo masa kukan rashin ganinsa, sai Annabi (S) yace masa: "kana son gani" sannan ya ambaci hadisin da ya gabata.
Malam Baihaqi yace – amma maganar ta Ibn Taimiyya ce - : haka nan dai Ahmad bn Shabiib bn Sa'iid ya ruwaito daga babansa da tsayinsa, hakanan dai Hishaamud-dastiwaa'iy ya ruwaito, daga Abu Ja'far, daga Abu Umaamah bn Sahal, daga 'yar'uwar baban Uthman bn Hunayf, sannan sai Ibn Taimiyya ya ambata yace wannan Hadisin yana da sanadai da yawa, kuma ya inganta shi zuwa inda yace:
An ruwaito wani abu daga wannan daga wasu salafun, kwatankwacin abinda Abud-dunyaa ya ruwaito a cikin littafinsa (Majaaniid-du'aa') da isnadinsa: wani mutumi yazowajen Abdul-malik bn Sa'iid bn Abjaru, ya cika cikinsa yace: kana da cutar da ba waraka. Sai mutumin yace: wace cuta ce? Sai yace: ciwon Dubaylah (wata cuta ce mai xumama cikin ciki, wacce take kai mutum ga mutuwa)! Sai mutumin ya canja yace: Allah, Allah, Allahu Ubangijina bana tarayya da shi da komai, ya Ubangiji ina fuskanto ka da Annabinka Muhamamdu Annabin Rahama (S) Ya Muhammadu, na fuskantoka zuwa ga Ubangijinka kuma Ubangijina ya jiqaina akan abin da ke gareni. Sai yace: sai ya cika cikinsa, sannan yace: ka kuvuta, babu illa a tare da kai …… Ibn Taimiyya ya qara yana faxin: ita wanann addu'ar da watanta an ruwaito ta akan cewar Salafu (Magabata) sun yi addu'a da ita, kuma an naqalto daga Ahmad xan Hanbali cikin (Mansakul-marwaziy) yin kamun-qafa da Annabi (S) a cikin addu'a. Ka duba cikin Attawassul wal-wasiilah: 97, 98, 101 – 103.
Hakanan dai yayi shaida akan vacin ra'ayinsa, da vacin da'awarsa da ta gabata akan cewar shi bai naqalto wani ya yi kamun-qafa da Annabi (S) bayan mutuwarsa ba daga Salafu (Magabata) ba, wannan da'awar da ya nace akan cusa ta, wacce ya kawo ta a littafinsa (Attawassul wal-wasiilah: 18).
Don haka da wannan ya tabbata kan cewar bai zamo komai ba akan abinda ya tafi akai, idan ba nacewa kan cusa vataccen ra'ayinsa ba, wanda ingatattun dalilai sun shaida wajen tabbatar vacinsu.
Wanda abinda yake na haqiqa shine abinda Salafu suka tabbatar mafi yawan hakan sosai, kuma basu taqaita akan kamun-qafa da Annabi (S) bayan mutuwarsa ba, kai sun ma yi kamun-qafa da waninsa, wanda suke ganin a tare da shi akwai kyakkyawa kuma suna qudurin a tare da shi akwai wata karvuwa da kuvuta ga Allah. Ka duba cikin Azziyaaratu wattawassul, Saa'ibu Abdul-hamiid: 148 – 152, Isdaar Markazur-risaalah.
DAGA QARSHE NAKE RUFEWA DA

Haqiqa mutuwa ba tana daga cikin rashi ba ne, domin haqiqa saduwa da rayuwar Barzakhu tabbataccene tabbas. Kuma tabbas tarihin Musulmai tun can-can yana gudana ne akan Kamun-qafa da Annabawa da Waliyyai ne rayayyu da matattu, ba tare da wani bambamci ba tsakanin mutum da addu'a, da ya ayyana ingancin ra'ayin da ke faxin halascin Kamun-qafa, kuma ya tabbatar da vacin masu faxin haramcinsa da haninsa.


Kamar yadda Kamun-qafar da shine yake kusanta Bawa zuwa ga Allah Maxaukakin Sarki ba ya fita daga Ijtihadi, kaxai dai shari'a tana fuskantarsa ne kuma ta yi masa iyaka, haka nan kuma akwai yiwuwar kaiwa gare shi daga inda ake kirdadonsa, kuma dukkanin tsanin da yayi wajen wannan kudurin to yana daga cikin Bidi'a da Vata.
Nuruddeen Ibn Muhammad (Darus-thaqalaini),

Kano – Nigeria.

+234 7028041972, +234 8037761798, +234 8098001766.
Yüklə 184,14 Kb.

Dostları ilə paylaş:




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin