DALILAI NA HANKULA WANDA SUKE NUNA KADAITUWAR ALLAH:
Jirgin ruwa zai nutse idan aka samu matuka biyu a lokaci daya, jagorancin yana tarwatsewa idan aka samu shuwagabanni biyu a lokaci daya, kasuwanci yana karye wa idan aka samu mutum biyu kowa yana son samun iko da isa da dukiyar, to idan haka ne ya kake gani ace wannan duniya me girman gaske wanda da za'a samu wani kwayar zarra daga cikinta ya lalace da ta fadi ta nemi gyara da ace akwai wani allah na dabanbayan Allah da an samu sa'insa da jayayya wanda zai haifar barna, Allah yayi gaskiya lokacin da yace: " da ace akwai wani allah acikin sama da kasa bayan Allah da sun lalace, tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin al'arshi daga abunda suke siffatawa (22)" suratul anbiya'i.
Daga cikin dabi'ar masu tarayya na kamfani ko kuma kungiya shine zakaga suna rigegeniya a tsakanin su wurin samun iko ya zama shine me bada umurni da yanke hukunci a kamfanin ko kuma kungiyar wanda hakan yake bata aiki kuma wannan rigegeniyar shine sababin samun sabani, Allah madaukaki yace: " Allah be rike wani yaro ba kuma babu wani allah a tare dashi, da ace akwai wani allan a tare dashi da ko wani allah ya tafi da abunda ya halitta kuma da wani sashi ya nemi iko akan sashi, tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffatawa (91)" suratul muminun.
Ko kuma kamar yada sarakunan duniya suke aikatawa tsakanin sun a yaki da fada kowa daga cikin su yana son kawar da mulkin dayan ya zama cewa shi kadai ne sarki, Allah madaukaki yace: " kace da ace akwai wani allah a tare dashi kamar yadda suke cewa da kuwa sun nemi kawar da ikon me al'arshi (42)" suratul isra'i.
Sayyid kudub Allah ya masa rahama yana cewa fadin Allah cikin wannan aya {Allah be rike wani yaro ba kuma babu wani allah atare dashi} …. Daga nan ne sai yazo da dalili wanda zai kore da'awar su da kuma sawwara ikidar su ta shirka na shashanci da kuma rashin yuwuwar hakan da cewa: {da ko wani allah ya tafi da abunda ya halitta} watan kowa ya rike abunda ya halitta ya zama yanada iko dashi ya juya shi yadda yake so, sai ya zama cewa ko wani bangare a duniya ko kuma ko wani bangare a cikin halittu yanada dokoki nashi na daban wanda baza'a samu wani doka day aba wanda zai rika jujjuya duniya. {da wani sashi ya nemi iko da wani sashi} watan da ya nemi samun galaba akansa wanda zai kwace masa ikonsa na tafiyar da nashi duniyar wanda babu wani doka guda daya da yake tafiyar dashi, dukkanan wannan surori babu su a duniya, wanda kasancewar duniya abu guda yake nuna cewa mahaliccin sa daya ne, sannan samun tsari daya a duniya shima yana tabbatar da cewa me tafitar da duniya daya ne. kowani bangare na duniya yana hade ne da sauran babu cin karo ko kuma sabani a tsakanin su…. {tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffatawa}.
Dostları ilə paylaş: |