HISABI:
Allah zai tayar da dukkanin halittun sa mutane da tsuntsaye da dabbobi sai ya tara su domin masu hukunci a tsakanin su a farfajiyar ranan kiyama domin a ciki masu hisabin su agaban me adalci baza'a zalumci mutane ba da komai, Allah madaukaki yace: " zamu shinfida mizanin awo na gaskiya ranar alkiya kuma baza'a zalumci rai da komai ba, idan ya kasance tazo mana da kwatankwacin abun cikin kwalln dabino na aiki ne zamu auna shi ya ishemu muyi mata hasabi akan sa (47)" suratul anbiya'i.
Za'ayima ko wace al'umma hisabi da shari'ar da Allah ya aiko masu dashi ta bakin manzon sa, sai asakama mumini a kuma hukunta wanda ya karyata, Allah madaukaki yace: " a ranar da zamu kira ko wace al'umma da shugabanta duk wanda muka bashi littafin sa da hannun dama to wannan sune wanda zasu rika karanta littafin su kuma baza'a zalumce suba da kwatan kwacin tsilin abun kan kwallon dabino (71) wanda kuma ya kasance makaho a wannan duniya to a lahira ma zai kasance makaho kuma zai zai bace hanya (72)" suratul isra'i.
Sai Allah ya sakawa mutane zalumcin su a tsakanin su, kamar yadda Muhammad manzon Alllah s.a.w ya bayyana haka cikin fadin sa cewa: " shin kun san wanene fallasashe? Sai suka ce: fallasashe a cikin mu shine wanda bashi dirhami ko kuwa kaya, sai yace masu: lallai fallasashe cikin al'ummata shine wanda zaizo ranar alkiyama da salla da azumi da zakka, amma zai zo ya zagi wancan yayima wancan kazafi ya kuma ci kudin wancan ya zubar da jinin wancan ya duki wancan, sai aba wancan cikin ladar sa da wancan idan ladan suka kare kafin agama biyan su sai a dauko zunuban su a daura masa daganan sai a jefa shi cikin wuta" sahihu muslim
Daga cikin cikan adalcin Allah shine madaukaki shine dabbobi da sauran halittu suma za'a masu hukunci a tsakanin su, saboda haka ne aka kira wannan rana ranan hukunci, manzon Allah s.a.w yana cewa: " tabbas za'a mayar da hakkoki zuwa ga masu ita hatta akuya mara kaho zata rama tunkurin ta da akuya me kaho yayi mata" sahihu muslim.
Idan aka gama hukunci tsakanin dabbobi sai allah yace masu ku zama kasa, a wannan lokaci ne kafiri zai ce kaice na dana zama kasa nima bayan yaga abunda ya tabbatar da halakar sa dashi, Allah madaukaki yace: " lallai muna maku gargadi game da azaba wacce take kusa a ranar da mutum zai duba abunda ya aiwatar da hannuwan sa sai kafiri yace kaice na dana zama kasa nima (40) suratun naba'i.
Bayan haka sai mutane su kaso gida biyu wanda babu na ukun su, yan aljanna da ni'ima da yan wuta da jahim zuwa rayuwa ta har Abadan wannan shine asara ga mutanen da suka karyata manzanni batattu, saboda haka ne mutum sai yayi aiki yayi tunani domin gujewa wannan asara, Allah madaukaki yace: " a ranar tashin alkiya ranar ne za'a rabu (14) wanda sukayi imani kuma suka aikata ayyuka na kwarai suna cikin aljanna ana masu ni'ima (15) wanda kuma suka kafirta suka kuma karyata ayoyin mu da haduwar lahira wannan suna cikin azaba tsundum (16)" suratu rum.
-
Dostları ilə paylaş: |