Kama tashar zuciyar ka, ka ji abinda



Yüklə 71,33 Kb.
tarix26.10.2017
ölçüsü71,33 Kb.
#13287

11

KAMA TASHAR ZUCIYAR KA, KA JI ABINDA



Ubangiji Ke Fada

Anna kuwa yadda yake a rubuce kenan cewa “Abubuwa da ido bai taba gani ba, kuma bai taba ji ba, Zuciyar mutum kuma ba da ko riya ba, wandanda Allah ya tanadar wa masu kaunarsa” mu ne Allah ya bayyana wa, ta Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma Zurfafau al’amuran Allah (1 Kor. 2:9,10)



Ka Lalubo Tashar Radiyon Zuciyarka, Ka Kama Muryar Ubangiji Allah.

Tunaninmu da gabobin jikinmu wato su kunnuwa da su idanun jiki ba za su iya karbar cikakkun budi na Ubangiji Allah ba. Dole ne ya shigo zuciyarmu ta ilhami bias aikin Ruhu mai tsarki wadda ke cikin mu (1 Kor. 2:9-16).

Na sha jin ana wa’yi da wannan kwatancin cewa zuciyarmu kamar radiyo ce wacce muke bukatan mu kama tassha mu ji abinda ke zuwa daga Ubangiji. Ni na amince da haka. Amma babu wanda ya taba bani yar hannun juyawa na neman tashan domin in iya kama tashan da kyau har in ji muryar Ubangiji din. Don haka, irin wancan wa’azin yakan kara badda ni ya sa ni cikin halin damuwa kuma.

A cikin wannan babin, za mu dubi hanyoyin kamo tasha wadda Ubangiji ya tanada mana domin mu iya sauraron muryar sa. Yawancinsu, suna nuna wa mutum yadda zai shirya zuciyarso ne, tunda ta zuciyar mutum ne Ubangiji yake magana da shi. Zamu dauki misalai guda uku daga cikin littafi Mai Tsarki. Na farko dai ita ce ta alfarwar sujada, na biye kuma Habakuk, sai kuma umurni da aka bayar a Ibraniyawa 10:22.

Ka Koyi Bude, ko Amfani Da Radiyo (Dandano, Irin Ta Alfarwa ta sujada)

Akan dutse ne Ubangiji ya ba wa Musa zanen alfarwa ta sujada wadda Ibraniyawa 8:5 ya bayyana shi kamar makamanci, da kuma isharar abubuwan sama. Ba wai kawi ya kafa musu hanya da al’umar Isra’ila za su sadu ya yi magana da su kadai ba, amma ya tanada mana hanya ne da zamu kusance shi har mu iya jin muryasa. Alfarwar, ya kamanta mana Ruhu, Rai da kuma jikin dan Adam, Farfajiyar, ya kamanci gangan jikin mutum, ta nan irin ta nazarin zamam hasken rana ne ke waskaka shi Wuri man tsarki kuma ya kamanci rai ko zuciyar mutum. Yana samun haske daga mai aka zuba masa, wannan an kamance shi da Ruhu Mai Tsarki wanda yake fayyace mana gaskiyar cikin zuciyarmu. Wuri mafi tsarki kuma ya kamanci ruhun mutum, nana ne daukakar Ubangiji yake haskaka cikin cikin mu, yana bamu budi na Ruhu kai tsaye cikin zuciyarmu saboda da haka Ubangiji yana magana da mu ta hanyoyi uku. An rubuta bishara ta hannun Luka a dandano na “wuri mai Tsarki,” Ubangiji ne ya haskaka zuciyarsa da wannan gaskiya (Luka 1:14). An rubuta Wahayin Yahaya a irin “dandano na wuri mafi tsarki” yayin da Ubangiji ya sa. Yana yiwuwa jadawahin da ke gaba ya nauna maka wannnan gaskiyar.

Kowane daya daga cikin wadannan abubuwa guda shida, suna madasin dandano da muke yi yayin da muke kusantar Allah.

  1. Bugaden Da Aka Dalaye Da Tagulla – Gicciye (Fitowa 27:1-8)

Wannan yana nuna alkawarinmu na fari da muka amince da Yesu a matsayin Ubangijini ranmu sa’annan muka mika jikunana hadaya rayayya abar karba a gabansa (Romawa 12:1, 2) Ba makawa, wannan dole ne in za mu nema mu kusanci Ubangiji Allah.

  1. Daron wanka Da Aka Dalaye Da Tagulla Maganar Allah. (Fitowa 30:17-21)

Wannan ya nuna wanke jikinmu ta wurin amfani da kalmar Allah wato (Logos) a rayuwar mu. Kalma (logos) da mutum yayi amfani da shi a rayuwarsa yana ikon tsarkake shi.

  1. Teburin Grurasar Ajiyewa – wato yardar mutum. Fitowa 25:23-30

Kamar yadda akan nika garin filawa ya yi laushi sosai don gurasa ta yi kyau, haka ma, mu yarda da ubangiji da dukan zuciya yayin da muka mika masa dukan kome a rayuwarmu.

  1. Alkuki Na Fitila Mai Rassa Bakwai Rassa Bakwai – Haskaka

Zuciyarmu. (Fitowa 25:31-39)

Ubangiji yana haskaka, ya kuma fayyace mana gaskiya a zuciyarmu yayin da muke nazarin maganar Allah.

  1. Bageden Kona Turare – Abin Sosan Rai (Fitowa 30:1-10)

Tawurin mika hadayar yabo ga Ubangiji a kullum, mukan jawo abin da ya sosa mana rai wato irin yadda mukan dadi a cikinmu a Karkashin bishewra Ruhu Mai Tsarki.

  1. Akwatin Alkawari – Budi Ta Ruhu Kai Tsaye Zuwa Cikin Zuciyarmu (Fitowa 25:10-22

Cikin Sujada da natsuwa shiru a gaban Ubangiji, mukan shiga zumunci na kurkusa, al’amarin zuci da Ubangiji. Daukakar Ubangiji kan cike mana Zuciya

Domin Karin haske ko bayyani kan wadannan abubuwa da na ambata, ana iya adar koyarwar da aka yi a kaset kaset mai suna:

The way into the Holiest” wadda Derek prince ya yi da kuma littafin nazarin da ke tattare da shi.



Daga Derek Prince,

P.O. Box 306, Dept. 6, Ft.

Landerdale, FL 33302
Kama Tasha Da Karfi Da Yaji Domin A Karbi Kalmar Allah Wato (Rhema) Kai tsaye (Irin Yadda Habakuk yayi A Habakuk 2:1-3)

Kalmar Allah wato (Rhema), wani tunani ne ko dabara, ko wani nauyi da mutum ya kan ji wanda Ubangiji ne yakan sanya a zuciyar mutum mu ne da hakkin bude zuciyarmu wa kalma (rhema) ta wurin:


  1. Kebe kanmu daga surutai ko yamusai. Mu nemi wani wuri shiru.

  2. Muna iya natsuwa a zuciyarmu ta wurin zuba wa Yesu ido wata gabadaya mu mai da hankalinmu kan Yesu shi kadai (muna iya amfani da sanya hotonsa a zuciyarmu ko wahayi)

  3. Tsare ciyarmu daga tunani barkatai ta wurin dauko rihoto

Don karin bayyani sai a maimata nazari na Habakuk a wannan littafi.

A Lalubo Tashar Da Kyau Domin A Karbi Kalmar Allah (Rhema) Kai Tsaye (Ibra. 10:22)



Saboda haka ya yan’uwa, tunada muke da amince war shiga wuri mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu, ta sabuwar hanyar, rayayya, wadda yabude mana ta labulen nan wato jikinsa, da ya ke kuma muna da Firis mai girma, mai mulkin jama’ar Allah Ubangiji, sai mu matsa kusa, da zuciya daya da cikakkiya bangaskiya tabbatacciya, da zukatanmu tsarkakken daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankke da tsattsarkar ruwa. (Ibraniyawa 10:19-22) Yayin da muka kusanci Ubangiji da muka kusanci Ubangiji cikin natusuwa shiru a gabansa domin mu ji muryarsa a zuciyarmu, murubuncin Ibraniya wa ya ce ga yadda zuciyarmu ya kyautu ya kasance.

Dandano Irin Ta Alfarwa Ta Sujada – Shiri Da Allah ya yi wa Mutum Ya Kusance Shi

i
yar Zuciya Mai Gaskiya

Dole mutum ya kasance da zuciya mai gaskiya, banda munafunci ko yaudaro bale kuma karya.

Da zuciya daya cikin kauna, da yabo, da aminci, bincike, da nema, ana kuka ga Ubangiji Allah ana kuma sauraronsa.

Cikakken Bangaskiya



Dole ne mu zo ga yarda, mu amince da dukan abinda Ubangiji ya fada mana a zuciyarmu.

…domin duk wanda zai kusaci allah, lalle ne ya gaskata, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu neman sa. (Ibraniyawa 11:6). Allah Ubangiji yana nan, yana shirye ya sadu da kai a zuciyarka, domin ya ba ka rai, kuma ya nuna maka abubuwa. Immanuel yana nufin, Allah tare da mu.
Zuciyar Da Aka Yi Masa Kaciya Daga Tunanin Zunubi
Dole ne mu kai ga amincewa cikin gangaskiya cikakken aikin da jinin Yesu ya yi a rayuwarmu.

Ya ku kaunatattu, in zuciyarmu ba ta ba mu laifi ba, sai mu je gaban Allah da amincewa (1 Yahaya 3:21)

Saboda haka, duk wanda ya san abinda ya kamata, ya kuwa kasa yi, ya yi zunubi kenan (Yakub 4:17).

Ba zamu kusaci Ubangiji Allah da zunubin da ba mu furta ba a cikin Zuciyarmu. Dole ne mu furta shi, jinin Yesu ya tsarkakemu. Dole sahihiyar Zuciyar Mai Gaskiya

Dole zuciyar mutum ya kasance da gaskiya, ba munafunci, ko yaudara bala kuma karya. Kauna ta kasance sahihiya ne zuciyarmu ta sake, ta kassance cikin salama muddin muna son mu ji muryar Ubangiji har mu gane ayyukansa ha cikinmu.

JIKI DA AKA WANKE DA RUWA MAI TSABBA

Kamar yadda Almasihu ya kaunaci ikkilisiya har ya bada kansa dominta, domin ya mika ta ga Allah Ubangiji, tsarkakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin kalma (rhema) (Afisawa 5:25, 26).

Dole ne mu biyayya, kuma mu yi aiki da kalma wato rhema da Ubangiji Allah ya bamu.

Sa Zuciyarka A Wuri Daya (Kamo Tasha)



Wani fanni na shirya zuciya ita ce maida hankali gaba daya cikin Kiristi Yesu- A tsabace shi daga fushi, dacin rai, abinda ba daidai ba, saurin karai; A kare; A Kare shi domin kada wadansu su cusa wadannan ra’ayin a cikinka; Kama lura da shi saboda ya zama magudanar rai, yana fitar da kalmar rai; tsayawa da karfi a kan bayyaba yarda ga sa zuciyan nan tamu, domin shi mai yin alkawari nan amintace ne (Ibraniyawa 10:23); muna kuma rika kula da juna, ta yadda za mu ta da tsimin juna ga kauna da aiki nagari (Ibra. 10:24); kada mu bar yin tsaronmu, yadda wadansu ke yi, sai dai mu karfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranan nan tana kusatowa ba (Ibrani. 10:25)
Tsarkake Radiyon Zuciyarka.
Azumi, ba tsaya kan tsarkake jikinka daga datti mai guba ba, amma yana tsakake ruhun ka domin ka kara kusawa kama kusatar Ubangiji Allah. Idan baka ganin cin gaba cikin wannan niyya, yin azumi zai taimaka ka sami karfafawa da nasara cikin ayyukan ruhaniya. Sura ta hamsin da takwas na littafin annabi ishaya ya kwatanta mana irin azumi da za mu da kuma ribarsa. Biyu daga cikinsu, sune “Ubangiji zai bi da mu kullayaumi” da kuma za ku yi kira, ku yi kuka ni kuwa zan ce muku ‘Ga ni.” (Ishaya 58:11,9).” Domin haka ina cewa idan baka ganin cigaba ko nasarori a rayuwarka na bi, sai ka yi azumi ta haka za ka gyara hanya. Na tarar cewa Ubangiji yakan kusace ni ya biya mini bukatuna idan na dauki kwanaki cikin azumi da addu’a ina bidar fuskarsa. Matakai mafi inganci da na dauka, na kuma karu a rayuwata kamar kirista shi ne wannan. Saboda Karin bayyani sai a nemi God’s chosen Fast wadda Arhtu Wallis ya wallafa.

Abinda Ke Jawo Cikas Da Damuwa Wajen Jin Muryar Ubangiji Allah

  1. Karancin bangaskiya – Yadda zaka magance wannan matsalar: Sa kai cikin abubuwa masu “gina iza bangaskiya” (misali, magana ko addua cikin harsuna, sujada cikin Ruhu, Yabon Allah, karatun alkawarai na littafi Mai Tsarki, maimata karatun rihotanni da ka dauko, amfani da kwatanta wasu labarai na littafi mat Tsarki a zuciyarka masu saukin fahinta, cikin bangaskiya, ka amince da Ubangiji mai aminci (Ibraniyawa 11:6)

  2. Ka kasa tsai da Zuciya – yadda zaka magance irin wannan matsalari ka fara morar dauko rihoto da kuma wahayi. Ka rubuta, ka yi addua ka furta dukan abinda ka zuciyarka. Ka tabbata zuciyarka ba ta baka laifi ba, in kuwa ya baka laifi sai ka tsarkake shi.

  3. Kana ji kamar Ubangiji Allah baya magana. Yadda zaka magance irin wannan matsalar: Gabadaya ka bude zuciyarka a gaban Ubangiji. Sai ka fara rubuta kalmomi da ke shigowa zuciyarka ko da kima ne. Ka tuna cewa muryar Ruhu a zuciyarka yana iya daukewa idan ka kawo naka iyawa ko hujja cikin tunani.

  4. Ubangiji Alllah bayar magana. Yadda za a magance irin wadannan matsololin: Yana yiwuwa kana tambayi kuma Ubangiji bai yi niyyar baka ansa ba. Watakila kana bukata ka yi azumi domin kofar amsarka ta bude. Ka yi bincike, kila kana da mugun guri (Yakub 4:3).

Kodashike Kiristi ya bude mana kofa na shiga wuri mafi tsari ta wurin tsaga labule da kuma tsarkake mu da jininsa, Kirista da yawa ba su shiga wannan wuri kullum. Hanyar, ba ta da wahala ba cudewa. Kiristi ne mai bamu bangaskiya, yana kuma bamu Zuciya mai tsaba. Mu dai kawai mu amince, mu cimoriyar aiki da Yesu ga gama. Dole ne kaunarmu da zuciyarmu ta tsaya akansa.

Duk da haka mukan rarabe hankalin mu. Ba mu cika neman nasara cikin ikonsa ba domin muna da sha’awar jiki. Ba mu shirye mu rasa ranmu domin mu sami ransa.

Har wa yau, sai mun kara himma sa’annan zamu yi tafiya cikin sabon salo. Da mamaki na sa ido na ga yadda ‘ya’ya biyu suke koyan tafiya. Suna ta fadi tashi, su ji ciwo nan da cn har sawon watanni da dama. Duk da haka ba su fasa. Tafiya yafi rarrafe haka kuma wuri mafi tsarki yafi wuri mai tsarki Na yi imani cewa kafin mu kware cikin tafiya cikin wuri mafi tsarki, zai zama kamar yaran can da na bada misalin, mu fadi a nan, mu tasshi, mu kuje nan da can har ma mu yi ciwo sosai watakila ma na sawon wadansu shekaru amma kada mu karai, ba kuma za mu fasa ba, sai mu kware din.

Mu dauki kalubale, mu kusaci Ubangiji gabagadi mu karbi rai da kuma kaunarsa. Allah Ubangiji ya taimake mu, mu yi dukan abinda ya wajaba. Allah ya bamu iko don kada mu yi tattalin ranmu domin ya bamu nasa rai.

KA YI CIKIYAR KAMO TASHAR UBANGIJI ALLAH

An tanada maka yadda zaka yi cikiyar kamo tashar nan a shafi na gaba, zai taimaka ka maimata, ka kuma gane wannan babin sosai. Ubangiji zai yi mana magana cikin zuciyarmu idan mun bude masa, kuma mun laluba tasharsa. Ta haka zamu yi addu’a wadda Ruhu ne ke bishe mu.

Manufa-mu raya wannan dabi’a na Ruhu, ta wurin horar da kanmu har mu gane tunani ko maganar da Allah Ubangiji da kansa ya sa a zuciyarmu.


  1. Mu Koyi Ruyuwa Kamar Ta Alfarwar Da Allah ya Tanada (Fitowa).




    1. Alfarwa-Ni hadaya ne rayayye.

    2. Duro na wanke jiki – Na wanke kaina ta wurin amfani da maganar Allah.

    3. Gurasar Ajiyewa – Ra’ayin kaina ya kare a gaban Ubangiji

    4. Alkuki na titila – Ubangiji yana haskaka zuciyana, yana mini budi ta Ruhu Mai Tsarki .

    5. Turare na Konawa – yadda nike mika wa Ubangiji godiya kullum, ya sa na iya kaskantar da kaina a gabansa yana yi mini jagora.

    6. Akwatin Alkawari – Na koyi tafiya a gaban shiru har in karbi maganar da ya sa a zuciyarta.

      1. Kamo tashar da karfi da yafi – kasancewa shiru a zuba ga Yesu (Habakuk 2:1,2) –

  1. Ina da wuri da na kebe musamman.

  2. Ruhuna kan natsu shiri ta wurin zuba idanu na ga yesu (Ibraniyawa 12:2)

  3. Ina iza aukuwa ikon Ubangiji ta wurin rubuta abinda ke zuciyata.

      1. Kamo tashar da Kyau-Kawar da matari na ciki. (Ibraniyawa 10:22).

        1. Zuciyata tsab, bani rokon zuci, ga gaskiya da rikon amana

        2. Ina zuwa gaban Ubangiji da cikakken bangaskiya

        3. Na tsarkake lamirina ta wurin karbar tsarka kewar Kiristi

        4. Na yi biyayya da kalmar Allah wato (rhema) da aka bani.

  4. Na Rinjayi Mugunta Ta Wurin Rayuwa Cikin Kalma (Rhema) Da Allah Ya fada mini (Ibraniyawa 10:23-25)




    1. Ina furta shi da bakina

    2. Ina kokarin neman hanya da zan iza wasu su yi tafiya cikin kalma wati Rhema da Ubangiji ya basu.

    3. Ina hada kai da yan’uwa don mu karfafa juna.

C Ina Tabbatar Da Kalmar Da Allah Ya Bani Ta Wurin Mika Shi Ga Na Gaba Da Ni (Ibraniyawa 13:17).


  1. Ina sarayadda kaina a karkashi shugaba na cikin Ubangiji, kuma ya amince in kawo kowacce shawara gare shi.

  2. Ina neman shawara gare shi. Muhimiyar batu wadda zai iya shafar rayu wata, ko ta fanni kudi da dai sauransu.

Abinda Na Dandana

Na tarar Ubangiji yana magana da ni a farfajiya ta waje, da, wuri mai tsarki, da kuma wuri mafi tsarki. Yakan bishe cikin sauki ta wurin karanta maganarsa wato littafi mai Tsarki. Yakan bada haske kan wani wuri da nike karantawa cikin zuciyata, yakan kasance kamar ba karatu nikee yi a, littafi, yana ban. Sani cewa kalma ce wato (rhema) daga gare shi a wannan lokacin. Ya sha magana da ni cikin zuciyana ta tunanin da ban shirya su ba, da sifar wani abu ko kamani kai tsaye cikin zuciyarta yayin da nike sauraronsa shiru. Yesu kasance hanya a fare ni, gaskia da rai kuma.

Haka kuma na tarar cewa dandano na wuri mafi tarki ya dauke domin ban kamo tasharsa da kayuba. Yana yiwuwa na shiga da karancin bangaskiya a zuciyata ko rashin amincewa, ban kasance da gabafgadi in kusaci Ubangiji ba

Yadda Zaka Yi Amfani Da Danko Rihoto



Ka dauki rihoton abinda ya fada. Kana amfani da wahayi da ya nuna maka, ka mika kanka ga kowane sashe na alfarwar da muka yi magana akai. Ka Zuba ido ga Yesu, kana tambayarsa abinda yake so ya fada ko ya bayyana maka game da rayuwar ka. Dagan nan sai ka kamo tashar abinda zai auku, kuma ka fara rubuta ko dauko rihoton abinda zai ce da kai. Kana iya rokon sa game da yadda zaka iya kamo tasha da kyen.
12

Yada Times – Lokatai Na Nuna Kauna Wa Juna.


Yada Times
Yesu ya ce, “Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah madaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko (Yahaya 17:3).” Ka ji kyakyawar batu: Rai madawwain shi ne sanin Allah Ubangiji! Amma wannan ba sanin shanu ba ne, irin ace ka dan saba da mutum ko ma ace abokinka. Wannan kalma da aka mora a nan game da “sani” shi ne ginosko, yana nufin a shiga dangantaka mai zurfi kuma ya rika girma yana bunkasa”. A juyi na Helenanci a tsohon alkawari wannan shi ne kalma da aka mora a Farawa 4:1, da aka ce “Adamu ya san Hauwwu kuma ta Haifa masa da” . Wannan shi ne dangantaka na kusa sosai na ainihi. Yesu ya yi wannan kalami mai ban sha’awa cewa wannan shi kwatankwacin Rai madawwami. Mutum ya shiga irin wannan dangantaka da Ubangiji dukan halitta da kuma makadaicin dan sa, Yesu. Tab, ka ga kaddarar Allah!

Bulus Manzo ya gano wannan gaskiyar, kuma ya rike ta gam. A cikin Filibiyawa 3:10, 11 sai ya ce babban muradinsa shi ne, ya san Yesu, da ikon tashinsa daga matattu, ya yi tarayya da shi a shan wuyarsa, ya kuma zama kamar sa wajen mutuwa tasa, domin ta ko kaka ya kai ga tashin nan daga matattu.” Kana da kunnen jin kukan Zuciyar Bulus manzo? Shi dai kawai ya san Ubangiji! Cikin wannan dangantaka ta matukar kauna, za mu ji mu gane ransa wato Ubangiji yana gudana a cikin mu, sha’awar jiki kuma sai ya mutu, wannan rai nasa kuma daga cikinmu har ya kai kan wadansu. Wannan ita ce baici ko dalilin ceto da aka bamu kyauta. Shi ya sa aka maya haihuwarmu.

Takwarar wannan kalma na Helenanci wato ‘ginosko’ a yahudanci shi ne ‘yada,’ Zamu mori wannan kalmar mu kwatanta kaunar zamumci da muke yi cikin addu’a. Addu’a ya fi ace roko muke yi don a biya mana bukata. Lokaci ne na zumunta, na numa sahihiyar kauna wato “yada” da yahudanci. Addu’a, hanya ce ta sadarwa tsakanin masoya. Zumunci ne da mai kaunarmu Yesu-saboda sananin shakuwa da juna, mukan dago kasancewar juna cikin zumuncinmu, muna kuma da lokaci domin mu kasance tare mu saurari sosai saboda yadda muka dauki juna da matukar muhimmanci muna ganin darajar juna ya sa muke dokin tarayyar mu tare, muna kome tare muna daukan nawayar juna. Biki ne kan kaunar da muke yi wa juna. Zumunci ne tsakanin masoya biyu. Soyayya ne, ba kaurarar dokoki ba. Kada mu mai da shi kamar tilas amma mu saukaka wa juna ya zama soyayya ta son rai mai dadi, mai ban sha’awa kuma. Ai masoya, dole su yi zumunta da juna cikin raha, su tattauna dukan abinda ya shafi rayuwar su. Dangantakar ya kahu kan matukar fahintar juna cikin murna, kwaciyar rai da salama ba fashin hankali da bauta saboda takunkumi da aka dora wa juna ba.
Al’amari Mai Kayatarwa Tsakaninka Da Sarkin Sarakuna

Yana da muhimmanci, don kanmu, mu nemi Ubangiji domin Shi Ubangiji na amma ba domin mun san cewa Shi mai biyan bukata ba ne. Yana da marmari mu kasance a cikinsa, mu more kaunar da ya yi mana. Yana son mu ji dadin zumunci tare kamar aminai. Yana marmarin mu nuna masa kauna a cikin zuciyarsa.

Ba ya jin dadi ko kadan saboda yadda muke watsi da shi, muna buge-bugen neman biyan bukata don kanmu har mu bude wa zunubi kofa ya lalata rayuwarmu da kuma dangantakarmu da shi. Daga Yanzu, mu name shi kamar babu wani abinda ya fi haka mu ba wa lokacin zumuncin mu tare da shi fifiko a rayuwormu kanaar ma babu wani abinda ya fi haka.

Saboda wannan soyayya tsakanimu, za mu fara ganin ikonsa yana bayyana daga rayuwar mu, muna biyan bukatun wasu, muna karfafa rayuwarsu ta hanyoyi daban-dabam. Ubangiji zai yi ta jin dadin aikata al’ajibai ta hannun mu. Irin wannan soyayyar wato dangantaka na kusa yana haifar da bangaskiya – irin bangaskiyar da kome kankantar sa wadda shi ne kasance kurkusa da Yesu har mutum ya san nufinsa game da kowace hali da ake ciki, aka kuma biya bukata daidai wa daidai kamar yadda ya yi bishewa. Hanya guda daya da za mu san abinda Yesu ke ciki, ita ce ta wurin bada lokacin mu cikin zumunci tare da shi – a kullum rayuwarmu cikin kasancewarsa yake. Kan wannan kam ba makawa! Amma kuma za mu sami cikakken murna da gamsuwa cikinsa.
“Ku Zo Gare Ni Da Dukan Zuciyarku”

Ubangiji ya yi maganar juyowa gare shi da dukan zuciya saboda mu iya morar alherinsa. Gaa fannoni biyar na juyowa ga Ubangiji da dukan da Allah ya bukace mu da su:

  1. Bari in Zama maka babban dukiya domin ni ma in bada hankalina gareka (Markus 12:30).

  2. Ka name ni da dukan zuciyarka domin in bayyana kaina a gareka (Irmiya 29:23)

  3. Ka amince da ni da dukan zuciyarka domin ni ma in iya lura da sawayenka (Misalai 3:5)

  4. Ka yabe ni da dukan zuciyarka domin in ma kasancewa ta ta zama gurbin ka (Zabura 9:1).

  5. Ka juyo gare ni da dukan zuciyarka, ni kuwa zan nuna maka jinkai in albarkace ka kuma (Joyel 2:12)

Daga Littafin Rihotona

Karasa wannan sashen da rihotanni biyu da na dauko game da wannan batu. A lura da yadda kalmar Allah wato rhema ya cude cikin kalma (logos), koda yake wannan ba bakuwar abu ba ne a gare ni amma ina bukatar in rika jinsa a kai akai, in amince da su kowacce rana a rayuwata.

“Ni Ne Alfa da Omega, farko da kuma karshe Ni Ne Farko kuma Ni Ne Karshe, Haske da kuma Iko. Ina iya aikatawa fiye da dukan abinda za ku roka, ko za ku zata nesa, wato ta karfin ikona da ke aiki a zuciyarku. Ku dai ku zo gare ni, ni kuwa zan zama karfinku . Zan zama masoyinku. Ku dai kawai ku zo gare ni. Ba zai yiwu ba idan ba kasance tare cikin Zumunci ba, don haka, ku rika zuwa gare ni kullum. Ina nan ina jira. Kullum ina shirye domin in saurare ku, in kuma amsa maku. Ni Ubangiji ne mai kauna, mai jinkirin fushi cike da juyayi. Nakan gafarta zunubanku. Ina suturce ku da adalci na. Dole ne ku name ni do dukan zuciyar ku, ku juyo ga barin muguntar ku, ku zo gare ni. Za ka amince ka yi wannan?”

Wata rana kuma:

Kawai nakan ji dadin kasancewa tare da ku, ba lalle sai mun yi wani ta musamman ba, amma dai mu kasance tare. Ina jin dadin kanshin sujafa da ku ke yi Lokatai kamar wannan yana da kyau da dadi a gare ni. Kamar ruwan rafin kan dutse ne yana gangarawa abinsa. Ina matukar jin dadi idan kun zo gare ni. Buri na ya cike kenan, idan kun zaba ku kasance tareda ni. Yana faranta mini rai. Ku rika zuwa kullum. Kada ku yi tsammani cewa lalle lalle in mun sadu, sai mu yi wani abu na musamman kasancewar mu tare ita ce jin dadi na. Kawai, ni dai mu kasance tare da juna. Ku zo mu ji dadin zumuncin mu tare.”



Karin littattafai Kan Wannan Batu.

The Gentle Breeze of Jesus Wadda Meltari ya wallafa.

Come Away, my Beloved wadda Frances J. Robberts ya wallafa.

Talking With Jesus wadda Evelyn Klumpen houwer ya wallafa.

Ana iya samun Karin haske ko bayyani kan kalmomin nan biyu wato ‘ginosko’ da kuma ‘Yada’ a shafi na 395-398 a The Dictionary of New Testament Theology, Vol. 2 wadda Colin Brown ya bayar.

Amsar Rihoton Da Akan Dauko.

A dauki dan lokaci ana dauko rihot, Rubuta wasika ta soyayya wa Yesu, ka saurare shi ya bada amsa. Ka fada masa yadda kake jin dodinsa, da muhimmancinda a gareka. Ka zuba masa ido sa’annan ka kama tashar abinda zai fada maka. Ka dauki rihoton abinda zai fada maka.
13

Ka’idodi Na Ruhu


Saboda tafiyarmu cikin duniyar ruhu ta zama mana da amfani, dole ne mutum ya fahinci dokoki na wannan sashe. Dokoki da ya kamata a fahita sosai sune wadanda suke kewaye da yadda Ruhu Mai Tsarki yake aikinsa. Mun rigaya mun nazarci yadda yake magana da mu a cikin zuciyarmu. Yanzu kuma Zamu yi nazarin yadda yake aikinsa.
Ka’idodi Nassi (a cika)
1. Mutum yakan yi addu’a Romawa 8:26

Sosai idan Ruhu Mai Tsarki

Ke bishe shi

2 Dole ne Ubangiji ya nuna Romawa 8:26a – Ruhu

cewa mu masu kasawa ne shi ke taimakonmu (yana

cikin yin addu’a kullum tarraya tare da mu)

saboda mu koyi dogaro cikin kasarwa. Ka roki Ruhu

kodayaushe kanizawar ya taimakeka ka yi nasara

Ruhu Mai Tsarki Dole mu kan kasawarka cikin niyyarka

Koyi hutawa ko cikin kasa- ta addu’a zai kuwa taimaka

Warmu, ba “naliya” a cikinsa Ibraniyawa 4:16). Kiwuya,

Ba kasalar jiki, daurewar kai da

makamantarsu.
3. Ya. Kamata dukan addu’ionmu Romawa 8:9

su kasance cikin Ruhu (izawa 1 Korintiyawa 14:14

bishewa, karfi, duka Ruhun ne 1 Korintiyawa 14:15

zai tallafa.) In ko ba haka Afisawa 6:18

ba, to adduarmu cikin jikina Yahuza 1:20

Muna da cikakken yanci

Mu zo wurin Allah Madaukaki Yahaya 14:6

Ta wurin Yesu Kristi. Amma duk

Da haka ainihi hanya zamu Afisawa 2:18

Sami cikakke zumunci

Ubangiji, ita ta aikin Ruhu Mai Tsarki

­­­­­­­­­­­­­­­­­­­­­5. Muna da wadanda suke Romawa 8:27

taimaka mana cikin addua, Romawa 8:34

wato masu taimako biyu

Ruhu Mai Tsarki yana taimakonmu mu tsarrafa addu’a cikin zuciyarmu, Yesu kuma yana gaban Allah Karin karatu: Ka yi addu’arka cikin Ruhu.
Abinda Kai Zaka Yi

Ka roki Ubangiji ya bayyana maka gaskiyar abinda ke cikin wannan babin. Ka zuba wa Yesu ido sosai cikin zuciyarka. Cikin wannan hali sai ka dauki rihoton abinda ke shigowa zuciyarka. Kada ka yi garajen gwada shi da koyarwar littafi mai Tsarki a yanzu ba takuna amma kana iya yin haka bayan ka idar. Cikin bangaskiya ka rubuta abinda ke shigowa

zuciyarka sa’annan ka yi wa Ubangiji godiya domin abinda ya sanarda

14

Wata Fanni Ta Addu’a Cikin Ruhu



Dole ne addu’a ya fito daga zuciyarka amma ba tunani ko ilminka ba, muddin zai zama addu’ar da Ruhu ne ya haifar. Zuciyarka ne zai tsarrafa yadda zaka yi addu’a, shi ne zai fara, shi ne mai bida ka, shi ne kuma zai cika ya karasa har karshe. Mutum yakan fara addu’a da saduwa da Ubangiji Allah a cikin zuciyarsa, yana tarayya da shi cikin bangaskiya, yana kuma bawa ikonsa dama – yana furci, yana kuma yi wa Ubangiji godiya domin ya cika aikinsa. A yi nazarin jadawahin da ke gaba domin zai bada Karin haske game da wannan batu.

Yanzu, sai mutum ya shiga addu’a bias bishewar kalm’ar Allah wato Rhema. Yana da amfani mutum ya bude wa Ubangiji zuciyar sa, ka amince da kowane abinda zai sanya a zuciyarka.

Ka yi amfani da wahayi domin ka fayyace kowace gaskiya cikin bangaskiya. Ka dubi Ubangiji Allah. Ka dubi ikonsa cikin tarayya da kai. Ka bashi dama ya sanya hoton ko kwatancin a zuciyarka. Ka dubi abinda kai kayi niyya amma ka bude idon zuciyarka. Ka roke shi ya nuna maka abinda shi yayi niyya. Zai baka daidai yadda yake baka kalmarsa wato rhema.

Wasu Abubuwa Kanana Da Za a Rika Tunawa



  1. Ka yi ta godiya domin kana rike ko tanadin bangaskiyar ka kenan dukan yini. Ka ci gaba da yi masa godiya saboda ayyukansa a rayuwarka.

  2. Ka kasance da nacciya da jimiri, ta haka zaka warke daga kowace abu mai wahala (da safe fa rana da yamma, kullum dai). “Ubangiji na gode maka sosai domin abinda ka yi mini da abinda za ka cigaba yi a nan gaba. Ka sabunta, yanzu, warkarwa kuma yana samuwa. Ubangiji” na, ina matukar godiya.”

  3. Dole ka sabunta bangaskiyarka kullum ka wurin kara cika zuciyarka da maganar Allah kodayaushe. (Joshua 1:8; Romawa 12:1,2)

Sauya

Da

Kowace tunanin soro--- Tunanin bangaskiya kowacce tunanin rashin lafiya….Tunanin rashin lafiya---Tunanin warkaswa kowacce tunanin mutuwa ….Tunani rai da rayuwa.

  1. Ka sabunta Kauna, ta kara ilimantar da Zuciyarka cikin kaunar Allah Ubangiji. Dole ne mutum ya kara ilimantar da zuciyarsa saboda ya kaunaci sauran jama’a hatta dabbobi da irin kauna ta Allah. Wannan yana da sauki gama kana rayuwa bias ka’idar halitta kenan. In ka tarar cewa ka gaza a wasu fannoni fushe wato ka ji haushin abin nan da kayi zai kara bata sha’ani ne kawai. A maimakon haka, sai ka amince ka yi kuskuri, ka yi gyara in ya yiwu sai ka cigaba da rayuwarka lafiya lau.

Addu’a Cikin Ruhu


Mataki Nassi Misali

1. Ka saki jikinka – Ka nutsu shiru, cikin jin dadi da kuranciyar rai, ka mance da kanka a gaban Allah da wanda kake addu’a dominsa.

Zabura 46:10

Kana zaune cikin jin dadi, kada ka takuri kanka kana hutawa amma a fadake. Ka karofo (kada ka bada umurni) kada ka takuri ko wani gaban jikinka, sai ka sa hotonsu wato ka kwatantasu Yesun da wanda kake masa addu’a a zuciyar ka

2. Cikin zurfin tunani, ka sa rai ga hakkakewar Allah Ubangiji, ku yi tarayya da shi cikin Ruhunka

Yana kurkusa da mu. Ayy. Manzanni 17:28 Filibiyawa 2:20 Zabura 123:1

Muna nasara kan mutumtakarmu (fargaba ko soro, bukatanmu, tunaninmu, kokarin kanmu da sauransu), ta wurin bude ruhunmu da karbar rai da Allah ya sanya a cikinmu (muna morar kowacce abu da ta sa Ubangiji ya zama zahiri a garemu). A maimakon a nema a ingiza shi kan bukatocinmu, a hankali cikin kwaciyar rai mu shiga cikin zumuci tare dashi kana iya amfani da wahayi.

3. Ka hade ranka da tasa-ka roke shi domin Ransa ya askance a cikinka

Luka 11:13

1 Yahaya 5:14,15

Muna nasara kan mutumtakarmu (fargaba ko soro, bukatunmu, tunaninmu, kokarin kanmu da sauransu), ta wurin bude ruhunmu da karbar rai da Allah ya sanya a cikinmu (muna morar kowacce abu da ta sa Ubangiji ya zama zahiri a garemu). A maimakon a nema a ingiza shi kan bukatocinmu, a hankali cikin zumunci tare dashi kana iya amfani da wahayi.

4. Ka gaskata cikin bangaskiya cewa ka karbi ikonsa, sai kaya masa godiya. Bangaskiya ce mabudin iko.

Markus 11:23,24

Kada ka rika cew kusu-don Allah kana ta roko, amma ka ce, Ubangiji nagode domin ikonka yana warkar da mi yayinda kake dubawa


Wata Fanni Ta Addu’ar Warkarwa
Ba a kayyade warkarwa wa mabiyan Kiristi kadai ba. Haske ne da kaunar Allah Ubangiji da ke shigowa cikin duniya da ka cike da duhu da wahala. Alherin Allah ne ke kai mutane ga tuba (Romawa 2:4). Daga cikin kutaren nan goma da Yesu ya tsarkake su, tara ne daga cikinsu suka karbe shi a matsayin Ubangijin su da mai ceto? (Luka 17:12-19) Bisa gaskiya ma al’umai wato yan duniya sun fi karbar al’ajibai na warkaswa fiye da ‘yayan Allah. Duniya tana karbar dandano ne na kaunar Allah ba domin sun cancanta ba, yana basu har da alherinsa kuma.

Idan zamu shiga addu’ar warkaswa, ka zabi wata misali mai sauki da ka sani nufin Allah ne (misali; warkewarka – Matiyu 18:16; Ayyukan Manzanni 10:38). Ka roki Yesu ya dora hannunsa kan wurin da kake bukata ya warkar. Kana daukawa kenan ta wurin kubawa cikin kauna daga warkaswa da ke cikin ruhunka. Yesu ne zai bisheka yadda zaka dibiya hannunka. Ku yi ta hira da Yesu har sai ka gane kasancewarca da ikonsa na warkarwa a cikin ka. Sai ka furta shi kamar yadda shi ya baka ikon furci.

In har rashin lafiya ya sananta, ta wai Ubangiji ya gaza ba ne, sai dai mu mu gaza cikin mutumtakarmu. Idan yakamata ba ko ma a ce ya lalace to sani fa wanda ya kirkiro wutar sai da ya yi ta jarraba shi har san 600 ba tare da nasara ba, bai kuma fasa har sai da ya zo ya yi nasara daga bisani.

Abinda Zaka Yi Game Da Addu’a



Ka gwada shiga addu’a da wadannan matakai hudu da aka ambato a wannan babi. Da farko dai ka saki jikin ka. Sai ka daga idanun ka sama wurin da taimakon ka da karfinka ke zuwa. Sai ka fara daukaka sunan Yesu. Yesu Ka sanar, ko ka raira wakar alherinsa, da jinkansa, da daukakarsa da girmansa, da al’ajibinsa. Ka dube shi zaune bisa kursiyin sarautarsa da daruruwan mala’iku da hallitu da suke ruku’u a gabansa suna yi masa sujada . Sai ka gode masa saboda ya kyale dukan wadannan domin ya kansance tare da kai. Ka gode masa domin Ruhunsa da taka sun hadu. Ka sa ido ka dubi wannan sarki da ya kasance tare kai yana gudanar da ayyukansa a cikin ka, ta gareka kuma. Ka gode masa saboda ikonsa da ke gudana a cikin ka . Sai ka rufe addu’ar ka da murna da shaidar godiya. Duk sawon wannan lokaci, ka mori wahayi.

15

Gwada Ruhohi da Littafi Mai Tsarki

Mun gane cewa duniyan Ruhu akan iya tauno ta ta wurin zurfafan bincike ne idan kuma an dauke ta da muhimmanci ba a matsayin kan magana kawai ba. Mu gane cewa mulkan sami damuwa da gane ya ake fahimtan wannan. Ko da shike, akwai wurin amfani da tunani domin gwada kowane ruhu. Gwada ruhohi da Littafi Mai Tsarki yana cikin daya daga abubuwan da zasu taimake mu kada mu yi kuskure, kuma, ko da shike kwakwalwanmu ba shine ke bayana mana wahayi ba (zuciyan mu ne), shine yake daukawa ya kuma gwada wahayi da Littafi domin ya tabattar da cewa daga Allah ne.

Akwai hanyoyi biyu da zaka iya amfani da kwakwalwan ka domin ka gwada wahayi da Littafi Mai Tsarki. Na daya shine, “To, ba a taba koya mani wannan ba ko kuwa in ganin daga cikin Littafi. Don haka, zai zama kuskure ne.” Dayan kuma shi ne ka nace cikin binciken littafi idan wani sabon abu ya taso maka domin ka gane ko akwai wasu misalan wannan cikin littafi. Na gane cewa ka da shike ban taba gani cikin littafi ba, yayin da na taba gamuwa da shi da kai na zan iya I koma littafi in binciko abubuwan da suke wurin kowane lokaci. Ko da shike ban iya ganinsu ba. Don haka, ka yi hankali domin ka yi amfani da kwakwalwanka da kyau yayin da kake amfani da shi domin ka gwada wahayin da ka samu. Za ka yi amfani da shi domin ka gwada yanayin ka da Littafi Mai Tsarki (ba sanin tauhidin ka ba), domin ka gani ko wasu cikin Bibul sun sami kansu cikin irin yanayin da ka same kanka. Yayin da kake gwadawa, sai ka dukufa aikin addu’a domin Ruhun wahayi yayin da kake binciken (Afi. 1:17,18). Na gaskanta da cewa mutane da dama suna amfani da kwakwalwansu inda bai kamata ba yayin da suke gwada wahayi. Sukan gwada da kanin tauhidi maimakon koyarswa da misalan Littafi Mai Tsarki. Musamman yawancin karatun tauhidin mu da ya kai shekaru 300 da ya ci gaba Kaman ya wuce. Da dama duk abin da nake koyarwa shi ne neman wani taimako na musamman.

Wani Kuskuren da mutane sukan yi cikin binciken Littafi shine suka karyata komai, maimako ganin cewa hakan ne. Ta haka sukan yi amfani da kalmomin yadda bai kamata ba, Kaman akulkin duka da bugun mutane, maimakon karfen da ke taimako da karfafawa.

Ana amfani da Littafi Mai Tsarki domin jimrewa da Karfafawa cikin bege (Rom. 15:4). Na yi amfani da Littafi Mai Tsarki yadda bai kamata ba cikin shekarun da suka wuce. Na tuba ina kuma koyarwa akan girma da ababan mamaki na Kristi mai rai cikin zuciyan mai bi mai kokari kebe dokokinsa. Allah ya ba Gal. 3:3 ya zama da muhimanci a gareni! “Da kuka fara da Ruhu, ashe yanzu kuma da halin mutuntaka za ku karasa? “Na kasa ta wurin karfafa mutane da su yi kokari da halin mutuntaka, a maimakon duban Kristi. San da na sha kan nawa kokarin na mutuntaka na kuma Koya zuwa wurin ikon Kristi kafin na iya ganin gaskiyan littafi. Ayoyin Littafi da dama sun yi ta zuwa ba ban taba ganewa ba a da.

ABUBUWAN DA KE DAMUN RUHUN KA

Idan kai Krista ne, Ruhun Allah na hade ba naka Ruhun (1 Kor. 6:17). Haka kuma, abubuwan da ke ba na Allah ba zasu iya su taba Ruhun ka. Wadannan an ambace su cikin ayoyin da ke biye. Ka duba ayoyin ka rubuta abubuwan da kan dame Ruhu a kowace wuri. Yanayin rayuwa (1 Sam. 1:1-15) Yanayin jiki (1 Sam. 30:12) shaidan (John 13:2) mutum (Karin Mag. 16:32)

Don haka, tunani, dabaru, da sauran su ba za su iya zuwa daga Ruhun Allah ba, amma daga wasu abubuwa. Ka gane yayin da wani abu banda na Allah yana damun Ruhun ka, ka kuma nemi alherin Allah domin ka yi nasara da shi.

Lokacin da tunani ka ya farara aikin tsabtace da kuma gwada tunani, zai zama.



  1. Yana neman bayanin ikon wasu Ruhohi bisa Ruhun Allah

  2. Ka tambaya, “menene amfanin tunanin? “(Tsakiyan zai zama da haske fiye da wajen.

  3. Duba ko kana karkashin ikon Allah ne lokacin da ka shiga tunanin. Biye ga wasu tambayoyi da za su iya taimakon ka tunani.

    • Ka mika kanka a matsayin hadaya mai rai?

    • An wanke ka daga rashi biyayyan ka?

    • An yi maka bayani da wadannan misalan

    • Ka mika kai tapka ga nufinsa?

    • Ka na son kai cikin bayaswanka da yabo?

    • Kana jira cikin hakuri da sa rai da idanun zuciyanka bisan sa?

Wadannan tambayoyin suna bayana abubuwan da Allah ya shimfida wa israilawa lokacin da suke zuwa gare shi ta hanyoyi shida na sandukin su kuma karfi saki cikin Tsarki mafi Tsarki. Wata hanya na tambayan wadannan tambayoyi shida zai zama, “Kana rayuwan sandukin nan?”


GWADAWA KO TUNANI DAGA KANKA NE, SHAIDAN KO ALLAH

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu gwada Ruhu, abin da ke ciki da wahayin domin mu san ko daga Allah yake, kwatancin da ke nana gaba zai fa dada bayanin karanta shi yanzu.

‘Ya’yan ruhaniya ta ciki Karin kauna ne, shiri, warkarwa da cika. Idan, maimakon haka, mun ga ba haka bane, sai ka janye jiran ruhun da kake yi sai ka sami taimako daga mashawarcin ruhaniya.
KANKA SHAIDAN ALLAH

Ka nemi tushen sa – ka gwada Ruhu (1 Yah. 4;1)


Haifaffe cikin tunani. Da sauri yana tunani. Tunani cikin mutum.

Yana da kawo Tunaninsa ba komai, zaman sai kuma cikin tunani

Shawarai banza? Tunani baya gina wa Hankalinka na kan

Yesu?
Ka Karance abin da ke ciki – Ka gwada kalmomin (1Yah 4:5)


Sa abubuwan da Banzan tunani, baya ginawa, bada umurni, ginawa,


Na koya. Ban tsoro, tuhuma, ketare ta’azantarwa Tunani

Maganan Allah. Tunani na yarda da gwaji

Na tsoron gwadawa

Ka duba ‘ya’yan – Ka gwada ‘ya’yan (Matt. 5:15, 16).


Ababan Tsoro, dolanta, dauri, Bangaskiya mai sauri


Rikicewa, kari, kwanciyan

Hankali ‘yaya

Masu kyau, ganewa

Ilimi.


SANIN ALAMU

Ya zama da muhimmanci ka san ka kuma karane Littafi Mai tsarki domin ka sami ma’auni mai kyau, domin gwada ruhohi. Littafi Mai Tsarki shine ma’auni na gaskiya mara chanzawa, na gaba daya, mara faduwa. Kaman yadda muke koya rarrafe kafin mu yi tafiya, haka kuma kafin ka fara tafiya cikin tunani, ka san alamun. Ya kamata, a Kalla, ka sami ganewa akan sabon alkawari kana kuma aiki akan sauran littafi gada daya idan kana so ka gane tunani da Kyau. In ba haka ba, za ka bada kanka ga yaudara cikin sauki.



BADA KAI GA WATA KUNGIYA

Allah ya hada mu, mu kuma tare jikin Kristi ne. Mukan sani tsaro cikin dangantakanmu a taruwan wadanda suka gaskanta Littafi. Dukan tunani wanda ke kumshe da shawarwari sai a bada shi ba shugaban Ruhohi. Afisawa 5:21 ya ce, ‘Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu, “Ya kuma ci gaba da barraba wurarren da Allah ya mamaye cikin rayuwanmu. Kowa ya shimfida tunanin sa gaban cikan Allah, wanda ke bada tsaro daga kasawanmu na mu yi wani abu wanda ke ba nufin Allah ba. “Al’umunar da bata da masu ja mata gora, za ta fadi. Yawan mashawartan Ikkilisiya, wadanda kuma ke cikin zumuntan su su bayyana masu tunaninsu domin su amince ko su gyarta. (Ibran. 13:17). A cikin zamanin rashin doka, doka ce za ta zama halin mutanen Allah. Ga wa kake bada Kai?




Wadannan

Su yi biyayya ga

Wadannan

‘Ya’ya

Mata


Maza

Dattawa


Bayi

Iyayengiji

Kowa

Mahukunta



Fit. 20:12; Kol. 3:20

Afi. 5:22-24

1 Bit. 5:1-5; 1 Tim. 5:17; Ibran. 13:17

A.M. 14:23; Afi. 5:21

Afi. 6:5-8 1 Bit 2:18-23

Afi. 6:9


Rom. 13:1-7; 1 Bit. 2:13-15

Dan. 2:20, 21;

Karin Mag. 21:1


Iyaye

Maza


Dattawa

Wa kima cikin Kristi

Iyayengiji

Allah


Mahukunta
Allah



GANE KA’IDODIN MAHUKUNTA

Domin ka yi zaman lafiya ka Kuma kiyayye dokoki cikin rayuwanka, dole ka gane wasu abubuwa.




  1. Allah ne ke nada mahukunta bisa mu. (Rom 13:1- “Goma ba wani iko sai da yarda Allah, mahukuntan da ke nan kuwa nadin Allah ne. “Zab. 75:6,7 – “Hukunci ba daga gabas ko yamma ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba. Allah yake yin shari’a, yana kaskantar da wasu, ya kuma daukaka wadansu.”)




  1. Allah ya fi kowane hukuma. Domin haka, ka sami Karfi cikin aikin Allah ta wurin hukuma. (Karin mag. 21:1 – Ubangiji ne ke mallakar tunanin tsarki a sowake kamar yadda yake da ruwan rafi; yaka yi da shi yadda yake so”)




  1. Ka nemi abin da ya sa Allah da daura hukuman bisan ka.




  1. Hali mawuyaci da kake shiga da hukuma da ke bisan ka yana nuna shhirin Allah cikin rayuwarka.




  1. Ka yi addua wa Allah domin ya yi aiki ta wurin hukuman (1 Tim. 2:1-4). Addu’oin mu za su nuna wani irin hukumane za su yi iko bisan mu




  1. Ka gane cewa ta wurin addua za ka birbishin sarauta su zama karkashin ikon ka (Afi. 1:20-22; 2:6). Don haka ka yi addua wa Allah domin ya jagorance zucciyanka. Ka kuma yi biyayya da dukkan dokokin littafi game da yanayin. Sai cikin murna ka yi na’am da hukumcin cewa daga Allah yake (1 Bit. 4:12-14).




  1. Abu da ya zama dabam ga biyayya da hukuma shine idan ya umurce ka da ka yi abin da ya saba wa dokan Allah na Littafi (Dan. 6; A:M. 4:19,20).




  1. Nassara ka zo ne ta wurin ganewa cewa Allah ke aiki ta wurin hukuman da ya daura bisa mu, yin tsayyaya da mukuma ya yi wa umurnin Allah ke nan. (Rom. 13:2 – “Saboda haka duk wanda ya yi wa ma hubumta tsayayya, ya yi wa umurnin Allah ke nan, masu yin tsayayyan nan kuwa za a yi musu hukumci.)

Wanda ke rayuwa cikin wannan tunani sai ya san ko ma wa yake biyayya ya kuma ajiye dukan shirye-shiryensa gaba shi. Wanda ya ki yin haka cikin girman kai da kuma “Allah zari iya yi da kaina “zai kuwa fadi ya hallaka.


Idan akwai wata zarafin da baka yi wata shirin na ruhu ba a cikin rayuwan ka kaman yadda aja umurce ka a babi na daya, ka gane cikin zuciyanka da tunaninka wanda Allah ya daura kanka. Sai ka je wurinsa ka nemi yardansa na biyayya da tunaninka gareshi.
MATAKAN DA ZA KA DAUKA IDAN KA YI TSAYAYYA DA MAHUKUNTA

Yayin da kuke tsayayya da mahukuntan Ruhaniya, bai kamata ka amsa Kaman mara hankali, mara kuma ruhu. Akwai matakan da suka dace.




  1. Ka tabbatta halin ka yana cikin kauna. Kada ka bar wata hali na tuhuma, mara tsarki da na taurarewa aikin zuciyanka (dan. 1:9)

  2. Ka tabatta halin ka na cikin hanya, ka gyarta halin ka mara kyau, ka kuma nemi gafara da tuba (Dan. 9:20). Ka ajiye naka abin da kake so domin na wande ke bisan ka.




  1. Ka san abin da wanda ke bisan ka ke so. Yana neman cigaban ka ne? menene abin son shi? (Dan. 1:10)




  1. Da wadannan abubuwan, ka nemi wata hanya da zata gamshe dukanku. (Dan 1:8)




  1. Banda zarginsa ka bayana masa wadannan matakan cikin roko. Kana bayana mashi yadda zai taimake shi ka bar shi ya yi tunani akai (Dan. 1:12, 3).




  1. Ka ba Allah lokaci ya sake tunaninsa (Dan 1:16). Ka san da cewa Allah zai sa Karfi gunsa; domin haka watakila shina ya sa karfi wurinka; haka kuma Allah ya yi amfani da wannan domin ya gina ka cikin saninsa. Ta yi kokari ka amsa cikin kauna da adalci.




  1. A karshe, wani lokaci, za ka iya wahala ko ba ka yi wani abu da ba daidai ba (Dan. 6:12-16). Allah ne karfinka



SAKE HUKUMA A RAYUWANKA

Akwai yakatan da zaka sami kanka cikin halin sake hukuma a rayuwanka; yayin da ka matsa, canza aiki, canza Ikkilisiya, aure, da sauransu. Duk lokacin da canji zai shigo ka tabbata ka yi duk abin da zaka iya domin ya zama da sauki ba tangarda.

In mai yiwu wa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa (Rom. 12:18)

Idan akwai domuwa cikin dangantakan ku, ka yi amfani da matakan da aka bayyana a bisa. Tai zama da muhimanci a zo ga shiri sakamin ka da muhukumta game da canjin da zai zo. Koda shike sau da dama ba haka yake ba.


Abu mafi muhimanci yayin da Kake barin wani dangantaka zuwa wani shine ka kasance, ka kuma kafu cikin jikin Kristi, a karkashi marafin kariya. Makiyayinka ya zama keman kariya mai kawo lafiya yana kuma kare ka yayin da kake lafiya cikin rayuwa.
Ya zama dole ka aikata daidodin mulki “ta wurin wahayin Ruhu cikin rayuwa. Don haka muna rokon ka da ka yi addu’a yayin da kake aiwata wadannan kaidodin, ta wurin hikimar Ruhu Kristi.
Bari “doka” ta zama wa’adin Ikklisiya cikin zamanin ‘rashin bin doka”
Yüklə 71,33 Kb.

Dostları ilə paylaş:




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin